Breaking News

THE GOVERNOR'S WIFE 10


 *THE GOVERNOR'S WIFE*

...... MATAR  GWAMNA....



 *©Azizat Hamza*

 wattpad Azi_zat 



Bismillahir Rahmanir Rahim




Book one



10






Lokacin da Ale Faruƙ ya auri Zainab Kurma matan sa uku ne, dan bai jima da sakin ta huɗun ba. Da ganinta da auren duka-duka sati huɗu ne.


Mama Asabe har ga Allah bata so aka yi auren ba, ba kuwa saboda halin Ale Faruƙ ɗin bane na auri saki sai dan saboda ayyukan da Kurma ke mata. Duk wani ƙarfin sana'arta to Kurma ce. 

Ita da Malam Sabo dai sun yi ƙarfa-ƙarfa sun mata gado da tabarma da buta daga nan kuma kowa ya tsuke Aljihun sa. Duk da kuwa irin kuɗin da Malam Sabon ya yaga a wajen Ale Faruƙ ɗin.


Inna Talatu wacce ta reneta lokacin tana yarinya da kuma wasu cikin 'yan uwan mamanta su suka haɗu suka mata sauran kayan ɗakin.



Lokacin da aka kawo Kurma gidan ɗakin Iyani aka fara kaita wacce ta ke Uwargida sannan aka wuce da ita ɗakin Fulani wacce ta ke matarsa ta biyu a gidan, matar da ta zame masa ƙarfen ƙafa ita bata haihu ba amma ta ƙi tafiya duk da kuwa rashin mutuncin da take shukawa a gidan. Sai ɗakin Halime matarsa ta uku wacce shekaransu uku kenan da aure.


Lokacin da aka kaita ɗakin Tabawa ko kallon kirki bata yi musu ba, ta ɓantari goro tana taunawa tace "Faruƙu kenan. Abin nasa yanzu ya koma kan Miskinai. Allah rufa asiri"

 Inna Talatu ta harzuƙa zatayi masifa wata yayarta ta hanata. Kafin su fita kuwa Inna Talatun ta kirata da tsohuwar banza. Tabawa ta biyosu tana zagi tana tsinuwa amma babu wanda ya kulata.


Rayuwar Zainab a gidan Ale Faruƙ tamkar 'yar aiki ce a gidan iyayen gidanta. Sati ɗaya da Ale Faruƙ yai yana kwasar amarci ya dinga tattalin Zainab, shi yake siyo mata abinci daga waje: nama, bredi, ƙwai da madara sune cimarta. Baiwar Allah har ta fara sake jiki tana godewa Allah tunda rayuwar da take ciki yanzu akwai daɗi ba kamar gidan Mama Asabe ba.

Lokacin da aka fara rabon girki nan ne ta ƙwammaci kiɗa da karatu. Gidan Ale Faruƙ babban gidane wadatacce dan kowacce mata ciki da falo gareta, shima sashensa ciki da falo ne, sai ɗakuna huɗu na yara sai ɗakin mahaifiyarsa Tabawa, sannan akwai ɗakuna uku a zaure na saukan baƙi. A lokacin daya auri Zainab 'ya'yansa goma shabiyar ciki kuwa bakwai ne da iyayensu. 'Ya'yan Iyani su guda shida, maza biyu,mata huɗu sai Halime dake da 'ya ɗaya.


Da farko Fulani ce ta fara ɗaurawa Zainabu nauyin girkinta daga baya Iyani da Halime suka biyo baya. Kafin kace me gaba ɗaya ranakun girkinsu ita ke yi. Fulani kam hatta Sana'arta na shinkafa da wake da take da rana sai da ya zamo Zainabu ce ke yin komai , ita dai sai kawai idan ta gama ta zauna ta dinga siyarwa.

 A hankali Yaran gidan da suka ga iyayensu na saka Zainab aiki sai suka fara taɓawa suma. Lokaci lokaci sai su bar mata wanke-wanken gidan ko kuma  su jiƙa kayan wanki su ƙi wankewa saboda idan Kurma ta zo ta gani tana son amfani da baho ko bokiti dole sai dai ta wanke musu kayan tunda bata da mugun zuciyar da zata bar musu kayan a ƙasa. Ranan da ta fara zuwa ta ga sunyi haka, ɗakin yaran ta je tana musu bayani akan za tayi amfani da bahon wanki. Haka suka manna mata hauka akan basu san mi take faɗa ba, abin takaicin yawanci bahon nata ne dan Fulani da Halime basa taɓa barin nasu a waje. Ita kuwa Kurma ko bata fito da su ba yaran sukan shiga ɗakinta su ɗauka babu yadda ta iya.


Cikin zalunci da ake yiwa Zainabu ba abar Tabawa a baya ba. Itama ba ta taɓa ragawa Zainabun ba, dama duk cikin matan Ale Faruƙ babu wanda ta ɗauki mahaifiyarsa da daraja haka ma jikokinta. Kafin zuwan Zainabu gidan Tabawa ke wanki da kanta, haka ma abinci sai abinda aka zuba mata amma Zainabu Kurma bata taɓa mata rowan abinci ba haka nan wankinta da gyaran ɗaki duk ita ke yi.


Kafin shekara ɗaya  Zainab ta zabge ta koɗe. Aikin da take a gidan Ale ko rabinsa bata taɓa yi ba a gidan Mama Asabe.

Ale Faruƙ ya san mi yake faruwa a gidan tunda shi ba makaho bane amma halinsa dama shine idan mace ta shigo gidansa komai ta tarar ruwanta ne, sai dai ta ƙwaci kanta daga sharrin sauran matansa amma shi ba zai tanka ba.


Akwai lokacin da Zainab tayi ɓarin cikin sati uku bata sani ba bata ma san cikine ba dan jinin  al'ada ta ɗauka.

Tana zaune ne a gidan amma gaba ɗaya komai na gidan ya fita mata aka. Akwai lokutan da take tunanin gara kawai Ale Faruƙ ya saketa. Sai dai dokar sa ce baya sakin mace kafin ta cika shekara biyu. A cewarsa lokacin bai gama morar kuɗinsa ba. 


A cikin shekara na biyu da auren Zainabu da Ale Faruƙ ta sake samun ciki. Cikin yazo mata da laulayi mai tsanani amma babu wanda yake tausaya mata a gidan. Ba ta son warin abinci, bata cin abinci sai ƙanzo da kunun tsamiya. Idan za ta yi girki sai dai ta sa tsumma ta rufe hancinta saboda kar ta ji ƙanshin. Ranan da ta ƙi yiwa Fulani girki ta nuna cewa sai dai tayi tunda ranan girkinta ne haka ta mata chaa har da mata kashedin indai bata yi girkin ba za ta mata duka a gidan.


Ranan da Ale Faruƙ ya dawo ɗakinta, tace masa ya gayawa matansa cewa ba zata sake yiwa kowacce girki ba. Abin mamaki sai cewa yai tunda ta riga ta fara sai dai ta cigaba da hakan har zuwa lokacin da zasu ce ta dena. Abin ya ƙona mata rai. Bata taɓa tunanin kai ƙaran Ale ko matansa ba, koda wasu cikin 'yan uwanta sun kawo mata ziyara nunawa take bata cikin matsala.


Washegari ta saka hijabi ta wuce gidan mahaifinsa.

Ɗan karatun allo da tayi kafin aurenta da shi ta  iya rubuta bayaninta da rubutun ajami a takarda ta miƙawa Mama Indo matar Gwani. Mama tana karantawa sai ga hawaye ya cika mata fiska. Tana tambaya ne akan ko addini ya bayarwa namiji daman ya yi rashin adalci tsakanin matansa. Sannan idan ta ƙi yiwa matan mijinta aiki akwai zunubi awajen Allah?


Mama bata bari Gwani ya gama karatu da almajiransa ba ta aika akan ya zo akwai matsala. Koda ta bayyanawa Gwani abinda Zainab ta faɗa ransa ya ɓaci sosai. A kullum tsakaninsa da Faruƙ shawara da addu'a domin muguwar tarbiyar da Tabawa ta bashi da kuma jahilci da ke damunsa shiyasa yake tafiyar da rayuwansa bisa ra'ayin kansa. Arziƙi dai Allah ya bashi amma ni'imar ilimi da kakansa Malam Falke keda shi, da Gwani keda shi da ƙannensa Malam da Zakari keda shi ya barranta masa. Bai nemi ilimi yana ƙuruciya ba kuma har yanzu da yake da damar neman ilimi kuɗi da mata sune a gabansa.


 Gwani ya fayyace mata hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa hakan yasa zuciyar Zainab ya ɗan yi sanyi.

Mama da kanta taje gidan ta tara matan Ale Faruƙ ta gaya musu saƙon Gwani akan duk wacce ta sake takurawa Zainab zai mugun saɓa mata. Yadda basa shakkan Tabawa haka suke tsananin shakkan Gwani.

Tabawa na zaune ƙofar ɗaki tana tauna goro ta fara faɗin "su matar Malam manya. Duk tsiyar ki dai Faruƙ ɗana ne. Idan Allah bai bashi ilimi ba ai ya bashi arziƙi" ...


Daga ranan kowacce mata ta karɓi girkinta.


Cikin Zainabu na wata bakwai Gambo wata maƙociyarsu ta fita daga takaba hakan ya sa Ale Faruƙ ya fito nemanta. Kamar kowacce mace arziƙinsa, kyaun surarsa da kuma gulmar ƙarfinsa da matan daya saka suke, shi ya kwaɗaita wa Gambo shiga gidansa, sai dai ta san mata huɗu gareshi.


Halime, Ale Faruƙ yai niyyan saka saboda ta kwana biyu a gidansa amma tunda ta masa rantsuwar duk ranan da ya saketa sai ta yanke masa gaba sai ya chanja tunani. Ba zai saki Iyani ba saboda itace uwar manyan 'ya'yansa sannan Fulani kuma ya rasa dalilin da yasa ya kasa sakinta. Kurma ce kawai zai iya saka a halin daya samu kansa sai dai kuma gaskiya bai shirya rabuwa da ita yanzu ba, har yanzu akwai ƙuruciya a tareda ita. Kuma ita kaɗaice macen da idan yace tayi abu za tayi idan yace ta bari ma zata bari.

Da dai yaga Alhaji Mato na ƙoƙarin kauda shi a wajen Gambo sai ya yanke ɗanyen shawaran sakin Zainabu.


Da sassafiya ya shiga ɗakinta ya miƙa mata takarda ya mata bayanin zata iya zama a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan har ta haihu.  Ba tayi boko ba shiyasa ko karanta hausar daya rubuta bata iya yi ba. Zuwa tayi wajen Jamilah ɗaya daga cikin yaransa wacce take da ɗan hankali tace ta rubuta mata abinda Ale ya rubuta da ajami. Jamilah ta rubuta mata kamar yadda ya rubuta da Hausa *na saki Zainabu saki ɗaya* bayan ta karanta rubuntun da Jamilar tayi a ƙasan na Ale, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauki takardar ta koma ɗakinta ta shiga haɗa kayanta. Zuwa ƙarfe sha biyu na rana ta gama tattara kayanta ta wuce gidan Inna Talatu. Ba zata iya komawa wajen Mama Asabe ba saboda a halin da take ciki wajen da zata samu kwanciyar hankali take nema.

A wajen Inna Talatu yar mahaifiyarta ce kaɗai zata iya samun wannan.


Haka kwanaki suka dinga tafiya har wata ranan Jumma'a ranan da cikin Zainabu ya shiga wata tara da kwana biyar ta haifi kyakykyawar 'yarta.

Suna dawowa daga Asibiti da ɗanyan haihuwa haka ta ɗauki 'yarta ta wuce gidan Gwani da ita haɗe da takardar da ta rubuta ranan da Ale Faruƙ ya saketa.


Gwani na alwalar sallar la'asar Zainab ta shigo ɗauke da jaririya a hannunta.

Tana zuwa gabansa ta ɗan rusuna sannan ta miƙa masa takardar hannunta.


Gwani da hankalinsa ya tashi da ganinta haka ya karɓi takardar yana ƙwalawa Mama kira.

Lokacin daya karanta takardar hawaye ya taru a idonsa. Tausayin ɗansa Faruƙ ya fi kamashi akan na Zainabu. Mama ta fito daga ɗakinta tana tambayar Zainabu yaushe ta sauka amma Zainabu bata kulata ba.

Gwani ya ajiye takardar ya ƙarisa alwalarsa sannan yai wa Zainabu alamar ta miƙo masa jaririyar. Zainabu ta miƙa masa 'yar.

Gwani yai wa yarinyar kiran sallah a kunnenta na dama sannan yai mata iƙama a kunnenta na hagu kafin ya gama Mama ta shiga ɗakinta ta ɗauko masa dabino, dake cimar Gwani ne ba a rasawa a ɗakinta.


Huɗuba yaiwa 'yar da suna Asiya Shahidah sannan ya shiga tofa mata duka addu'o'in da Zainabu ta rubuta a takardar data kawo.


Yai addu'ar kada Allah ya sa ta ɗauko ko ɗaya daga cikin halayen mahaifinta da ta kakarta Tabawa. Yai addu'ar ta zamo mai ilimi, mai tausayi, mai imani da riƙon amana. Yai addu'ar kada ta zamo azzaluma mai tauye hakkin mutane, yai addu'ar yadda mahaifiyarta bata ji bata magana Allah ya sa ta ji ta kuma yi magana. Yai addu'ar ta zama jaruma marar tsoro wacce akoda yaushe neman gaskiya da aiwatar da gaskiya shine halinta, yai addu'ar Allah ya kareta daga sharrin Mutane, Aljanu, Dabbobi da kuma Shaiɗan la'ananne. Yai addu'ar ta zamo abin alfahari ga iyayenta dama al'ummar musulmai gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa  yana addu'ar ta samu tabarakkin mai sunanta wato Nana Asiyah.


Bayan ya gama addu'o'in sannan ya karɓi dabino a hannun matarsa ya gutsura ya tauna sannan ya sakawa Asiya a baki. Sai alokacin Zainabu ta fara murmushi.

Ita da Mama ne suka koma gidan Inna Talatu wacce ta birkice saboda rasa Zainabun da akayi a gidan...



A gidan Gwani aka yi suna dan kwana huɗu da haihuwan ya nemi Zainabun ta dawo gidansa. Kunyar Baban tsohon mijinta ya sa bata iya musawa ba. Ale Faruƙ ma dai nauyin Gwani daya ji ya sa shi kawo rago da kuɗi dan a yi suna da shi.



***



Tun kafin Asiya ta cika shekara biyu Inna Talatu ke yiwa babban ɗanta mai suna Nuhu kwaɗayin ya auri Zainabu. Matarsa ta farko ta rasu sannan Yahanasu da ya aura wacce ita ɗin 'yar dangin mahaifinsa ce sai ta kasance fitinanniyar mace. 


Shekarar Asiya uku aka yi auren Malam Nuhu Principal da Zainabu Kurma. Lokacin da Ale Faruƙ ya ji labarin auren baƙinciki kamar ya kashe shi, duk cikin matan daya rabu da su babu wacce yake jin rabuwar da ciwo kamar rabuwarsa da Zainabu. Ya rabu da Halime ita kuma Gambo data shigo gidansa tama fi Fulani fitina.


Malam Nuhu Gidaɗo Malamin makaranta ne da ya kai matsayin Principal inda yanzu yake shugaban makarantar Special School Congo.

Matarsa ta farko Hassana sati biyar da haihuwa ta rasu hakan ya sa rainon ɗansa Ubaydullah ya koma wajen 'ya uwarta Hussaina. Shekaru uku da rasuwan matarsa kafin Mahaifinsa ya haɗa shi aure da Yahanasu wacce take marainiya a lokacin.  

Lokacin daya auri Zainabu yaran Yaha uku ne duka mata. Aisha da suke kira da Ummi sai Fatima sai kuma Hindatu daga baya ne ta haifi Musa bayan ita Zainabun ta haifi ɗanta na fari wato Muhammad Habibu sai Lukman da suke kira da Gwani sai autanta Aliyu.


Sanda Zainabu ta tare ko wata huɗu batayi ba Malam Nuhu ya sata a makarantar kurame inda ake koya musu rubutu da karatu da kuma sana'o'i.  A nan ne ta koyi ɗinki da saƙa.


Asiya Shahidah ta taso ne tsakanin gidan Gwani da Inna Talatu bata zuwa gidan Mahaifinta sai dai idan shine yazo ya ɗauketa dan Allah ya saka masa ƙaunar Asiya. Saboda ita ne ma ya dage da zuwa gidan Gwani duk bayan kwana biyu maimakon da da sai yai sati biyu uku bai leƙa mahaifin nasa ba. A duk lokacin da ya zo idan yaji Gwani yana yabon kwanyar Asiya akan tana ɗaukan karatu sai ya dinga jin wani nishaɗi a tattare da shi. Duk yaransa a wajen Gwani suke zuwa ɗaukan karatu tun suna shekara biyu da rabi yake sawa a tisa ƙeyarsu wajen Mahaifinsa. Kuma duk cikinsu idan ka cire babban ɗansa Nafi'u daya rasu babu wanda ya taɓa ji Gwani ya yabi kaifin ƙwaƙwalwarsa kaman yadda yake yabon Asiya. Wani lokaci idan yazo sai ya ce Asiya ta ɗauko Allonta ta biya masa karatu ya ji. Duk da idan ka cire karatun sallah shi kam Jahilin Ƙur'ani ne hakan bai hana shi jin daɗin karatun Asiya ba.

 Allah ya buɗa masa arziƙi amma hakan bai hana wani lokacin ya ji kishin ƙannensa Malam da Zakari ba, wanda suma Malamai ne yanzu domin sunyi karatu mai zurfi.

Dake idan Asiya tazo gidan Ale Faruƙ damunsu take da rigima shiyasa basa ma son zuwanta gidan musamman Fulani da Tabawa. Bata taɓa yin shiru idan aka gaya mata magana.


Bayan Gambo tayi yayinta ta ƙare, lokacin maganinta ya dena ci, a lokacin ne kuma Ale Faruƙ ya lalubo musu wata mata mai suna Yawo. Daga chan wani ƙauye ta fito wanda ake yawan cewa ƙauyen akwai mayu a wajen.  Ba budurwa bace dan aurenta bakwai amma tacewa Ale Faruƙ aurenta biyu. A rumfarsa suka haɗu ta zo siyayya, farar fatarta ya ja hankalinsa.



Sati biyu da tarewarta Ale Faruƙ ya fara ciwo. Idan ya tashi da safe sai yaji duk jikinsa na masa ciwo musamman hannu da ƙafafuwansa. Tun yana iya fita kasuwa har ya koma zaman gida saboda ko bai fita ba haka kawai jikinsa sai ya dinga ciwo. Ya je Asibiti an bashi maganin ciwon jiki amma duk da haka abun ba sauƙi.

Ana hakane kuwa biyu daga cikin 'ya'yansa suka rasu mace da namiji dukkansu 'yan ƙasa da shekaru goma. Abin duniya yabi ya isheshi, rashin fita kasuwa kamar yadda ya saba duk ya saka shi damuwa dan gani yake baza a kula masa da dukiyarsa kamar yadda ya kamata ba...


A gindin wata bishiyar giginya wasu mata guda uku suka haɗu a talatainin dare. Cikon ta huɗunsu ta taho tana basu haƙuri akan dalilin rashin zuwanta taron nasu da wuri.


"Ni kam Yawo keda kike da nisa ya akayi kika rigani zuwa?" Wacce ta zo yanzu tayi tambayar tana kallon farar cikinsu wacce duk da kasancewar dare ne sosai farin fiskarta na haskawa.


Yawo tayi dariya tace "ai dokina shegen gudu gareshi.  Gashi chan na ɗaure shi a wancan bishiyar"


Matar ta juya ta kalli inda Yawo ta nuna mata sannan ta ƙyaƙyale da dariya tace "ashe zaki bani aronsa idan zan je taron mutanenmu da za ayi na ƙasa"


"A ina za ayi taron?"  Wata tsohuwa tukuf a cikinsu ta tambaya.


"Wancan shekaran anyi a Kaduna ne amma wannnan shekaran a Ogbomosho za ayi"


"Kai yayi nisa ba zan je ba" tsohuwar ta faɗa tana lashe baki ganin naman da aka kawo musu wacce jaririyar Gambo ce da ko wata bata cika ba.


"Kai! Yawo gaskiya aurenki da Ale Faruƙ akwai daɗi. Kullum cikin ƙoshi muke"


Yawo ta baza haƙora tana dariya tace " nan gaba naman wancan 'yarsa daya fi so zan kawo, nasan ba ƙaramin daɗi za ta yi ba"

Dukkansu huɗun suka bushe da dariya marar daɗin ji.


Washegari Asma'u 'yar Gambo ta rasu. 'Yarta ta biyu kenan a gidan Ale.


Da yamma Mama da Asiya da matar Baffa Malam suka zo ta'aziyya gidan.


Suna falon Gambo Yawo ta shigo gaishe da Mama. Suna haɗa ido da Asiya ta fara mata murmushi. Asiya ta ce " Maman Rabi'u ga wadda ta cinye miki Asma'u" gaba ɗaya sai suka maida dubansu ga Yawo da Asiyar ke nunawa.

Yawo ta kama salati tana salallami harda fashewa da kuka.


Mama ta kwaɓi bakin Asiya tace "bana son shegen surutu Asiya. A ina kika ji wannan banzar maganar?"


Asiya ta tura baki tace "in ta cinye duka 'ya'yan Baba ai shikenan, nikam bazata iya cinyeni ba"


Mama ta ranƙwasheta tace ta rufe musu baki. Sannan ta shiga bawa Yawo haƙuri.


Maganar ta tsaya a ran Mama shiyasa da suka koma gida tace zata  faɗawa Gwani idan ya dawo daga tafiya.


Ranan da dokin Yawo ya je Ogbomosho washegari Ale Faruƙ ya tashi ko yatsarsa baya iya ɗagawa. Yadda ka san wanda jikinsa ya shanye haka yake kwance a sanƙare ko'ina yana masa ciwo kamar anyita dukansa da taɓarya.


Bayan kwana huɗu da rasuwan Asma'u Gwani ya dawo. Da ya huta Mama ta gaya masa abinda Asiya ta faɗa, tareda faɗa masa cewa ranan da suka dawo, da dare Asiya ta dinga sunbatu cikin baccinta tana cewa babu wanda zai iya cin namanta.


Gwani ya ɗau Allo ya rubuta ayoyin shifa ya wanke da ruwan zamzam ya zuba a gora ya miƙe da kansa ya wuce gidan ɗansa.


Lokacin daya isa gidan kai tsaye sashin Ale ya shiga inda Ale Faruƙ ke shimfiɗe a kan tabarma a tsakiyar falonsa. Fulani da ɗansa Bello wanda shine babban ɗansa namiji ya gani a kusa dashi suna ƙoƙarin bashi kunu.


"Ya jikin nasa?" 


"Yau kam Malam ko hannunsa ya kasa ɗagawa" Fulani ta amsa cike da tausayawa mijinta wanda duk yadda yake tana sonsa a haka.


Bello ya taimakawa Gwani wajen bawa Ale ruwan rubutu. Bayan ya sha, Gwani ya karanto addu'o'i ya tofa a hannunsa  ya shafa masa a goshi, hannu da ƙafafuwansa. Da yamma ma yazo yai masa haka, washegari ma ya sake zuwa yai masa haka safe da yamma.


A rana ta uku kuwa da Yawo ta tashi hawa doki zata je majalisansu doki ya ƙi tashi, tayi tayi amma inaa ya ƙi ko matsawa gefe hakan ya sa ta haƙura da ɗaukansa. Da ta isa majalisa ta kai ƙorafin abinda ya faru wajen shugabarsu tsohuwa Ayya. Ayya tace ai mahaifin Ale Faruƙ ne ke shirin ɓata musu aiki kada ta bari ya sake zuwa wajensa. Naman Asiya ma da suke son ɗauka shima abin ya gagara shiyasa suka koma kan ƙanwarta Farida 'yar Halime wacce nan da kwana uku zasuyi abincin dare da ita.


Washegari ya kama kwanan Yawo dan haka ita ce ta kasa ta tsare a gefen Ale Faruƙ. Ƙarfe tara na safe sai ga Gwani ya zo yiwa Ale addu'a. Yawo ta garƙame falon da kwaɗo ta zauna a dakalin ƙofar shiga falon, yana zuwa tace masa Ale na barci yace kar a tashe shi.


Gwani yace ta buɗe masa ƙofa ya shiga ya dubashi ba zai tashe shi ba. Yawo ta tura baki tace sai dai ya dawo wani lokacin. Yadda ta dage ba zai shiga ba ya sa ya juya ya tafi, cikin ransa yana tunanin tabbas maganar Asiya gaskiya ce. Da yamma tareda ɗansa Malam suka zo, nan ma a ƙofar falon suka tarar da Yawo tana zaune daram kamar da safe. Wannan karan sai da Iyani da Fulani suka leƙo suna cewa Yawo ta buɗewa Gwani ƙofa domin tunda ya fara yiwa Ale addu'a suka fara ganin sauƙi.


Tana cikin magana Malam ya fito da wata dorina ya tsura mata a jiki yana faɗin "ƙarya kike la'ananniya, ƙarya kike Mayya"

Yawo ta saka ihu tana kuka.

 "Kin cinye masa 'ya'ya za ki cinyeshi ko? Asirinki ya tonu" ya cigaba da zaneta. Ƙoƙarin gudu take amma Gwani da sauran Matan da yaran Ale kusan biyar sun tare wajen sun hanata gudu. Bello ma daya shigo bada jimawa ba itace ya sunkuco ya shiga taya Baffan nasa dukan Yawo.


Sai da Gwani ya tsaida su kafin suka dena dukanta. Ya tambayeta ta faɗa musu gaskiya. Yawo baki da hanci duk jini ta fara cewa ta tuba a yafeta.


Baffa Malam ya daka mata tsawa hakan yasa ta fara faɗan abinda tayi tace da gaske ne ita ta cinye yara uku a gidan amma Ale Faruƙ doki take da shi bawai cinyeshi zata yi ba.

Tabawa da ke gefe tayo kan Yawo da gudu ta fara dukanta tana yaguni. "Shegiya ɗan nawa shine doki, ɗan nawa kika mayar doki"

Da ƙyar Baffa Malam da Bello suka janyeta akan Yawo.


Gwani yace su ɗaureta kar wanda ya sake taɓata amma ina, samarin anguwa sukace basu yarda ba aka fita da Yawo ana bugu. Lokacin data suma aka fara ƙoƙarin ƙonata saiga wata tsohuwa ta ratsa cikin mutane ta zo ta taɓa Yawo shikenan ita da Yawo suka ɓace. Mutane  kowa yai ta kansa sai 'yan tsiraru da suke da ƙarfin zuciya suka tsaya suna ihu suna faɗin duk ranan da suka kama Yawo ko wani maye ko mayya a garin ƙonashi za suyi.


Kwana uku da aka cigaba da yiwa Ale Faruƙ addu'a ya warke sarai kamar ba shi ba. Lokacin da yaji labarin cewa Asiya ce ta fara gane cewa Yawo Mayya ce hakan ya sa shi dagewa Gwani akan sai dai Asiya ta dawo gidansa da zama. Gwani bai musa ba tunda dai 'yarsa ce ya dai jaddada masa akan koyaushe Asiya ta dinga zuwa karatu.


Bayan Yawo sai da Ale Faruƙ yai shekaru huɗu kafin ya ƙara wani auren.

No comments