KIBIYAR AJALI 10
*10*
*Tun* daga wannan malam Auwal yake dan yi min mutunci ba wai da yawa ba, saboda a cewar sa kada na raina shi dan ba kunya ce dani ba idan yana sakar min fuska zan dena ganin mutuncin sa. Yanzu ta kai ta kawo da kai na nake zuwa makaranta ba sai an tuna min ba dan sosai nake jin dad'in yadda ake koyar damu hanyoyin da zamu yi tsafta, kula da iyayen mu da ma jin maganar su.
Yau ma kamar yadda malama Mardiyya ta koya mana, muna tashi
daga makaranta na koma gida na cire kayan makarantar nasa wasu riga da skirt
wanda malama Mardiyya take kawo min, na yarta ne da kuma 'ya' yan yan uwan ta
shine take kawo mana nida su Uwande dan kar su ce ni kawai take yiwa shi yasa
take hadawa dasu. Naje na dauki bokiti na debo ruwa a rafin durb'un, na dawo
tare da dakko ragowar sabulan wanki na da nake boyewa idan ya ragu, na wanke
kayana tas suka yi kyau na shanya can inda hannun Gajiyalle ba zai kai ba bare
tayi min mugunta ta yarmin dasu. Sannan ne na fara tunanin abinda zanci, dan
dazu da safe tas na cinye buredin da malam Auwal ya bani jiya.
Babban buri ne ya sake mamaye zuciya ta shi yasa nake son
dagewa wajan ganin nayi karatu wato na zama cikakkiyar yar jarida, wannan shi
ne mafarki na a duk lokacin da na samu ina shakar numfashi. Muryar Dara'ifa ne
ya fito dani daga cikin daki ina daura mayafi na a kugu duk kuwa da cewar
malama Mardiyya da malam Auwal sun hana ni yin hakan, amman sabo da kuma ganin
al'adar kauyen mu ne yin hakan yasa na kasa denawa, ko na yafa idan na fara
tafiya sai na zaro na daure a inda na saba. Na saki murmushi lokacin da na
ganta da faranti a hannunta, ina ta addu'a Allah yasa ni ta kawowa.
“D'an malele ne nayi shine na kawo miki, Na rasa yaron da
zan aiko shi yasa na taso da kai na kici shi da zafinsa.”
“Walle naji dadi Dara'ifa, nagode Allah ya hi miki albarka.
Sittin ta Ubangiji ina ha'awar dan malele sosai.”
“Toh gashi nan kuwa ai ta sha Dijen Baffa.”
Nayi murmushi tare da karbar filet din ta tafi ni kuma na
samu guri wajan dakin Baffa na zauna ina ci ina santi dan yajin ba karamin dadi
ya yi ba. Cikin ikon Allah Gajiyalle ba ta fito ba har lokacin tana daki tana
baccin asara. Ina gamawa na dauraye filet din naje na kai mata tare da godiya
sannan na tafi wasa na gidajen kawaye na, wasu muyi fada na tafi wani gidan,
idan naje muyi ta musu da su a kore ni na fito a haka har dare yayi na koma
gida na kwanta.
Babu abinda yafi ilimi dadi a rayuwar dan adam, saboda tun
da aka bude makarantar boko da islamiya a kauyen mu muka fara samun sauye-sauye
da yawa. An dan rage kauyancin da ake fama dashi, ana barin yara mata suna
karatu dan sun fara ganin alfanun karatun a cikin rayuwar mu mata. Duk da cewa
bana yin na farko a ajin mu, amman ina yin gaba ina kuma zama mai kokari har ta
kai ta kawo ina zuwa ta daya ko ta biyu ko uku, da taimakon malaman mu da basa
fushi akan duk wani shirme da muke yi musu. Har na kammala primary muka shiga
bangaran secondary, nan din ma dai malam Auwal sai da ya bimu can yana koyar
damu, A hankali kuma yana ta jefa sakon soyayyarsa gare ni inda ni kuma naki
bashi fuska dan gani nake tamkar so yake ya sake samun dama ta yadda zai horani
iya son ransa.
*BAYAN WASU SHEKARU*
*’KAUYEN DURB’UN*
Nana Khadijaa (Dije, Dijangala ta mai gari/Oganniya yar
Baffan ta!) Duk sunaye na ne na yanka dana lakani. Da farko dai: Baba na na
kira na da Ummi na, Saboda kasancewar sunan mahaifiyar sa da naci. Matar baba
na na kira na da Dije itada wasu tsirarrun mutane a karkarar mu. Mafi yawancin
yan karkarar mu na kira na da Dijangala ko Ta mai gari. Kawaye na da matasan
karkarar mu na min laqabi da Dije Oganniya. Kasancewar a lokacin ina karama ina
da kiriniya da siyan fadan da ba’a kasa da ni ba.
Duk wani cincirindon ruguntsumi idan ka cakuda zaka ga ni ce
akan gaba. Lamari na dai addu'a ce kawai ta kare ni. Na kasance ni kadai ce
awajen iyaye na. Tun ina ‘kankanuwa mahaifiya ta ta rasu, Mahaifina ya auro
wata matar, Ya zamto riko na ya koma hannun kishiyar uwa. Na taso cikin wata
irin kuntatacciyar rayuwa wanda alqalami yayi ka’dan wajen bayyana muku ita, Manufa
dai na sha wahala sosai. Duk da azabar da kishiyar uwa ke gallazamin, Sai Allah
yasa mahaifi na yakan kyautata min a duk sanda yake da iko.
A yau January 1, Zan kammala jarabawar kare karatu na na
secondary, Alhamdulillah Allah kai ne abun godia. Na karanta b’angaren art
saboda inaso na karanci fannin Mass-Com/journalism. Na kanyi daria a duk sanda
na tuno kuruciya ta ta da. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u, Na sake daga
kai na dubi allon zayyana ta wanda nayi sauka bara a tahfiz din da su Malama
Mardiyya ke koya mana.
Shekaru na goma sha bakwai a yanzu. Ina kuma sana’ar kitso,
Na kuma fara koyon dinki a gidan Bara’atu tela (Babbar mace bata ajin mu ba)
Alhamdulillah da wannan yar sana’a tawa nake rik’e da kai na dama Baffan mu.
Wanda a yan shekarun nan ya kamu da lalurar nakasar shanyewar barin jiki
(hemiplegia/hemiparesis.)
Hijabi na na janyo sabo fil dashi Bara’atu ta dinka min,
Wuta ta ruru na zubata a dutsen guga, Cikin kwanciyar hankali na shiga goge
hijabi na. Na kammala na shasshafa turaruka masu sanyin k’amshi dana siya a
shagon Falalu.Ban tsaya wata kwalliya ba na dai goga farar hoda da basilin a
lebe na. Gashi na mai matukar tsawo da cika naita ko’karin daurewa, Dak’yar ya
dauru. Domin ina daure shi yana kuncewa saboda santsin sa, Ko kitso ake min
kasan na warwarewa. Zura hijabin nayi, Na goggoge takalmi na samfarin sandal.
Safa tama sabuwa ce sai sheki take. Wajen Baffa na nufa na coka biro a gefen
kunne na, Ji na nake on top yau zan kammala sakandire, Sai kuma fanni na biyu.
Yana malale a taburma kamar ruwa, Dakyar yake iya magana.
Gajiyalle na gefen d’akin girki tana kwashe tuwo. Na san ba zata bani ba bare
Baffa na. Domin tunda rayuwa ta ta sauya daga bak’a izuwa fara Gajiyalle ta
dena bani abinci, Duk abinda zan sanya a ciki na tadena min shi. Ko banda
hantara da kyara yanzu babu abunda ke shiga tsakani na da ita. Zan gayshe ta
Sau dubu ba zata amsa ba, Sosai take jin haushin karatun da nake yi. Kullum
cikin yada min da magana take. Kan naki aure ina yawon ta zubar, Ga k’awaye na
nan duk sun hayayyafa. Ni da Siyama da Uwande da Nafisa ne kadai ke yin karatu
yanzu a sa’oin mu. Gaba d’aya sunyi aure sun tara yara. Ajiyar zucia na sauke
ina kallon Baffa na, Dama ance sai ka rasu ake gama canza maka halitta. Yanzu
Kalli Baffa da sumul k’alau yake. Tashi d’aya ya samu wannan ciwon,
“Baffa na..! Sannu ya
jikin naka?”
Baffa ya lumshe idanu ya bud’e alamun lapia. Kafin ya bude
bakin sa hankali,
“Allah... Ya bada
sa’ar jarabawa Ummi na.!”
“Aamin Baffa na!
Allah ya tashi kafad’un ka yasa kaffarane.”
Rufe idanu yai. Na mike dakyar jikina duk yayi sanyi.
“Na tafi Gajiyalle.”
Harara ta dankaramin ta cigaba da kada miyar ta.
“Na tafi jarabawa
Gajiyalle.”
“Ko an tafi yawon ta
zubar ba. Mude kada a kawo mana abun kunya gida, Atoh!”
Girgiza kai kawai nayi na fice rai na babu dadi. Nera dari
da hamsin din hannu na na tsaya na mikawa Safarau me sayar da abinci,
“Gashi ki zubamin a
kwanon jiya ki wanke dan Allah sauri nake zan tafi jarabawa, Idan na dawo zan
tsaya na karb’a.”
Saurin Karb’a tayi ta koma wajen zaman ta. Iyayen ta sun
hanata karatu sai dai tallen abinci, Wai ta haka zata tara kudin kayan daki.
Abun takaicin ma mazan yar kasuwa sun mai da ita tamkar matar su. Su yita bata
kudi suna taba ta. Haka na shige da tunanin da safarau ke ciki na tafi
makaranta. Lalle na godewa Allah daya kadarta za’ai makaranta a kauyen mu, Da
hakimi daya samo mana tallafin yi, Dama mai gari daya wayar da kan dattawan
karkarar mu, Sai Baffa na, Jigon rayuwa ta. Wanda ya tsaya min a komai, Ya so ni
bai kyamace ni ba kullum cikin min adduar shiriya yake. Ga bani shawarwarin
yadda rayuwa ke ciki. Da yadda zan gudanar da al’amura na ba tare da na gunduri
kowa ba. Bayan Baffa na sai Malamai na. Musanman Malama Mardiyya data dauke ni
tamkar ‘yar data haifa, Itace mace ta farko data gyaramin rayuwa ta. Gaba d’aya
acikin duhu nake. Zuwan Malama Mardiyya shi ya samar da yadda na zama a yanzu.
Ba abinda zance da kowa sai fatan alkhairi.
*_GOVERNMENT JUNIOR/SENIOR SCHOOL DURBUN*_
Kide kide muka fara da bencina muka d’akko muka kawo su
farfajiyar makaranta, Yau munyi candy. Mun kammala makarantar secondary. Allah
mungode maka. Wakoki muka fara na candy, Muna yi fuskokin mu dauke da farin
ciki da annushuwa,
_2005 muna tare, 2006
muna tare, 2007 muna tare.. 2014 zata raba mu. Malam Auwal mude kayafe mu, Mude
mun yafe, Muma ka yafe mu, Malama Mardiyya mude kiyafe mu, Mude mun yafe mu de
kiya fe mu..🎶_
Haka Mukai ta yi har akazo kan sunayen dalibai, Nima na mike
ina hawaye,
_Khadija Basheer
Inuwa inayin ban kwana, Nide ku yafen, Nima na yafe ku.🎶_
Ina k’arasawa na fashe da kuka, Saura na ban haku’ri, Mu
kaita koke har aka kammala, Aka babbawa prefects kyaututtuka. Ni ce ‘sanitary
prefect’ kasancewar nafi kowa tsafta. Domin tunda na Kile na koma yar gayu, Har
kawaye na ke kira na da ‘Dije wanka-wanka’ Idan zanzo makaranta ko banida kudin
guga tun dare nake yiwa uniform dina ninkin guga na kwanta akai da safe kuwa
sai kuga sunyi ‘das dasu tamkar nasa dutsen guga.
‘’ Ina sanitary
prefect? Nana Khadija Basheer..”
A hankali na mike daga zaunen da nake na isa gaban makaranta
inda Malam Habu ke kiran mu dai-dai, Sunana ya tashi daga Khadija Baffa ya koma
na ainihi wato Nana Khadija Basheer. Tun a Jss3 na canza lokacin da mu kai
jarabawa. Malam Auwal na gefen Malam Habu yana min wani kallo tunda ga sama na
har kasa,
“Dan iska...”
Na furta ahankali ina gatsine baki. Murmushi yai yayi magana
da labban sa bansan meya ce ba. Malam Habu ya dankamin kyauta ta, Na tsaya muka
dauki hoto da sauran malaman kamar yadda ake da kowa. A haka aka kammala komai
bayan anyi walima mekyau. Mardiyya bata bari mun kara sallama ba ta tafi bayan
ta dankamin number wayar ta a paper, Kan cewar zata dawo ta dauke ni muje birni
nayi jamb. Nasan idan muka kara had’uwa kafin tafiyar ta sai nayi wani sabon
kukan itama haka, Shi yasa ta tafi. Amma Malam Auwal ya ki tafiya yananan ya
kasa ya tsare. Da wani Malamin ya kira wo ni zai dakatar da ni. Sai kace wani
miji na.
Ko ta kansa ban sake bi ba, Na bi su Uwande muka dauki
hanyar gidan su ganin kayan barar ta da aka kawo, Kamar hadin baki Siyama ma jibi Za’a kawo
nata, Nafisan kansila kuwa an kusa bikin ma, Wani dan uwan su na birni zata
aura yanada mashin dinsa Lifan. Ni kuwa ko oho. Banda Malam Auwal da kama sunan
sa haushi yake bani ma sai Mubarak dan gidan Bala driver, Shi kuwa babar sa ta
dira tsallen albarkar danta ba zai auri wadda tai boko ba. Muna tafe a hanya
ina tunanin duniya, Malam Auwal ya shiga zabga min kira tamkar wadda naci
bashin sa na gudu. Nifa gaba d’aya haushi yake bani, Ada babu wadda ya tsana
iri na, Yana kallo na tamkar kashi. Duk abunda nayi bana birge shi. A kullum
cikin kuntata min yake. Amman yanzu ya nanike min kamar super glue. Duk inda
nai bina yake sai kace rak’umi da akala.
“Na’am..”
Na amsa masa bayan ya kira sunana a karo na ba adadi. Ya
sake marairacewa yana zuba hannayen sa a aljihun jeans dinsa,
“My Baby K! Meyasa
kike wahalar da zuciar masoyin ki ne? Na gaya miki tunda Allah yasa son ki ya
mamaye bargon jiki na da tsoka, Kullum da begen ki nake kwana nake ta shi. “
Namiji mayaudari ji wata karya dan Allah! Duk da a k’auyen
kayau na tashi, Naki jinin irin kalaman soyayyar nan. Konamin rai suke. Gashi
duk karyar banza ce. Don takaici rasa me zance masa nayi.
“Baby K!”
Wai Baby K! Kamar wata diyar cikin sa. Murtuke fuska nayi na
juya gefe ina dagawa su Uwande hannu alamar su tsaya ni kar su tafi.
“Malam Auwal jira na
ake..”
“Naki jinin yadda
kike ambatar sunana Baby K! Ni ba malamin ki bane, Masoyi ne agare ki. Ki
tallafawa zuciya ta ki karbi kokon barar soyayyar ta. Shekaru nawa ina rokon
ki, Ya kamata ace kin tausaya min, Gashi yau zan koma inda na fito. Kuma ba
naso na koma batare da kwakkwarar amsar ki gare ni ba.”
Ajiyar zuciya na sauke, Ni kai na nagaji da kulaficin da
yake yi min, Mutumin da sam baisan darajar dan adam ba, Rashin mutuncin da yai
wa Baffa na bazan taba mantawa dashi ba, Yazo zance Kwana ki, Baffan mu ya fito
zai tafi gona da y’ar fatanyar sa bai ko kalle shi ba. Ina tsaye ina gwada
hankalin sa. Dana tambaye shi meyasa bai gaida wanda ya wuce ba? Wai ya dauka
me gyara ne. Gyaran uwar baban sa? Ranar naci masa mutunci sala-sala bansan
meyasa baida zuciya ba ya nanuke min.
“Kayi hak’uri Malam!
Gaskia bana ra’ayin soyayya, Karatu zanyi. Allah ya baka wadda ta fini komai.
Ina maka fatan alkhairi. Allah ya kiyaye hanya.”
Ina gama fada nai gaba abuna, Na barshi a tsaye ya sandare.
Mukai tafiyar mu dasu Uwande, Wannan itace rana ta karshe tsakani na da Malam
Auwal. Ina wa dukkanin mu fatan alkhairi a rayuwa. Muka je gidan su Uwande muka
gano kaya, Wallahi Uwande tai goshi, Kaya nasha-nasha. Daga nan na tsaya na
karb’i abincin dana bada Kud’i dazu, Gida na nufa, Ina shiga na hango Baffa na
a inda na barshi ya kwarara amai yana numfarfashi dakyar, a sukwane na zubar da
kyautar hannu na kwanon kuma na ajiye a gefe na shek’a da gudu na isa wajen sa
ina tallafo shi da karshen karfi na,
“Baffa na...! Sannu!
Amai kayi! Sannu! Jinjiri (Almajirin dake kula dashi Idan na tafi makaranta ko
bana nan) bai zo ba? “
D’ankwalin hijabi na nasa na gogge masa fuskar sa, Kafin na
debo ruwan dumi dana ke had’a masa shayi na surka na gogge masa jikin sa, Riga
na d’akko na sauya masa da Wadda ya b’ata, Ina ta faman masa sannu. Gajiyalle
ta fito daga d’akin ta tana wake wake, Ta shiga kitchen ta ebo abincin ta ta
wuce ko kallo bamu ishe ta ba. Ni bansan meyasa Baffa ya auro taba. Silar ciwon
sama itace ta haushi da kokawa ya zume a bandaki.
Abincin dana sayo na janyo, Na raba shi kashi biyu, Na shiga
bashi a hankali dakyar yaci rabin sa, Ni kuma na cinye sauran. Na wanke tulin
kwanukan da na gani awajen, Kafin na ha’da wuta na dora ruwan wanka na. Baffan
mu na shiga nunnunawa kyaututtukan yai murna kwarai tare da kwarara min addu’a.
Ruwa na na zafi na shiga band’aki na yo wanka. Ina futowa mu kai kicib’is da
Mudi na koma ciki da sauri, Domin kwanan nan haka yake yi. Sai yaita kallo na
yana lashe lebe hade da kashe min idanu. Ya zama direban hayis, Ya siyarda
tumakin Gajiyalle da sauran jarin ta ya sai mota yana lodi gari gari, Ga shaye
shaye da yake yi du ya bata maza yaran karkarar mu da yi.
Sai danaga ya fuce sannan na shige daki da sauri na canzo
kaya na, Bana sallah. Hakan yasanya na canza auduga na zura hijabi na d’auki
kayan koyan d’inki na mufi gidan Bara’atu me koyamin dinki. Baffa na yana ta
baccin sa. A hanya muka had’u da Balki da gayyar yara rab’e rabe wasu na bin
wasu har su bakwai. Ta manyanta sosai tamkar ba Balki ba.
“Balki..”
Na fada cike da mamakin ganin ta.
“Dijengala!! Rai
kanga rai? Yauhe rabon da na saki a ido na?.”
“Ai kuwa dai an jima,
Ina wuni Balki, Yaran ki ne wannan?”
“Eh nawaje na ne,
Biyu sun rasu ma..”
“TubarkAllah. Allah
ya raya su. Balkin Haladu, Ina Haladu?(mijin ta)”
“Uhm dan
bankadaddiya, Mayaudari. Ke fa kihiyoyi na biyu. Namiji ba tabbas ingaya miki
an sa ranar sa da y’ar gidan babire farkon watan gobe. Mu hud’u kenan. Ke shika
biyu yamin saura d’aya auren mu ya datse.”
Na rike baki ina mamaki,
“Subahanallahi! Allah
ya tsare, Yasa ku zauna lapia.”
“Amin dai. Walle ki
tsaya ki cigaba da karatun ki. Yanzu ba hi nan ba tamkar na haife ki. Aure ba
dadi kud’in cefa nema nera talatin.”
Sirrin gidan ta data fara fad’amin yasa na dan gyara tsayuwa
ta ina kallom agogon hannu na,
“Allah sarki! Bara na
wuce Balki sai gani na biyu.”
Na zaro ragowar hamsin din jakata na mikawa yaran, Kafin su
karb’a ta wafce tana cusawa a kanta,
“Mungode Dije. He
anjima.”
“Mu jima dakyau.”
Gaba nayi abuna na wuce gidan Bara’atu, Hankali kwance ta
cigaba da koyamin d’inki, Sosai nake ganewa. Sai bayan magriba na koma gida..
Haka rayuwa ta cigaba da garawa yau da dad’i gobe babu...
..
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN
BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu
hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku
ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da
saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a
shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers
0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin
kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma
wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai
sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike
neman sauƙi😻😻😄🤗.

No comments