MIN QALB 27
MQ 27_*
Tana shiga palonsu ta zube qasa Kan gwiwowinta tareda
fashewa da wani irin kuka me tsanani da zafin Rai,
Da sauri momynta ta qaraso ciki tana rikota tana Kiran
sunanta cikin nata ciwon ran me tsanani da tausayin 'yarta tana sake kamota
tace"
Nuratu please kada kiyi irin wannan kukan wlh karyamin
zuciya zakiyi bazan iya ganinki cikin irin wannan halin ba Dan Allah kidaina
kuka zamu samu mafita,
Bazan taba Bari Khalil ya auri wadda bake ba musamman wannan
barauniyar karuwar yarinyar Dana Gama alwashin bazata taba aurensaba kodan
yanda ya fifita sonta akanki.
Tsananta kukanta yayi tana girgiza Kai tana cewa''
Momy wlh inoson Khalil fiyeda yanda 'dan Adam zai iya
lissafawa,
Zuciyata zafi takeyi sosai bazan iya kallonsa ya auri wata
ba,
Gwara na mutu danaga wannan ranar.....
Da sauri momyn ta rufe Mata baki tana girgiza Mata Kai cikin
tashin hankali tace"
Dan Allah Nuratu kidawo hayyacinki ki daina wainnan
maganganun
Zan zamo Mana mafitarda zamu Kori Amatun daga rayuwarmu gaba
daya da duk ahalin zabeera ma bama Khalil kadai ba.....
Dagowa nuratu tayi da idanuwanta dasukai jajir suna tsiyayo
hawaye tana qoqarin fahimtar zancen momyn ta zabura da sauri tana tunowa da
takardun data karbo hannun manager na kaf asalin Amatun harma da qarin rayuwar
karuwanci datasa aka qara Mata akai,
Dakinta ta nufa kamar mahaukaciya ta nufi inda handbags
dinta suke tahau wargazasu tana neman jakar da tasaka envelope cikin hauka,
Ganin yanda take wargaza Kaya yasa momyn saurin qarasowa
tana sake riqota saigashi ta zaqulo jakar
Jikinta har rawa yakeyi ta bude ta dauko envelope din gaba
cewa''
Momy yau Babu Abinda zai Hanani wulaqanta wulaqantacciyar
rayuwarta,
Saina sakata kuka ninkin Wanda ta sakani tun zuwanta
zabeera,
Ayau zata San asalin irin girman soyayyar Dana kewa Khalil.
Juyawa tayi ta fice tana share hawayenta dasuke sake
bulbulowa cikin tsananin zafi da baqin cikin da zuciyarta ke ciki
Da gudu momy tabi bayanta tana Kiran sunanta sbd ayanda take
yanzu ba acikin hayyacintaba komai lalacewa zaiyi Bata haka zasu tona asirin
Amatun ba so takeyi harda umme ta fito cikin zancen....
A firgice ta biyo bayan Nuratun tana Kiran sunanta Amma tuni
nuratun ta hada da gudu gudu tana sake sakin sabon kuka ta nufi sashen Andi
inda tasan Modibbo nacan taredashi a daidai lokacin.
Ganin takasa cimma Nuratun data nufi hanyar sashen Andi yasa
hankalinta mummunan tashi tuni ta firgice sbd wlh tasan Kwana zasuyi aciki Suma
sbd zancen ba qaramin tashin hankali da masifu zai janyo ba,,,
Salman dake qoqarin parking yaga wucewar Nuratu da gudu gudu
kamar tana kuka Yana qoqarin kashe motar
ya fito saiga momynsu cikin sauri itama tanabin bayan Nuratun hankalinta
amatuqar tashe daga ganinsu yasan ba lafiya ba bare ganin sunkama hanyar sashen
Andi koma meyene to ya girmama dan duk Abinda yasa aka wuce Modibbo aka nufi
Andi to da matsala babba.
Kashe motar yayi da sauri ya fito yana qoqarin bin bayansu
saiga Dr khalil ya fito daga sashen ummen tareda Amatu da ummen zasu mayarda
Amatu
Da sauri Khalil ya taresa ganin Yana Shirin gudu yace"
Lafiya likitan qashi???
Kallon hanyar Sashen Andin yayi cikin sauri sauri yace"
Inaga akwai matsala ne Naga Nuratu da momy sun nufi sashen
Andi kowannensu Babu nutsuwa atare dashi Nuratu ma kamar kuka takeyi...
Juyowa yayi ya kalli khalil din cikin fargaba yace"
Ina Jin tsoron Abinda zaisa suje gurin anty musamman Nuratu
nasan halinta da tsananin fushi da rashin tunani Wanda kowa yasan yawancin
fushinta akan Abinda ya shafeka ne
Akwai Abinda yafaru yanzu a tsakaninku ne????
Dukkaninsu su ukun da sauri suka kallesa cikin wasi wasi da
shakku
Da sauri umme ta kalli me aikinta dake fitowa dan kawo Mata
wayarta dake ringin cikin sauri tace"
Shafa'atu Maryam da Nuratu sun shigo sashena bayan shigowar
su Khalil????
Da sauri cikin tashin hankali duk suka zubawa shafar Ido
jiran amsarta
Tace"
Eh da Kuna ciki sun shigo Amma.......
Bata qarasaba Salman ya juya da mugun gudu Yana cewa'"
Innalillahi-wainna ilaihirrajiun.....
Da sauri Dr khalil ya juyo ya kalli umme da zufa ya katse
Mata ya kalli Amatu da tuni qafafunta suka Fara daukar rawar tashin hankali ya
riqo hannuwansu duka su biyun cikin qoqarin bawa kansa nutsuwa Dan kwantar musu
da hankali yace"
Umme duk tsanani karku Fadi asalin abinda yafaru na gskiar
Abinda yafaru tsakaninku Kika kawo Amatu zabeera,
Amatu komai zai faru karki bude baki kiyi magana nine zanyi
Magana ok???
Kallonsa umme tayi da sauri tana cewa''
Ta yaya Zan tsaya Ina kallonka ka dauki hukuncin Abinda
bakaine kayiba...
Umme please kuyi kawai Abinda nace ku koma ciki Bari nabi
bayansu tun kafin su Isa.
Da sauri yabi bayan su Yana share zufan goshinsa akaro na
farko dayaji yanawa wani fatar faduwa ya Suma sbd Jin yake inama Nuratu kafin
takai tafadi ta suma a hanya..
Kasa hakuri ummi tayi takasa komawa ciki ta tsaya gurin tana
zarya cikin tsoro da fargabar Abinda zai
biyo baya....
Bakin qofar shiga momy tayi nasarar damqe Nuratu da sauri
tana sauke numfashin wahala da tashin hankali tace"
Nuratu kidawo hayyacinki kada kiyi Abinda masifarsa zata
qare kanmu sbd wannan alamarin ba Abune me sauqi ba dazamu Bari Modibbo yaji
daga garemu ba bare Andi
Maza kawo takardun Nan mukoma muyi Magana a nitse......
Qwacewa tayi tareda
tura qofar palon zata shiga har lokacin kuka takeyi sosai tace"
Momy yau idan ban tona asirintaba duniya tasan ko ita wacece
ba hankalina bazai taba kwanciyaba
So nake ta dandani 'dacin rabuwa da Abinda kakeso....
Fixgota Salman yayi da qarfi Yana qoqarin kwace envelope din
ta fizge da qarfi tana cewa''
Kaima bayanta zakabi aci gaba da barin karuwa tana rayuwa acikin
zabeera?
Me take Baku da duk mazan zabeera kuka haukace akanta??
Abinda take bawa sauran mazan waje........
Wani wawan Mari salman ya sauke Mata Wanda yasata haukacewa
cikin tsananin firgici da masifa tace"
Wlh ka sake dasamin tsanarta me tsanani Koda Zan rasa Raina
saina tabbatarda Andi da Modibbo sunsan karuwace ita,
Barauniya ce,
Yar bola ce,
Me aikin karuwanci a gidan abinci.......
Ba zata Marin dayafi na farko zafi da qara ya sauka akan
inda Salman ya mareta
Wannan karon radadin yayi tsananin data kasa riqewa saidata
zube a qasa ta dago ta kallesa idanuwanta na qarasa rinewa hawaye masu tsananin
zafi da baqin ciki suna gangaro Mata murya na rawa tace"
Khalil duk akan wannan karuwar ce??
Cikin tsananin bacin Ran dabasu taba ganinsa aciki ba ya
bude baki zaiyi Magana akai gyaran murya daga bakin qofar Shiga palon kusan duk
atare suka juya cikin firgici da tashin hankali sukaga Andi ne da kansa a tsaye
Modibbo na gefensa kowannensu kallo daya zakayi Masa kasan dukkanin fushi da
bacin ransu a bayyane yake
Cikin nutsuwa Modibbo ya qaraso gaban Nuratu da itama
tashiga firgici ya sanya hannu ya zari envelope din hannunta batareda yace qala
ba ya juya yadawo gefen Andi Yana bude envelope din Wanda yasa tuni kowannensu
ya shiga rawar jiki musamman momyn tuni ta durqushe qasa tan neman sakin kuka
Andi yayi wa gefenta kallo daya take ta hadiye kukan
batareda yafitoba yakoma tana rawar jiki.
Duk inda tashin hankali da sanyin jiki yake Yana tareda
Amatu da umme sbd kowannensu yakasa samun nutsuwa ta ja qafafunta dasukai nauyi
ta nufi hanyar sashensu idanuwanta na sake kadawa bayan kumburin dasukayi na
kukan data gama sha,
Tana shiga palon da anty zarah dake zaune tana qoqarin
kiranta tayi saurin miqewa ta qaraso gabanta cikin tashin hankali da tsoro take
Kiran sunanta tana tambayarta lafiya.
Kasa motsi tayi bare Magana sai kawai ta fashe da sabon kuka
me shiga Rai tana zubewa qasa...
Innalillahi-wainna ilaihirrajiun" anty zarah ke
maimaitawa tana zubewa qasan itama cikin tashin hankalin ganin irin kukan da
Amatun keyi cikin rudu muryarta na rawa tace"
Amatu meya sameki kifadamin tun kafin kisa zuciyata fashewa
itama Dan Allah,
Kukanki na bani tsoro tareda sani cikin tsananin firgici Dan
Allah kiyimin mgn.....
Dagowa tayi ta kalli anty zarah din jajayen idanuwanta na
tsiyayo da hawaye masu zafi tanajin tausayin kanta Dana zarah din sbd tasan
lokacin rabuwarsu ne yazo,
Abinda Bata saniba shine zarah din zata tsaneta idan taji
Abindake faruwa?
Koda zata tafi zatayiwa anty zarah adalcin fada Mata gskia
da bakinta ko Dan zallar qaunarta gareta.
Wasu hawayen ne suka Kuma tsayayo Mata ta rintse ido
zuciyarta na radadin Abinda zata fada ahankali tace"
Anty zarah ki gafarceni na zamo babbar butulu me mayarda alkhairi da cin
Amana,
Na cutatar dake ta hanyar wahala akan Abinda Kika saka Rai
da burika akansa,
Na hanaki bacci da sukuni gurin dawainiya Dani akan qarya
yaudara...
Anty zarah banida ciki ajikina,
Bantaba daukar cikiba,
Bantaba sanin namijiba bare nayi Abinda zaisa nasamu ciki,
Dr khalil ba Mijina bane.........
Sakinta anty zarah din tayi cikin tsananin firgici da mamaki
tayi baya tana zaman 'yan bori idanuwanta na silalo hawayen tsoro da karyewar
zuciya ta Fara girgiza Kai tana son yin Magana takasa sai hawaye....
Anty zarah bantaba sanin a duniya akwai masu irin
tsarkakakkiyar zuciya irin tasu kawu ba sai Dana hadu da Dr khalil dake da
salman kuka kawo wani irin farin ciki da sanin mutuncin Kai arayuwata Amma Babu
Abinda nakawo Muku sai yaudara da damuwa.....
Cikin rawar murya anty zarah dake rawar jiki gaba daya cikin
firgici tace"
Idan duk Abinda Kika fada hakan ne to meya kawoki cikin
rayuwarmu????
KUDI"""""tafada Kai tsaye tana
sauke Kai hawayenta na qaruwa..
Son kudi da burin samunsu kota halin Yaya yasani shigowa
rayuwarku
Saidai bayan haduwata daku na fahimci samun mutanen dake
sonka da son farin cikinka tareda zama acikinsu shine asalin farin ciki da
walwala Wanda kudi baya siya maka suba,
Anty zarah girmanki da qaunarki alqawarine da bazai taba
gogewa azuciya da rayuwataba,
Anty zarah idan lokaci yayi Zan fada Miki gaskiyar duka Amma
ayanzu iya Abinda Zan fada Miki kenan.
Miqewa tayi da sauri ganin irin hawayenda anty zarah din
keyi tana bin cikinta da kallo burirrikanta akan cikin suna tarwatsewa daya
Bayan daya,
Cikinda akai alqawarin Bata Abinda za'a Haifa Wanda tuni
tafara kallon kanta amatsayin uwa Nanda lokacin qanqani.
Buga kofar da akayi da qarfine yasasu kallon kofar tun kafin
su motsa aka sanarda saqone Andi nayiwa Amatu Kiran gaggawa.
Rintse idanuwanta tayi hawayen ciki suka gangaro ta juya ta
nufi qofa.
A tsaitsaye suke Babu Wanda yasamu damar motsawa daga Inda
yake sbd tashin hankali kusan mintuna suka share ahakan sbd shock dinda su Andi
suka Shiga Bayan Gama sanin wacece Amatu dakuma irin qazamtacciyar rayuwar
karuwancin datayi qarshe ta qare acikin zuria mafi tsafta da mutunci,
Umme da sauran manyan yaran Andi da Modibbo da tuni aka
kirasu suka qaraso Babu wanda ya zauna duk tsaye suke cikin tashin hankali da
jimanin abinda zai biyo Andi kawai ake jira yayi Magana.
Dagowa yayi cikin wani irin yanayi na tsanani yayiwa Khalil kallon dayasa kowa sake
Shiga firgici cikin amo me firgitarwa yace"
Kowace tambay amsa daya nakeso,
Ka auri wannan yarinyar??
Aa,
Acikin takardan Nan anrubuta cewa
Ita din Mara asali ce,
Yar bola ce,
Karuwa ce,
Barauniya ce,
Gidajen abinci,hotels da gidan rawa take aiki,
Babu police station dinda batayi zamaba har gidan yari
Gaskia ne ko qaryane???????
Cikin tsananin firgici da tashin hankali muryarsa na rawa
yace"
Gskia ne Amma Banda.......
Hannu Andi din ya daga Masa fuskarsa na nuna dukkanin
fushinsa da bacin ransa.
Take yace kowa ya watse ya sallamesu ya juya yayi ciki
'yayansa na binsa abaya.
Kasa motsi kowa yayi sbd sanin abin bazaiyi kyauba.
Daga ciki kuwa kallon alhaji qarami yayi Kai tsaye
yace"
Yarinyar da mariqanta a daukesu a rufe a central station
dinda Khalil zaifi shekaru goma Yana nemansu baigansu ba a sanarda commissioner
laifin datayi ta yanda zasusan girman laifin Bata sunan zabeera.

No comments