SARAN BOYE 22
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
No 22
*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI
SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA
WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA,
WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA
JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU
GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN
AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA
BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA
SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI
DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC
(MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE
HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR
INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN
MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE
YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN
KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI..
MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 22
...............Hankali tashe guards ɗinsa ke kallon juna,
kowa nama ɗan uwansa tambaya da idanu dan bakunansu sun musu nauyi har Yoohan
yabar sashen church ɗinma gaba ɗaya.
Jigum-jigum sukai da fatan ALLAH yasa ya dawo
da wuri kafin madam Chioma ko papa wani ya fito daga cikin church ɗin.
Sai dai kuma addu'ar tasu bataci ba, dan
bayan kamar mintuna ashirin da barin Yoohan wajen Rich da ya ga bai dawoba ya
miƙe ya biyo bayansa bisa umarnin Madam Chioma. Yanda yaga Guards ɗin sunyi
diri-diri da idanu lokacin da yake tambayarsu ina Yoohan ya sakashi daka musu
tsawa. Sake rikicewar sukayi, kowa na inda-indar bada amsa. A haka Madam Chioma
itama data biyo bayan Rich ɗin ta samesu. Sake ruɗewa sukayi, dan sunsan idanma
azaba ce tafi papa akan Yoohan, ga Rich shima ɗan babu sauƙine.
Da ƙyar driver ya iya dauriyar faɗa musu yanda
akayi, jikinsa har rawa yakeyi. Yanda Madam Chioma ta rikice sai ka rantse
yaronta ɗan shekara biyu ko uku ne ya ɓata. A take ta birkice lissafin Guards ɗin
Yoohan da securitys ɗin church ɗinma kansu. Ta kuma tabbatar musu nanda awa
biyar idan Yoohan bai dawo ba saisun gane kuransu.
Ana a cikin wannan dambarwar ne aka
tashi daga church ɗin. Mutane suka fara tururuwar fitowa suna nufar inda ake
rabon abinci. gudun kar ai abin kunya Rich ya shiga lallaɓa madam Chioma akan
ta kwantar da hankalinta maybe Yoohan gida ya nufa, tunda duk sunsan a yanayin
da yake baya buƙatar kowanne kalar hayaniya. Zata iya yuwuwa ya ƙosa ne da
zaman shiyyasa. Da wannan ya samu yaci ƙarfinta suka koma ciki inda suka tarar
duk wanda zai fita sai yaje ya jefa kuɗin baikon sa tare da karɓar wani abu da
papa ke saka musu a baki sannan mutum ya fice.
Matsawa madam Chioma tai kusa dashi tai
masa magana a kunne, kansa kawai ya gyaɗa mata yana murmushi. Ita kuma ta juya
ta fito yaranta da su Mira na biye da ita. Koda suka fito sai manyan mata suka
zagayeta anata miƙa gaisuwa ga matar Pastor, harma da mazan da matasa kowa
burinsa ya gaisheta. Yayinda wasu keta tambayar ina Yoohan dan sun riga duk sun
gansa ɗazun. Da yake shi dama zuwan nasa bawani sosai bane saboda yanayin
aikinsa sai yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa
a daren sha biyar.
Cike da yaƙe madam Chioma ke basu amsa
da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay
gaisuwa da kowa.
Da ƙyar ta samu kanta daga wajensu,
gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira yaƙi ɗaga
waya. Daga ƙarshe ma wayar bata shiga.
Tun shigowar motocinsu ƙaton harabar
gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya
shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam
Chioma ta ƙwalama maigadi kira cikin ƙaraji. Jikinsa na ɓari ya ƙaraso gareta
cikin cika umarni.
Kafinma takai ga
jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar
Yoohan baizo gida ba. Gaba ɗayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo
waya suka shiga nemansa..........😒
🙄😏Mufa an ishemu kamar wani ɗan gwal🤕😤.
_____________________________
Koda Yoohan yabar gidan
wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ƙyar yake jan motar saboda nauyin jiki
dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
Yana tsaida motar a inda ta dace
ya ɗan kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman
masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ɓangaren na ƙarfafasa akan
dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna
har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. Ɗagowa
yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa
tana gab da tsinkewa.
“Na shigo” ya faɗa kawai
cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da
buɗe motar ya fita.
Wani matashin saurayi da zasu
iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ɗauke da murmushi.
Kallo ɗaya zakai masa ka shaida shiɗin musulmine, dan yana sanye cikin shadda
bara sol dataji ɗinkin tazarce, ga ƙaton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza
baƙar dara mai taushi.
Tunda ya tunkaro
Yoohan ɗin kallonsa yake ta ƙasa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci
yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa
yana busar iskar dake kaɗawa ta hantsi mai gauraye da ɗumin rana.
“Ina fatan dai baƙo
nane?”. Saurayin yay maganar fuskarsa ɗauke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa
ya gama shaida Yoohan ɗin ba musulmi bane.
Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai
batun yanzuba, a mabanbanta ƙasashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da
su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar
yanda aka ɗorasa a hakan tun ƙuruciya. Ya dai yarda zai ƙyautatama mai buƙatar
taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da
gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
Sai dai kuma gashi yau a karan farko na
tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a
jikinsa. Duk da babu ɗigon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya
jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai miƙama saurayin hannu.
Saurayin ya sake faɗaɗa fuskarsa
da murmushi yana faɗin, “Ina godiya ƙwarai da amsa wannan gayyata tawa da banyi
zaton zata karɓu ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan
kamfani namu mai albarka”. Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi
haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya
mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. “Dr Yoohan Goshpower”. Ya faɗa a
hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ɗinsa mai amo fita
da ƙyau ba. “Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor”.
“Karka damu” Yoohan ya faɗa a
taƙaice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ɗinsa dake
a haɗe masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci
da lafiya ga jikin al'umma.
Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya
kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ɗin. Godiya
Yoohan ɗin ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gyaɗa kansa tare da
yima kansa mazauni shima.
Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan
ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ɓoye-ɓoye Hamza
Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da miƙa masa envelope yana faɗin,
“Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai
tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar
amma taƙi isa gareka. Shiyyasa na buƙaci dama nazo ni gareka da kaina na kawo
maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
Yoohan daya gama duba takardar ya
ɗan ɗago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya haɗiye
abinsa a rai yana ƙoƙarin maida takardar cikin envelope ɗin.
Duk da Hamza yayi mamaki
da ganin Yoohan ɗin a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya
haɗiye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce,
kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan
gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin
hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, “Yallaɓai ina fatan dai zaka
amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata
alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a
gareka domin nuna girmamawarsu a kanka”.
Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman
hikima sukai masa daɗi a rai, har yay wani ɗan motsi da laɓɓansa mai kama da
murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ɗan lumshe na wasu sakanni yana
nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar
hayani, ba kuma ya buƙatar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ƙuntatama
wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa.
Buɗe idanunsa yay a hankali ya ɗan gyaɗa
kansa, “Babu damuwa zanje ɗin, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai”.
“Ni kuma Doctor?”. Manager ya faɗa yana ɗan waro idanu. “Indai kace bazakajeba
nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da
sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka buƙaci yimin karamcin da bai
shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai
shiga tarihin farko da ƙarshe na rayuwata”.
Manager ya gyaɗa kai a
ransa yana faɗin ‘daga ganin wannan a Christians ɗinma inaga ɗan ɗariƙar
Catholic ne, ALLAH yasa ina ɗaya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu
haske’ a zahiri kuma sai yay murmushi da faɗin, “Babu damuwa, indai kana
buƙatata a tawagar masu rakkiya bazan ƙi ba”.
Hannu Yoohan ya miƙa masa tare da yin godiya,
kafin ya miƙe alamar zai wuce dan yasan hankalin families ɗinsa nacan a tashe
da rashin ganinsa.
Har mota Manager yay masa rakkiya yana ƙara
masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ɗin ke jin daɗin
shigowarsu cikin manyan Customers.
★★★
Lokacin da Yoohan ya iso
gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma
yana shirin kiran police station yay report.
Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai
abinda ke faruwa a gidan, dan yaga baƙin motoci da yake ƙyautata zaton na
Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ɗinsa da sauran securitys ɗin gidan
na sauke manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba
ya nufi ƙaton ƙofar falon nasu na glass da yaja manya kuɗaɗe masu nauyi koda
ba'a faɗaba.
Wani ihun farin ciki Miracle ta kurma
dan itace ta fara ganinsa, kafin ta kwaso a guje tazo zata ɗane masa jiki. Sai dai
yanda ya wani uban tsumewa ya sakata jan birki a gabansa ta kama hannunsa kawai
ta ƙanƙame a ƙirjinta. A take sauran yaran gidan da baƙin ƴammata da samari
yaran Uncles ɗinsa suma duk suka taso kansa. Basubi takan tsumewar tasaba sukam
duk suka rungumesa.
Da ƙyar madam Chioma ta samu suka
sakesa, itama ta matsa ta rungume abinta tsam yanda takeso hawaye na gangaro
mata akan fuska. Hannunsa yasa ya ɗan buga bayanta kaɗan tare da ɗagota yana
mamakin hawayen na miye? Batare da yace komaiba ya ciro handkherchief a
aljihunsa ya share mata hawayen.
Ƙarasowar su Papa da
Uncles nashi uku yasa madam Chioma matsawa suma duk suka rungumesa, hakama
matansu. Shikam dai kansa sake ɗaurewa ya keyi, dan haka ya tambayesu wai ko
lafiya?.
Basu bashi amsaba sai da Madam Chioma
data kama hannunsa ta kaisa har saman kujera, Victoria ta kawo masa ruwa dan
kowa yasan yafi ƙaunarsa sama da kayan zaƙi. Bai musaba ya amsa yasha kusan fin
rabi, sannan ya sake binsu da kallo da sake tambayar yaya akayi wai?.
Gebrail ne ya sanar masa da
komai. Hakan ya saka Yoohan ɗin dafe kansa dake sara masa kaɗan-kaɗan yana ɗan
lumshe idanu. Shi abin nasuma takaici ya bashi sosai. Amma sai baice komaiba.
Sanin bazai ceɗinba yasa babu wanda ya damu da jiran sai yace ɗin. Saima ringuɗa
da sukai Dining domin yin breakfast ɗin da suka kasa yi tun ɗazun.
Shi dai Yoohan duk a takure yake
matuƙa, amma sanin baƙar masifar Uncle Zamani yasa shi haƙura ya zauna akai
breakfast ɗin da shi, wanda shi sam ma baici wani abin kirki ba. Bayan sun
kammala sukai sama shida sa'anninsa su uku, sai Rich daya dawo daga nemansa.
Amma duk masifar da yay masa akan ɗaukar mota ya fita shi kaɗai a wannan halin
da yake ciki sai bai kula Richard ɗinba. Shima bayan gama masa masifar sai ya
watsar dashi ya biyema su Osen kawai da suka baje a falon Yoohan ɗin suna
kwasar dariya da hirarsu ta shaƙiyanci akan ƴammata.
A haka Solomon ya shigo da kwalaben
barasar da sukai Order, sai kofuna da ƙanƙara. bayansa cikin ma'aikatan gidanne
ɗauke da tray da aka shiryo gasashen naman kaji a cikinsa wanda zasuyi amfani
dashi wajan shan barasan.
Sai da suka jera musu komai yanda ya
dace kafin su fice su barsu. Miƙewa Yoohan yay zai shige bedroom dan ya rage
kayansa. Da sauri Godwin yace, “Mr-x ina zuwa?”. (Dan haka duk abokansa ke
kiransa da shi, Rich kawai yafi kiransa da Doctor) Yamutsa fuska Yoohan yay
yana hararsa, dan dama abokin bugawarsa ne, kawai dai dan yau baya cikin good
mood ne. “Ina zuwa” ya bashi amsa a taƙaice yana shigewa.
“Wai mike damun
Boss ɗinka ne?”. Joseph ya faɗa yana kallon Richard. Cikin damuwa Rich
yace, “Matsalarsa ce dai ta rashin barci ta motsa, nayi-nayi yasha barasa ko
nai masa allura yaƙi”.
Godwin ne yace, “Shegen
taurin kan Mr-X ai ba ƙarewa yakeba, ni wlhy sonake wataran na samu wata na
biyata tai disvirgin ɗin gayen nan kozai ware yaji daɗin rayuwarsa. Duniya ai
sai da jin daɗi, amma shi yabi ya wani ƙanƙame kansa kamar wanda bai wayeba ko
ba'a turai yay rayuwa ba. Minene a giya? Dama da shanta kawai nishaɗine, kuma
tunda munada aikin yinmu sai fa lokaci- lokaci muke shanta, ba kuma mai cutarwa
ba.......”
Katsesa Joseph yayi da faɗin, “Kaga G.
Ka barsa, Mr-x tsarinsa kenan shi da ra'ayinsa, koka manta tun muna secondary
shi dama komai nasa da ƙa'ida ya keyi. so ni banga abin damuwa da har zaku
shiga masa rayuwa da yawaba, kubarsa ya tsara ma kansa yanda yake buƙatar ya
rayu Ok?”.
Richard yace,
“Hakane Joseph, amma idan ka lura shima fa bawai jin daɗinne baya buƙata ba,
kawai shi dai ya ɗauki burin duniyane ya ɗaura akan aikin nan namu, a tunaninsa
duk abinda zai sha zai iya shagaltar da shi akan aikinsa, sannan mata ma zasu
iya takura masa su hanashi yin rayuwarsa da ƙyau, kunsan mutum namu ɗan hutune,
ko mace bata faɗa masa son jiki ba”.
Dariya suka kwashe dashi gaba ɗaya suna
mai haɗa kofunan da suka zubama barasa a ciki alamar chssss.
Hakan yayi dai-dai da fitowar
Yoohan daga ɗaki, ya canja kayansa zuwa wando da riga duk blue na kamfanin
adidas. Duk da hayaniyar tasu bai sonta haka ya zauna a cikinsu dan gaba ɗayansu
childhood Friends ɗinsa ne, kuma ƴan uwansa na jini dan duk ƴaƴan ƙannen papa
ne, sai Osen ne kawai ɗan aboki shima kuma iyayen nasu sun zama kamar ƴan uwa,
sai kuma Richard shi kuma abokinsa. Amma tare sukai secondary school dukansu,
hasalima duk ajinsu guda.
Osen ne ya miƙa masa cup duk da yasan ba
sha zaiba. Aiko Yoohan ɗin ya yamutse fuska da girgiza masa kai tamkar mai
ƙyanƙyamin giyar ma. Dariya suka sanya masa suna zuba masa shaƙiyancin da suka
saba, tare da labarin daɗin da ƴammatansu ke jiyar dasu harma da karuwai dan
dukansu ji suke da ƴan kuɗaɗe a aljihu. iyayensu kuma sun tara, sanna suma ɗin
gwasaken kansune sosai. Shiyyasa suke zuba tsiyarsu a garin Abuja da Lagos
kamar babu gobe.
Duk abinda sukeyi saboda
Yoohan yaji haushine yay budurwa, dan har maganar ƴammatansa dake bala'in sonsa
suke kawowa harda Miracle, tare da koɗa ƙyawunta dama na sauran ƴammatan da
Yoohan ɗin shi yake nuna kullum basa gabansa.
Joseph yace, “Mr-x daga yau
ka fara taka tsantsan da G-boy, dan ya shirya yanda za'a maka fyaɗe, kaga sai
kasan zaman da zakai da shi”.
Mangare ƙeyar Joseph Godwin yayi yana faɗin,
“Munafiki, halan giyan ya fara kai maka karo zaka haɗani da shi”. Dariya suka
kece da ita duka. Yoohan dake harar Godwin ɗin yace, “Barma wani kare kanka
naji sanda kake faɗa ai, an faɗa maka ni irinka ne da baida damuwa saita kwana
da mata. Please, try and change your habit kaima”.
Nanma dariya suka sanya, dan sunsan kam
G-boy shege ne akan mata, duk yanda zai yaudareki ya biya buƙatarsa ya sani.
Rich yace, “Calm dawn my Doctor, duk randa ya aikata maka haka zuwa zakai kawai
ka tona masa asiri wajen babien sa, dama gata da shegen kishi kamar taci wuta a
cikinta.......”
Osen dake ƙoƙarin yagar nama
yace, “Ashe ka ganota, nifa haushi take bala'in bani, amma G-Boy sam baya ganin
laifin hakan da take masa, da kayi magana saiya nuna cewar son da take masa
ne”.
Ajiyar zuciya Yoohan da warin
giyar ya fara hawar masa kai ya saki, ya miƙe a hankali ya ɗauki basket ɗin da
aka zubo musu kwalaban giyan ya nufi hanyar fita. Da sauri suka shiga kwala
masa kira akan ya kawo musu abinsu, amma baiko juyoba ya fice yama kullesu ta
baya ya sauka ƙasa. Canma iske su Papa yay suna ɗora tasu suna hira da dariya
harda su Momy suma sha suke. Sosai ransa ya sake sosuwa, sai kace ba yanzu
papan ya gama wa'azi a church ba. Tsaki yay ciki-ciki ya wucesu batare da ya
tanka musu ba yana ƙwalama Solomon kira.
Da gudu ya shigo kuwa, ya miƙama
masa basket ɗin kawai babu bayanin komai ya fice a falon. Garden ya nufa. Sai
dai kuma yana shiga ya hango su Miracle a cikin swimming pool suna wanka. Cike
da farin ciki duk suka zuba masa idanu, kowacce kwaɗayinta a kansa na fitowa
fili saman fuskarta. sai dai kuma tuni ya juya yana jan wani tsakin takaici.
Wannan taron yasa sam bayason zama gidan ranar lahadi, yanzu haka zuwa anjima
gidan sake cika zaiyi da wasu baƙin kuma. Solomon ya bama key ɗin ƙofar
sashensa daya kulle su Rich, yace yaje ya buɗesu, shi kuma ya fice gidan a ƙafa
duk da kuwa rana ta fara ɗagawa kuma akwai ɗan zafi............✍
Amin afuwa jiya ciwon kai ya hanani sukuni na kasa typing ɗin🤦🏻.

No comments