MIN QALB 44
******
Zama tayi a palon zuciyarta na wani irin tiririn takaici da baqin cikinsu su dukan sbd itama anty zarah din taga damane su hadu su Bata laifin daba nata ba Dan me daga abin arziki zai cillo Mata maganganunsa bacin Rai?
Miqewa tayi ta nufi kicin ta dauko ruwan sanyi Tasha ko
zataji saukin zafin zuciyar Amma a banza qarshe tsoki taja tabar kicin din
Takoma dakinta tayi kwanciyarta.
Da safe sanyawa gidan key tayi takuma qi ajiyewa a inda suke
ajiye keys na gidan Dan idan waninsu ya dawo ta sakasu jaka ta tafiyarta
makaranta tana ganin kiransa taqi dauka.
Bayan zuwanta makaranta da kusan awa shida Yayi Mata kusan
Kira fiyeda biyar Taki dauka ganin hakan tasan zasu iya zuwa makarantar nemanta
Dan haka tayiwa annah Magana ta tafiyarta tabar cikin makarantar.
Duk yanda sukaso ganinta su karbi keys na gidan taqi Bari
Dan blocking dinsa ma tayi a qarshe anty zarah ma Kira daya tayi Mata Bata Bari
tai Mata na biyu ba ta sanyata blacklist tana cewa''
Kun Manta waye Amatu idan shi baisaniba aike matarsa kinsan
waye Amatu halina Babu inda yaje boye abuna nayi.
Sai dare tadawo gidan ga mamakinta sai Bata tarar dasuba a
gidan suna jiran isowarta ta bude tashigewarta ta rufe dayake taciyo abincinta
sai kawai tashige tayi wankanta ta kwanta sai bacci.
Washe gari ma haka ta tafi da keys ta wuni a school taqi
dawowa da wuri sai dare Kuma still ma dai Babu ko inuwarsu.
Al'amari na Wasa Wasa saigashi ta share sati guda cur babusu
Babu labarinsu Kuma ko awaya Basu taba maganaba duk inda zuciyarta takai ga
girma ta 6aci Dan kuwa iya qonuwa ranta ya qonu wato ko ohon Mata tunda ta
rufewa shida matarsa gida ko ohon Mata sunyi tafiyarsu sun bar Mata gidan ita
ciwon idan yazo kanta tadade Bata mutu ba kenan.
Exams suka kammala ta daina fita gabaki daya abun duniya
yazo ya sanyata gaba Babu Abinda ke sake sanyata baqin ciki irin yanda ita ko
oho da ciwonta da lafiyarta tunda matarsa taso na taredashi ita Kuma tunda a
tausaya Mata a taimaka Mata itada 'danta dasuke marayu shiyasa aka maqalo Masa
ita ya aureta gashi tun yanzu ya nuna Mata iyakarta dashi biyan buqata tunda
matarsa ta auren so ce agabansa.
Kukan datasha a Daren ranar saidaya sanyata zazzabi me qarfi
ga ciwon Mara daya sanyota gaba ga zuciyarta baqin ciki kawai takeji daqyar
taga safiyar ranar ta lallaba takai kanta asibiti duk da alamomi da yanda
takeji tana tunanin ciki atareda ita zamtowarta gynecology student datake gab
da zama likitar.
Lokacinda aka Bata result din she's 2month pregnant wani
yanayi na tausayin rayuwarta tasamu kanta har Saida hawaye suka ciko idanuwanta
suka sauko Kan kumatunta ta share ta kamo hanyar gida tana sakawa ranta tunanin
komawa Nigeria Dan zamanta anan baida amfani gwara takomawarta inda akasan
darajarta cikin iyayenta masu qaunarta idan yaso zabeera ta Dade Bata Yi abun
kunyar anyi rabuwa acikintaba Amma rabuwa zatayi da MAHMOUD ZABEERA ta huta sbd
yagama nuna Mata baisan darajartaba ko daya.
Ta waya tayi booking ticket din komawa Nigeria Amma Babu
jirgin zuwa Nigeria a ranar saidai Nanda 4 days ba Bata lokaci tayi booking
tayi payment tana isowa gida ta wuce daki ta zube Kan gado wani wahalallen
bacci yayi gaba da ita.
Cikin bacci taji doorbell na qara sama sama ta bude idanuwanta
dake cikeda baccin wahala takalli agogo taga yamma tayi sosai ta murgina ta
tashi ta sauko gadon tashiga toilet ta wanko fuskarta tareda yafo qaramin gyale
Kan doguwar rigar dake jikinta Mara hannu ta nufo qofar tana cewa''
Am coming.
Bude qofar tayi bama tareda tafara duba ko wayeba ta camera.
Da MAHMOUD ZABEERA tafaracin karo yayi fresh Abinsa cikin
brown Armanis sai Zarah zabeera a gefensa itama tayi fresh haddasu manyan
kumatu da Naman wuya sai qananun luggage dinsu ko kallon second daya Bata qarai
musu ba ta juyowarta tana zame gyalenta ta nufi hanyar kicin tana receiving
call din daya shigo wayarta batareda ta nuna tamaji sannu da zaman gidan da
anty zarah ke mata ba tayi banxa da ita.
Bayanta anty zarah tabi da kallo tanajin rashin dadin yanda Amatun
ta kwashesu ta watsar ba musamman MAHMOUD dayake mijinsu ai ya cancanci
sannu da zuwa.
Hanyar bedroom dinsa yayi Yana janyeda akwatinsa ita Kuma
anty zarah kasa hkr tayi tabi Amatun kicin.
Tana shiga Amatun na qoqarin juyowa daga hada tea da biscuits
din dazataci ta kalli fuskarta tana cewa''
Amatu lafiya Naga munshigo ko gaisuwa Kuma MD ma Naga ko
sannu baki.....
Wani kallo Amatun tafara aiko Mata dashi kafin tabude Baki
tace"
Anty Ina ganin girmanki kabari muje ahakan.
Wucewa tayi tabar anty zarah tanabinta da kallon mamaki da
tsoro kafin itama tabar kicin din takama hanyar dakinta.
Sanin sundawo sunajin yunwa gasa anty zarah fitowa tai musu
Abinda zasuci taje har dakin Amatu takirata Amma tayi bugun duniya ko cewa waye
Amatun taqiyi bare tasa ran zata bude Mata ganin haka MAHMOUD yace tadawowarta
tazo taci abinci Tasha maganin taje ta kwanta tana buqatar hutu,
Yasan masifa da rigimar dake cin Amatun shiyasa shima bazai
shige mataba duk da yayi matuqar kewarta Amma rigimarta har fargaba take sakashi
Sam bayason tashin hankali musamman yanxu da zarah Allah yabata Abinda takeso
bayan shekarun jira masu tsayi,
Harga Allah shi baisaka damuwar rashin haihuwa aransa ba
kodan yataso cikin kadaicinda har yake sha'awa da son rayuwa shikadai ne?
Sai lokacinda aka haifi Muhammad yaji son 'yaya yashigesa
Amma dai still bai saka abin a Rai ba zarah ce ta qwallafa Rai ason haihuwa
yanxu gashi Allah zai Bata sanin yanda ta dauki alamarin cikinta yasa yake
tayata tattalawa da kulawa sbd taji farin ciki Amma wainnan kwanakin a
Santorini shikadai yasan yanda yayi su day tunanin yanda Amatu take anan.
Abincin sukaci sama sama kafin ya miqe yashige Yana sake
trying numbern Amatu daya Gama tabbatarda blacklist tasanya shi.
Washe gari dukkanin wasu kayanta masu daukuwa ta hadasu a
akwatina ta rufe na Shan iskar dazata Sanya yau da gobe kafin jibi ranar
tafiyar kawai tabari a waje ta shige toilet tayo brush da wanka tazo tayi
sallah Dan tayi lattin tashi ta sanya jeans da baqar cardigan sbd sanyi sanyi
datake ji Wanda tasan hadda na zazzabin dayaqi sakinta Wanda a nazarinta kozata
daina qananun zazzabi zazzabin saita fita early months dinta na pregnancy.
Fitowa tayi taje cikin ta soya kwai da uban tomato sauce da
bread ta dama oat tazauna a qaramin table din kicin din nacin abinci tana
breakfast dinta cikin nutsuwa.
Ta windon kicin taji motsinsa yana balcony tasan geamin
yakeyi a balcony kullum safe,
Batason ganinsa Dan haka taqarasa cinyewa Dan tabar kicin
din Takoma daki sbd Yana gamawa kicin yake yowa direct Dan amfani da ruwan
sanyi.
Bata shanye sauran oat dinba ta dauka zata Sanya fridge
cikin tsautsayi kofin ya subuce daga hannunta ya fashe oat din ya zube gurin
tareda glasses na cup din.
Juyawa tayi zuwa store dauko mop da Abinda zata kwashe
glasses din kafin tayi mopping tana cikin tsore din saiga anty zarah tashigo
kicin din idanuwanta plates din Kan table da akaci abinci dasu take kallo Bata
ankara da abindake qasaba ta taka lokaci daya akai sama sosai da ita tafado da
qarfi Kuma ta saki wani razanannen ihun dayasa Amatun fitowa batareda ta dauko
Abinda taje daukowa ba.
Cikin sauri tace"
Sorry sorry nice na zubar wlh Bari nakoma na dauko mop
sorry...
Juyawa tayi da sauri Takoma daidai shigowarsa ya qaraso gun
zarah din da sauri ganin tana juye juye cikin azaba cikin sauri ya riqota Yana
kallon fuskarta da tuni ta hada uban zufa yace"
Me wannan abin yakeyi a qasa Kika Fadi?cant you watch where
you are going...
Fitowar Amatu da mopa a hannu yasashi dagowa ya kalleta ta
dauke Kai tana qoqarin tattara gurin Kai tsaye cikin fada fada yace"
Ta Yaya wannan abun yake zube qasan kicin din?Kai tsaye
tace"
Nice na zubar Kuma banzubar ba Dan wani ya Fadi duk Wanda
yafadi qaddararsa ce ahaka,
Idan zaka dauketane na tattara gurin to....
Rintse Ido yayi ya bude akanta Yana cewa''
Meyasa kullum kinfison tashin hankali akan zaman lafiya?
Wannan kishin da kike is nothing but madness idan zaki ji
haushin wani come to me not my wife sbd itane tafi cancantar wannan madness din
not you sbd itace aka aurewa Miji....
Na aka aure mijin inaga ai bani nace a auramin ba sbd Nima
inada nawa mijin qaddara ta rabani dashi harna qare anan and idan kanajin ka
gaji da da madness dina bana tunanin akwai Wanda yasaka zama Dole Dani infact
ma ni nagaji da auren na mijin wata sbd Nima bashine gabana ba Mijina da duk
duniya yafimin kowa na Rashi na dangana to waye Zan rasa ban hakura......
Cikin wata irin tsawa data Sanya anty zarah bude idanuwanta
ta kallesa cikin tsoro sbd Bata tabajin ya daga murya hakaba kaf zamansu ita ko
sa'insa haka Bata taba Jin yayiba idanuwansa na sauya launi da bacin ran
kalamanta yace"
Get out of my sight.
Not only your sight am going out of your life gaba daya...
Daqyar anty zarah ta bude baki ahankali tace"
Amatu Dan Allah kiyi shiru meye amfanin tashin hankali....
Hannu ta daga Mata idanuwanta na rufewa tace"
Dashi nake magana sbd shiya kawo zancen,
Kuma tashin hankalin waye yajawo tun farko ayishi?
Muna zaune gida daya muna kwana cikin guri daya gari baitaba
wayeba ba banje har dakinki na gaidakiba,
Bantaba fita makaranta ba banzo nace Miki na tafi ba Amma da
ciwo ya kamaki nida nake cikin gari baki kirani kin sanar daniba Dan nice akusa
saikina Kirasa shida baya gari sbd shine zai baki lafiya nikuma ciwo Zan qara
miki,
Daya Kira Yana kirana careless meya Hana ki sanar dashi baki
kiraniba kokuma bansan bakida lafiyaba?
Anty zarah Ina ganin girmanki haryanxu so please stay out of
this.
Wurgi tayi da mopar Tana ficewa zuciyarta na mugun tafarfasa
idanuwanta dasukai jajir suna bushewa.
Su duka kallonta sukeyi shi cikin mamaki da takaicin kansa
dayake kasa daukan mataki akanta itakuma anty zarah sai alokacin tasan eh
lallai bata kyautaba Amma Kuma itama ba laifinta bane Babu Wanda ya cancanta ta
sanarwa batada lafiya bayan mijinta.
Daukar zarah din yayi Wanda sai alokacin su dukan suka
lurada jini yafara gangaro Mata batasan lokacinda tasaki wani razanannen kukaba
tana qoqarin qwacewa daga jikinsa Dan ta miqe yayi saurin riqota Yana daukarta
gabaki daya ya fito ya fice zuwa asibiti da ita lokacin mararta tafara mugun
ciwo sosai tuni tafara ficewa hayyacinta ga wani irin hawayen tsoron karta rasa
cikinta datakeyi Dan kuka Yama daina fita.
Suna Isa asibitin aka karbeta ya nufi reception ya cika duk
wasu formalities ya zauna zaman jira.
For morethan 3hours Yana jira kafin likitocin suka fito suka
sanar dashi tayi loosing jini sosai Amma sun samu sun tsayar cikin baiyi
komaiba Yana nan saidai akwai yiyuwar zai iya barewa sbd mahaifarta batada
qwari ko kadan Dan haka zasu daure Mata sbd kada cikin ya zube.
A asibitin suka yini sai dare sosai akai discharging dinta
suka dawo gida duk da taji jiki Amma zuciyarta farin ciki ne fal sbd tunda ta
auri MAHMOUD baitaba Bata lokacinsaba bare irin wannan kulawar datake samu a
yanzu daga garesa wadda ta tabbatarda bawai Dan tanada ciki bane sbd tun kafin
samuwar cikin ya sauya Mata tana samun kulawarsa Wanda tasan ba kowa bace
tafara sauyasa qarfi da yaji sai Amatu Dan Nan gaba ma qila abin yafi haka Dan
qila har kalmar so zata samu wata ran ya furta Mata.
Murmushi tasakar Masa tana riqo hannunsa ahankali tace"
Thank you.
Batareda ya kalletaba ya Dan jinjina Kai Yana lumshe
idanuwansa zuciyarsa gabaki daya batada sukuni har lokacin kalmomin Amatu na
dazun akan mijinta daya rasu dashi kansa suna yawo cikin kansa da kunnuwansa ko
asibiti zaune kawai yake amma kalmomin suke ihu cikin kansa.
Meyasa zuciyarsa zata kasa sukuni akanta Bayan itace ciwon
kansa gabaki daya ita Bata tsoron tashin hankali ko fitina,rigima cikinta take
Bata ko gajiya ya tabbata yanzu tanacan tana zafin zuciya ko abinci qila bataci
ba.
Suna shigowa har daki ya raka zarah data gama yanke shawarar
komawa gida cikin satin data samu qarfin jiki kafin ya fito.
Ya jima tsaye a qofar dakinta hannuwansa zube cikin aljihu
Yana tunanin halinda take ciki yasan koya buga bazata bude ba Dan haka ya sauke
ajiyar zuciya tareda juyawa yabar gurin ya nufi dakinsa.
Washe gari daga zarah harshi Babu Wanda tabari yaganta a
daki tayi komai nata amatse takeda gari yasake wayewa ta tafiyarta.
Ranar dazata tafi Kwana tayi kuka zuciyarta mugun zafi take
Mata,
Ranar harda kukan mutuwar Dr khalil saidaya dawo Mata sabo.
Marartace tafara ciwo kadan kadan ta tashi zaune tana dafe
cikin saigashi ciwon yafarayin gaba gaba ta rarrafo ta sauko gadon tana duba
agogo taga qarfe ukun dare tana qoqarin komawa gado qafafunta suka riqe azabar
tafara fin qarfin ta zube agurin tana Kiran sunayen Allah cikin tsananin azabar
da Bata taba jiba tafara rarrafowa tana hawaye ta bude qofa ta fito tana Jan
numfashi daqyar tanajan jiki ta Isa bakin qofar dakin anty zarah a taba qofar
batada qarfin bugawa sbd qarfinta da ciwon yaci sosai sbd zuwa lokacin ciwon ya
zaburo gabaki daya take ta zube gurin tana numfashi daqyar idanuwanta na
gangaro da hawayen azaba.
Anty zarah dataji kamar antaba kofarta tana zaune ne farko
Tasha ruwa ta kalli qofar cikeda mamaki ta taso ahankali ta bude kofar batasan
lokacinda takira sunan Amatun da qarfi ba tana zare Ido akan jinin dake kwance
qarqashin Amatun tace"
Innalillahi Amatu??
Hanyar dakinsa ta nufa ta Murda Kai tsaye tashiga tana Kiran
sunansa a rude ga mamakinta shikuma zaune ta tarar dashi ya dafe kansa Sam ba
alamar yayi bacci kozaiyi bacci ataredashi tana kallonsa da mamaki take cewa''
Amatu ce gatacan kwance ba lafiya.
Dagowa yayi ya kalleta saidata Kuma maimaita sunan Amatu ya
dawo hayyacinsa ya miqe Yana ficewa dakin.
Yana ganin jinin jikinsa yabasa cikine da ita take wani irin
mutuwar jiki takamashi bai damu da jininba ya rungumeta gabaki daya ya fice
Yana mantawama da zarah dake tsaye.
Tun a hanya yake Kiran sunanta Yana shafa fuskarta cikin
tsananin damuwa da kulawa yake cewa''
Please please please Amatu I can't bear to loose this
pregnancy idan babyna ne ajikinki please ki daure karki Bari yafita.....
Tanajinsa sama sama Amma Bata iya motsi sai hawaye dake gangaro
mata har suka Isa asibiti
Suna Isa ana karbarta cikin na qarasa barewa.
MAHMOUD ZABEERA baitaba sanin yanason haihuwa hakaba saidaya
rasa cikin jikin AMATULLAH Wanda yaji dukkanin burinsa da farin cikinsa kamar
ya ruguje ne musamman yanda Amatun ke hawaye ko kallonsa batason Yi taqi bude
idanuwanta ko kallonsa tayi.
Duk yanda yaso kusantota taqi Bari qarshema kuka ta fashe
Masa dashi na tana buqatar kasancewa ita kadai.
Dole ya fice yabarta yadawo harabar asibitin ya zauna cikin
mota tareda Kiran Gida Nigeria yacewa kawu Dan Allah anty salamatu ta shirya
tadawo zaisa asiya musu tickets itada Muhammad dake hannun umme yanzu.
Gida yakoma yayi wanka ya sauyo Kaya sbd har qarfe goman
safe tayi Masa tun asibiti,
Tea kawai yasha yakoma asibitin yabar anty zarah da kallon
ikon Allah Koda yakoma har an taimaka Mata tayi wanka an sauya Mata Kaya da
green patient cloth zuwa blue tana zaune anbata tea da magani Tasha tareda
snacks.
Tunda yashigo ko dagowa batayiba sai sauraron nurse din dake
qoqarin cheering dinta up take ga idanuwanta dasukai jajir bayan uban kumburin
dasukai tabbas MAHMOUD ZABEERA baisan waye AMATULLAH ba,
Zaisan ita Bata cikin matan dabasusan darajar kansu ba,
A banza yasameta shiyasa baisan darajarta ba Amma yanzu sai
San AMATULLAH SALEH daban ZARAH ZABEERA daban,
Sunansu ba dayaba,halinsu ba dayaba hakama yanayinsu ba
dayaba.
Agogo ta kalla taga akwai sauran awanni biyar kafin jirginsu
ya tashi Dan haka tana buqatar komawa gidan kafin ta dauki komai nata ta wuce
airport kafin lokacin.
Qarfe biyar na yamma yabar asibitin ta karbi discharge
papers dinta ta fito ta tari mota ta fada.
Koda suka Isa gida Bata sallamesaba tashiga gidan Kai tsaye
dakinta ta nufa ta sauya Kaya ta janyo kayanta tafara fitowa dasu takai qasa
tadawo tadauki handbag dinta ta jakar labtop dinta ta fito ta bugawa anty zarah
qofa tana budewa batareda ta kalli fuskarta ba tace"
Anty Zan wuce Nigeria Kuma Ina baki hkrn maganganun Dana
fada Miki idan na Bata miki Rai.
Juyawa tayi Bata jira Abinda antyn zatace ba ta fice.
Koda ta Isa airport lokacin tafiyarsu yayi Dan haka kawai ta
wuce ta karbi ticket dinta ta bada ta wuce.
Ko mintuna arba'in basuyiba jirginsu ya tashi suka bar
qasar.

No comments