SARAN BOYE 43
No. 43
............Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba
ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba. A hankali ta saki wani irin
nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan
hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da
masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na
wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani
lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a
hankali cikin kunnen nata.
Ihun Nu'aymah duk sai da ya
shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na
tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa
ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta
faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin
aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a
haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta
ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi.
Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai
hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka
ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba.
Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar
ajiyar zuciya.
Shirun da su baba malam sukaji
babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai
lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin,
“Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
Kusan a tare duk suka murmusa.
Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi
kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi.
Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a
bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon.
Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a
hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take
murmushinsa ya sake faɗaɗa.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali
tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga
Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi
zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”.
Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu'aymah a kujerar
da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana
bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka,
saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
Ƴar dariya Ahmad yayi yana
ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A'a Doctor
karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah
jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara
zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar
bindiga ɗin? Tab za'aga likitoci kam”.
Da haka suka fito Ahmad na
dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar
ba.
Kusan duk a tare su Abbah ke
tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta
tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
Duk kallon Yoohan sukai cike da farin
ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin,
“Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba
dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya
birkita ta, ruɗanin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu
bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
“Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya
saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
A tare suka amsa da amin, harsu hajjo
da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.
A cikin gida kuwa dai
hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai
shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar
musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
Bayan wucewar Yoohan duk suka
shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan
haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa
akan auren na Aymah.
Koda suka koma can baba malam da
kansa ya ɗauki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa.
Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar
magriba.
Biki yayi biki masha
ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama
sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga
abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana
idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah
dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan.
Kamar yanda kowa ya sani baba malam
shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda
yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan
amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar
da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai
amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin
lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka
taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take,
Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da
gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito
dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai
baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren
Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar
ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a
ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban
Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai
Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne.
Haka suka fita a jere ana bin amare da
addu'ar tafiya a sa'a. Dama mafi yawan ƴan biki na kusa duk sunata guduwa suma.
Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun
tafi.
★★★
Su baba malam sun fara miƙa
Hajarah ne dan itace ƙarama. Gidanta mai ƙyau da tsari a anguwar GRA, kowa ya
yaba da addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa
daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan
Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ɗin suma cikinsu harda maza uku.
Bayan sun ɗan zauna a falo akai addu'a baba malam ya kama hannun Hajarah har
cikin Bedroom ɗinta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu'a da
saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta riƙe hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa
jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa
har ƴayan ƴan uwan nasa ƙaunarsu yake har cikin ɓargonsa. Duk kuma sanda yay
irin wannan rakkiyar sai yayi ƙwalla dajin ɗacin rabuwa da yaran nasu ta dalilin
aure ƙanin mutuwa.
Hajarah data buɗe fuskarta ta share
hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, “Abbah dan ALLAH
inason in roƙeka wani abu”. Kansa ya jinjina mata, yace, “Komi kikeso zan miki
inhar baifi ƙarfina ba Hajarah, dan haka faɗamin koma miye kinji”. Sake share
hawayenta tayi tana jinjina masa kai. “Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace
bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa”. Jimmm baba malam yay
yana kallonta. Sai kuma yace, “Uhm Hajarah miyasa kika buƙaci hakan? Bayan
kinsan shi ɗin mai laifine”. “Abbah zan faɗa maka dalilina amma ba yanzu ba,
dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na roƙesu har
Hajjo”.
Numfashi baba malam ya ɗan sauke,
sai kuma yace, “Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki
zazzaɓi. ALLAH ya baku zaman lafiya”.
Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da
rabzar kukanta.
Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama
dai gidan ya haɗu masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta
uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da
mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ɗakin ya ƙara mata addu'a sannan
ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.
____________________
A ɓangaren Yoohan
kam tunda suka baro gidan su baba malam sai ya koma Hotel ɗin da su papa suka
yada zango. Babu yanda baba malam baiyiba akan su sauka a ɗaya daga cikin
gidajen baƙinsu amma papa ya ƙi fir. Wajen ɗaurin aurenma da yake jirgin 12
suka shigo suna isowa ana idar da sallar juma'a, hakan yasa saida ma aka ɗan
jirasu kafin su iso wajen ɗaurin auren daga airport. Yoohan ne kawai yazo tun
goma na safe. Bayan an ɗaura auren aka ɗunguma har dasu hall ɗin da su baba
malam ɗin suka tanada domin gudanar da walimar cin abinci. Anan akaci aka sha
cike da farin ciki. Babu wanda zai kalli baba malam da papa yace akwai wani abu
na rashin jituwa a tsakaninsu. Suma su papan sun sake sosai a cikin mutane
bazaka taɓa cewa ga daga addini ko ƙabilar da suka fito ba. Musamman ma daya
kasance a cikin manyan mutanen ƴan ɗaurin aure akwai waɗanda suke da alaƙa dasu
sosai musamman ma ƴan siyasa. Wasuma papan ya sake gayyatarsu bayan gayyatar da
baba malam yay musu.
Bayan an kammala walimar ne mafi yawan
baƙin suka kama gabansu, su kuma su papa da tawagarsa suka nufi hotel bayan
sunƙi amsa tayin baba malam. Hakan yasa yanzun acan Yoohan ya iskosu. Sai dai
kasancewar jirgin ƙarfe bakwai da rabi zasu bi zuwa Abuja duk ya iskesu sun
fito shi ma suke jira. Basu wani zauna zaman ɓata lokaci ba duk suka shiga
motocinsu. zasu kaisu airport ɗinne su dawo su kwana da safe suma su ɗauki
hanya. Dama da safe suka taho kafin su papan.
Ko mintuna goma cikakku
basuyi da zuwa airport ba jirginsu ya lula birnin tarayya abuja. Inda a canma
dai ɗaukarsu akazo akayi. Abokan papa kowa ya nufi gidansa, papa da Gebrail,
Richard, Joseph, Godwin, Osin, Uncle Marcel, Uncle Anthony, kuma suka nufi
gidan papan. Sai Solomon jelar Yoohan😂.
Sun iske gidan a hargitse da rikicin da
suka bari su Mama Debora nayi akan auren Yoohan ɗin. Faɗa mai lasisi sosai
akasha tsakanin tsofin biyu. Kuma duk akan sufa basu yarda jikansu ya aure
bahaushiya mai salla ba. Momy da papa ya gama sanar mata komai akan manufar
auren tanata ƙoƙarin fahimtar da su duk da kuwa jitake kamar tafi kowa shiga
tashin hankali, amma sun ƙi fahimta. Sai kiran dangi suke na nesa a waya suna
sanar musu. Miracle kam yanke jiki tayi ta faɗi a sume dama tunkan su Yoohan su
wuce. Akace kuma ya dubata ya tsallake yay ficewarsa batare daya ko tanka musu
ba.
Hakan daya aikatane ya sake fusata kakanninsa
sabon wutar bala'i ya ƙara ruruwa. Sai asibiti aka kai mira bayan wucewarsu ɗaurin
auren.
Tunda Yoohan ya shigo idonsa ya
sauka akan kakannin nasa sai ya sake tsuke fuska fiye da yanda take. Ɗauke
kansa yayi ya nufi upstairs duk da yaga yanda suka miƙe zumbur suna kallonsa
cike da wutar masifa.
Cikin yare, mama Debora ta shiga ƙwala
masa uban kira kai kace gidan zata fasa. Ko waiwayensu baiyiba ya buɗe ƙofarsa
ya shige bayan ya amshi babbar rigarsa a hannun Solomon dake biye da shi a
tsorace. Ruf ya rufe ƙofar ya murza mata key yama barshi a ciki dan kar wani
yay tunanin amfani da wani key ɗin.
A falo ya zube yana sauke
numfashi da jan dogon tsaki. Jin an fara buga ƙofar tasa da ƙarfi ana masifa ya
kuma jan wani tsakin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Bai zaunaba anan, kayansa
dake ta zuba ƙamshinsa dana Nu'aymah ya cire yanata faman lumshe idanu. Dan a
matuƙar gajiye yake. Babu abinda yake buƙata a yanzu sama da kwanciya. Ya gaji
harma baisan tataya zai faɗa ba a tausaya masa. Ga ihun su Mama debora da yake
jiyowa sama-sama yana neman saka masa ciwon kai. ‘Nasan maganinku ai. Kwanan
nan zaku bar gidan nan ku koma inda kuka fito’. Ya faɗa a fili yana harar ƙofar
kamar sune wajen tsaye.
Daga haka ya shiga yay wankansa
kamar yanda ya saba. Ya jima bai fitoba daga bayin kamar mai naƙuda🙄😏.
Sai kuma gashi ya fito a yanayin gajiyar da yake ciki. Sama-sama yay shirin
barci cikin tausasan kayan barci, yana fesa turare wayarsa tai ring. Kallon
wayar yay, ganin Richard ne sai ya basar ya cigaba da hidimarsa. Sai da Rich ya
sake kira bayan ta katse sannan ya ɗaga. A dakile yace, “Kana damuna fa”. A
fusace daga can shima Richard yace, “An damekan, shine dan tsabar wulaƙanci ka
wani kullema mutane ɗaki? Da ace babu wasu ɗakunan ina kake tunanin zamuje mu
kwanta?”.
“Oho muku” Ya faɗa a taƙaice da yare.
“Zakace oho kuwa tunda mun gama maka
wahala, mtsoww! Ka wani saka mutane zuwa cikin.....” Katse wayar Yoohan yayi
batare da ya bari Richard ya ƙarasa ba. Ya taɓe bakinsa yana cilla wayar saman
gado. Yanaji Rich ya sake kira bai kulaba. Sai da ya kammala shirinsa tsaf yay
sallar magriba da isha'i da shafa'i da wutiri da addu'oinsa sannan ya mike ya
haye gadon. Wayarsa daya cillar gefe ya ɗauka. Number baba malam ya lalubo yay
dailing. Ring uku kuwa ya ɗaga.
Tamkar Yoohan yana gabansa haka ya
risina cikin girmamawa yana gaishesa. Daga can kuwa baba malam na amsa masa da
kulawa.
“Abba mun iso babu jumawa. Ina fatan
jikin nata babu wani matsala zuwa yanzun?”.
Murmushi baba malam yayi da duban
Nu'aymah da Umm ta gama canjama kaya zuwa na barci. Ya ɗauke kansa yana sauke
numfashi. “Alhmdllh Yahya. ALLAH ya huta gajiya, ya kuma saka albarka. Dama
yanzun nan muka gama waya da baban naka shima ya kira ya sanarmin isar taku.
Mamana kuwa har yanzu barci ma take batako farkaba tun bayan allurar”.
Sassanyan murmushi Yoohan yayi
babu shiri, yace, “Alhmdllh Uncle, insha ALLAH zuwa da safe zata farka normal, ALLAH
ya ƙara lafiya. Bara na barka ka kwanta sai da safe”.
“To Yahya ALLAH ya huta gajiya”.
Daga haka sukai sallama. Baya yay ya kwanta
ƙafafunsa a ƙasa yay filo da hannayensa. Idanunsa ya lumshe a hankali ya faɗa
duniyar tunanin da shi kaɗai yasan akan abinda yake yi.
__________★★★★_________
*_To masu karatu
sace shin ina Abdallah da Nasir😱🤗?._*
Tam nima dai tsayawar wannan
tambayar a raina ce taja ra'ayina shiga bulayin nemansu a cikin gidansu
Nu'aymah. Sai dai na karaɗe ko ina da ina tsaf babusu babu mai kama da su ɗin.
Sai acan bakin su Omar dana tsinkayi yana faɗama Momynsu yanda ɗaurin auren ya
kasance naji.
Ashe faɗan da Abdallah da
Naser suka tafka ne a daren shekaran jiya daya bama kowa tsoro yajawo su baba
malam canja shawara akan zaɓin Nu'aymah. Ananah da hajjo sukai dogon nazari da
shawarar canja komai. Dan yanda abubuwan ke nan canja salo tabbas zumincinsu
zai iya girgiza akan matsalar Naseer da Abdallah. Dan haka suka kira su baba
malam a wannan daren tare da Abban Naseer daya iso suka tattauna. Abban Nasir
shine ya bada shawarar hana Abdallah da Nasir gaba ɗaya. Ya kuma bada shawarar
aurama Yoohan kamar yanda ya bukata dan a samu zaman lafiya. Hakan zai kawo
masalahar Abdallah ya maida matansa. Nasir kuma yaje ya auri wata.
Kowa yayi na'am da wannan tunani na
Abban Naser. Babu ɓata lokaci ko jinkiri suka kira Yoohan suka sanar masa.
Yoohan kuma bai ɓata lokaci ba wajen sanarma papa. Sai dai yayi matuƙar mamakin
ganin yanda Papa ya bashi goyon baya babu wani ja inja ko ƙalubalantar lamarin,
ya kuma gargaɗesa karya sanarma Momynsa (Madam Chioma😸) shi zai sanar
mata.
A wannan daren papa ya bada akai
masa invitation na layin waya aka turama duk wanda yake da buƙatar gani a wajen
ɗaurin auren ɗan nasa. Washe gari kuma ya ƙarasa dukan kai kawo da yake buƙata
tare da bincikar duk yanda al'adar auren hausawa yake. Duk abinda ake buƙata
sai da papa ya saya aka shiryasu a mota.
Anan kuwa kano su Abdallah basusan wace
wainar ake toyawa ba. Kowannensu dai ya ɗauki alwashi akan ɗan uwansa tsakanin
shi da Nasir. Hakan yasa sukaje ɗaurin auren kamar kowa cikin kwalliya ta
musamman. Sai dai kuma ganin Yoohan da tawagar ƴan uwansa da abokai ya basu
matuƙar mamaki. Gashi waje ya ƙure balle su tambayi iyayen nasu. Basu fita daga
ruɗanin ganin Yoohan ba aka fara ɗaurin auren. An fara ɗaura na Kubrah da
angonta Al-ameen yuseef durɓi, sai Hajarah da angonta Dawood Sulaiman Rano.
Naseer na jiran yaji shi da Nu'aymah sai yaji Zainab Sooraj Hashim jibiya da
Yahya Goshpower”.
Turƙashi zance ya girma. Ba Nasir
kawaiba ne a ruɗani, Abdallah kansa hajijiya yaji tana ɗibarsa. Hakan yasa Omar
dake kusa da shi ya taimaka masa suka fito daga cikin hayaniyar ya kaisa mota.
Shima acan Nasir sai Ahmad ne ya kamashi ya fito da shi. Sun koma sanarma su
baba malam, Abdallah ya tada motar da Omar ya sakashi ciki ya bar wajen batare
da kowa ya sani ba. Nasir kam da ƙafa ya bar wajen shima a birkice.
Daga wannan tafiyar ne har yanzu
babu wanda yasan ina suke. Su baba malam sunyi neman a waya harsun gaji. Dan
duk wayoyinsu a kashe suke. Halin da suka ahigo suka iske Nu'aymah a gidane ya
sakasu yin shiru da zancen rashin su Abdallah ga kowa. Duk da kuwa Hajjo nata
tambayarsu bataga Abdallah da Nasir ba.

No comments