MIN QALB 43
Daqyar Amatu ta iya daga hannu takai wuyanta tana Dan sosawa akunyace zuwa kanta sai alokacin taji gashin kanta azube Kan kafadunta Wanda kallo daya zakamai kasan a jiqe yake duk da bawai tsiyayar ruwa yakeyiba,
Tayi saurin kallon anty zarah da itama sai alokacin ta
lurada sanyin kan Amatun take ruwan bakinta suka qwareta tafara tarin dayasa
Amatu Jan akwatinan tabar gurin da sauri tana sakejin kunya da takaicin kanta
da fitowa ahaka Amma Kuma batai tunanin ganin anty zarah a palon ba adaidai
lokacin ita gabaki dayama ta manta da itada antyn tatace keda MAHMOUD din.
Zama tayi bakin gado tana Dan shafa goshinta cikin yanayin
datakejin kanta da zuciyarta akan MAHMOUD ZABEERA,
Wani boyayyan murmushi tasaki ita kadai tana rintse
idanuwanta tana Jin kowace irin kalmar daya fada Mata a Daren yau din suna zagaya
jini da jikinta,
Idan har samun kalmomin yabawa daga garesa ya sanyata cikin
wannan daddadan yanayin to Yaya anty zarah daya Dade Yana furtawa kalmarso
takeji ita....
Faduwa gabanta yayi da qarfi harsaida ta Dora hanunta Kan
qirjinta ahankali tana lumshe ido
tunanin yanda zasu riqa sharing dinsa na sata Shiga wani rububi tsawon mintuna
Jin zuciyarta na neman tarwatsewa yasata miqewa ta nufi toilet tashige ta
sakarwa kanta ruwa tana rufe idanuwanta.
Anty zarah ma daddafawa tayi takai kanta daki tana Jin
zuciyarta na radadin mema yakaita biyo MD Nan tun farko sbd duk wannan abin
tasan Dole Yana faruwa tsakaninsu tunda zaman aure suke Amma to ganewa idonta
shine babbar masifar gashi tazo ta zauna tana ganin Abinda zai iya Sanya
zuciyarta fashewa wlh badan zata koma Santorini ganin likita harso biyuba da
ayau saita koma Nigeria Dan tafi ganin darajar kanta Dana aurenta acan Dan ko
shi mijin acan yafi ganin girma da darajarta sbd anan tazama kamar baquwar data
kawowa matar gidan cikas ne Amma ko ahaka Dole tana buqatar fita Tasha iska sbd
acikin gidan yau numfashinta sassarqewa yakeyi.
Wanka tayi ta shirya tafito ko qofar dakin Amatu kasa kalla
tayi sbd kada taci gaba dajin zafinta Sam Bata iya tsanar Amatun duk da mijinta
data aure Mata Koda yake ummantace koyaushe akan taimaka Mata da addua da
shawarwari da nuna Mata kulawa akan kada ta dauki zafin kishi me tsanani da
hauka tazo qarshe tayi biyu Babu sbd dangi da mijin zasu tsaneta idanma tasamu
anbarta da igiyar auren kenan shiyasa itama take iya qoqarinta sbd sanyawa
ranta salama duk da akwai zafi da ciwon kishi me tsanani saitana duba wani
lokacin ko ba kishiya ya kaqare da baqin ciki da takaicin namiji Wanda
sometimes ma kishiyar is just an excuse dakake sauke haushi da laifin akanta
Amma mijin ne me asalin baqin cikin wani lokutan.
Text tayiwa MAHMOUD din na tafita zuwa gida momy professor,
Bata tsaya jiran reply dinsa ba ballantana tasan ba lallai
yayo reply dinba musamman yanxu datake zargin da wuya idan wayarsa Bata kashe
ta ficewarta.
Shine yafito da wayarsa Kan kunnensa Yana amsa waya cikin
nutsuwa da wani irin izzar dake qarawa kwarjininsa cikawa mutane ido,
Dogon wandon Lou's ne fari qal ajikinsa sai sky blue
transparent shirt Mara nauyi ko kadan data bayyana jikinsa sosai ya nufi dining
yaga bakomai ya juyo ya nufo hanyar bedroom din Amatun ya tura yashiga Kai
tsaye.
Tsaye take gaban madubi sanyeda bra Fara qal sai towel dake
daure iya qugunta tana shafa body mist ajikinta ta dago Kai ta kalli cikin
madubin taga shine yashigowa ya tura qofar ta qura Masa Ido ta cikin madubin
har batasan lokacinda ya qaraso bayanta ba sai saukar hannuwansa Kan shafaffen
cikin tayi numfashinta yayi sama tayi saurin dora hannunta akan nasa din tana
dafewa ta kallesa ta cikin madubin tana girgiza Masa Kai a kasalance tace"
Anty zarah na Palo kashigo Kan??
Share tambayarta yayi Yana kallon white pushup bra dinta
yakai hannu akai Yana tabawa yace"
I love white colours.
Inda hannunsa ke yawa ta kalla tareda sake zamewa zata Kira
Masa sunan anty zarah ya Dora hannunsa Kan bakinta tareda waiwayawa ya kalli
wardrobe dinta yaja hannunta zuwa bakin wardrobe din yace ta bude.
Saidata kalli idanuwansa dake kallonta ta saki murmushin
dake bayyanarda farin cikin da zuciyarta ke ciki ta bude wardrobe din still
tana kallonsa cikin dinbin mamaki da farin cikin data rasa Kona meyene.
Wasu Kaya ya nuna Mata batareda shima yasan ko wainne iri
bane ya nuna
Ta janyosu tana Masa kallon mamaki saidai tunda ya zabesu
itakuwa sanyasu zatayi duk da tasan anty zarah na gidan Amma dai zata Sanya
saidai zata kaucewa ganinta.
Riga da mini skirt ne skirt din blue rigar white,
Toilet tashiga ta sanyo ta fito tanason taji kunya Amma
yanayin rayuwarta ta yanzu da yanda ta Saba da rayuwar turawan yahana taji
kunyar yanda yakamata.
Daure kanta tayi da band baqi ta nufi hanyar fita dakin tana
cewa''
Zanje na hada breakfast.
Riqota yayi yadawo da ita gabansa Yana kallon fararen
cinyoyinta dake tafiya suna daukar hankalinsa zuwa cibiyarta dake fili rigar
Bata rufe ba ya maida kallonsa Kan wuyanta zuwa Rabin qirjinta dasuma suke a
bayyane ya maida kallonsa Kan lips dinta
data shafawa hot red lipstick suka zauna daram ba inda ya durje yakai bakinsa
ahankali ya shanye jambakin tsaf kafin ya janye band dinda ta daure Kai dashi
Yana cewa''
Yafi kyau ahaka.
Da wani sabon mamakin ta kallesa tana murmushin mamakinsa ta
zame hannuwansa ahankali tana cewa''
Muje kaduna idan anty zarah tana Palo.
Wucewa gaba yayi Yana cewa''
Ta fita Batanan Ina buqatan abinci am going out too.
Tea da fried eggs sai toasted bread kawai tayi musu sukaci.
Baifitanba sai maraice Yana fita Takoma tasake wanka ta
sanya doguwar fitted grown ta kanti ta rufe kanta da hula bayan tayi drying
dinsa tazo kicin ta Dora abincin dinner.
Tana cikin aikin anty zarah tadawo tana bude Mata guda suka
sakarwa juna murmushin daya zama Dole sukayo ciki tana cewa''
Anty zarah sannu da dawowa Ashe fita Kikai bansaniba Saida
dady yace bakyanan.
Idan Amatu na kiransa da dady tanajin abin har ranta Amma
tasan badan Dadi aure yasa take kiransa dadynba sbd Muhammad ne ya saki
numfashi tana nufar dakinta tace"
Wlh gajiya nayi da zaman shiyasa nafita nadan Sha iska gashi
Kuma wlh naji dadin fitar.
Daki tashige tayi wanka ta sauyo Zuwa doguwar riga itama
tafito tazo kicin din tana cewa''
Bari natayaki fira koban tayaki aikin ba Naga dare yayi
kinje makaranta ne?
Aa banje ba wlh baccin yamma nayi shiyasama nayi lattin
aikin.
Boye Mata cewan sai yammar MAHMOUD yafita tayi sbd gujewa
bacin Rai da damuwa ta fake da cewar baccin yamma tayi.
Sai Bayan duhun magriba suka kammala Amatu ce ta jera
abincin a dining kafin itama ta nufi bedroom dinta tayi sallah Bata sake wani
wanka ba sbd ba wani jigatar dasukai a aikin tabari sai idan zata kwanta tayi
wani.
Baidawoba sai dare sosai shiyasa Basu wani jirasa ba sukaci
abincin su tana waya da USI harta bashi anty ZARAn suka gaisa Yana qara yimata
godiya akan yanda ta fahimci auren Amatun da MAHMOUD tace Masa ba komai dai
Amma har yanzu tunda akai auren haryanxu takasa zama tayi tunanin irin daukar
dazatayiwa Amatun Wanda take ganin kamar ba yanzu ne lokacin dazata zauna yin
wannan tunanin ba Kuma tana riqon Allah dakuma fatar kada tasamu wannan lokacin
har abada sbd tana zama shaidan ne zai zauna shawarar da ita.
Tashi tayi ta shigewarta bayan tayiwa Amatun Saida safe
itama Amatun miqewa tayi tattara dining din tasake jera Masa nashi abincin tana
gamawa Yana shigowa a gajiya Dan haka Kai tsaye daki yanufa Yana cewa takai
Masa abincin can wanka zai shiga.
Kadan ta dibar Masa tareda fruits data San yanason sha yawanci
da daddare takai Masa tareda ruwa power drink dinsa
Tana zaune yagama ci ta kwashe kayan ta fita dasu ta sake
gyarawa tareda fesa Masa peach blossom airfresh ta qara Masa sanyin AC kafin
tashiga wanka anan dakin nasa qarshema shirt dinsa Fara tasanya wadda Tai mata
yawa ta kwana da ita.
Washe gari tanada zuwa makaranta daqyar ta tashi ta shirya
ko aikin abinci bata iya yiba hakanan suka fita bataci komaiba driving dinma
cemasa tayi bazata iyaba very weak take jinta shiyasa yakaita da kansa Bayan
yakaita wani private restaurant din dayafi so taci abinci kafin ya jiyeta
makarantar yadawo gida.
Kamra Wasa da zazzabi ta yini ko makarantar da qyar ta
lallabo tadawo gida tashige ko abinci Bata fito ci ba tace ta qoshi sbd kada
abin yayi Mata yawa Dan tasan yau anty zarah ce zata Kwana gunsa.
Annushuwar da zarah take ciki bayason Bata Mata ita Dan haka
bai nemi Amatun ba yadai Yi Mata text takuma yimasa reply.
Kwanan zarah biyu Amatu ta karbi girkin ta ringa Jin wani
iri kamar bazata iya wannan rotating din ba shima daya lura da ita gudun tashin
hankalinta da rigimarta yasa yaqi nuna yagane tana cikin damuwa.
Sannu ahankali yafara sabawa da canjen kwanan har tsawon
wata daya ana haka saiga anty zarah tafara rashin lafiyar ciwon baya da
zazzabin dare ga Amatu Kuma Kai yadauki zafi exams sukeyi Bata cika zamaba
shima MAHMOUD din bai cika zamaba ga ciwo kadan kadan Yana cin anty zarah din
basuda masaniya.
Ranar wata talata tadawo daga makaranta ta tararda anty
zarah Bata Nan sai Bata damuba harsai dataga dare yayi sosai Bata dawoba takira
wayarta Bata daga ba harso uku sai hankalinta ya tashi takira MAHMOUD din Yana
dauka ko gaisuwa bata tsaya Masa ba tace"
Dady anty zarah fa Bata gida inata kiranta wayan ba'a
dauka..
Numfashi ya sauke Kai tsaye yace"
Tana taredani muna Santorini batada lafiya.
Santorini?" Tafada cikeda mamaki tana qarawa da cewa''
Yaushe kadawo ne dahar kuka tafi yau din?
I came back because you're too careless ta Yaya Kuna tareda
mutum Yana fama da rashin lafiya haka sosai Amma kice baki sani ba this is
unbelievable...
Tayaya zangane tunda Bata fadaminba Kuma kullum ni lafiya
nake ganinta Kuma karka manta ni makaranta nake zuwa tayaya kake....
Kashe wayar yayi Yana cewa''
Idan nagama Abinda yakawoni I will call you back.
Wayar tabi da kallo zuciyarta natafarfasa dama kwanakin
kullum zuciyarta a kusa take batasan dalilina,
Take tadauki mugun zafi tana cewa ni zai datsewa waya cikin
wulaqantawa sbd nace bansan ciwon anty zarah dinba??
To uban kowa da kowama tace Bata saniba ayi Abinda za'ayi
din.
##mamuh#
Manage please.

No comments