SARAN BOYE 24
No. 24
...............Baba malam daketa kaikawo na ƙoƙarin ganin komai ya kammala yanda yake buƙata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar baƙonsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ƙarfe biyun ran take a kan ƙafafunta tana hidima. Sauƙinta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta.
Omar ne biye da
shi, dama yafi shaƙuwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai
ada kam sunfi shaƙuwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ɗin yafi Abdallah
zaman kano sai shaƙuwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar
yarone mai tsananin ƙwazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban
malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son
zaman Abuja ba shi.
Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka
iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya
rage ɗin. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, “Umm
Muhammad yaya kun kammala?”.
Ɗagowa Umm tai taɗan kalli mijin nata,
sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, “Abban Nu'aymah wlhy nikam dai
zakama sake rikitamu gaba ɗaya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa
kai kayi wanka dan magrib ta gabato”.
Murmushi shimfiɗe a fuskarsa ya ƙaraso
yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su haɗa. “Ke dai kawo na
taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ɗakkosu fa”.
Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya
ƙaraso wajen baba malam ɗin yana faɗin, “Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka
ba. Dan nikam yau namafi kowa zumiɗin son ganin wannan baƙo mai daraja a
wajenku Abba, dan naga gaba ɗaya hankalinku na kan son ganin an ƙyautata masa,
yau kota abincin buɗa bakinmu bakwayi sai na baƙo”.
“Kace ido ka saka mana? Hakama
malam ƙarami (baban yaron Addah) sai da ya gama ƙorafi kafin ya wuce airport ɗakkosu”.
Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ƙarasa haɗa komai
ita da baba malam ɗin. yayinda Omar da Addah kuma suke ɗorawa tray. Omar ne ya
ƙarasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu inda za'a sauke baƙon.
Hakan kawai ya isa kasan an daratta baƙon sosai, dan duk baƙon da su Baba malam
zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.
Sai da yaga an fita da komai sannan ya
sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike
da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai
dan Baba malam ɗinne ya basu dariya.
Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka
shirya abincin, suka ƙara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air
Fresheners masu ƙamshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar
fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a baƙin asamu mai Asthma ya cutu. Ta ɗan
ɗaga labulen Windows ɗin kaɗan hayaƙin turaren ya ragu sosai. Cikin sa'a ma sai
gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka
tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ɗinsa Umm nama Addah godiya.
Dan tasan badan itaba da aikin baiyi
sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San
jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ƴan
aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.
Motocin na shigowa anguwar
ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera
idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka
tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam
da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara
amma iya mazan kawai.
Duk da yanda guards ɗin Yoohan
suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba
malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya
fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan
ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar
fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin
ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan
yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne,
amma sai ya dake ya basar.
Duk yanda yaketa
faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa,
saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha
har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da
Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai
tsaye.
Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su
Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar
baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba
malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.
Tun a farkon shigowa
gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai
nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma
sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu kamar
wasu jela ko suna ganin za'a cutama Yoohan ɗinne oho musu. Sai da sukaga ya
zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai buƙata sannan sukai masa sallama suka
fito, duk da basuji ya amsa musu da ƙyau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci
inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da buɗaɗɗen ra'ayinsa ya shiga masa
zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ɗin nasu
wani abin yaci a tsafesa.
Yana cikin shawara da zuciyarsa
ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ɗinsu sai ga sallamar su
Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan.
Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama
Momy text message ko za'a dace wayar na a hannunta ta gani.
Koda suka shigo Yoohan
na'a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ƙasa
ido. Abban Adawiya da suka taɓa haɗuwa a orphanage ranar da suka buge yaron nan
sai ganin Yoohan ɗin ya sakashi matuƙar jin mamaki. Duk da ya jima a ransa yana
zargi da hasashen kodai shine mai musu wannan ɗawainiyar. Rashin tabbas ɗin
hasashen nasa yasa bai taɓa yin magana ba sai yanzu ya ɗan gwargwaɗa ma baba
malam cikin harshen larabci.
Murmushi kawai baba malam ɗin yayi, cike
da kulawa ya maida hankalinsa akan Yoohan da suka fahimci a takure yake da
kasancewarsa a wajen. Basu damuba, dan sunyi gamo da waɗandama suka fisa taurin
kai da aƙida amma cikin amincin UBANGIJI sun sami nasarar canjasu. To balle shi
kuma dama suka fahimci zuciyarsa nada rangwame tunda har ya iya kasancewa
maison ƙyautatawa marayu.
Duk da baba malam yaga saɓanin abinda
yay tammani daga Yoohan hakan baisa ya canja komaiba daga ɗokantuwa da mutunta
baƙon nasu. Hakam ɗan uwansa da ƴaƴansu basu nuna wani mamakinsu a fili ba ko
ƙyanƙyamin su Yoohan ɗin, kowa ya shanye a ransa. Ba Yoohan kawai ba, dai-dai
da guards ɗinsa an mutuntasu fiye da zatonsu, dan suma ca akai su zauna ayi buɗa
bakin dasu. Duk da suna noƙewa saboda boss ɗinsu haka baba malam ya matsanta
musu. Ganin Yoohan kuma bai tanka musu ba, yamayi kamar baisan mi akeyiba sai
suka saki jiki aka kwashi gara da su, a ransu kuma suka koma zuba santi dajin
kimar mutanen musamman yanda aka nuna musu suma mutanene masu daraja ba bautace
kawai aikinsu ba.
Yoohan kansa da keta noƙewa da farko
tuni baba malam ɗin ya tsaresa sai yaci, harda nuna masa idanfa baici da
hannunsaba shi zai basa da kansa to, kuma ɗura zai masa. Karan farko a rayuwata
da ni kaina mai ɗakko muku rahoto naga murmushi a fuskar Yoohan yau. Dan shi
kansa a bazata ya saki lallausan murmushin ga baba malam ɗin.
Baba malam yace, ‘Masha ALLAH’ a ransa,
duk da yau ya fara ganin Yoohan sai yaga murmushin yay bala'in masa ƙyau. Haka
dai suka gudanar da buɗa baki cikin nishaɗi da farin ciki. Guards ɗin Yoohan
dake ɗar-ɗar harda Solomon mai hasashen banza sai gasu sun kwashi gara suna
washe baki dajin farin ciki a ransu.
Kiran sallar isha'i ya saka su baba malam
ficewa massalaci akabar Yoohan da tawagarsa. Sai dai kuma bayan fitarsu babu
jimawa shima sai ya miƙe da nufin ɗan yin tattaki ko cikinsa zai sauka. Shi
kansa yasan ya jima a rayuwarsa baiyi irin wannan cin abincinba, ballema a ɗan
tsakanin nan da yake cikin halin ha ula'i. Ta ƙaramar ƙofar da yaga su baba
malam ɗin sunbi shima ya bi, kai tsaye ta kaisa ƙatuwar harabar massalacin
kuwa.
Ko'ina ƙwanyar yake da
haske tamkar rana. Ga mutane maza da mata harma da yara cike da massalacin
harda mata. Yoohan yay tsaye jikin katanga yana kallonsu cike da nazari har aka
tada salla. Ba massallacin kawai ba hatta anguwar kanta sai yaji ta ɗauki shiru
gaba ɗaya, babu abinda kakeji sai sautin karatun salla da baba malam keyi.
Lokacin da ya kammala karanta fatiha mamu suka amsa da “Amin!!!!” sai gaba ɗaya
tsigar jikin Yoohan ta tashi, zuciyarsa tai wani bala'in tsargawa har saida ya
rumtse idanunsa.
Baisan dalilin daya hanashi
komawa ciki ba, haka ya cigaba da tsaiwa har sukai ruku'u. suka sake ɗagowa
sukai sujida. Tsigar jikinsa sake tashi tayi a karo na biyu, dan yanda sukai
sujidan gasu a sahu nagartacce dolene ko musulmin ya gani yaji ƙarin imani a
ransa balle wanda bai taɓama yin sujudar ga UBANGIJI ba.
A hankali Yoohan ya ɗaga ƙafafunsa ya
fara ja baya da ƙyar harya fice a harabar massalacin ya koma cikin gidan. Haka
ya cigaba dajan jiki harya isa falon da aka saukesu da ƙyar. Tsitt guards ɗinsa
daketa faman surutun santin abincin da sukaci sukayi ganin ya shigo kamar a
birkice. Da sauri duk suka miƙe tsaye domin girmamawa. Solomon ya taimaka masa
ya zauna.
Sai kuma duk hankalinsu ya tashi, amma
yanda baiyi maganaba suma sai basuyiba sukai dai masa tsaye cike da tsoron
kodai an cutar dasu ɗinne kamar yanda sukai hasashe tun farko?.
Har aka idar da sallar asham
Yoohan bai dawo hankalinsa ba. Baba malam da ayau baije tafsir ba dama ya ɗauki
alfarma suka sake shigowa. A yanda yaga Yoohan ɗinne ya saka hankalinsa tashi.
Tambayar guards ɗin ya shigayi a ruɗe. Nan sukai masa bayanin abinda suka sani
kawai. na cewar Yoohan ya fitane shan iska sai ya dawo musu a haka, dama kuma
bashi da isashen lafiya, bama suyi zaton zai iya zuwa nan lafiya lau hakaba.
Ɗan shiru Baba malam yayi cike da
nazarin bayanin da Solomon yay masu na rashin yin barcin Yoohan, kafin ya zauna
kusa da Yoohan ya janye hannunsa daya dafe kansa da shi ya maye gurbinsa da
nasa, addu'oi ya fara masa yana tofawa, ya kuma saka Abban Adawiya yin wasu
addu'oin a ruwa ya miƙo masa. Kamar Solomon zaiyi maganar karsu bashi sai dai
ya kasa saboda nauyin da bakinsa yay masa da kuma kwarjinin mutanen.
A gabansu akaba Yoohan ruwan
addu'ar yasha. baba malan ya zuba a hannunsa kaɗan ya kuma shafa masa a fuska.
A take ya fara sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ya buɗe baki da ƙyar
yace, “Thanks”. Murmushi baba malam yayi kawai, kafin yace, “inaga ya kamata a
kaiku masauki ka huta, dan da alama idanun nan naka barci sukeji”. Cike da
mamaki Yoohan ke kallon baba malam, duk da dai ya kasa yarda su haɗa idanu da
ƙyau dan bala'in kwarjini baba malam ɗin ke masa shikam. Sake murmusawa baba
malam ɗin yayi. Ya ɗauke kansa ya maida gasu Omar.
“Farukh a kaisu masauki ko”. Da sauri
Omar yace, “To Abba”..
Da gaske Yoohan barci yakeji fiye da
zatonsa, dan haka ya kasa musama baba malam duk da kuwa shi a yau yaso su juya
zuwa Abuja shi da Solomon da Manager, guards ɗinsa kawai yay shirin bari su
kwana a kanon da safe suma su wuce. Amma sai yaji babu abinda yafi buƙata kamar
kwanciya a yanzun.
Su Malam ƙarami sun kaisu
gida mai ƙyau matsakaici dake gaba da gidansu kaɗan, inda nanne masaukin da su
baba malam ɗin kan sauke baƙi daman. Tsaf yake gidan, saima uban ƙamshi mai
saka kwanciyar hankali da ya keyi. Duk da babu wutar nefa nanma an tada
gen.....
Abin mamaki sai ga Yoohan kamar bugagge,
suna shiga wajen kwanciya ya buƙata. Yana ganin gado kuwa ya zube akai yana
sauke ajiyar zuciya abin tausayi.
Takalma da necktie ma sai Solomon da
Manager ne sukai
dabarar zare masa. Hakama jacket ɗin suit ɗinsa. Sai suka
barsa da shirt ɗin da dogon wando kawai.
Manager ne ya kwana tare da Yoohan duk da shi
Solomon baiso hakaba. Bawan ALLAH nan yanda ya kwana bautar UBANGIJI haka ya ja
doguwar addu'ar samun haske daga Yoohan ɗin. Hakama su baba malam, ranar mafi
yawan addu'oinsu akan Yoohan suka yisu da ga su har iyalansu. Da asuba aka
kawoma Hamza abin buɗa baki, daga Yoohan har guards ɗinsa barci suke kwasa masu
a lokacin.
★★★WASHE GARI★★★
Washe gari
sai ga kowa ya tashi banda Yoohan, barci yake cike da kwanciyar hankali, dan
haka baba malam daya zagayosu har sau kusan uku ya hana a tadashi.
An kawo musu lafiyayyen breakfast
sukaci suka ƙoshi, wajen sha biyu ma aka sake kawo musu abinci nanma. Ganin har
ɗaya saura bai tashiba Solomon ya bama sauran ƴan uwansa shawara akan su tafi,
shima zaije ya sayoma Yoohan kaya ya kuma nema musu ticket. .
Basu musama wannan shawara ba, suka
shirya suka tafi harda Solomon ɗin, dan sai da suka kaisa ya kammala uzirinsa
kafin su sake maidosa gida, sukaje sukai sallana da baba malam da yake a
lokacin sun samesa tsaye a ƙofar gidansa ya dawo daga orphanage ne..
Baiso tafiyar tasuba, amma sai
bai hanasuba tunda ƙila sunada uziri. Ya musu godiya sosai tare da basu
tsaraban da aka shiryama Yoohan ɗin dan suyi gaba da ita, suma kuma aka basu
tasu. Yanda su baba malam ke musu godiyar sai duk abin ya ɗaure musu kai da
saka jikinsu yin sanyi akan a ƙidarsu. Har suna hasashe a ransu dama haka
musulmai keda kirki da karamci amma ake aibantasu da nuna musu suba mutanen
kirki bane? To su dai gashi jiyane karon farko da sukai mu'amula da musulmai
hausawa mai tsaho amma sai basuga hali mara ƙyau ɗin da ake faɗar suna da shiba
saima alkairi da ƙyawawan halayya abin koyi.
Sun tafi da wannan alkairai da akai musu
cikin rai sosai.
Bayan wucewarsu baifi da mintuna
talatinba Yoohan ya farka. Yayi matuƙar mamakin ganin inda ya kwana, manager ya
taimaka masa da ruwan wanka, Solomon zai shiga gabatarma Yoohan ɗin da kayan
daya siyo masa sai ga malam ƙarami da kaya sabbi fill ya kawo. Sai kuma abinci
da aka shiryoma Yoohan ɗin tunda sunsan bai karyaba shi.
Haɗa kayan Solomon yay
gaba ɗaya ya kai ɗakin ya ajiye. Ya juya zai fita Yoohan ya fito. Dakatawa yay
ya gaidashi cike da girmamawa. Yoohan da kejin kansa sakayau kamar ba shiba ya
amsa masa idanunsa nakan kayan da Solomon ɗin ya ajiye masa. sai dai baiyi
maganaba sai shi Solomon ɗinne yay masa bayani.
Zama yay ya gyara
jikinsa tsaf, ya buɗe kayan duka, na Solomon ƙananun kayane, nasu baba malam
kuma shaddace ruwan zuma da akaima ɗinki mai ƙyau kuma dai-dai shi kamar an
gwada. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa saka kaya makamanta hakaba. Duk da kuwa
suma a nasu yare suna ɗinka shigensu amma shi bai taɓa sha'awar yin hakanba. A
yau kam sai yaji sun birgesa har yay sha'awar sakawa. Haka ya warwaresu ya
saka.
Baisan lokacin daya furta kalmar
‘Woow!’ ba a fili yana sake kallon kansa a mirrorn ɗakin. A haka manager da
shima yay shiri tsaf a kayan da aka kawo masan ya shigo ya samesa. Sosai yake
yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan shima, sai ko Yoohan ɗin ke sanar masa shi
bai taɓa sakawa ba sai yau. Hamza yayi mamaki sosai, duk da daga jiya zuwa yau
ya fahimci su Yoohan sunada tsauri ko a cikin Christians ɗin ma, dan ya karanci
yanda guards ɗinsa suka ringa gudanar da al'amiransu.
Sun fito falo Yoohan yaci abinci,
bayan ya kammala babu jimawa sai ga Abba da Baba malam sun shigo. Su kansu
bakinsu bai iyayin shiru ba sai da suka yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan. Ya
duƙar da kansa ƙasa saboda kwarjinin da suke masa yana godiya a garesu,
musamman yanda suka sakashi yay barci jiya bayan kwanaki tara daya kwashe baiyi
ba.
Cikin hikima ta masu ilimi baba malam ya
nuna masa basune ba, UBANGIJI ne yay ikonsa, su nasu kawai roƙone cike da
yaƙinin samu. Duk da Yoohan bawai ya fahimci maganar tasu bane sosai saiya gyaɗa
kansa kawai. Sun ɗanyi hira kaɗan, duk da Yoohan dai bai saki jikiba sosai.
Hamza ne ke biyema su baba malam ɗin, Solomon ma baya saka baki. Wannna ɗan
zaman nasu ya saka Yoohan ɗin sake jinjina mutuncin mutanen da sanin darajar ɗan
adam ɗinsu. Sai da su baba malam sukayi sallar la'asar sannan sukai musu
rakkiya har airportda kansu suna sake roƙon Yoohan ɗin yazo musu bikin salla
harma da Manager.
Yako amsa zaizo kodan yay gaisuwa da yaran
orphanage.
________________
Guards ɗin Yoohan sun iske madam Chioma
ashe bata gari tayi tafiya zuwa ƙauyensu mamarta babu lafiya, saƙon kuma ya
risketa bayan wucewarsu kano babu jimawa. Dan haka ta wuce hardasu joy da
Gebrail. Su Victoria ne kawai da ƴan aiki suma saboda makaranta ne.
Sun shiga da tsaraban cikin gida suka
ajiye har boss ɗinsu ya iso. Aiko zuwa biyar na yamma sai ga kiran Solomon yace
suje su ɗaukesu a airport.
Su Abraham sunyi murna sosai na
dawowar yayansu, sunata kallon kayan jikinsa mamaki na cinsu. Sai dai sun kasa
tambaya dan babu fuska. Shi kuma bayan yaji komai na ciwon kakar tasu sai ya
shige sashensa yay kiran momy.
Sun tattauna sosai ya basu shawarar ɗakkota
a taho da ita nan Abuja ya dubata, dan ashe dama tun jiyan suke neman layinsa
amma bai shigaba. Bayan sun ajiye wayar sai yay kwanciyarsa. Wani barcinne ya
sake ɗaukarsa mai nauyi yauma. Bai kuma farkaba sai gabannin asuba.
Washe gari tun kusan goma na safe su Momy suka iso abuja,
sun iske Yoohan ɗin ya gama shiryawa tsaf game da jikin kakar tasu. Suna isowa
kuwa ya dukufa kanta. Cikin amincin UBANGIJI sai gashi tun aranar jikin nata ya
fara sassautawa.
Wannan hidimar jinya ce ta
mantar da madam Chioma sake bin ba'asin zuwan Yoohan kano har ma hutunsa ya
ƙare yabar abujan.
*_A KWAN A TASHI_*
Babu wahala wajen UBANGIJI, dan
gashi yau saura kwana biyu kacal salla, kowanne yanki na musulmi suna cikin
shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan😢.
Yayinda su Nu'aymah ƴan saudia keta
shirin dawowa suma a ranar sallar...........✍

No comments