MIN QALB 40
##Mamuh#*_MQ 40_*
Auren mijin wata Sam baya cikin mafarkinta ko tunaninta sbd
itama tafison ta bugi gaba da mijinta natane bawai na wata tazo ta aura ba
Wanda koma dai yayane mijin wata ta aura za'a ce,
Babbar damuwarta yanxu shine rashin sanin makomarta a wannan
auren yanxu,
Tarigada tasani tabbas yaudarar kanta take da tunanin rabuwa
da Rabin ran Anty zarah sbd a zabeera Kam ba Maganar saki sai bisaga
girmammiyar qadda ko mutuwa,
To ita ga mutuwar ma ta raba Amma Basu barta ta tafiyarta ba
an daureta da auren Wanda takewa kallon ya haramta gareta sbd Yana mijin
Zarah....
Motsin bude qofa taji Wanda yasata sake rintse idanuwanta
tana sake yin tsit sbd sanin shine yadawo
Bata tunanin iya kallonsa sbd dai ba tantama a daki daya
zasu kwana dan haka gwara ta lafe gari ya waye su Dan inda dare yamusu.
Kallonta yayi yaga yanda take lullube har Kai sai bai damuba
ya nufi closet ya tube yafada toilet yayo wanka Yana fitowa shima kayan baccin
ya dauka ya sanya tareda fesa mist ya nufi gadon ya hayewarsa ya kwanta tareda
Dan Jan lullubin ya shige a gajiye yake shiyasa Yana kwantawar bacci ya daukesa
ba Bata lokaci.
Mamakinsa takeyi ta yanda ba wani tunani ya hau gadon ya
kwanta bayan yaganta akai kwance,Abinda Bata saniba shi Sam baima San wani Wai
ka kwanta qasa ko Kan kujera ko wani dakin Kan kowane dalili ba Abu daya yasani
baya sauya gurin kwanciyarsa akan komai,
Ko agida zarah ce ma idan ta fahimci Yana tattareda gajiya
wani lokacin take komawa dakinta ta kwana tabarsa ya huta shikuma tunda
raayaintane wannan baitaba hanata tafiyar ba saima sakewa dayafi Yi da hakan
wani lokacin
Tana cikin tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita.
Da asuba saidata Gama sallah ya tadata ta tashi tayo alwala
da jallabiyarta tayi sallar tana gamawa ta cire Takoma tayi kwanciyarta Takoma
bacci abinta sbd itamadai bazata iya takura kanta sbd shi ba musamman ma data
lura idan ta takura kanta din ko ajikinsa.
Shima tana jinsa yagama wayoyinsa yazo ya kwanta kusan atare
bacci Yakuma daukesu Basu farkaba sai guraren 10 na safen.
Itace tafara bude idanuwanta ta sauke akan fuskarsa dake
fuskantar tata tafara kallonsa ahankali tana tuno haduwarsu ta farko data biyu
data uku duk agun sata ne take taji kunyar abin nadawo Mata har batamasan tana
rufe fuskarta ba tana girgiza Kai saijin tayi cikin muryar bacci yace"
Kadama kifara wani banzan tunani akaina I can smell your
blushing..
Zaro Ido tayi da sauri cikin wata sabuwar kunya Amma
saidatace"
Wane tunani zanyi akanka dazaisani Abinda kace kanaji?ni
bana tunanin komai....da sauri ta yunqura ta tashi zaune zata sauka ya riqo
hannunta Wanda yasata saurin juyowa ta kallesa zuciyarta na Fara bugawa da
qarfi shima ahankali ya bude idanuwansa dake rufen bacci baigama dakinsu ba ya
sauke akan fuskarta tayi sauri dauke Ido zuciyarta na tsananta bugu har
kirjinta na sama da qasa
Ya gangaro da idanuwan nasa Kan kirjinta dake sama da qasa
da sauri alamar zuciyarta ce ke harbawa da sauri batareda yayi Magana ba sai ya
saketa ta dira da sauri ta shige toilet batareda tasan abinyi ba sai kawai ta
bude sabbin brushes din data gani ta dauki daya tafara brush tana kasa kallon
fuskarta ko a madubi sbd Jin wani iri kamar kunya kamar fargaba da tsoro.
Murtsike kunyarta tayi ta fito tana daure fuska ta
tarardashi zaune Kan sofa Yana kunna wayarsa daya kashe da asuba ta nufi fridge
ta bude ta aduko lemun carrot da lemon ta zauna a wata kujerar ta bude tafara
Sha ahankali batareda ta kalli inda yake ba.
Yana cikin toilet aka kawo musu breakfast din dayayi oda da
kayan sawa ta karba tareda ajiyewa tana qoqarin duba kayan sbd jeans ne da
riguna take gani Abinda takeda burin yiwa Dr khalil zabeera kwalliyarsa har
saiya manta da kowace mace duniya Bayan mahaifiyarsa Amma Ashe basuda wannan rabon.
Astaghfirllah" tace tana ajiye kayan daidai fitowarsa
Taso Fara cin abincin Amma gabaki daya Babu Abinda ta taba
gani aciki bare tasan ya akecinsu shiyasa ta haqura harya Gama Jan ajinsa da ja
Mata Rai yazo ya zauna Kai tsaye tace"
Nifa yunwa nakeji bansan wanne ne naciba wanne ba'a ci Yi
sauri ka nunamin....
Baisan lokacinda ya juyo gaba daya Yana kallonta ba wato
yamayi sauri...
Irin yanda take kallon abincin yasashi sakin wani boyayyan
murmushi akaro na farko
Jin shiru tafara hasala tace"
Nifa yunwa nakeji nace fa.
Baisan lokacinda bakinsa yace"
Ok" ba
Fara zuba Mata tea yayi ya miqa Mata kafin yafara zuba Mata
egg source cikin boiled veggies sbs taji dadin ci Amma Ina tana shanye tea din
taci spoon daya na abincin taji zuciyarta na neman tashi ta ajiye tana kallonsa
tana girgiza Kai alamar bazata iya ciba.
Tea din yasake zuba Mata kafin yasanya spoon yacire komai na
cikin tsakiyar burger dinsu ya miqa Mata yana nuna Mata Tasha da tea din.
Kaf tea din ita tashanye shi sbd shikadaine Abinda zata iya
sawa cikinta shikuma tana kallo yanacin abincin cikin kwanciyar hankali ganin
abin zai tayar Mata da zuciya yasa ta miqe ta shige toilet wanka.
Bata San yanzu akeyintaba Saida tagama wanka ta daura towel
takasa fitowa ta zauna ciki ta shafa Neutrogena oil din data gani aciki tazo
jikin qofar ahankali tace ya miqo Mata kayanta...harta juya ta tsaya cak sbd
tuno hadda bra zai miqo kenan saiya taba Mata gidan nono da sauri ta fito tana
cewa''
Barshi barshi nafito Zan dauka da kaina,. tsayawa tayi tana
Masa kallon mamaki ganinsa zaune ko alamar ma zai miqo Mata kayan beyiba kamar
yanda ta zata kenan da barinta zaiyi a toilet din tayita zaman jira.
Takaici yasanyata daukar kayan da qarfi tana daure fuska
zuciyarta na zugata akan tabi takan qafarsa ta take Amma ta share ta nufi
wardrobe ta bude ta dauko undies dinta tana juyowa taga bayanan kenan yashige
toilet a fili taja guntun tsaki tana cewa''
Anty zarah kinada qoqari gskia.
Turarensa ta fesa kafin ta shirya cikin kayan ta tsaya tana
kallon kanta tanajin wani iri sbd irin pencil jeans dinnan ne yakama Yan
dogayen siraran cinyoyinta har gwara rigar is loose me Fadi ce sosai Amma ba
wani tsayi gyalen jallabiyarta ta daura akai bayan tagyara Daurin talwataccen
gashinta daya dan yamutse gurin bacci.
Zaunawa tayi abinta tana lallatsa wayarta sbd dama can ita
Allah beyita da nuku nuku ba Kuma burintane samun wayayyar rayuwar Jin Dadi da
sakewa, Bata samu daga Wanda taketa mafarki da buri ba wato Dr khalil dinta
yanzun dinma bawai tana maida burinta akan MD bane kawai dai zata sakewarta ne
bazata takura kanta ba shiyasama batai wata doguwar damuwar akan kayan ba.
Dagowa tayi Jin motsinsa idanuwanta suka sauka Kan budadden
jikinsa dake tsiyayar ruwan wanka qugunsa Kuma daureda towel brown da sauri ta
dauke kanta tana Dan Sosa kanta daya dau qaiqayin bazata.
Ganin da gaske shiryawa zaiyi gata a zaune yasata saurin
miqewa Takoma gaban TV ta qurawa Mata idanuwa ko qyaftawa batayi tana jinjina
ko inkularsa lallai wannan mutumin dasuke gani a zabeera Basu sanshi ba.
Tsaf ya shirya cikin qananan kayan wainda suke kalar nata
sky blue jeans da farar transparent shirt ko zama beyiba ya kalli Inda take
yace ta tashi suje.
Da sauri ta miqe zata dauko jallabiyarta yace no need for
that
Aiko tabiyosa suka fice.
Wata kyakkyawar mota ya karba daga hotel din tareda driver
suka fita.
Gurin abokanan aikinsa suka Fara zuwa wani hotel dake kusada
wani ruwa acan suka kwasa sukai bakin ruwan taredasu da abokin nasa mr folaye
da matarsa me sabon qaramin ciki daya 'dan fito kadan.
Sakewa tayi da meenat matar folaye sbd yanda tayita janta
ajiki take suka Fara sabo anan ne ma taci abinci sbd na Nan yanada dama sosai
akan na hotel dinsu sbd akwai chips da noodles akwai pasta duk tasamu taxi daga
Nan suka kwasa zuwa wani farm house inda Nan ma sunyi ciye Amatu tasamu
abokiyar ciye Nan tasake suka ringa cin duk Abinda bakinsu zai iya daukar
dandanonsa Dan itama meenat zuwansu na farko ne Nan da mijinta yayi da ita.
Basu Fara Shirin komawa ba sai dare sosai inda taji tafison
masaukinsu meenat yafi Dadi ba kunya ta roqesa su koma can ga mamakinta kuwa
baice komaiba Amma saigashi anyi musu folaye yasa anmusu reserving suite sukai
kwanciyarsu anan.
Washe gari sukaso komawa Amma suka shiririce itada meenat
wani gurin shopping da aka kaisu gashi yau dinma qananun kayan ne ajikinsu na
yau sunfi daukar kalar fatarsu da yimusu kyau sbd black ne gashi ba laifi
dukkaninsu sunada hasken fata matuqa
Suna zaune a wani snacks and coffee restaurant dake bakin
ruwa saiga Kira yashigo wayarsa Yana dagowa yaga video call zarah na Masa.
Sam baisan meyasa zarah yanzu take Masa video call ba Bayan
shi tunda sukai aure bai tana cewa sunyi video call.
Dauka yayi a natse saigata ta bayyana kyakkyawar fuskarta
dataji simple makeup na Masa murmushi
Ahankali ya sauke numfashi Yana amsa gaisuwarta da dorawa da
cewa''
You look great.
Wani irin Dadi ne yakusa kasheta sbd baitaba yaba
kwalliyarta ba sai yau din ta washe baki tana kallon kyakkyawar fuskarsa dake
fidda wani sirrin kwarjini da kyau tace"
Thank you,ya kake?ya Athens?
Dan kallon wuyanta dake bayyane sbd fadin wuyan rigar
jikinta yayi ba laifi yanayin shigar ya burgesa baisan yaushe zarah tafara koyan saka irin kayan Nan ba ya bude
baki a hankali yace"
Alhmdlh..
Amatu dake hotuna da meenat tunda yafara wayar hankalinta ya
Dan koma kansa tafara qoqarin sharewa gano da anty zarah yake wayar meenat ta
kalleta tana cewa''
Da waye MD ke video call and he seems to be relaxed and cool
da yanayin wayar?
Numfashi Amatu ta sauke tana murmushi tace"
Da matarshi yake waya antyna.
Kallonta meenat tayi dakyau tana sake duban MD dako inda
suke baya kallo sai kawai tura Amatun kansa da qarfi tana cewa''
Oh I'm so sorry I lost my y balance.
Kyakkyawar faduwa tayo ajikinsa sbd Saida gaba daya qirjinta
ya hadu ya manne da nasa dayake shima a bazata yajita jikinsa saiya riqeta sbd
karsu Fadi qasa daka Kan kujerar dayake.
Anty zarah maganar da zatayi bace Mata tayi sbd ganin Amatun
jikin MD ba qaramin raunana ganinta da zuciyarta yayi ba ta maida kallonta Kan
kayan jikin Amatun saitaga komai iri dayane Dana MD din banbanci nata na Mata
nashi na maza hakama budewar wuyan rigar Amatun yasa taji tana kamo nata tana
rufewa sbd Abinda taji Yana danne maqoshinta Kai tsaye ta kashe Kiran da kanta
tana barin hawayenta saukowa ta kife Kan gadon datake zaune tareda fashewa da
wani irin kuka Mai ciwo.
Su kuwa can Amatun ce tafara sakinsa ta sauka daga Kan
jikinsa tana qin kallonsa sbd yanda taji hankalinta ya tashi da yanda anty
zarah ta gansu wani bangaren na zuciyarta Kuma wani irin nauyi takeji saitaji
gurin ya gundureta ma gaba daya ta wuce batareda tacewa kowa komaiba.
Washe gari Koda qarfe dayan Rana tayi sundawo harsunyi
Shirin zuwa asibiti sbd ranar ne ranar sallamar Muhammad shiyasa duk damuwarta
ta kau cikin tsananin farin ciki take su umme ma sunyi waya zasu hade a
asibitin gurin daukosa sbd zumudi tarigasa fitowa Yana saukowa suka fada mota
suka nufi asibitin.
Koda suka Isa sun tarardasu umme
Kallo daya umme tai Mata tasan komai yafara daidaituwa sbd
yanayin 'yar walwalarta daya Fara dawowa.
Bayan dogon formalities aka sallamesa aka Basu dansu murna
agurin kowannensu ba'a mgn saidai anbasu kakkauran sharadin kada aringa barinsa
sanyi na shigarsa sosai sukace sunji.
A gida sasai aka ringa kiransu ana murnar samun nasara
saidai anhana ashigo jirgi dashi saiyayi qwari sosai yasamu lafiya shiyasa ana
sake kwana biyu umme ta tahowarta shima
MAHMOUD din wata tafiya takamashi aka bar Mata anty salamatu.
Ahankali suka Saba da zaman qasar da Jin Dadinta tareda Fara
sanin gurare Dan suke Kai kansu siyayya da sauran wasu abubuwan musamman dasu
meenat Suma sundawo garin saita haihu zasu koma,
Ga Muhammad tuni ya warware yayi girma abinsa yanzu Yana
samun nono koyaushe take ya canza yafara girma gashi hadda jiki sosai yayi
gwanin sha'awa,
MD na kiranta lokuta da dama Amma iyakacinsu gaisuwa sai ya
tambayi Muhammad wani lokacin ma anty salamatu yafi Kira.
Abu daya ne matsalarsu a garin shine rashin turancin arziki
tayiwa kawu mgn saigashi kawu yaje har zabeera da kansa yayiwa su Andi tunin
alqawarinsu na barinta karatu Allah yasa MAHMOUD din na Nan sai sukai Masa
maganar yasanyata makaranta acan da zaman banzar.
Tunda anty zarah taji tafiya zaiyi zuwa Greece taji
hankalinta nason tashi Amma ta danne sbd ba laifi ya Dade sosai a gida wannan
karon saita danne harda saqon gaisuwarta ga Amatu sbd har yanxu tunda akai
auren basuyi mgn ba sbd kowa bai Gama daidaituwa da al'amarin ba.
Zaune suke a Palo itada Muhammad dake koyan zama anty
salamatu Bata Nan taje gidan meenat dake Dan zazzabi sosai ta tayata hidima.
Riga da guntun skirt ne ajikinta Wanda bai kamata ba ko
kadan sai hular babies dake kanta Bata Gama rufe Mata gashin Kai ba Wasa takewa
Muhammad sosai Yana dariya taji bude qofa batareda anyi knocking ba ta juyo da
sauri cikin mamaki sai idonta ya gane Mata shi batasan lokacinda ta saki baki
ba tana kallonsa da dukkanin zuciyarta.
Shima ita din yake kallo yanda Takoma kamar wata yarinya
qarama Babu me cewa itace uwar yaron gabanta tafi Kama da yayarsa ta kusa bama
ta nesa ba.
Muhammad dake bangala dariya ya kalla har baisan lokacinda
ya sakar Masa kyakkyawan murmushi ba yana nufosu.
daukarsa yayi Yana kallonsa cikin tsananin qaunar yaron
yace"
Muhammad you're looking great and handsome.
Kallonta yayi ta sauke kanta tana cewa''
Sannu da zuwa.
Bai amsaba bai Kuma dauke idonsa akantaba saima kissing
Muhammad da yayi a fuska Yana cewa''
Thank you.
Bedroom dinsa ya nufa daukeda Muhammad Yana cewa''
Ko Zaki gyaramin dakin bazai rasa quraba.
Bayansa tabi da kallo tana mamakin kyawun daya qaro da wani
irin haske
Kodan ta Dade Bata gansabane.
Akwatinsa ta tura zuwa dakin nasa ta kallo sbd shine
shigarta na farko
Dakin komai na cikinsa farine Wanda ta fahimci shi din
yanason farin Abu ta dauko mop da bucket da sweeper ta a ajiye tafara gyaran
dakin bayan ta sauya Masa zanin gadon ta goge komai Yana palo tafito Bayan
tagama komai ta karbi Muhammad ya wuce bedroom.
Da daddare Koda anty salamatu tadawo ta tararda zuwansa
tunda tashige daki Bata sake fitowaba Saida safe shima tana Gama shirya musu
komai ta wuce gidan meenat sbd zasu sake komawa asibiti da ita yau.
Dakansa ya dauketa yaje ya Samar Mata admission da komai na
makaranta ya damqa Mata daga can gidansu meenat sukaje dubata.
Dagacan gurin cin abinci suka biya sukaci kafin suka dawo
gida.
Kwanansa takwas a qasar kafin yatafi da kewar Muhammad daya
shaqu dashi cikin kwanaki qalilan Dan kullum a hannunsa yake Rabin kwana sai
dare sosai yake maidasa hannun mamansa.
Itama bayan tafiyarsa yabarsu da kewarsa sbd kwanakin kullum
Muhammad na taredashi.
Sosai ta nitsa cikin karatunta gadan gadan musamman dayake
me wuyane karatun sbd medical ne tana karantar gynecology sai yazamto
hankalinta nakan karatu yanzu fiyeda komai,
USI yazo Mata tareda Dr Salman har so biyu Wanda yasata Jin
Dadi fiyeda tunani musamman usi daya dauki Muhammad a hannunsa ji yayi kamar
zai hadiyesa sbd so da qauna,
Kawu da iyami ma kullum cikin waya suke Gama umme Anty zarah
ce dai har yanzu ba wani sauyi sbd takirata har so kusan uku Bata taba daukar
wayarta ba shiyasa ta Dan dakata tukuna.
Ta bangaren MAHMOUD ZABEERA kuwa Babu wani sauyi a rayuwarsu
saina qaunarsu data zama kamar daya akan 'dansu sbd tunda Muhammad yayi wayon
sanin babansa yake zuwar musu akai akai sbd yaron dako yaushe dadynsa yakeson
gani Dan tuni yayi wayo sosai Dan kusan shekararsa biyu kenan harda watanni.
Duk Wanda yasanta abaya yanzu bazai iya ganetaba idanba
farin sani kayi mataba,
Ta sauya sosai daga Amatun blue fox Takoma AMATULLAH
zabeera,
Sam halayyarta da yanayinta sun sauya,
Yanzu ita mace ce me nutsuwa da Kamala,
Mace ce me aji da ilimin Boko ya shigeta yake Kuma bayyane
atareda ita sbd ko zaman awa daya kayi da ita zaka fahimci da likita kake zaune
musamman gashi suna shekarar qarshe ta kammala karatunta,
Amatse take data samu hutun wannan shekarar taje gida sbd
tayi masifar kewar iyayenta Dan tunda tazo bataje gida ba
Har gwara anty salamatu taje gida harta Dade sosai kafin
tadawo gashi ko yanzu tana Shirin zuwa ganin gida Kuma tareda Muhammad zataje
wannan karon,
Ga USI ma yagama karatunsa yanzu yadan Fara aiki a asibitin
zabeera.
Yau su Anty salamatu da Muhammad suka wuce tana dawowa daga
rakiyarsu airport ta shige daki ta tube tayi wanka tana fitowa ta sanya
three-quarter pink da farar riga Mara nauyi ta daure gashinta da band ta saka
qaramar hula ta nufi kicin ta hado flakes da sabuwar madarar ruwa me sanyi ta
fito Palo tanasha taji ana qoqarin bude qofa Kai tsaye tasan MD ZABEERA ne ya
shigo qasar sbd tasaba da duk zuwansa saidai suji bude qofarsa kawai baya knocking
kamar sauran baqi.

No comments