Breaking News

SAI A LAHIRA 30

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 30*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*



RAYUWAR SU

Siyama da baby kaduna





........ goggo Hime ta rungumi yaran da zuciyar ta guda Daya tuni suka Saba da mutanen da suka bude ido da su har suka zamo Yan gida inda Kuma Allah ya kaddaro auren badariyya da Khalil Wanda Azumi ta Kara dorawa Hime jakar tsaba inda hajiya Azumi tace su dawo gabanta su zauna inda lamis yace Bai yarda ba kasancewar can kaduna Khalil din ya samu aiki don haka aka bashi gida cikin gidajen ma aikata inda Azumi ta kyale ba don taso ba


***** ***** ***** ***

    KWANCI  TASHI


Kwanci tashi asarar me Rai tuni  baby da siyama suka girma suka zamo Yan mata masu tsananin kyau da cika ido kowanen su kyawunta na musamman ne baby black beauty yayin da siyama ta zamo farar mace alkyabbar mata. Sai dai halin su ya banbanta. Baby akwai Isa da izza ga yauki da Jan aji ga tsiwa da son fantamawa.

Yayin da siyama ta kasance mace me sanyin hali da kawaici da Al kunya hakuri da kawar da Kai.

********************

Siyama ta leko daki ta hango baby gaban madubi tana ta faman fente fuska tana kwalliya.


"Anty baby mun fa kusan makara kin Kuma San idan muka makara ba za abarmu shiga ba. Ta juyo tana kallon ta a sheke.

"To sai menene in mun makara? Idan sauri kikeyi ki tafi ko na daure Miki kafafune ? Goggo ta leko dakin "Wai Ashe baku tafi ba siyama"?

"Eh goggo Wai kwalliya takeyi....

Wace irin kwalliya Kuma ? Fito wallahi ko in iskeki adakin Nan

Goggo ta korota ta fito suka Isa makaranta inda baby ke can baya ita da kawarta humaira suna ta fira tamkar ba a cikin makaranta suke ba har dai malamin da ya shigo ya fidda su waje saboda sururun su da aka tashi ma baby tace motar gidan su humaira zata shiga ayi Mata  lift inda siyama tace ita Kam zata taka a kasa

Humaira tace itama ta shigo ai sun Zama daya ba don taso ba ta shigo suka taho 

Goggo tayi faten tsaki inda baby tace ita Kam wallahi tafi karfin fate don haka ta ciwo bashin indomi wurin danladi tazo ta girka. Inda Kuma baba shitu ke sangarta baby duk abinda take so sai yayi Mata sai dai in bashi da ikone.


Baby Allah yayi Mata farin jini duk in ta fita sai ta dawo da Wanda zai biyota  yace Yana so yayin da siyama kuwa kwarjinin ta ke sawa ana shakkar ta ko da an nufota da batun soyayya zata bawa mutum hakuri tace karatu take. yayin da kuma  zuciyar baby cike take taf da buri da Kuma kwadayi inda take fadin wallahi ba zata taba auren 

Talaka ba sai babbar harka don haka in dai ba ka da kudi to tafiyar ku ba zata zo Daya ba in ma bakayi sa a ba ta gurza maka Rashin mutunci. 


Wata Ranar asabar ta nufi gidan su humaira inda napep tayi wahalar samuwa inda wata katuwar mota seaner tafaka agabanta inda tayi sauran dauke kanta inda me motar yake Mata sallama  ta share shi inda yace ta shigo  ya kaita. Ta dube shi tana yamutse fuska"na sani ko Dan yankan Kai ne Kai? Yayi murmushi "Ai ko Ina yanke Kai ba Zan yanke Kan kyakkawa kamar ki ba.

Ke dai shigo in Kai ki inda Zaki 

Ta bude motar ta shiga inda Wai ta ke fadin wannan direba Bai kyauta Mata ba.


Suka hau hanya inda yake tambayar ta Ina zai kaita? Ta ce malali zai kaita inda suka iso malali   ta nuna wani tsararren gidan da Bata San me shi ba tace Nan zata shiga inda ya shiga har cikin gidan inda take fadin ya sauketa awaje don kar karyar ta ta Kare sai dai tuni ya faka motar inda wata Mata ta fito da Shirin ficewa tagansu

"Marhabin lale da Dan kane yanzu kake tafe? Wata kunya ta Kama baby tamkar ta nutse akasa Ashe Ramin karya kurarrene

Ta dafa kafadar baby 

"Kar dai matar ce ka kawo min?

To ku shigo.

Baby tayi tsamo tsamo lallai karya fure take ba ya ya'ya ba

Suka shiga inda matar ta kawo Mata ruwa da lemu inda baby ta kasa sakewa inda matashin ya  ke Mata murmushi Wanda ta Gane na keta ne. Inda tayi sa a aka Kira wayar shi yace zai je ya dawo inda ya bada ajiyar ta wurin antin shi. Yana fita matar tace zata Dora Mata girki tunda wuni zatayi. Inda dabara ta fadowa baby tace zata shiga Nan bayan gidan su ta dawo

Matar tace to Bari inzo in rakaki don amanar ki aka bani....

"A a anty yanzu fa Zan dawo. Da haka tafice daga gidan tana Wai waye inda ta tsaida napep ta fada tana fadin "sa wuta malam don Allah Kara wuta wuta sallau. Aiko me napep ya sa wuta har ya kawo ta kofar gida inda ta sauke ajiyar zuciya "Kai Allah ya tsinewa karya tunda iya karta fure ba ya'ya.....

No comments