Breaking News

FURUCI 67-68

 


🗡 *FURUCI*🗡

         💔💔

       

*(Murd'add'iyar Soyayya)* 💓❣💘


Story and written 

            By 

NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸



              🅿️67 to 68


                   Dedicated 

                          To

           My lovely  

                     *Ummi*

                         and  

                       Lovely          

                     Daughter 

                     *ZARAH*


           My Novels

*NAYI RAYUWA DAKE* 

*SANADIN ACCIDENT*

*SAKAYAR CUTA* 

*RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*HAYATUL MAHAYAT*

*MUGUN SARTSE*

         Loading....🖊

🗡💔FURUCI!!!!💔🗡


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




 🅿 67 to 68




Mai da duban shi Maher yayi sosai yace " Ayna ada bakay shiri da Gimbiya Bahijjat sabida tayi miki kutse ma'ana ta auri wanda kike mutuwar so ki aura amma segashi kwatsam kinje gidan cikin sakin fuska harma Kika taya gimbiya Bahijjat Hira wanine yayi miki nasiha Kika gane abinda kikeyi badede bane ko Kuma wani kud'irin nakine yakaiki ? " 


" Ihh ihhh dama dama kawai de naga hakan baidace bane tunda tsayin shekaru bashida niyyar auran nawa shine nahaqura " 


Jinjina Kai Barrister Maher yayi yace " nafaminta to maiyasa kikacema baby tacema Momyn ta wato gimbiya Bahijjat takai mata abinci a ranar ? " 


Zaro ido Ayna tayi tajuya tadubi Barrister Jamil rumtse ido yayi cikin matuqar razana dajin tambayar  da Maher yayi dan Kam batayi tunanin wani yaji wannan FURUCIN ba hakane Ayna babu wanda yaji akwai de tsabar qwarewar aykine irin na Maher tunda kinyima baby magana a qasaqasa shine yake kyautata zaton hakan Kika fad'a to amma marar gaskiya ko cikin ruwa gumi yakeyi bari muji wace amsa Ayna zatabama Barrister Maher cikin rud'ewa darawar baki tace 


" Am hakanan kawai nace haka " kenan babu wani dalili ? " d'aga mishi Kai tayi alamar eh murmushi Barrister Maher yasake saki sannan yace " to bayan gimbiya Bahijjat tagama ma baby abinci tashiga wanka maiye yakaiki cikin kitchen d'in ? ko gubar kikaje zubawa shiyasa Kika bar gidan bakijira fitowar gimbiya Bahijjat daga toilet ba ? "  


Objection yamai sari'a yakamata Barrister Maher yadena jinginama Ayna lefin dabata aykataba " Barrister Jamil qorafi bai karbuba duk tambayoyin da Barrister Maher yakeyi akan hanya suke cigaba Barrister Maher " cigama Barrister Maher yayi " kotu tana sauraranki " wata irin zufa tafara karyo mata cikin sanyin jiki tace 


" Eh nashiga kitchen amma ruwa kawai nasha Kuma dalilin dayasa natafi inada wani uzuri ne na gaggawa " 


" Idan nacinka dede uzurin zuwa Skul kaima baby wannan yoghurt din ne ko ? " Girgiza kai tayi tace " a a ni banje Skul d'in su baby ba " kin tabbata ? " Jinjina Kai tayi sake tamke fuska Maher yayi sosai sannan yajuya yace 


" Yamai sari'a Ayna ta tabbatar ma kotu cewa ita bataje Skul d'in su baby ba a wannan ranar to nikuma inada qwaqqwarar hujjar dazata tabbatar makowa cewa taje Skul d'in wani bawan Allah Wanda yabuqaci da a boye sunan shi sabida kudin fuskantar barazana yad'auki video Ayna alokacin dataje cikin Skul d'in sabida yadda yaga yanayin ta yasa yaji bai yarda da itaba video yana cikin wayata ayanzu haka zan miqomaka yamai sari'a a kunna makowa yagani miqawa yayi akabama Alqali hayaniya kotu tad'auka tsawatar wa Alqali yayi sannan kowa yayi shiru aka kawo abu aka kunna 


tun lokacin da Ayna tafito daga mota har zuwa lokacin da tabama baby yoghurt da hannunta bayan tarage tajuyo dashi tana sakin murmushi bayan tafito daga cikin Skul d'in tajefar da sauran yoghurt din tashiga mota tajata aguje " hayaniya kotu tad'auka sosai itako Ayna sosai tarikice Aunty Bahijjat kuwa kuka tasake saki da qyar Alqali yasamu akayi shiru sannan Barrister Maher yasake maida duban shi kan Ayna yace 


" Kince bakije Skul d'in ba sekuma gaki kowa ya tabbatar da kinje yanzu kotu tanason sanin a Ina kikasaka gubar cikin abincin ko cikin yoghurt d'in ? " Cikin kuka Ayna tace nifa wallahi bansan komiba itace tace nasiyamata yoghurt shine nasiya nakai mata " ok hakane ? " yanzu idan har kin tabbatar babu komi cikin wannan yoghurt d'in to kishanye sauran gashi nan " ayni banashan yoghurt idan nasha amai yake sakani " ayko yazama dole Kisha dan tabbatar da babu guba acikin shi "


Objection yamai sari'a " tace batashan yoghurt yana qoqarin tursasata akan doke tasha " Barrister Jamil qorafi bai kar'buba yazama dole Ayna nasha wannan yoghurt d'in kotafadin gaskiya " cikin sanyayyar gyuwa Barrister Jamil yakoma yazauna kuka Ayna tasaki tace 


" Bazan iya Shan wannan yoghurt d'in ba " dubanta Barrister Maher yayi sosai yace " to sabida mai ? " sake fashewa dakuka tayi tace " sabida idan nasha mutuwa zanyi " sabida mai ? " Sabida akwai guba acikin shi amma Allah nima bansan waye yabayarba nide ankirani da boyayyar number akabani aykin sabida inajin haushin Gimbiya Bahijjat yasa na amsa amma wallahi ni bansan baby zata iya mutuwa ba idan tasha " kina nufin bakison ko wayeba sabida mugun Sha Shanci da hauka irin naki  to yanzu gashi komawaye yatsomaki ciki " yamai sari'a Ina roqon wannan kotu mai alfarma data wanke gimbiya Bahijjat agaban kowa tunda ayanzu kotu ta tabbatar batada lefi sannan Ina roqon abada umarnin bamu gawar baby danyi mata sutura sannan a qarshe inaso kotu tad'age wannan shari'ar zuwa wani lokaci yadda zamu binciko duk wani mai hannu cikin wannan kisan nagode yamai sari'a " 


D'aga haka Barrister Maher yakoma yazauna bayan 'yan rubuce rubuce Alqali yace 


" Bisaga qwararan hujjoji da kotu tasaurara ta tabbatar cewa gimbiya Bahijjat batada lefi dan haka kotu ta wanketa sannan tana bata haquri akan sakata cikin damuwa da akayi sannan Kuma kotu tanama gimbiya Bahijjat gaisuwar rashin 'yarta Nuratu Zaffar wato baby Allah yayi mata rahama sannan kotu zatatsare Ayna har zuwa lokacin da za'a tabbatar cewa dagaske sata akayi sannan kotu tana umartar ACP Kabir da yayi jagora abada gawar baby ayimata sutura sannan ayi qwaqqwarar bincike agano gaskiyar abinda Ayna tafad'a azama nagama wannan kotu tad'age wannan shari'ar zuwa 13 ga wannan watan 13 February kooooooootuuuuuuuu " 


Aguje gimbiya Bahijjat tarugo ta rungumai Maher wani irin kuka take saki Wanda batasan wane iri bane Kama hannun ta yayi suka fita Ammin da Umma Sarki Zaid da su Aunty suka nufi Maher taruwa sukayi suka d'agashi  sama suna murna adede lokacin Zaffar ya iso kama hannun Gimbiya Bahijjat yayi yace 


" Nagode ma Allah dama niyi imanin bazaki iya kashe baby ba muje gida " janye hannun ta gimbiya Bahijjat tayi  tace " bazan koma gidan kaba Zaffar sabida abu 2 na farko nasake tabbatarwa Mahaifiyar ka bata sona sannan bazan iya cigaba dazama a cikin gidan kaba bana ganin baby hakan babban tashin hankali ne agareni " taqarashe fad'ar hakan cikin tsananin kuka 


Comments please

No comments