SARAN BOYE 40
No. 40
............Ƙarfe sha ɗaya na dare Yoohan da Solomon suka bar kano zuwa Abuja. Tafiyar da bata kulle awa guda ba jirginsu ya sauka. Sun iske guards ɗinsa tuni suna a airport ɗin ma, dan haka basu ɓata lokaciba wajen wucewa gida.
Kamar yanda yay tsammani
ya iske gidan nasu shiru, alamar duk sun kwanta, madam Chioma kawai suka iske a
falo zaune cikin kwalliyar riga da wando da sukai mata ƙyau sosai. Yanda ta
zubamasa ido haka shima kallonta yake babu yabo babu fallasa. Cikin takun nasa
ya ƙarasa gareta, itama sai ta miƙe tana mai buɗe nasa hannayenta alamar yazo
gareta.
Gabanta yaje ya tsaya batare da
ya shiga jikin nata yanda ta buƙata ba. Ya kamo hannunta ɗaya yana ɗan shagwaɓe
fuska kaɗan. Cikin sanyin muryar da tabbatar da agajiye yake, da yarensu yace,
“Mom na girma ni”.
Ɓata fuska tayi itama
cikin wani yanayi, muryarta na harɗewa wajen fita tace, “Please my boy”. Karan
farko ya saki lallausan murmushin da ya nema sumar da ita a wajen. Ya ɗora
hannunsa na haggu saman tattausan sajensa ya shafa yana ɗan kauda idonsa daga
gareta zuwa ƙafar benen dake a falon inda Miracle ke tsaye cikin kayan barci,
ƙirjinta rungume da madaidaicin teddy bear ta wani kafesa da idanu tamkar zata
haɗiyesa ta huta.
A hankali ya janyesu gareta yay
wani luuuu da su kamar zai rufe sai kuma ya buɗesu yana sakin hannun Mom yaja
baya. Hannayensa duka biyu ya ɗaga mata da faɗin “Sweet mom gudnit”. Kafin tace
wani abu harya fara hayewa upstairs ɗin da ɗan sauran kuzarinsa batare da ya
sake duban Miracle ba ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Su duka da kallo suka bisa harya ɓacema
ganinsu, mira ta share ƙwallar data cika mata idanu ta juya da gudu zuwa ɗakin
barcinsu ita da joy. Wata malalaciyar harara Mom ta raka Mira da ita. Kafin ta
taune lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi zuciyarta na ƙuna fiye da yanda gangar jikinta
ke tsuma.
Yoohan daya iske ɗakinsa
kamar yanda yay fata komai fes bai wani zauna ba ya shige toilet. Bayan wasu
mintuna masu ɗan tsaho ya fito jikinsa na ɗigar da raɓar ruwan wanka. Da sauri
yaja ya tsaya ganin Mom zaune bisa sofa. A ɗan daburce yace, “Mom lafiya
kuwa?”. Saurin ɗago idanunta dake akan wayarta tayi ta dubesa, dai-dai shi kuma
yana ƙoƙarin saka farar t-shirt ɗin daya ɗauka. Miƙewa tai ta nufosa tana wani
sakin tattausan murmushi, ta ɗauka ƙaramin towel ɗin daya fito da shi a hannu
ta nufi sumar kansa alamar zata tsane masa gashinsa dake ɗigar da ruwa. Da ɗan
hanzari yaja baya kaɗan yana tsuke fuska.
“Mom!!”
Ya faɗa aɗan tsawace. Jin a yanda yay maganar
ne ya sakata tsayawa cak daga yin abinda tai niyya.
Da ɗan shagwaɓa yace,
“Haba Mom! Miyasa kike son maidani baya ne kullum? Nifa ba Abraham bane ko
Victoria Please”.
Ƙanƙance mayatattun idanunta
tayi tana ɗan matsosa, cikin muryarta dake wani irin rawa tace, “Kaine kake ɗaukar
kanka babba John! Ita uwa ɗanta kullum yaro ne a gareta. Ina sonka Yoohan fiye
da yanda kake tunani, kai ɗin farin cikinane fiye da sauran ƙannenka”.
Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe a
kanta, ya ɗan sassauta muryarsa da fuskarsa dake a tsuke. Dan shi harga ALLAH
bai fassara maganarta da komaiba face soyayyar ɗa da uwa. “Na sani Mom, nima
ina sonku da ƙaunarku fiye da zato ke da papa da ƙannena. Amma Please ki ringa
rage cewa zakimin wasu abubuwan. Bama ni ba ko Abraham ɗan shekara goma ba
komai zaiso kimasa ba yanzun. Mun rigada mun girma, hidimar da kikai mana muna
ƙanana ta wadatar uhmyim?”.
Yanda yay maganar cike da
lallashi ne ya sake narkar da ita a wani irin yanayi mai wahalar fassara. Ta buɗe
baki zatai magana aka turo ƙofar aka shigo. Gaba ɗayansu ƙofar suka kalla. Papa
ne cikin kayan barci da alama ma ya fara barcin tashi yayi.
Cikin ƴar shagwaɓa Yoohan yace, “Yauwa
papa Please kwashi matarka ku wuce dama ta sakani a gaba nikam”.
Papa dake bin Mom da wani irin
kallo ya haɗiye yawu da yin guntun murmushi yana maida idonsa akan Yoohan ɗin
da ya sake ƙwaɓe fuska. Muryarsa da alamun barci ya tashi yace, “Yaushe ka
dawo?”.
Mirror Yoohan ya nufa yana
faɗin, “Yanzun nan babu jimawa nazatama baka gida ai”.
Komai papa bai ceba ya kama hannun Mom
suka fice yana faɗin, “Huta abinka sai da safe”. Suna fita Mom ta fisge
hannunta da ga na papa tana kumbura kumatu. Baice mata komaiba yay gaba abinsa
dan jin Yoohan yana sakama ƙofarsa key. Yasan ko mi zatayi bazai sake buɗe
mataba kuma. A ransa kuwa mamakin yanda Matar tasa ke nuna tsananin so ga
ƴaƴansu yakeyi. shi bai taɓa ganin mahaifiya mai ƙulafucin ƴaƴa irin Madam
Chioma ba.
Yoohan kam koda ya kammala
kimtsawa falo ya fito ya haɗa tea ya koma bedroom ɗinsa. Zaman sha yay
zuciyarsa da tunaninsa duk na wajen Nu'aymah. Ji yay yana buƙatar sanin yaya
take yanzun, dan haka yaja wayarsa ya nema Dr Aysha a karo na farko a
rayuwarsa.
Ita kanta Dr Aysha ba ƙaramin mamaki
tayi ba ganin kiran Dr Yoohan a wayarta. Abinda bai taɓa faruwa ba. Jikinta har
tsuma yake wajen saurin ɗauka. Ta kara a kunne murya a narke tace “Hello!
Doctor good evening”. Maimakon ya amsa mata sai cewa yay “Assalamu alaiki”.
Idanu taɗan zaro waje jin sallama yayi, saɓanin da da sai dai ya ce maka hii.
Itafa dama gaba ɗaya a wannan zuwan nasa abubuwa da yawa taga idan yanayi
tamkar ba shiba. Shekaranjiya ma har ganinsa tai kamar ya fito massallaci......
Sallamar da ya sake maimaita matace ta
katse mata tunaninta. “I'm sorry sir. wa'alaikissalam. Kunje lafiya?”.
“Humm”
ya faɗa a taƙaice yana lumshe idanu da kai kofin tea ɗin
bakinsa. Sai da ya kurɓa ya haɗiye kafin yace, “Ya yarinyar nan ta farka ne?”.
Ta gane Nu'aymah yake nufi, dan ita kaɗaice patient ɗin daya kwantar dai. Cikin
sanyaya muryarta tace, “A'a har yanzu tana barci, amma an saka mata drip ɗin
daka ce ɗin yanzun babu jimawa”. “Okay night” ya faɗa a taƙaice da yanke wayar
batare da ya ƙara komai ba.
Nannauyan ajiyar zuciya Dr Aysha
ta sauke tana ɓata fuska kamar zatai kuka. Akan laɓɓanta ta furta, ‘Ɗan
wulaƙanci’.
Oho baimasan tanai ba, dan shi tea ɗinsa
ya ƙarasa sha kafin ya miƙe ya nufi toilet. Alwala yayo. Ya saka sallayarsa
sabuwa da baba malam ya bashi ya tada salla kamar yanda ya keyi yanzu a kowanne
dare. Idan har ya samu dama yakan fara daga ƙarfe ɗaya ko biyu, zuwa uku sai yaɗan
kwanta kafin asuba.
*_WASHE GARI_*
A gidan su Nu'aymah
kuwa a safiyar yau bayan kammala breakfast ɗunguma sukai asibiti suka duba
jikin ta, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Baba malam ne kawai
dasu Abba Musbahu. Sai hajjo da Ananah. Umm dama batajeba dan tanason zuwa
gidan Gwaggo mahaifiyarta. Daga can zata biya asibitin tare da Gwaggon.
Basu jima a asibitinba suka dawo gidan,
baba malam da ƙannensa uku da hajjo sai Ananah a falon hajjo suka yada zango
domin tattaunawa. Sunyi zaman kusan awa guda sannan Abba Musbahu yay kiran
Abdallah da Naser a waya. Ba a rufa mintuna biyarba kuwa sai gasu dan dama duk
suna gida. Zama sukai inda Ananah ta nuna musu kowanne kansa na a ƙasa..
Fuskar baba malam a ɗaure ya
dubi Abdallah, “Abdallah zan fara ta kanka, dan karka zata shirun da mukai maka
kamar mun ƙyalekane bisa abinda ka aikata mana. Gani ga ƴan uwana ga Hajjo
harma da Ananah. Inason ka faɗa mana dalilinka na aikata abinda ka aikata. Shin
bamu da daraja a idanunka ne mu da muka baka auren yaranmu kokuwa raini ne dan
kaga ka girma?”.
Cikin sauri Abdallah ya ɗago yana
kallon baba malam ɗin da girgiza kansa. “Wlhy sam ba haka bane ba Abbah. Kuna
da darajar da bayan MANZON ALLAH babu mai ita a idona a duk faɗin duniya sai
ku”.
“Ban yarda ba Abdallah, inda ace
munada wannan darajar da bazaka aikata abinda kayi ba. Mu aura maka yara ka
sake mana su akan wani banzan dalilinka mara amfani”.
“Abba ku gafarceni, amma wlhy
ina son Nu'aymah, son da zaku iya rasani idan kuka hanani mallakarta. dan ALLAH
a wannan karon karkuce mani a'a”.
“Ba maganarta nai makaba
ni ai, maganar yarana daka saki nake maka”.
Shiru Abdallah yay zuciyarsa na
masa ƙuna da zafi mai raɗaɗi, sai faman haɗiyar zuciya yake kamar budiddigin
ƙwaɗo. Ganin yaƙi cewa komai hajjo ta amshe zancen da cewa,
“In banda zancen banza taya dan
kawai nayi maka magana zakaje ka aikatama yara wannan wautar, ina iliminka
yake? Ina wayonka yake? Kaine fa babba a gidan nan, kuma ka tabbatar abinda ka
aikata da shi na ƙasa da kai zasuyi koyi. Ta hakane zaka iya zama jagora uba
garesu a randa ƙasa ta lulluɓe idanunmu mu da iyayen naka?”.
“Kiyi haƙuri hajjo”.
Ya faɗa muryarsa na zuga.
“Idanma banyi haƙuri ba dukan ka
zanyi Abdullahi. Yanzu dai ka maida matanka, batun Zainabu kuma gaka ga Nasiru
yanzun, sai ku sasanta kanku dan babu mai shiga a wannan karon. Duk wanda ya
sameta a cikinku mu abin farinciki ne a garemu, kuma zamu saka albarka. Sai
kuje ku nema yarda daga gareta, wanda duk ta zaɓa magana ta ƙare”.
Hukuncin hajjo yayma kowa
dai-dai, sai dai banda Naser da Abdallah. Dan a kallo ɗaya zaka hango tsantsar
tashin hankali cikin idanunsu. Lokacin da suke ficewa daga falon har tafiya
suke kamar zasu kifa, musamman ma Abdallah.
*_ABUJA_*
Aɓangaren Yoohan kam yau
da azumi ya tashi kasancewarta al-hamis. Azumin litinin da alhamis yana ɗaya
daga cikin ibadar da tun bayan musulintarsa ta fara zame masa jiki. Bayan ya
idar da sallar asubahi yay zaman yin azkar kamar yanda baba malam ya koyar da
shi ta bidiyo kol da sukeyi a kullum. Sai dai kasancewar bai gama haddacesu ba
sai yake karantasu a littafin. Sai da gari yay haske kamar yanda shari'a ta
koyar sannan ya miƙe zuwa ɗakin motsa jikinsa.
Kamar yanda ya saba ya farayi yana haɗa
uwar zufa, kasancewar kwana biyu bai samu damar yin na kirki ba a kano sai yau
yaji jikinsa yay masa ɗan nauyi. Hakan ya sashi zarta lokaci kaɗan, dan har
Solomon ya shigo masa da tatattun kayan itatuwa (fruit) bai kamalla ba.
“Good morning sir”
Solo ya faɗa yana ɗan risinar da kansa tire a hannunsa.
A taƙaice Yoohan dake ɗan hakki ya share zufar
goshinsa da cewa “Same”. Da ga haka ya cigaba da abinda yakeyi. Shigowar Solo
da kusan mintuna sha biyar sannan ya kammala, lokacin har an fara gudanar da
program ɗinsa a NTA. zama yay Solo ya miƙo masa juice ɗin. Kai ya girgiza masa
yana goge zufar dake tsiyaya masa da ƙaramin towel, yace, “Barsa kawai”.
Sosai Solomon yayi mamaki. dan a
watan nan ya fara lura da wani abu daga ogan nasa. Duk monday and Thursday da
wahala kaga yaci wani abu har yamma. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru.
Shima Yoohan ɗin bai sake tankawa ba, sai ma maida hankalinsa da yayi ga
television ɗin gaba ɗaya. Ana kammala program ɗin ya miƙe, anan yabar Solomon
na kimtsa ɗakin.
Tsaf ya tadda ko'ina Solo ya
gyara, sai ƙamshi da sanyin ac dake ratsa ko ina. Toilet ya nufa yay wanka, ya ɗan
jima a ciki kafin ya fito. Bashi da sha'awar fita ko'ina yau ɗin nan, dan haka
body spare kawai ya saka da boxer ya haye gadonsa ya kwanta yana sauke ajiyar
zuciya. Cikin mintuna kaɗan barci kuwa yay gaba da shi.
A falo kam koda su madam
Chioma suka haɗu dan yin breakfast kakarsa data haifi papa ce ta saka Destiny
wai taje ta kira Yoohan ɗin. Sosai Destiny ta waro idanu waje. cikin yare tace,
“Granny inajin tsoro gaskiya. Brother John baya son mutane”. Harara mama ta
zuba mata, cike dajin haushi ta duba Madam Chioma. “Ai ga wadda ta watsa shi
nan bai ganin kowa da gashi sai ita data haifesu. Yaro sai masifar taurin kai”.
Banza Momy tai mata, sai mamanta ce ta karɓe zancen da faɗin, “Inma a bauɗen
yake ai ba ita kaɗai ta bauɗar da shiba harda ɗanki. Debora ki daina sakama
yarinyata baki akan rayuwarta fa, ni dama nasan masiface ta kawoki ba komaiba.
dan kawai kinga nazo, yanda kikejin gidan ɗankine nima gidan inlow ɗina nen
ai”.
Ai kafin kace kwabo sun hargitse da
cacar baki kamar wasu kaji. Su dai jikokin duk idanu suka zuba musu kawai suna
kallo da ƙannen papan dama momy ɗin kanta. Abun nasu zattakaici da dariya.
Basuyi shiru ba sai da papa ya fito yay musu magana cikin damuwa.
Daga haka suka koma harar juna suna huci
kamar wasu zakuna. Daga ƙarshe basuci abincin a Dining ɗinba sai dai kowa
masaukinta ta koma aka kai mata nata.
Yoohan da baisan sunayi ba kam sai
wajen sha biyu ya farka. Wanka ya sakeyi yay shiri cikin ƙananun kaya. Blue
jeans da t-shirt fara ƙal an rubuta HERO da kalar blue a gaba. Ya gyara sumarsa
da sajensa yanata zabga ƙamshi. Slippers masu taushi ya saka dan ba nisa zaiyi
ba. Ya ɗauka wayoyinsa ya fito.
Da sauri Favour ta ɗauki remot ta rage
kiɗan da suka saka a sifiku kamar zai tsaga falon lokacin da yake sakkowa.
Fuska a matuƙar tsuke ya dubesu, baiko amsa gaisuwar da suke jera masa ba yace,
“Wannan kiɗan da kuka cikama mutane kunne da shi fa?”.
Cike da tsoro Victoria tace,
“Brother sai da nacema Favour karta kunna bakason ƙara da yawa, amma tace
sai......”. Wani irin zabura Favour tayi ta danne bakin Victoria dan karta
ƙarasa faɗa. Ba komai ta tuna ba sai marin da ya taɓa kashe fuskarta da shi
ranar X-max ɗin last year da sukaje a ƙauye ya iske ta samu ciki. Cikin rawar
murya tace, “Ƙarya take Uncle John, na rantse bance komai ba”.
Shi baimabi takansu ba ya fice abinsa
saboda jin kakarsu data haifi papa na ƙwala masa kira da alama sunansa dasu
Victoria suke ambata ta jiyo.
Da ƙafa ya fice a gidan bayan ya
gaisa da ma'aikatan gidan a tsaitsaye. Can bayan layinsu ya nufa, inda yake
ganin wani masallaci. Acan ya gabatar da sallar azhar, koda aka idar ya dawo
gidan garden ya wuce kai tsaye. Babu kowa a ciki, sai sassanyar iskar dake kaɗawa
daga ni'imar itatuwan cikin garden ɗin. Anan yay zamansa har la'asar tayi,
kasancewar yanada alwalarsa massallacin ya sake komawa yayo sallar la'asar, ya
cigaba da zamansa a ciki har zuwa biyar sannan ya fito.
Daya dawo ma bai shiga ciki ba,
duk da kuwa Solomon ya sanar masa Momy nata zuwa nemansa tun ɗazun. Aika solo ɗin
yay ya ɗakko masa key ɗin mota a ciki. Tare suka dawo da Miracle. Koda ta
gaishesa sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kansa, cikin damuwa ganin zai shiga motar
tai saurin fada masa Momy tace yazo yaci abinci. Bai amsata ba sai da ya shiga
motar mazaunin driver, dan ya hana kowa binsa. Kallonta yay sau ɗaya ya ɗauke
kansa. “Ki sanar mata ina azumi”. Daga haka yay reverse ya fice a gidan.
Koda ta koma ta sanar ma
madam Chioma sosai sukaita mamakin azumin mi Yoohan ɗin keyi? dan sunsan dai su
azuminsu yanada lokutansa a addininsu. Ganin basu da mai basu amsa suka haƙura
harya dawo gidan.
Yoohan kam koda ya fita wajen
Hamza Ibrahim ya nufa, can suka haɗu gidan wani haɗaɗɗen abinci daya gaji da ƙawatuwa.
Sun ɗan zauna kusan na mintuna talatin kafin a kira sallar magriba. Zuwa sukai
sukayo salla suka sake komawa gidan abincin, anan Yoohan yay musu order ɗin
abincin buɗa baki dan shima manager axumin ya keyi. Da wannan damar sukai
amfani wajen sake faɗaɗa hirar tasu da duk ta kasance akan abinda ya faru a
kano, wadda dama duk ya sanar masa ta waya. Hasalima shine ya bashi shawarar
kawai yacema baba malam zai auri Nu'aymah ɗin koda a yanzunne. Shi kuma aranar
bai wani ja zancenba ya amince da shawarar duk da a idanunsa yana ganin Aymah
tayi ƙanƙanta da aure.
A fahimtar manager dai anya dama Yoohan
ɗin ba ya na son Nu'aymahn bane kuwa?. Da yake baida mai bashi amsa sai ya
watsar da zancen.
Duk yanda ake gudanar da bikin aure a
musulinci da hidimar da hausawa keyi a al-adance manager ya sanarma Yoohan, dan
haka basu rabu ba sai kusan goma na dare.
Koda Yoohan ya dawo a harabar gidan ya
iske papa nashan iska. Zama yay a wajen suka tattauna abinda ya shafesu. Sai
kusan ɗaya saura suka shiga cikin gida. A hakanma Yoohan ɗinne ya nuna ya gaji.
*_BAYAN KWANAKI UKU_*
A kwanaki ukun nan kullum sai
Yoohan dake a birnin ikko yanzun sai ya kira Dr Aysha yaji yanayin jikin
Nu'aymah da suka maida sumammiya, dan tunda ya bar kano a yanayin barci take,
sai dai drip da ake ƙara mata a koda yaushe da allurai a ciki. Haka suke buƙata
ta sami isashen hutu. Allurar kuma daya sa aka kawo masa daga canada tun wadda
akai mata randa aka kawo ba'a sakeba. Dan ƙa'idar allurar sai bayan sati ɗaɗɗaya
za'ayita, hakan yasa bai bama kowa ba ya ajiyeta a office ɗinsa a waje mafi
sirri. Dan daga Lagos nan kano yake fatan dawowa ya duba Nu'aymahn. Kamar yanda
ya sabarma kansa kuma kullum sai ya kira baba malam sun gaisa safe da maraice.
A gidan su Nu'aymah kuwa
shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dan yau saura kwanaki shida
kacal a ɗaura auren su Hajarah. Da Abban su Adawiya yace a ɗaga har sai
Nu'aymah ta samu sauƙi. Amma sai baba malam ya hana hakan. Ya ce babu abinda
za'a fasa ALLAH zai bata lafiya itama.
Yayinda aketa shirin biki
Abdallah da Naser ƴar tsama a tsakaninsu kullum sake faɗi da tsauri takeyi akan
Nu'aymah. Gashi sun maida asibiti wajen yininsu duk da ita wadda sukeyi
domintama batasan sunayi ba ma. Duk sunbi sun tashi hankulansu akanta. Yayinda
Adawiya ita nata hankalin yafi nasu tashi. Dan har yanzu Abdallah yaƙi maida
auren nasu. Su baba malam kuma babu wanda ya sake cewa da shi komai akan hakan.
Sosai Adawiya ta rame, kamar ba itace
suka dawo ta zama lukuceciya ba. Tabi ta ɓoye kanta a gidan babu mai ganinta
sai ƴan sashensu. Ita kuma Addah tayi kamar bama tasan halin da Adawiya ke a
ciki ba. Dan tun lallashin datai mata na farko taki saurarenta saita watsar da
ita bayan ta babbanka mata zagi da yi mata kaca-kaca.
Ƴan uwantane kawai da Umm ke
tausayinta, dan Hajarah tamafi kowa damuwa da halin da Adawiya ta jefa kanta.
Har kwatance take mata da yanda Yusrah tai kamar komai bai dametaba tanata
harkokinta ita. Hakama Nu'aymah lokacin da aka rabasu aka bashi aurensu. Amma
sam Adawiya taƙi fahimta. Sai bin hanyoyin da zatai magana da Abdallah takeyi
shi kuma ya toshesu ya hanata kowacce dama. Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ga
takarar neman yardar Nu'aymah da take a rabin duniya da barzahu.
A washe garin da Yoohan ya cika
kwanaki huɗu da tafiya su Papa sukazo kano shida ƙannensa da abokansa uku. Babu
wanda yasan abinda ya kawosu. Shi kuma baba malam bai faɗama kowa ba sai ƴan
uwansa da Hajjo da Ananah kawai.
Amma yanda Papa da gayyarsa suka koma
ransu a ɓace zai baka tabbacin zaman baiyi daɗi ba. Dan shima baba malam ɗin
dai ranar yini yayi babu walwala tattare da shi.
★★★★
Ana saura kwanaki huɗu ɗaurin
auren su Kubrah Yoohan dake a birnin ikko har yanzu ya kira Dr Sa'ad ya sanar
masa su tsagaita da yima Nu'aymah allurar barci haka nan, idan ta farfaɗo a
kowanne lokaci a kirasa a sanar masa.
Haka kuwa akayi, ƙarfe kusan sha biyu
na daren rar Nu'aymah ta farfaɗo............✍

No comments