SARAN BOYE 21
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
No. 21
*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*
*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*
*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA
WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA,
WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA
JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU
GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN
AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA
BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA
SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.
*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI
DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC
(MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE
HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR
INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN
MU TUNTUBE MU TA_*
_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac
_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz
_NAMBAR TARHON MU_
08169380189
*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE
YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN
KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI..
MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*
__________________________________
No. 21
.................“Adawiya!!” hajjo ta faɗa a ɗan tsawace.
Yayinda Ahmad da Abdallah ma sukai wani zallon mamakin abinda Adawiya tayi
suma.
Kallonsu tai a firgice idanunta na tara
ƙwallar takaici da jin zafin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Ta buɗe
baki zatai magana a zafafe sai kuma ta tuna abinda ta nema mantawa. Saurin
sauke numfashi tayi tana fashewa da kuka, tare da juyawa ta kalli Nu'aymah dake
tsaye dafe da kujerar data taimaketa ta hanata faɗuwa lokacin da Adawiyar ta
turata.
“Nayi fushi wlhy Aymah, yanzu
dama dake za'azo amma kikaƙi sanarmin saboda ke yanzu kinma daina sona?”.
Adawiya ta faɗa cike da makirci da waskewa.
Ajiyar zuciya Abdallah da Ahmad suka
sauke, dan duk zatonsu Adawiya da gaske da faɗa tayi abinda tayi. Hajjo dai
bata motsa ba, amma ta kafesu da kallo su duka huɗun tana nazarin kowa.
Jin abinda Adawiya tace ne ya saka
Nu'aymah sakin murmushi, dan tsaf ta fahimci Adawiya canja hanya tayi, inkuwa
hakane ai itama tanada wayonta, dan wani abun ma sai dai ta koyama Adawiyar duk
da kuwa ta girmeta da wasu wattani. Sake tahowa tai da ɗan gudunta ta rungume
Adawiya tana faɗin, “Afuwan habibiya, surprise nai niyyar miki shiyyasa na hana
kowa faɗa miki”.
Leɓe Adawiya ta cije dan ta
juyama su Hajjo bayane, itama cike da ɗacin zuciya ta rungume Nu'aymahn tana
magana cikin kuka, “ALLAH saina hukunta ki tunda kika sani kuka”. Nu'aymah tai
dariya hawaye na sakko mata itama, ta ɗago Adawiyan daga jikinta tana durƙusawa
gabanta da riƙe kunnuwanta, “Afuwan hassanata, kaina bisa wuya Please”.
Karan farko Adawiya ta saki dariya, itama sai
ta durƙusa kamar yanda tayi sunama juna kallon ido cikin ido, Nu'aymah murmushi
takeyi, Adawiya kam ta haɗe fuska ganin su hajjo basa ganinta. “Kin haƙura
kenan?” Nu'aymah ta faɗa tana wani ɗage ma Adawiyar gira ɗaya da sakin mata
lallausan murmushin da yay mata tsaye a maƙoshi.
Kasa magana Adawiya dake mata kallon
tsantsar takaici da haushi tayi, sai kawai ta rungumeta a jikinta tana gyaɗa
kai........
Gyaran Murya Yah Ahmad yay yana
faɗin, “Kunga malamai ya isheku haka, ku barmu mu ƙarasa ƴar yunwar azuminmu da
sauran yawu a baki dan ALLAH, idan akasha ruwa komaima sai kuyi zamu tayaku da
sulhu”.
“Faɗa musu dai”. Abdallah
ya faɗa a wani irin yanayi yana komawa kusa da hajjo ya zauna. Ƙaramar dariya
Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta, sai kuma ta kalli Abdallah tana faɗin, “Kaga
Audillahi kaini ɗakina na huta kaji, bazan iya luguden laɓɓa ba da azumina a
baki”.
Fuskarsa ƙawace da murmushi ya
miƙe tare da taimakama hajjon itama ta tashi. Har ɗakin da zata zauna ya
rakata, tana zama Nu'aymah na shigowa itama. Duk kallonta sukai shi da Hajjon,
ta ajiye jakarta tana zama a kujerar dake a ɗakin ƙwaya ɗaya tal, batare data
kalli Abdallah ba tace, “Yah Ab! Ina yini?”. Kallonta yay a karon farko suka haɗa
ido, sai ta ɗauke nata gefe tana komawa jikin kujerar ta jingina.
“Kunzo lafiya?”. Ya amsa mata shima cike da
basarwa, dan haka kawai yanzu yakejin zafin abinda ta aikata a ranar ɗaurin
aurensu. Ƙin sake tanka masa tayi, hajjo kuwa tamayi kamar bata a ɗakin.
Ƙofa ya nufa dan kai Ahmad nasa
masaukin yana faɗin, “Ki taso ki koma ɗakin Adawiya, ita hajjo sai ta zauna
anan...”. Kafinma ya rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan zauna anan tare da
Hajjon”.
Da ga Hajjo har Abdallah kallonta sukai,
amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Hajjon tace dole sai taje.
Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa ya fita kawai.
“Miyasa bazakije can ɗinba? Bayan ƴar
uwarki na cike da ɗokin ganinki?”. Hajjo ta faɗa bayan ficewar Abdallah.
Nu'aymah dake ƙoƙarin cire kayan
jikinta tace, “Babu komai Hajjo, nafison kawai na zauna da ke kodan himma akan
ibadar da mukazoyi, sannan nifa ma ittiqafin zan shiga insha ALLAH”.
Murmusawa Hajjo tayi kawai tana ɗauke
kanta batare da ta sake cema Nu'aymah komai ba, itama Nu'aymahn sai ta shige
bayi abinta batare data jira amsar hajjon ba.
★★★
“Kuturun ubancan kayyasa! Yanzu
wane algungumine mai wannan shirya tafiyar a gidanmu?”. Adawiya daketa faman
zagaye ɗakinta ita kaɗai ta faɗa tana cizar laɓe kamar zata hudashi. Ganin babu
mai bata amsa ta rarumo waya ta fara neman maman Aaida. Bugu biyu kuwa ta ɗaga.
Harta fara tsokanarta Adawiyan ta katseta da faɗin, “Maman Aaida yanzu ba
lokacin wasa bane, ko kinsan sister ɗin nan nawa da zata auri Yah Ab da, ta
biyo kakarmu sunzo Umrah tare?”.
Da ƙarfi Maman Aaida tace, “Na shiga
uku, da gaske dan ALLAH?”. Adawiya da ranta ya ƙara dugunzuma tace, “Wlhy kuwa.
Bama zuwan nata bane tashin hankalina Maman Aaida, kinga kuwa yanda Yah Ab duk
ya susuce, gashi kakarmu ɗin nan shegen sa idone da ita wlhy”.
“Tab, lallai aiki ya samemu, dan
kuwa wlhy mukai sanya to ki tabbatar nanda wata ɗaya ko sati biyu ma mijinku
zai koma na mata uku....”
“ALLAH ya kiyaye” Adawiya tai saurin
katse Maman Aaida hawaye na ziraro mata a idanu. Takaicin maganganun maman
Aaida ya sakata katse kiranma gaba ɗaya tai wurgi da wayar kan gado.
Abdallah dake ƙoƙarin shigowa ɗakin
yace, “Lafiyarki kuwa kike wurgi da waya? Kamar ba kuɗi akasa aka saya ba!”. Da
sauri tasaka hannu ta share hawayenta, kafin ta nufesa ta rungume da ƙarfi.
Saurin tureta yay yana faɗin, “Haba Adawiya, shin wai kina mantawa muna azumi
ne? Duk hanyar da zaki raunanama mutum azumi kin santa”.
“Kayi haƙuri Yah Ab, wlhy ɗokin
zuwan Nu'aymah ne ya sakani yin hakan”.
“Umyim! Kina ɗokin zuwan natane kika
barta tafiya ɗakin da Hajjo zata zauna ta sauka”. Kamar zatai kuka ta kallesa,
acan ƙasan ranta kuma tamkar ana babbaka wuta, cikin shagwaɓa tace, “Damafa
jira nake kazo na kawo maka ƙararta ALLAH, nayi-nayi tazo mu zauna anan taƙi,
wai batason shiga haƙƙinmu”.
Kafeta yay da idanu kamar mai
nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa ya fice batare daya bata
amsa ba.
Harara ta raka bayansa da shi harya
fice, taja gajeren tsaki, ‘Wlhy tunda aka munafunceni sai yarinyarnan ta
gwammaci kiɗa da karatu a gidan nan, ni kama ƙaramin haske akan dawowarta ɗakin
nan Yah Ab, dan wannan itace babar damar da zan riƙe wajen tarwatsa zuciyarta,
saina maidata mahaukaciyar gaske idan da ƙaramin haukane a kan nata mtsoww!!
Aikin banza kawai’.
Oho, ita Nu'aymah ma batasan tanayiba,
dan bata sake leƙo falonba har lokacin shan ruwa ya ƙarasa, itama Adawiya bata
shiga inda sukeba ta maƙale akan shirya kayan shan ruwa takeyi. Duk da kuwa ba
ita ta girkaba. Fita Abdallah yay ya musu order ɗin komai daya dace, dan yasan
Adawiya bazata iyaba ita kaɗai tunda sunada yawa. Bai kuma kamata asa Nu'aymah
shiga kitchen ba daga zuwansu.
Aikin da Adawiya tayi kawai shine
shirya abincin a tsakkiyar falo, wanda saida Abdallah ma ya tayata suka tsara
komai a inda ya dace.
Koda aka kira
salla ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallar magriba.
Daga hajjo har Nu'aymah basu zaƙeba akan abincin, sukai zamansu gefe suna tsumayen
tayi daga Adawiya. Itako hankalinta ma baya garesu, tana can tana ƙullama
zuciyarta abinda zata aikata a wajen shan ruwan idan an zauna danta cusama
Nu'aymah takaici. Shiyyasa ta fara ƙoƙarin shiryama Abdallah nashi tunkafin su
shigo.
“A'a Hajjo ya naga
baku fara buɗa bakin ba?”. Abdallah da ke ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai ya
faɗa idonsa akan Nu'aymah dake danna waya. Wando da rigane marasa nauyi a
jikinta, sanin basu kaɗai bane ya sakata ɗoro hijjab a sama wanda yaje mata har
gwiwa.
Murmushi hajjo dake kallon Adawiya cike
da nazari tayi, sai kuma ta maida kallonta ga Abdallahn tana faɗin, “Ku muke
jira mana, dan zaifi daɗin ci ai”. Cike da jin daɗi ya kama hannunta ya
sumbata, kafin ya zauna kusa da ita yana gaisheta da mata barka da shan ruwa.
Nu'aymah dake a ɗayan gefen Hajjo itama tace, “Barkanku da shan ruwa”. Ahmad
dake ƙoƙarin zama kusa da Abdallah ne kawai ya amsa, sai hajjo data ƙwace wayar
tana harararta da faɗin, “Sai yanzu kika san damu?”.
“Waini miyasama na
biyoki?”. Nu'aymah ta faɗa cikin haushin amshe mata waya tana tura baki cike da
shagwaɓa. Hajjo da Ahmad sukai dariya, hajjo tace, “Tambayi kanki mana, ja'ira
kawai”.
Adawiya da abun sam bai
burgetaba, ta kalli Abdallah da gaba ɗaya hankalinsa akan Nu'aymah yake.
Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Yah Ab ga abincinka”. Kallo
ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. “Gasu hajjo da suke baƙi baki haɗa musuba sai ni
da ko shigowa banyiba........?”
Katseshi Hajjo tai
da faɗin, “Kaga barta, ai abincinma so nake a haɗesa a babban tray mu haɗu tare
mu sami ladan juna”.
‘Tabɗi jan’ Adawiya ta faɗa a
ranta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki, a fili kuwa sai ta kafe Abdallah da ido
a zatonta ko zaice wani abu. Duk da ya ganta sarai baice uffanba, saima ɗauke
kansa yay abinsa.
Hajjo da duk take lura da motsin kowa
tace, “Zainabu zuba abincin, ki haɗe da wanda Adawiya ta zuba duk a haɗu kowa
ya saka hannunsa”.
Murmushi Nu'aymah tayi a
karon farko, ta gyara zamanta tana faɗin, “Angama Hajjaju uwar masu gida, uwar
gida ran gidan malam Hashimu ɗan jibiya”.
Sosai Abdallah, Ahmad da Hajjo
suka sanya dariya da kirarin na Nu'aymah. Hajjo ta ranƙwasheta akai tana faɗin,
“Ja'ira”. Adawiya kam wani baƙin cikine ya kumeta a rai, harta kasa daurewa ta
miƙe.
Abdallah yace, “K kuma ina
zaki?”. Da ƙyar ta iya haɗiye kukanta tace, “Zan ɗakko abune a kitchen”. Bata
jira amsarsa ba tai gaba.
Wani shegen murmushi Hajjo da Nu'aymah
suka saki, wanda kowa da manufar nasa.
Hawaye sosai Adawiya tayi a
kitchen, sai dai gudun kar wani ya biyota yasata saurin wanke fuskarta ta ɗakko
ruwa ta fito.
Koda ta dawo babu wanda ya tanka mata, saima
ƙoƙarin kai abinci suke a cikinsu. Yayinda Abdallah duk Motsin Nu'aymah na
gunada ne a idonsa. Itama Nu'aymahr dai hankalinta na a kansa. Sai dai tana
ƙoƙarin fuskewa ita babu mai ganeta.
A haka dai suka kammala buɗa bakin,
yayinda kowa yaci komai dai-dai misalin da bazai cutu ba. Duk da akwai gajiya
tattare dasu haka suka rarrafa zuwa massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su
dawo kowa ya nema makwanci.
Abin mamaki sai ga Adawiya
tayi shiri ta tafi kwana ɗakin Abdallah.
(😂ta wajena Adawiya gara ki dage ki samu kan,
gaskiya fa, dan naga su o'e anzo saudia da shirin Snatching mijin mutane.😎🙄🚶🏻)
_______________________________
*_NIGERIA_*
“Wai tunanin mi kiketayi ne haka da
zurfi Darling? indai akan Yoohan ne na samo mana mafita”.
Da sauri Momy ta juyo tana kallon papa
da ke maganar da yarensu, bakinta har ɗan rawa yake wajen tambayarsa wace irin
mafita ya samo?.
Sai da ya rungumeta kafin yace, “Mu
lallaɓashi ya auri Miracle kawai”. A wani irin zumbur ta miƙe zaune tamkar
wadda maciji ya sara. Ta nuna Papa da yatsa tana faɗin, “Kasan mi kake faɗ kuwa
Darling? duka-duka shekarar Yoohan ɗin nawa da kake maganar yay aure? Indama
son Miracle ɗin yake to da sauƙi, amma kana ganin yanda yake mata a gidan nan
ai ko”.
Tsuru papa yay yana kallon yanda matar
tasa ke masifa kamar zata haɗiye harshenta, sai da takai ayar zancenta tana
wani huci sannan yay saurin jawota jikinsa yana girgiza kansa. “Ki fahimceni
mana, idan Yoohan yay aure matarsa zata dinga ɗebe masa kewa a duk lokacin da
ya shiga irin wannan damuwar, kum.......”
“Kaga nifa bani da lokacin
wannan maganar, ka barni barci nakeji”. Ta faɗa ranta a ɓace da ƙwace jikinta
taje gefen gadon ta kwanta. Da kallo kawai ya iya binta har na tsahon lokaci,
kafin shima ya kwanta ɗin yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. A cikin ransa kuwa
ya ƙudiri aniyar lallaɓata ita da Yoohan ɗin har sai sun amince da ƙudirinsa.
*_WASHE GARI_* safiyar lahadi, tunda safe jama'ar gidan suka
shiga hada-hadar shirin fita church, dan papa ma tun da sauran duhun safiya ya
fice shi.
Rich daya fito wanka ya kai dubansa ga
Yoohan dake zaune kan sofa, ƙafafunsa miƙe akan table, ya jingina bayansa kansa
na kallon sama. Duk da idanunsa a lumshe suke ya tabbatar ba barci yake ba.
“Doctor ya kamata ka tashi kai shiri mu
shiga church ko? Idan mun fito sai mu ɗan zaga gari danni yau da yamma zan koma
Lagos”.
Shiru Yoohan bai motsaba, duk da kuwa
sarai yanajin Rich ɗin. Sai da ya ɓata wasu mintuna kafin ya buɗe idanunsa da
sukai wani irin kumburowa, fatarsu tayi jaa sosai alamar jin barci tattare da
shi, hakama fuskar tayi jajur sosai abin tausayi. Miƙewa yay batare da yayi
magana ba, ya wuce toilet yana ɗan ɗingisa ƙafarsa da bata gama sakiba, sai dai
hakan kuma sai ya bama tafiyar tasa wani style daban kamar mai tafiyar izza.
Baija dogon lokaciba ya fito ɗaure
da towel ruwan gwaiduwar ƙwai. Babu kowa a ɗakin dan Richard ya gama shirinsa
ya fice. Ya ƙarasa gaban mirror, shafe jikinsa yay da mai da kayan ƙamshi
tamkar yanda ya saba, kafin ya nufi wajen kayansa. Fararen suit ya ɗakko yana ɗan
yamutsa fuska da kallonsu. Sai kuma yabar wajen dasu zuwa gaban gado. Tsaf ya
shirya a cikin suit ɗin da sukai masifar zama masa a jiki, tare da fiddo
surarsa mai jan hankalin mata dama mazan kansu. Necktie ɗin ya ɗauka a hannu
tare da jacket ɗin suit ɗin, dan shi kam har yanzu ɗaura tie na masa wahala.
Gaban mirror ya sake komawa ya feshe kansa da kalolin designers ɗin
turarurrukansa, kafin ya ɗau sarƙa ɗaya a cikin sarƙoƙinsa na Cross da taji
zallar diamond tanata ɗaukar idanu ya saka. Ya ɗauki agogo ya ɗaura tare ɗan
wani abin hannu na gayu ya ɗaura a ɗayan hannun, ya kuma manna ɗan kunnensa a
kunne ɗaya. Yayi ƙyau sosai, duk da kuwa fuskar a turɓune take matuƙa. Amma
yanda yau ya gyara kansa da sajensa sai yay ɗas da shi kamar ka suresa ga gudu.
Tun fara sakkowarsa daga benen
Mom da Rich, Solomon dake a falon duk suka zuba masa idanu, sake ɗaure fuska
yayi yana ƙarasa sakkowa. Saurin tararsa Solomon yay da kofin coffee daketa
turiri akan tray, yace, “Good Morning sir”. Kansa kawai ya ɗaga masa yana gyaɗa
kai, tare da ɗaukar coffee ɗin ya nufi Mom da ta tsatstsaresa da idanu tun
sakkowar tasa, sai dai fuskarta sam babu walwala. Tayi ƙyau sosai abinta tamkar
zata gasar sarauniyar ƙyau. Necktie ɗin hannunsa ya miƙa mata batare da yayi
magana ba, saima kofin coffee ɗinsa da yakai baki yana curɓa kamar bayaso.
Tsaye ta miƙe, duk da ya fita tsaho,
amma da yake tana kan tudun dining ne saita samu damar kaiwa wuyansa cikin
sauƙi. Ɗaura masa tie ɗin tayi, tare da amsar jacket ɗin ta koma bayansa.
Hannunsa guda ya miƙa mata ta saka masa, ya sake miƙa ɗayan ma ta saka, sannan
ta zagayo gabansa tana gyara masa da ƙyau.
Ta ɗan saki murmushi tana masa
wani narkakken kallo, kafin takai hannunta saman fuskarsa ta shafa kwantaccen
sajensa dayin magana ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Ɗanja baya yay yana zame
hannunta, murya a cinkushe yace, “Thanks Mom”.
Kafin ta samu damar yin
magana ƙannensa dake fitowa cikin nasu gayun suma suka shiga gaishesa ɗaya
bayan ɗaya. Hannu kawai yake iya ɗaga musu yana cigaba da shan coffee ɗinsa
cike da basarwa.
Ganin yanda Mira ke binsa da wani
shu'umin kallone ya sakashi miƙama Solomon kofin duk da bai ƙarasa ba, batare
da yayima kowa magana ba ya nufi hanyar fita abinsa cike da takun nutsuwa da
ƙasaita sai kace wani jinin mulki.
Dukansu baya suka take masa,
yayinda Gebrail yay saurin kaiwa inda yake yana riƙo hannunsa. Batare daya
kallesaba yace, “What happend?”. Murmushi Gebrail yayi yana susar kai, cikin ɗan
in ina yace, “Brother Yoohan kuɗi nakeso Please”.
Yoohan baice
komaiba, ya zare hannunsa daga cikin na Gebrail ɗin, ƙarasawa yay jikin motar
da yaga Rich tsaye yana waya. Da sauri ɗaya a cikin Guards ɗinsa ya buɗe masa
yana gaishesa. Hannu kawai ya ɗaga mar ya shige. Richard ma shiga yay ta ɗayan
gefen, Solomon da driver ma suka shiga. Cike da ɗoki Gebrail da yasan
matsalarsa ta yanke ya shiga motarsa shima tare da su Mira da taso bin motar
Yoohan ɗin. Sai dai ganin Rich datai tunanin ba a gidan ya kwanaba da, ya
sakata haƙura ta shiga ta Gebrail ɗin ita da joy.
Motocin na gama fita a gidan
Yoohan ya zaro wayarsa dake cikin aljihu, transfer ɗin kuɗi masu yawa yayma
Gebrail tamkar baisan ciwonsu ba, kafin ya ajiye wayar gefensa ya maida kansa
ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa.
Har motocin suka tsaya a
katafaran church ɗin da papa ke riƙe da shi Yoohan bai motsaba, duk da kuwa
Rich na masa bayani ne akan wata harkar business ɗinsu da sukeyi tare.
Katafaren church ne mai girman gaske,
wanda akaima gini na ƙawa da ɗaukar hankali, dan a gaba ɗaya gaban church ɗin
da idanuna ke iya gani anyisane da zalkar glass. Yayinda akasa ƙaton tambarin
Cross da akayisa da golden ɗin abu. Tun a farkon shigowar titin zaka faracin
karo da muryar papa dake lecture. Gaba ɗaya titin wajen sun kashesa babu maibi
saboda motocin da duk akai parking masu tarin yawa. Securitys ɗin church ɗin da
sauri suka shiga bama motsocin su Yoohan ɗin hanya cike da tsantsar girmamawa.
Sai da sukai parking a waje na musamman da aka tanada domin motocin nasu dama
sannan aka shiga buɗe musu suna fitowa.
Yoohan ne ƙarshen fita, dan sai da ya
gama jan ajinsa kafin ya ziro sandarsa ta gayu sannan ya fito gaba ɗayansa.
Gebrail da tun a hanya yaga alert yay saurin ƙarasowa ya rungumesa yana godiya.
Baice dashi komaiba sai shafa masa baya da yay kaɗan.
Yanda securitys ke
basu kariya da tsantsar kulawa sai ka ɗauka dajin sambisa zasu shiga🤥🙄,
suna zagaye dasu har ta ƙofar da take ta musamman domin iyalan papan kawai da
shi. Tanan suka shiga cikin church ɗin dake a cike maƙil da mabiya kamar zai
fashe.
Duk suka zuba musu idanu suna
miƙewar girmamawa a garesu cike da sha'awa da ƙauna. Sai da suk suka ɗaga musu
hannu banda Yoohan da ko kallon basu ishesa ba sannan suka ƙarasa wajen zamansu
na musamman dake a gaba duk suka zauna.
Papa dake a gaban wani glass mai ƙyau da aka
ƙawata da golden ga abin magana kusan huɗu a jiki yay murmushi yana ma iyalan
nasa barka da zuwa, kafin ya cigaba da zubo bayani cikin kwakwazo da karaɗin da
aka san fastoci da shi, ko haɗiyar yawu bayayi😕.
A hankali sai hayaniyar
ta fara takurama Yoohan, duk da kuwa tunda ya zauna yana jingine ne da kujera
idanunsa a lumshe kamar mai barci. Siririn tsaki yaja yana yamutsa fuska. Ya
shafa kunnensa na dama dake manne da Bluetooth yana cizar lip. Sai kuma ya buɗe
ido da motsawa zai miƙe Rich yay saurin riƙe masa hannu. Ransa a ɓace ya
kallesa, sai dai baice komaiba.
“Please ka daure” Rich ya faɗa
cike da marairaicewa dan kar Yoohan ɗin ya bijire. Siririn tsaki ya kuma ja kaɗan
ya maida kansa ya sake kwantarwa ya rufe idanu.
Kusan awa guda Yoohan nata sake daurewa
duk da kansa ya fara masa wani azababben ciwo. Kiran daya sake shigowa a
wayarsa ne a karo na babu a dadi ya sakashi yamutsa fuska, duk kiran da ake
masa bai amsa ko guda ɗaya ba, amma yanzu sai yaji buƙatar amsawar. Miƙewa yay
zai fice Rich yay saurin sake riƙosa. Nuni yay masa da Bluetooth ɗin kunnensa
batare da yayi maganaba. Hakanne ya saka Rich sakinsa yana gyaɗa kai.
Sama-sama ya amsa mutumin dake
gaishesa, kafin yay shiru yana sauraren bayaninsa da magiyar da yake masa akan
buƙatar mutanen da kimarsu ta wuce ace Yoohan ɗin yaƙi buƙatarsu.
Ajiyar zuciya Yoohan ɗin ya
sauke a karon farko, batare da ya amsaba ya yanke kiran kawai. Wayarsa ya ciro
yay ɗan typing ya tura abinda shi kaɗai ya sani. Mintuna uku ba'a rufaba saiga
reply an naido masa. Buɗewa yay ya gani, batare da yayi maganaba ya maida wayar
aljihu yana ɗan dube-dube kamar mai neman wani abu. Sai kuma ya sake zaro wayar
ya sake yin wani abun.
Yanzu kam ya kai tsahon mintuna biyar yana
jiran reply ɗin kafin a turo masa. Shiru yay yana ɗan kallon wayar kamar mai
nazari, kafin ya gyaɗa kansa da nufar inda motocinsu suke da wasu a cikin
guards ɗinsa tsaye a wajen.
Batare da yayi maganaba ya miƙama drivernsa
hannu da masa nunin ya bashi key. Kamar driver zaiyi magana sai kuma ya haɗiyeta
da sauri ganin kallon da Yoohan ɗin ya zuba masa. Saurin bashi key ɗin yayi,
shi kuma ya buɗe motar da kansa ya shiga mazaunin driver yay mata key tare da
yin reverse ya bar wajen securitys nata risina masa cike da
girmamawa.............✍
To ɗan dabe ina zuwa kuma🤥🤐?.

No comments