Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 39-40

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 39 & 40




'kwafa Muzanbil yayi yafita afusace cikin matsanancin tashin hankali Arfat take safa da marwa cikin parlour ta tarasa abinda yakeyimata dad'i dede lokacin mu'azzam yafi cikin shirin fita hospital  cikin sauri tasha gabanshi fuskarta d'auke da matu'kar nadama cikin muryar lallashi tace 


" haba doctor  kaifa mai afuwane kuma zuciyar ka mai tausayice katausayamin wallahi  zuciyata gaf take data tarwatse dan Allah  Doctor  kayimin afuwa wallahi ayanzu duk duniya babu wanda zuciyata takeso kamar kai karka horani da fushin ka a gareni bazan iya jurar hakan ba dan Allah kayafemin nayi al'kawari bazan sake aykata kwatankwacin hakan ba kaji my everlasting darling " 


Sosai yaji shigar kalamanta cikin zuciyar shi amma yayi saurin dannesu tsaki yaja yakauce daga gefanta yayi ficewar shi bin bayanshi tayi da kallo tanajin wani irin ba'kin ciki cikin zuciyar ta fad'awa tayi saman cushion  tasaki kuka mai tsuma zuciya  


Rayhana tana isa cikin parlour Momy  ta iske Muzaffar  zaune cikin sauri ta dur'kusa gaban Momy  tace 


" barka da hutawa uwar kirki ha'ki'ka samunki amatsayin uwa babban rabone ina sauran iyaye kuyi koyi da halin Momy na ina matu'kar godiya gareki tabbas ada nacire burin cigaba da karatuna amma segashi Momy kin cikamin mafarkina Allah yasakamiki da mafificiyar aljannah "


Juyawa tayi kan Muzaffar tace 


" dadyn Farooq kagani Momy  tasa burina zai cika katayani yimata godiya "


Mi'kewa Muzaffar yayi yazura hannun shi cikin aljihun wandan shi yace " tayaya keda mahaifiyarki harse wani yatayaki yimata godiya nakima kad'e ya'isa " maida duban shi yayi kan momy yace " to amma Momy  yaran fa ina ganin tabari seta yayesu kamar zaifi ko ? "


Murmushi Momy tayi takamo Rayhana tazaunar da ita kusada ita tace 


" yara bazasu hana Raihan karatuba sekace babu hadimai kuma naga ay ana had'amusu da madara ko ? " jinjina kai Muzaffar yayi yasake cewa " hakane amma sede tad'inga saka babban hijab da ni'kaf da safa idan bazatayi hakanba sede tafasa " 


Daga haka yasake yafita fuskar shi a tamke cikin damuwa Rayhana ta kalli Momy tace " amma momy senike ganin kamar baya bu'katar wannan karatun nawa idan har bayaso zan ha'kura Murmushi Momy tayi tad'an bubbuga bayanta tace " bahakabane Raihan shi Muzaffar haka halinshi yake baka gane mishi alokaci d'aya amma bawai bayason karatun ki bane kishi ne kawai " 


Saurin kallon Momy tayi sekuma ta du'kar da kanta sake bubbuga bayanta tayi tace " kinayin mamakine ? to kibari tunda yashigo maganar mukeyi amma yanata kawomin wasu dalile wanda suke nuna kishin ki afili kuma ayanzuma kinji idan baya kishin ki bazai damu dan wasu sun kalli surar jikinki da fuskarki ba dan haka karki damu ke dai kizama mai kiyayewa skul d'in su Zarha ne nasan zakifi sakewa idankuna tare yayan ku Ibrahim shi yacike miki komi acewar shi yasan ra'ayin shi zaizo d'aya danaki se kiduba kigani "


Sosai Rayhana tayi farinciki amma cikin zuciyar ta tanata nanata wannan kalmar " kishi ni Muzaffar yake kishi to bana 'karyata Momy ba amma dakamar wuya dan kawai Momy  batasan auran yarjejeniya mukayiba shiyasa nasan yayi hakanne dan takurani badan kishi ba amma ace 'katon hijab da ni'kaf ga safa lalle zafima kad'ai ya'isa yatakura rayuwata amma hakanan jan jure Allah yabani iko " sallama tayima Momy  tafito part d'in kaka tanufa shiko Muzaffar yana fita cikin lambu yanufa zama yayi yanasake nanata " Skul Raihan hmmmm yazama dole nasamata mugun tsaro danna lura tanada matu'kar rawar kai "


Cikin fari'a Mubarak yaron kawu Yusuf yanufi cikin lambun inda Muzaffar yake hannun shi ri'keda Apple yanaci daga gefan shi wata hadima ce ri'keda tiran kayan lambu da lemon da Cup guda 2 sallama yayima Muzaffar yaja kujera d'aya yazauna cikin girmamawa yace " yaya barka da hutawa " d'aga mishi kai kawai Muzaffar yayi yaciro wayar shi yashiga latsawa tsiyaya lemon Mubarak yayi yami'kama Muzaffar  amsa Muzaffar  yayi ya aje janshida hira Mubarak yashigayi amma ko sauraran shi Muzaffar bayayi su kawu Yusuf kuwa suna daga nesa suna hangen komi sun 'kosa suga Muzaffar yasha cikin mamaki Rayhana tahangosu suna le'ke ahankali tanufi gurin dan ganin mai sukeyima le'ke zaro ido Rayhana tayi cikin sauri tanufi gurin 


dede lokacin Muzaffar  yad'auki Cup d'in lemon harya nufi bakinshi dashi sekuma yajanye yana sake maida hankalin shi kan wayar shi amma Cup d'in yana hannun shi sauri sosai Rayhana takeyi zuciyar ta tana wani irin bugu tana isa daf dashi yakai Cup d'in bakin shi cikin sassarfa ta'isa wata irin runguma takaimai wanda tayi sanad'in fad'uwar cup d'in hannun nashi 'kasa yatarwatse afusace yami'ke saurin sake rungumoshi tayi cikin 'kasada murya tace 


" kayi ha'kuri amma katuna bamu kad'ai bane kabri idan muka koma part d'inmu se kayimin hukunci bada sanina lemon ka yazube ba muje nahad'ama wani " cikin mugunta yarungumota fuskarta yakamo bakin shi yazura cikin nata yashiga yimata wani irin kiss namugunta ganin haka yasa Mubarak barin gurin bayan Mubarak yabar gurin Muzaffar yasaketa yana sauke numfashi ahassale yace 


" idan  kika sakeyimin irin wannan to kisani senayi miki abinda baki ta'ba zataba " barin gurin yayi rai 'bace itama barin gurin tayi tana ta'ba lip's d'inta dake zafi cikin 'bacin rai kawu Yusuf yari'ko Mubarak  mari yawatsa mai sannan yace 


" tur da'irin wannan abin wallahi da Nura ne datuni yasashi yasha amma kai kana zaune kana shashanci har waccan 'yar figigiyar yarinyar tazo talalata komi " rai 'bace Mubarak yace " gaskiya Abba nikam se yanzuma nike addu'ar gara dabai shaba sabida nace kusanar dani lemon nameye amma kun'ki sannan ance ni karnasha to tabbas akwai wani abu dan haka ni gaskiya kar akuma sani cikin irin wannan abun idan kuma naga wani abu yasami yaya Muzaffar tofa Abba sede kayi ha'kuri zanfad'i abinda  nasani sabida Allah baice nayimaka biyayya ba wajan aykata fasadi " 


daga haka Mubarak yabar gurin cikin mamaki kawu Yusuf yabishi da kallo ajiyar zuciya waziri yasauke yace " dama kasan bazai bada had'in kai ba amma kasashi to ay yanzu gawata matsalar nan munsake shiga tunda yace idan wani abu yasamu Muzaffar seya sanar mune hmmm abubuwa de se 'kwa'bewa sukeyi yaya zamuyi "  dafashi kawu Yusuf yayi yace " karka damu dazancen Mubarak nasan yadda zanyi dashi kusa ad'auke wancan lemon  karwani yasha asirinmu yatonu " daga haka kawu Yusuf  yabar gurin harara waziri yabishi dashi yace " banza kawai sefama samu abuyakeyi amma har yanzu babu wata nasara se fad'uwa hmmm zanyi maganin ka idan abin ya'isheni wallahi " 


Misalin 11:40pm Rayhana  tanufi part d'in Ummi  zaune take tana kallon TV  babu kowa cikin parlour  se ita'kad'e yara duk suna cikin bedroom  wasu sunyi bacci wasu sunata chanting cikin waya Rayhana tale'ko ganin ita 'kad'ece yasata sauke ajiyar Zuciya  nannad'e paper tayi tawurgo mata cikin sauri Ummi tami'e waigawa tayi amma babu alamar kowa cikin sauri da rawar jiki tabud'e parpar tun kafin ta'karasa karantawa zufa taji'keta shakaf dukda sanyin A.C dake cikin parlour  duk Rayhana tana kallon ta cikin karfin hali Rayhana tashiga cikin parlour  ganin mutun cikin fararan kaya yasa Ummi bud'e baki zatayi ihu cikin sauri Rayhana  tajawota rufe mata baki tayi sannan  tasha'ke mata wuya tashiga furgitata sabida tsananin tsoro yasa ummi sumewa cikin sauri Rayhana  tasaketa tafita part d'in mami tanufa adede lokacin  suna zaune su biyu itada umma suna tattauna yadda zasu billoma wannan al'amarin dankam suna cikin tsoro wurga paper tayi cikin mamaki 

 Mami tace " wannan kuma daga ina?  kode iskace takawota " arazane umma tami'ke tace " ina garinda babu hadari taya iska kuma " d'aukar papar tayi tabud'e tare suke karantawa saurin ri'ke cikinta mami tayi sabida wani murd'awa dayayi cikin shihada Rayhana tashigo parlour  sandar hannunta tad'aga tace


" duk wanda yayi ihu to tabbas yau zamutafi tare dashi dan haka kusanar dani yadda kuka shirya kasheni idan kukayi haka zanbarku natafi amma idan  kuka'ki to babu shakka tare zamu tafi kunga de irin halinda kaka tashiga to nata mai sau'kine tunda babu hannunta cikin kisan sede 'kiyayyar datake yimin ina yarana ? Cikin razana Mami tace " Wallahi babu hannuna cikin sace yaranki Ummi ce da umma suka shirya haka kuma suka aywatar haka kisanki banibace d'anane Nura yayi yayi kibashi had'in kai kin'kin shine yayi miki fayd'e ganin idan yabarki zaki tonamai asiri yasa yakasheki amma ni babu ruwana sede nasashi yagudu " cikin  raunin murya Rayhana tace yana ina ? yana cikin India kefa Umma ina yarana ? murya sha'ke tace " Allah bamu kashesuba amma munyi nesa dasu mun kaisu cikin wani daji dayake cikin 'kasar Cameroon amma Allah duk Hamdiyya ce tashirya hakan jin 'kamar motsin tafiya yasa Rayhana  saurin cewa 


" kuyi gaggawar sanarda maimartaba komi da Mijina Muzaffar idan bahakaba to zandawo kuma idan nadawo kasheku zanyi cikin tsoro " Rayhana  tad'ago agogon hannunta tayi magana 'kasa 'kasa yaya Ibrahim akwai matsalafa ana shirin shigowa gashi zanfita saurin tashi yayi yafita  dede lokacin da Jafar yashigo cikin parlour  lokacin mami tasaki ihu kuma dede lokacin wutar cikin masarautar  tad'auke duka aguje Rayhana tafita tana isa cikin part d'insu tashiga bedroom d'in Nabila toilet  tashiga tana sauke ajiyar Zuciya  sedata numfasa sannan tafito dede lokacin Muzaffar  yashigo tamke fuska yayi yace 


Tun d'azu nike shigowa cikin bedroom d'in nan amma sede najiki cikin toilet  ko mai kikeyi cikin shi har yanzu  ? seda kikaga wuta tad'auke sannan kika fito ajiyar Zuciya tasauke dajin bai san bata cikin part d'in ba cikin 'karfin hali tace 


" ina ruwanka da zamana cikin toilet  ? naga babu wani amfani danike dashi agareka tun safiyar yau kake wani shareni toya kakeso nayi nalura bakason ina shiga cikin hurumin ka  dan haka daga yau nadena shiga kuma kuma kasani nakusa barma masarautar ku sabida aykin daya had'amu yakusa rabamu ayanzu mungano wa'inda suka kashe Nabila  da 'batar da yaranka dan haka kashirya sakina daga yau natashi daga 'kar'kashin ikonka bakada hurumin takurani kuma auran yarjejeniya ya'kare daga yau " 


Gefan shi tabi tabar bedroom d'in parlour takoma tazauna tana kuka mai tsuma zuciya  dede lokacin wutar gidan tadawo cikin mamaki yaya Ibrahim yake maimaita " auran yarjejeniya kuma Muzaffar da Raihan to su Shureem kumafa kay a'a " part d'in yanufa kai tsaye 


A'bangaran ummi kuwa fitowar yarta daga bedroom yayi dede da farkawarta cikin ihu tana ambaton Nabila kiyi ha'kuri dan Allah karki kasheni nayi Al'kawari zandawo miki da yaranki dandanan sauran 'yayan suka furfito idanunta arufe amma se bama Nabila ha'kuri takeyi tana fad'in yadda tasa aka sace Farooq da haidar dan danan parlour yacika a'bangaran su mami ma haka abin yake cikin tashin hankali maimartaba yami'ke dajin wannan labari sawa yayi aka tattarasu cikin parlour kaka yaransu da manyansu ganin babu Muzaffar yasa maimartaba ayka mu'azzam kiran su jin kiran yasa yaya Ibrahim barin maganar dake cikin shi har zuwa bayan amsa kiran maimartaba  cikin bedroom Rayhana tashiga wannan zoban ta d'akko had'ida kayan sanyin dake jikin su Haidar lokacin data tsincesu jin maganar wannan aljanar tayi 


" Rayhana lokacin barinki cikin masarautar nan beyiba domin akwa wani kullin nadaban bayan wannan sannan yin karatunki yanada matu'kar amfani dan haka karki sake kibari kibar gidan yanzu kisan abinda zaki fad'a idan kinje cikin taron sannan karki sake kice auran yarjejeniya kukayi keda Muzaffar ki kiyaye shiko Muzaffar fita yayi shida yaya Ibrahim  yana jinjina karfin halin da Rayhana tasamu da 'kwarin gyuwar fad'amai magana sedata dakko yaran tagoya daya ta d'auki d'aya sannan tafita nishi kawai takeyi sabida duk sunyi bacci nauyinsu ya'karu


tana shiga Momy tayi saurin tashi ta amshi Sudees  tana fad'in " mai makon kibarsu cikin bedroom tunda bacci sukeyi "Murmushin 'karfin hali Rayhana tayi tace " ina gudin karsutashi suyi kuka " jinjina  kai Momy tayi tana sakin Murmushi gyran murya maimartaba yayi yayi addu'a sannan yafara dacewa 


" wani tashin hankali yashigo cikin masarautar nan naganin fatarwar Nabila  jiya mama tagani yau kuma su Hamdiyya har su 3 hakan yana nufin cewa Nabila tanason ayimata adalci to amma Allah yana ganin yadda muketa faman yin bincike akan gano wanda yayi kisan amma har yanzu shiru yaranma har yanzu ko gawarsu bamu samu damar ganiba to amma abin mamaki yadda wa'innan suketa wasu maganganu kamar sunada hannu wajan wannan lamarin ko gaskiya ne ko furgicine oho " cikin sauri Ummi tace 


" furgicine kawai maimartaba fatalwa fa ? " cikin sauri suma su mami sukace haka Murmushi yaya Ibrahim  yayi yami'ke yace 


" Allah ya'karamaka lafiya inada magana sannan inaso kowa ya kalleni a matsayin jami'i na musamman  ba Ibrahim ba sannan inaso kowa yasaurari wannan d'aukar " kunnawa yayi tuni maganganun su suka fito ras cikin tashin hankali Ummi tami'ke zata 'karyata Rayhana tami'ke tace 


" Allah yataimakeka nima inaso abani dama nayi magana " jinjina kai maimartaba yayi kunna wani recorder tayi cikin wayarta lokacin da ummi da umma suke magana akan wannan box d'in sannan tace kowa ya kalli wannan  zoban " cikin sauri Muzaffar yami'ke ya amsa yace " wannan ay zoban Nabila ne " Murmushi Rayhana tayi takwance ledar hannunta taciro kayan sanyin Farooq da haidar tace " ko akwai wanda zai iya gane wannan  kayan mi'kewa momy da Aunty Sumayya sukayi sukace " tabbas wa'innan kayan Farooq da haidar ne nice nasamusu su aranar " 


Jinjina kai Rayhana tayi tace " to inaso kowa yasani Sudees da Shureem sune Farooq da haidar idan har kuna tantama kuduba tabon dake jikinsu nice natsince su cikin wani daji dake 'kasar Cameroon kud'in da akasa cikin box d'in sune sukasa nasan 'kasarda yaran suke ciki hakan yasa nasha alwashin had'asu da iyayensu se Allah  yabani sa'a nahad'u da Mahaifin su a Pakistan nakuma gane hakanne sabida tsananin kamarsu dakuma irin zoban dake hannun shi naga iri d'ayane dana cikin wannan box d'in tabbas ni 'ban ta'bayin aureba balle har nahaihu amma su Farooq  sukasa nazama tamkar matar aure wadda ta haihu nabi hanyoyin dazansa ruwan jikina yakawo danna shayar dasu sabida Allah ya d'auramin 'kaunar Farooq  da haidar  nakuma samu nasarar haka dukda ina had'a musu da madara amma ina shayar dasu har yanzu nashigo cikin masarautar nan amatsayin 'kanwar Muzaffar  amma nidashi kawai mukasan haka dan mugano wa'inda suka kashe Nabila  amma babu ala'kar aure a tsakanina da yaya Muzaffar  to Alhamdulilh tunda angane gaskiya zankoma 'kasarmu dukda banida kowa nacigaba da ri'ke marecina tabbas zanyi kewar yarana Farooq da haidar " 


Kuka Rayhana tasaki cikin mamaki Muzaffar yake kallon Rayhana amma yakasa furta komi tashi Momy tayi tarungumo Rayhana tace " babu inda zaki Raihan  kinadani dan haka bakida marayci kuma bazaki rasa su Farooq ba zan ri'ke'ki tamkar Zarha nizan aurar dake ga mijin dakika za'ba da kanki zanbaki rayuwa ingantacciya dan Allah  Raihan ina ro'konki daki zauna gurin Momy ki dan Allah  " 


Ri'ke hannunta Rayhana tayi tace " kibar kukan Momy na ha'ki'ka ked'in uwace kuma nayi al'kawarin cigaba dazama dake amatsayin 'ya kuma mai biyayya agareki nagode da wannan  kyautar yaya Muzaffar  ina matu'kar godiya agareka sanadin ka nasamu uwa da uba harma da yayye musamman big brother na yaya Ibrahim  " 


Cikin farin ciki maimartaba yace 


" tabbas kincika 'ya Raihan Allah yayi miki albarka  mungode ma Allah daya nunamana munafukan cikin masarautar HAYAT  kuma za'ayima kowa hukunci dede da lefinshi Ibrahim  Muzaffar Mu'azzam  da kai Muzanbil inaso a kawomin Nura duk inda yake asafiya gobe sukuma su Hamdiyya  akaisu cikin kurkuku a ajesu kafin karbar hukuncin su dole naji cikakken bayani daga Nura naji mahaifiyar shice tasashi ko ra'ayin kan shine  "


Kuka sosai sukeyi cikin kuka Hamdiyya tace " kayimin afuwa maimartaba tunda gasu Farooq d'innan babu abinda yasamesu " wani irin kallo maimartaba yayi mata ita kuwa Mami ri'ke 'kafar mijinta tayi wato Yusuf  tace 


" kana gani za'a kaini kurkuku wannan ay abin kunyane abban Nura " cikin fushi ya kalli kaka yace " haba mama kiyimai magana mana " murtuke fuska kaka tayi tace " lallema Yusuf wato nagoyi bayan zalunci ko kunaganin yadda aka furgitani wajan bincike to sune baza'a hukuntaba sabida sunfi kowa nikam ama fitarmin dasu daga parlour  " 


barin gurin kaka tayi shiko kawu idris cewa yayi '" tur da irin wannan  halin kowa ya aykata to shima a aykata mai dan haka nima babu ruwana sosai samha da Arfat suke kuka ganin iyayen su cikin wannan halin itako arfat sake shiga tetayinta tayi d'aukar Sudees Momy tayi itakuma Rayhana  tad'au'ki Shureem suka nufi part d'in Momyn tashi kowa yayi yabar parlour masu farinciki sunayi masu ba'kinciki sunayi har kowa yabar parlour  amma shi Muzaffar yakasa tashi yarasa wane irin tunani zeyi


Ganin yarasa mafita yasa yami'ke yanufi part d'in Momy  cikin mamaki Momy  tace 


" lafiya Muzaffar ? kaje ka kwanta kayi ha'kuri addu'a zakayi ma Nabila kuma kagodema Allah daya bayyana gaskiya  Allah yadawo maka da Farooq da haidar  cikin 'koshin lafiya  gaskiya  kayima Raihan godiya akan wannan  jahadin datayi maka zanbama Raihan kulawa tamkar nice na haifeta Allah yanunamin auran ta zanyi mata gata wadda ko Zarha banyi mawaba " 


zama Muzaffar yayi dankam shi yayi matu'kar mamakin furucin Rayhana  na nuna babu aure a tsakanin su tuna lokacin datake bama Shureem nono yayi cikin zuciyar shi yace " dukda ba itace mahaifiyar suba amma ta'iya shayer dasu ashe bata ta'bayin aure ba ? amma ta'iya jure munanan kalamaina akan haka yaya zanyi kenan ? " 


Mi'kewa yayi yace " Momy tana ina zamuje mu kwanta ne " cikin mamaki Momy tace hakan bazai yiyuba Muzaffar kwana cikin bedroom d'aya ya haramta kai da Raihan tunda ba matar kabace wanda yafaru abaya dan banida msaniyar hakan ne shiyasa daga yau Raihan tana nan tare dani itada yaran ka " 


Cikin takaici Muzaffar yace " Momy duk abinda Raihan tafad'a gaskiya ne amma banda abu d'aya Raihan matata ce bawai 'kanwaba kamar yadda tafad'a tun damuka shigo cikin masarautar mu akwai aurena akanta sannan nima se yau nasan Farooq da haidar sune Shureem da Sudees  Momy kitasota muje mu kwanta dare yanayi kumani bazan iya kwanciya babu su Farooq ba " 


Jinjina kai Momy  tayi tace " lalle ma Muzaffar  idan son Raihan kakeyi to kasanar dani amma bazan yarda da wannan maganar takaba inada tabbacin  Raihan bazatayimin 'karyaba maiyasa bakafad'i hakanba cikin taron jama'a kowa yaji se yanzu kasanar dani sonta kakeyi senaji ra'ayinta idan ta amince da kai shikenan amma seka jira ta kammala karatu "

girgiza kai Muzaffar yayi yace " har yanzu banajin son Raihan amma ina bu'katar zama tareda ita sabida su Farooq  nine yadace tazauna dani  Momy  bawaniba kodan yarana sabida ayanzu ita suke kallo matsayin uwa kuma banaso susan ba itad'in bace dan karsu d'andani zafin maraici nine yadace Momy Allah Raihan matatace "


Wani irin kallo Momy tayi mai tace " kafita idona Muzaffar  banyarda da zancan kaba se idan Raihan ce tasanar dani haka koda hakane to babu shakka senaji nakuma yarda cewa tana sonka kuma kaima kana sonta bazan bayar da Raihan ga wanda bayason taba ko ita bata son shiba dan haka kar in sakejin kace Raihan matar kace karka hana masusonta zuwa kaji nagayamaka zaka iya shiga ka gansu dan darajar yaranka suna bedroom d'in Zarah kafin zuwa gobe agyra mata wancan bedroom d'in na Sumayya dukda baiyi komiba amma andad'e babu wanda yashiga yakamata a gyara shi 10 minutes nabaka sabida zan kwanta " 


Daga haka Momy tabar parlour cikin bedroom tashiga cikin takaici Muzaffar yanufi bedroom d'in rai 'bace yana shiga yasameta zaune tanabama Shureem nono  wani irin tsaki yaja yace 


" kitashi muje kisanar da Momy  cewa akwai aure na akanki muje mu kwanta inajin bacci " kallon shi Rayhana tayi cikin rashin nuna tsoro tace " ayni jira nakeyi kabani ta'kardar saki sabida nasan kai baka 'karya al'kawari kuma dama yarjejeniyar tamu zata 'karene daga angane gaskiya dan haka bazan iya cigaba dazama da wanda babu kowa cikin zuciyar shi se wadda bata raye zan cigaba da shayar maka da yaranka sabida darajar Momy harsu isa yaye nikuma bayan nagama karatu naza'bi miji dede da ra'ayina kai kuma kanemi babbar mace kabar yarinya 'karama "


Cikin matsanancin 'bacin rai yace " idan kuma na'ki sakin nakifa zakiyi aure da aurena akankine ? kuma kibar shayar dasu Shureem haka sabida bana bu'katar breast d'inki su canza daga na budurwa ayanzu zasu iya rayuwa da madara sabida sun kusayin shekara ki shirya sanar da Momy  gaskiya zuwa gobe dasafe " 


Kwantar da Shureem tayi tace " ba dai maganar auran muba karabudani cikin sirri kamar yadda muka shirya komi cikin sirri na auri wanda raina yakeso nagode ma Allah dayasa babu abinda yashiga tsakanina da kai balle nazauna da kai dole kum......... " 


Kanta yayi cikin zafin rai yace " to bari wani abin yashiga senaga dame zakiyi tun'kaho hawa yayi saman bed d'in yajawota jikin shi cikin sauri ya kwantar da ita yarufamata baya yana shirin rabata da kayanta jin maganar Momy yasashi saurin sauka daga bed d'in shigowa Momy tayi wani irin kallo tayimai tace fita zan kulle part d'ina seda safe 10 minutes  nace amma gashi har kusan 20 "


rai 'bace Muzaffar  yafita yana isa cikin part d'in shi ya iske Mu'azzam  tasowa Mu'azzam yayi yarungume shi yace 


" natayaka murna d'an uwana sannan nazo neman alfarmar ka kasan ance bari yahuce shike kawo raban wani inaso kayimin jagora wajan auran Raihan nasan zatafijin maganar ka sabida kai tafi sani kaji dan....... " 


Turashi Muzaffar yayi cikin zafin rai yanunashi yace " wallahi  idan kasake zuwamin da irin wannan maganar senayima abinda zakace anya kuwa ni d'an uwan kane ? fitamin daga part " 


'Daga 'kafad'a Mu'azzam yayi yace " ok kabarshi zannemi soyayyar ta batare da taimakon kaba " daga haka yasakai yafita cikin 'bacin rai Muzaffar yashiga yin watsi dakayan cikin parlour cikin wani irin yanayi yashiga cikin bedroom  toilet  yanufa ruwa yasakar ma kanshi cikin zuciyar shi yace 


" zanyi maganin ki Raihan idan baki fad'i gaskiya ba hmmmmm har kinja anfara kawo miki hari lalle zanyi maganin duk wanda ya ra'beki "



Daga Al'kalamin.....🖊


NPEEDY A AJI🌸🦚🌸


Comments and shine please

No comments