Breaking News

A GIDA DAYA 45-46

 


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


      🌹A GIDA D'AYA🌹

            🏘️🏘️


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾




    Story & written by mmn fareesa




🅿️ 45&46




....... B'angaren Jamil kuwa"Koda akaje station basuyi mishi komaiba. sbd yamusu alk'awarin zai basu y'an canji"fargabansa

guda, cikin dake jikin  kharat! yatabbatar muddin ba'a cire cikin nan ba. da matsala sbd y'an k'ungiyarsu bbu Mai d'a .gamasu irin shekarunsa"inmutum yayi haihuwar farko Dole yabawa dodo jinin yaron...kasancewar (k'ungiyarsu d'aya dasu Alh mudi)

da wannan fargaban Jamil ya kwana"washe gari Abba yazo aka zuba mgn. sbd shima akwai wad'anda yasani a station d'in.dg karshe dai Saida sukaje kotu da Jamil".akayiwa Jamil bulala20"da tarar dubu100.sannan Dole yakula da khairat sbd cikinsa dake jikinta...iya nan  aka tsayar da maganar"Jamil kuwa saima yaji dad'i"da dodo zai Sha jinin y'a ko d'an da khairat zata Haifa nan gaba".ko banza Tasha wahalar rainon ciki da nak'uda .bayan nan tazo y'ar ko d'an  ya mutu"ko wannan bak'in cikin yatabbatar ya ishesu itada iyayenta dasuke bada goyan bayan abar cikin..


Fitowa Abba yyi dg station d'in"shima Jamil yafito sbd yakira driver d'in sa yazo yad'aukeshi.yayiwa Abba wani kallo Yana murmushi"kafin yace"zan kula da y'arka insha ALLAH!amma sai bayan inta haihu "zakuji wanene ni"alokacin zakuyi nadamar sanina da Kuma barin cikin jikinta...Yana fad'in hakan yajuya ya shige mota.

gaba d'aya maganganun Jamil sun saka Abba jin shakku da fargaba"amma sai wata zuciyar tace mishi"k'ila sbd yatsorataku yyi wannan burgar...da wannan tunanin Abba ya yakice maganar Jamil aransa"yashige mota yanufi gida..komai da komai yayiwa mama jummai bayani bayan dawowarshi"amma banda mugun furucin da Jamil yyi...khairat datayi tagumi tanata sauraronsu.mama rabi gaba d'aya takacewa komai..kuka sosai kharat tafashe dashi"idan ta tuna tazama bazawa "Kuma zata haifi d'a ko y'ar da ubansu bayasonsu.tab'e baki abba yyi yace"uwar kice ta d'oraki akan turban kwad'ayi !Kinga ga yadda hakan yazamar miki.inkun gyara ruwanku"akasin hakanma kuyashafa."dakin haihu zan karb'i abinda kika haifa"na rik'e Dan bazan barwa matsiyacin yaron nanba.sannan na had'aki aure da muhseen d'an abokina. da tuni yaso ya aureki kikace baki sonsa"dakisoshi da karki soshi  bedameni ba.aure bbu fashi $inkuwa kin bijeremun saidai ki nemi wani uban"Kuma itama uwar Taki ta nemi wani mijin..yana fad'in hakan yaja tsaki yabar musu parlourn.


*************

Duk iya binkicen da doctors sukayi akan su gano meke damun su alh mudi da alh Ayuba?akan basu gani"Amma basuga komaiba"sai ihu da sabbatu kawai sukeyi."dukda shi alh mudi yatabbatar da cewa Yaya mahmod ya warke"abin yadawo akansu kenan.kuma dodonsu yafad'a musu har abada bazasu warkeba.hakan yasa yasaki kukan bak'in ciki"musammun daya tuna bashida d'a ko y'a"haihuwarshi 1 Kuma yabawa dodo jinin y'ar tun tana jinjira"dg baya yazo yabada jinin uwar yarinyar"hakan yasa besake aureba.saidai yabi k'adangarun bariki...

       Amma k'ila ibbi yakula dasu su duka"ya ayyana aransa..sbd yasan ibbi zai kula da mahaifinsa..shimadai alh Ayuba surutai kawai yakeyi"hakan yasa aka musu alluran bacci"ibbi inbacin kuka Babu abinda yakeyi"fatansa mahaifin sa yasami lfy...gaba d'aya asibitin Yan jarida nata zarya sunason jin gskyar meke damun su alh mudi..ibbi kuwa haushi da bak'inciki yaji akan y'an jaridar"hakan yasa yadinga zage zage akan zai fed'e mutum da wuk'a ba'a komai... doctors ne suka bashi hakuri yakoma yazauna"duk abinda yadace ibbi ne ya biya"sai dare suka farka.kasancewar a room 1 aka ajiyesu..yaran alh mudi sune suka taimaka mishi yashiga bayi yaci abinci.yyinda ibbi shima yakula da mahaifin sa.sai bayan kowa yafita d'akin yarage dg ibbi sai alh Ayuba da alh mudi...


     Cikin bak'in ciki alh Ayuba yafara mgn kamar haka"mudi nayi nadamar saninka arayuwata.ina cikin rufin asirina kazo kanamun burgar kud'i"Wai business kakeyi kozan shiga.ashe business d'in Shan jinine"kakaini nashiga qungiyyarku.... subahanallahi dad mekake fad'a haka?cewar ibbi in a shock.


Alh mudi yakarb'e zancen da cewa" wannan ai zancen banzane.akanme zaka tonamana asiri agaban yaro haka .danace kashiga meyasa baka shiga ba?saiyanzun da aka sami matsala zaka ce haka...cikin fushi alh Ayuba yace"eh nace Allah ya isa tsakanina dakai"sbd natabbatar inba wani abu dg Allah ba har abada bazamu warkeba .sbd haka dodo yace mana.duk kuwa abinda yafad'a da wuya yak'i tabbata....cikin tashin hankali ibbi yace"dad dama dukiyarka ta Haram ce?naci nasha, nasaka sutura,nayi ilimi dukda haram dad????"alh Ayuba yace hmmm! kayi hakuri ibbi"karatunka badasu bane "sbd haka inaso kaje inda nasamar maka aiki. kaje kacigaba" tunda takardunka nada kyau.. natabbata komai na siyasa karbeshi zasuyi"sannan tunda munzama haka"natabbata dodo duk wasu kud'i daya bamu zasu koma takarda"arikice ibbi yace account naka duk kud'in ne?ah ah 500k ne a account nawa subana jini bane"kaje kaciresu sbd Kar ahad'a dasu"nasan har gidan damuke ciki karb'e wa za'a yi.alh mudi yace"lallai kacika matsiyaci Mai son kansa"aikuwa bazai yuyuba Dole d'anka yakula Dani"nima yafito mun danawa kud'in...tsaki ibbi yaja yace ai zunubinka yafi na dad"sbd Kaine kaja ra'ayinsa"sannan ni b'antab'a zaton kune kukayiwa mahmod Adam asiri ya makanceba.dukda alokacin bani lfy (sadda yasoyiwa zee fyade) amma dana dawo dg Egypt kunsanarmun ,harda cewa ya b'uya.duk iskancina banaso naci haramun"sannan yanzun Zan rufeku naje nadawo" Kai kuma Zan d'aure maka baki sbd bakada idon gani"balle kakira waya kasa arufe account d'in...alh mudi yace"Allah ya isa tsakanina dakai Ayuba ka cuceni"yafad'a Yana lalibe sbd son yagudu"ibbi yatad'e shi da k'afa yafad'i"kafin yajashi ya daure mishi baki da wani Abu...cikin damuwa yace"nanda 15 minit Zan je nadawo dad..bejira cewarsaba yafice..


Duka yaciro kud'in"yakoma gida yasanar wa mahaifiyar'sa "dama batason abinda alh Ayuba yakeyi da lalata ibbi da yayi"saidai tace aikuwa nagama Zama dashi"saiku k'arata da mugun halinku"har kuka ibbi yyi Yana gamata da allah.kafin ta Dan sakko" suka kwashe kayansu nasawa kawai sukabar gidan..lokacin da ibbi yadawo asibiti yasami securities acikin d'akin"gabansa yafad'i sbd ganin alh Ayuba da kansa duk jini"tambar meyafaru yayi?aka sanar mishi da lalube alh mudi ya Isa inda yake suka kaure da kokawa harsuka jima juna ciwo sbd bbu Mai gani acikinsu.hakan yasa sukayi amfani da duk wani abu dayazo hannunsu suna makawa juna.


K'arar ce tasaka akazo aka balle k'ofar"hankalin ibbi yatashi dayaga jinin dake fita akan alh Ayuba.... emergency akayi da alh Ayuba.yyinda alh mudi bewani ji ciwoba haka akabarshi anan room d'in...ibbi kuwa betab'a shiga tashin hankali irin na yau ba....


****************


Yaya mahmod na fita yaga nura zaune Yana jiransa asaman motarsa.dafe Kai yyi yace"I'm sorry abokina wlh nasha fa'a dakai"maimakon ka shiga ciki.saikace wani bak'o.nura yadiro dg kan motar Yana cewa ah ah aibana shiga gidan surukaina Kai tsaye ba.tunda kafito Zan wuce gida saida safe "zandawo na d'auke ka muje office... murmushi Yaya mahmod yayi yanacewa hakane kumafa "sbd haka kadinga gaidani atsugunne.shigewa mota nura yyi had'e da cewa karka damu indai akan my zee ne Zan iya komai..

Saida nura yafita"sannan Yaya mahmod yayi alwallah Yana murmushi"aransa yace"ikon Allah bantab'a zaton nura zaice yanason zainab kodan sbd yasan komai akanta.gashi Allah yabatashi be duba halayenta na bayaba.sbd ko yanzun shi bewani yarda ta kimtsuba.da wannan tunanin ya wuce masjeed.


Lokacin daya fito yahad'u dasu Abba najiransa"sbd anty ta Kira Abba tasanar mishi wannan daddad'an labari na warkewar mahmod.shine shida daddy suka baro office suka nufo gida.


Cikin farinciki yaje yarungume su"suna tayashi murnan samin lafiya suka shigo cikin gida.yaya mahmod kuwa part d'in mazan gidan ya wuce"yasamu angayara mishi d'akin sa"wanka yayi ya shirya cikin k'ananun Kaya"kafin yaje parking space yad'auki motarsa" dake wanke a ajiye yafice dg gidan..


Cikin gida kuwa anty sawa tayi khadija ta tsefe kanta bayan tayi sallar la'asar"anty ta wanke matashi ta busar Matashi da hand driyer"bayan tayi wanka.tamata turaren jiki"tabata wasu had'in magunguna tace"ta shanye"itadai Khadija mamakin abun kawai takeyi aranta.batadai ce komaiba sbd tasan anty batasan tambaya...bayan angama sallar magrib saiga hjy ta shigo sashen anty rik'e da kula ahannunta"Khadija dake zaune da khalifa akan cinyarta"tayi saurin tashi tsaye tana cewa hjy sannu !kawo na d'aukar Miki"mik'a mata kular hjy tayi tana murmushi tace" ai takicema kula khadija.abincinkine nakamiki"anty dake fitowa dg kitchen tace"Kai hjy basai ki Aiko tazo ta karb'a saikinzo da kanki"hjy na murmushi tace bbu ruwanki tsakanina da Y'ata ne.murmushi kawai anty tayi.hjy tace in mahmod yazo yace kibishi bance kije ko inaba"bayan sati 2 zaku koma gidanku insha Allah.kan Khadija ak'asa tace to hjy nagode.anty batace komai ba"Amma Tasha alwashin muddin yazo wlh sai Khadija tabishi...


Farfesun kaji ne"hakan yasa Khadija taci tayi kat"Tasha ruwa ,kafin taje tayi sallar isha'i.

       kwanciya tayi"wayarta ta fad'o Mata arai.tayi murmushi tayi sbd tasan agidan mlm tabarta....


Yaya mahmod kuwa gaba d'aya hankalinsa nakan Khadija"dama kud'i yaje yacire ,yasiya musu kayan mak'ulashe"yanufo gida anata Kiran magrib"yanayin parking yafito yawuce masjid.bedawoba Saida akagama isha'i...


Babban parlourn gidan yanufa"bbu kowa"hjy na shashen Abba"su ummi da hafsat duk waya suke yi da samarinsu.bbu wata kunya ya wuce shashen anty... sallama yyi"anty na zaune ta amsa "yace anty sannu da gida.yauwa mahmod !kaci abinci kuwa?da sauri yace"ah ah"

To bara Khadija takaimaka acan.baki washe yace to Yana fita...anty ta tashi ta wuce d'akin da Khadija keciki..



Tafe take tana turo baki"sbd badason ranta tazoba.tsoromtakartasha matsa ahannun gwanin nata.


"Ahankali ta murd'a k'ofar ta shiga"sallama tayi ta ajiye tray d'in hannunta"Yana zaune kan carpet Yana jiran isowarta"tashi tsaye yyi yanufi k'ofar yasaka key...zaro ido tayi had'e da cewa nifa yaya tafiya zanyi karufe Kuma.


Hmmmm!my khady aikeda tafiya sai Allah yakaimu gobe lfy tukum"shagwabe fuska tayi had'e da cewa hjy fa tacemun karnasake nabika nanda sati 2 zamu koma gidanmu.yanzunma anty ce ta tursasani"nidai kabud'emun pls"kafeta yyi da ido yanata kallonta"komai tayi burgesa takeyi"my khady ita yanzun hajiyar batana gun nata mijinba"shine zata hanaki kizo guna..dafe baki tayi cike da mamakin kalaman sa.d'age gira yyi had'e da cewa k'arya nayine?"batace komai ba kanta ak'asa.kinga sarkin kunya zomuci abincin to"um um hjy takamun abinci naci ak'oshe nake.my khady hjy fa nayin sankai "gaba d'aya kin amshemun gwamnati agurinta"murmushi tayi tana k'ok'arin zama tace"eh Mana yanzun Dani takeji.to ai nima dad'in abun inada anty ko?hmmm ai anfi ji Dani"kikadaice ba"yafad'a Yana Zama yaxuba abincin kad'an ta tashi takamishi drink dke cikin frige.

      Cikin y'an mintina yagama cin abincin"Khadija na zaune gabanta nata fad'uwa"Allah yasa yabarta ta tafi take fata..my khady tashi muje ciki ki had'amun ruwan wanka"tamkar tamishi musu"haka ta daure ta tashi tanufi bed room d'in.


Tana fitowa dg toilet d'in tasameshi dg shi sai boxer"janye idanunta tayi tana cewa kashiga nizan wuce cikin gida.my khady yaushe muka Fara y'ar musu dakene?"bbu inda Zaki agurin mijinki Zaki kwana.bejira amsarta ba ya wuce toilet.


Zama tayi jikinta asanyaye"bema jimaba yafito Yana cewa shiga kiyo alwallah"cikin fad'uwar gaba tace"nayifa isha'i Yaya!hmmmm!agidan mlm inzamu kwanta dama bamayin sallah ne?"batace komai ba ta wuce ta nufi toilet.yasaki shu'umin murmushi"boxer d jallabiya Fara yasaka"yashimfid'a prayer mata"alokacin ta fito,hijab nata dake gefen bed ta d'auka" ta rab'a gefensa yajasu Sallah raka'a 2.amamakinta saitaji yadafa kanta yanamata adduar.wayyo Allah!wani mugun tsoro da fargaba taji.tama gama yadda bata tab'a kubuta dg hannun Yaya mahmod.sbd komai yyi shine ayadda manzon ALLAH (S A W)yakoyar adaren farko"parlour yatashi ya nufa"bbu jumawa yadawo da wasu ledoji"cikinta saida yajuya sbd tsoro.kallonta yyi yaganta zaune har yanzun kan prayer mat d'in"Zama yyi kusa da ita yanacewa koki cire hijab naki koni naciremiki da kaina.batayi wani Jan mgn ba ta cire"yadubi gyaran gashinta ya lumshe ido"k'amshin turaren jiki da akamata yadaki hancinsa.my khady ga ice cream ga shawarma,gakuma frash milk ga suya gasassa duka zakici??girgiza kanta kawai tayi.hmmm aibazai yuyuba nasiyi Abu danke kice bazaki ciba.zansha ice cream d'in d'an Allah wlh cikina acike yake. Bece komaiba ya miko Mata roba guda"shima Roba guda yashanye"yadanci naman kad'an"sbd Jan mgn Saida yagutsiri tsoka yasaka Mata abaki.batayi musuba ta cinye.komai yakwashe ya nufi parlou"itakuma toilet ta wuce tasami brush sabo tayi tukum ta fito"yanatsaye yacire jallabiyan jikinsa sai boxer kawai yarage mishi.kafeta yyi da ido"sbd yalura atsorace take"my khady Kinga ga sleeping drass nan kisaka ki kwanta zanyi brush da karatun alk'ur'ani Mai girma.dato ta amsa "shikuma ya wuce toilet.


Lokacin daya fito ta kwanta"dukda batayi bacciba"sbd tsoron Yaya mahmod.


Yakai kusan 20 minit ,tukum yarufe alk'ur'anin yanufi kan bed d'in.


Ahankali ya haura kan bed d'in yakwanta agefenta"Murya can k'asa yace"my khady kinyi bacci kuwa?shiru tayi gabanta nata fad'uwa sbd tsoron karyamata wani"hannunsa guda yasaka ya juyo da ita gabansa.kallon fuskarta yyi sbd akwai hasken fitilar dake kan bed side drower.yana murmushi yace"Mai k'arya?nasan kinajina ko my khady kibude idonki inba ga tsoro ba... murmushi tayi tana turo baki tace nafara baccifa Yaya"hmmm!me bacci Yana mgn dama ?"Kinga tashi kirage kayan jikinki,nima da boxer ne ajikina.gabanta taji yafad'i "Bata auneba taji hannuwansa ajikinta Yana k'ok'arin cire mata rigar baccinta.yayaaaaaaa!my khadyyyyyyy ! yafad'a Murya asark'e"barinta yyi hakan yarufesu da blanket"ahankali yajanyota jikinsa ya Fara shafarta zuwa nashanunta"yahad'e bakinsu gu d'aya"inbacin rawa bbu abinda jikin Khadija keyi"shikuwa romancing d'in ta kawai yakeyi azafafe"kuka tasaki sbd jin alamar yarabasu da komai na jikinsu"Bata auneba taji yyi swech off d'in fitilar dake kan bed side drower"d'akin yagauraye da duhu..yyinda Yaya mohmod yayi nisa baya jin kira,hanyarsa kawai yake k'ok'arin bi....wata razananniyar k'ara khadija tasaki...burin Yaya mahmod yacika.....✍️


Happy Friday🥰

No comments