MIN QALB 26
26_*
Zaune suke a Palo itada anty zarah anty zarah na Mata fira Dan sakata nishadi ganin duk tazama so serious Wanda Sam kowa yasan ba halinta bane tafi sabawa da hayaniya shiyasa duk inda take to hayaniya na gurin.,
Ana bude qofar palon atare dukkaninsu suka kalla qofar
shigowar kowacce fuskarta daukeda murmushin yiwa Dr khalil din maraba Musamman
Amatun da murmushinta na yau ya banbanta Dana kullum sbd yau sauran zuciyar
Khalil takeson qarasa sacewa sbd ta zamo Tata ita kadai shiyasa yau komai nasa
na musamman ne agareta saidai sabanin ganin fuskar Dr khalil zabeera a cikin
idanuwan MAHMOUD ZABEERA idanuwanta suka sauka murmushinta me sanyi da tsada
akan fuskarsa yafara sauka gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye sauran
murmushinta fuskarta na sauya cikeda mamaki da fargaba da sanyin jiki..
Tsayawa yayi kallonsu fuskar na bayyanarda mamakinsa daba'a
cika ganewaba ganin yanda dukkansu suka waiwayo suka zuba Masa Ido kowacce
fuskarta daukeda murmushin daya mugun daukar hankalinsa da sakashi wasi wasin
mamakinsu musamman Amatu datafi bayyanarda murmushinta da dukkanin farin
cikinta dabai taba ganiba,
Ganin Ahankali Amatu ta dauke idanuwanta dake cikin nasa
tana kallon bayansa murmushinta da farin cikinta fiyeda na farko Yana dawowa
yasashi dawowa MD dinsa ya sauke boyayyan numfashinda Babu Wanda yaji ya Fara
takowa ahankali idanuwansa na sauyawa cikin wani boyayyan yanayin dayake ciki
sbd sai alokacin ya fahimci Khalil ne keda wannan murmushi da farin cikin,
Zama yayi Kan couch din dakinsa Yana rintse idanuwansa
tareda yamutsa kansa yanajin wani irin zafi na ratsa dukkanin jikinsa
Take kuwa zufa ya kakkaryo Masa Tako ina bayan ga kukan AC
Nan yanaji yasan a kunne yake....
Zarah ya tuno da itama taketa washe baki tana murmushi to
idan ita waccar tayi Dan Yana sunan
mijinta to itafa???
Jin kansa ya dauki zafi Yana neman saukewa zarah laifin sai
kawai ya miqe ya fada toilet yayo wanka yayi clearing mind dinsa ya shirya
cikin kayan bacci ya dauki laptop yafara wani aiki Yana basar da tunanin komai
da kowama.
Dr khalil kuwa duk yanda yake tunanin Amatu takai cikin
ransa sai yanzu yake gane ta wuce Nan sbd wannan murmushin datake jifarsa dashi
yagama hargitsa Masa Kai da tunani.,
Zama yayi bayan sungama gaisawa da zarah ta wuce tabasu guri
ya juyo suna fuskantar juna Yana kallonta cikin kulawa yace"
Hw are you AMATULLAH???
Zuba Masa idanuwanta tayi har lokacin murmushinta bai daina
fitaba tace"
Nayi fushi ka koma na barwa Nuratu.
Wani irin Dadi yaji ya kamasa me sanyi cikin nutsuwarsa
yace"
Kishi kikeyi ita tafara tarbona???
Harara ta sakar Masa tana cewa''
Zanyi maka kuka idan kasakemin maganarta.
Kallonta yayi Yana cewa''
Ok tom yanzu duk wannan adon sbd zandawo akayisa?
To Meyesa baki shafamin Dan lipstick dinnan naku danaga ana
sakawaba Nuratu tasaka ita......
Miqewa tayi a fusace tayi dakinta Yana kiranta ko waiwayosa
batayiba tana shiga gaban mudubi ta wuce Kai tsaye
Ta dauki janbaki hot red tashafa a bakinta tana kallon
madubin saikuma taga tayi kyau saita dauki turare taqara fesawa tadawo palon
tana kallon yanayin dayake kallonta fuskarsa na bayyanarda farin ciki sosai sai
taji farin ciki yakamata sbd ganin ta kyautata Masa shiyasama take nuna kishin
Nuratu sbd ganin hakan na sanyasa farin ciki.
Cake din datayi da fruit drink dominsa taje ta dauko takawo
Masa Nan suka Fara fira cikin nutsuwarsa yake cin cake din duk da a qoshe yake
Amma sbd itace tayi da kanta yakeci cikin alfahari.
Sai guraren qarfe goma yabar part din ta rakosa har waje
kafin tadawo ciki ta wuce dakinta tanajin farin ciki kamar bazata iya bacci ba
yau din.
Washe gari ataredasu Dr khalil din yayi breakfast kafin suka
fita tare harda Dr Salman daya Fara aiki asibitin Dr khalil kafin ya kammala
shirye shiryen sa danshi ba anan qasar yakeson aikiba.
Gidansu kawu suka Fara zuwa tunda ta Isa gidan kowa ke Mata
wani irin kallon burgewa suna tayata murna Wanda yasata sakin baki tana
kallonsu cikin mamaki.
bakin dakin iyami tagan akwatina a jere tsaf su maman junior
sai washe baki sukeyi suna budewa iyami ma yau bakin Nan har kunne sai
annashuwarta takeyi tana sake bubbudewa su maman junior kayan suna gani suna
shewa.
tsayawa tayi tana kallonsu cikeda mamaki kafin ta juyo ta
kalli su Dr khalil dasuka tsaya qofar shigowa suna Magana da kawu Wanda shima
yau harda saka babbar rigar farar shadda wadda itama Dr khalil ne ya dinko
mishi su kusan kala bakwai.
Sake juyowa tayi gurinsu iyami da suke Mata barka da zuwa
Maman junior kuwa rawa tahau Yi tana janyota tana waqarsu ta yarbawa tana
cewa''
Amatunmu tasamu mijinda zai Bata farin ciki da suna me girma
na mutunci.
Kallon rashin fahimta tayi Mata gabanta na mummunan faduwa
ta qwace da sauri zatayi Magana iyami datasan Abinda zata iya fada tayi saurin
cewa''
Kayan Dr khalil ne jiya da daddare aka kawo.
Kallon iyamin tayi da sauri tareda juyawa ta kalli inda suke
Magana da kawu Yana Dan sato kallon inda suke Dan yaga reaction dinta..
Wani irin farin ciki Mara misaltuwa ya shigeta da sauri ta
rungume maman junior tana cewa''
Alhamdulillah ya Allah.
Dariyar farin ciki iyami ta sake tana sake sakawa Khalil din
albarka sbd duk iya bincike kawu yayi akansa Kuma sun Dade da yaba nutsuwarsa
da halayensa sbd a wannan zamanin basu taba haduwa da yaro me nutsuwa ba kamar
Khalil din,
Shiyasa Babu wani dogon janye janye na al'adu kawu yabasa
auren Amatun kawai waliyan Khalil din yake jira idan sun daidaice da khalil din
sbd Khalil ya sanar dashi akwai Yar hayaniya a zuriar tasu idan ta lafa zasu zo
idan Kuma akasin hakan ne ya amince asamu waliyai a daura musu aure.
Zama tayi gefen iyami ta bude kayan tsaf taga abinta tana
sake Jin inama gobene ranar auren ayi kowama ya huta.
Ciki su Dr khalil din suka qaraso suka gaida iyami tareda gaisawa
da sauran mutanen gidan suka koma waje suna jiran Amatun tagama ganin kayan su
fito.
Kusan awa biyu ta Bata kafin ta fito suka wuce asibiti inda
ya ajiyeta a office dinsa suka Shiga meeting tayi zamanta tareda miqewa a
kujerarsa tana game a wayarsa daya barmata wadda kyakkyawan hotonta yake
shimfide lock screen dinsa na ummensa Kuma a main screen dinsa sai hakan yasaka
jikinta yin sanyi sbd a rayuwar Khalil yanzu duk Wanda yasansa yasan itada
ummensa sune sanyin zuciyarsa da idaniyarsa Amma Kuma gashi Sam ko inuwa daya
basa zama a taqaicema ummen Babu Wanda ta tsana a rayuwa kamarta ita Kuma Babu
wadda take ganin ta rainawa wayo kamarta
sai kawai taji Bata girmama soyayyar Dr khalil dinba.
Sai qarfe uku suka baro asibiti sai kawai suka wuce gurin cin
abinci a 5star daganan ma gurin shopping suka wuce sai gab da magrib suka shigo
zabeera
Kai tsaye sashen ummensa ya nufa tana ganin sunyi parking
bakin flat din tayi saurin kallonsa shima ita ya kalla Yana cewa''
Inason ganin Mata biyu masu mahimmanci gareni sun zama daya
wannan shine babban fatana,
Amatu please kiyi hkr da duk Abinda umme ke Miki ki Bata
dama kigani tanada zuciya me kyau,
Abinda nasani shine duk Abinda nakeso ummina na sonshi bare
ke datasan Ina Miki tsaftatacciyar so Wanda bazan iya dainawaba
Dan haka nasan zata soki wata Rana ko Ina Raye ko bana Raye
nasan wata Rana saita soki kamar yanda takesona,so please AMATULLAH ki
qaunaceta ki kulamin da ita I promise you wata Rana zata daina tsangwamanki
zata qaunaceki kamar yanda take qaunata.
Wani irin sanyi jikinta yayi sosai saitaji kunyarsa ta
kamata ta dago a sanyaye ta kallesa ya da yayi saitaji kamar Bata girmama
soyayyarsa ba tunda takasa girmama mahaifiyarsa.,
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin sanyi tace"
Inshallah Zan kiyaye zancenka daga yanxu zanyi iya qoqarina
gurin kyautata Mata.
Numfashi ya sauke ahankali yace"
Thank you AMATULLAH.
Fitowa sukayi suka nufi ciki Yana gaba tana gefensa jiki a
sanyaye take tafiyar sbd yanayinsa duk ya Gama sanyayata ga wani irin damuwa
daya shigeta ga faduwar gaban yanda zasuyi da ummen Amma koma menene tayi
alqawarin jurewa sbd shi.
A palon farko dasuka shigo take qoqarin zama ya tsaya tareda
juyowa ya kalleta yana girgiza Mata Kai tareda cewa''
Follow me.
Falonta na qurya suka nufa Wanda dagashi sai bedroom dinta
Yana gaba tana bayansa.
Zaune take tana kallon wani Shirin girke girken larabawa da
akeyi a mazzika taji shigowarsa tareda sallamarsa ta juyo fuskarta daukeda
murmushin dake bayyanarda girman son datakewa Dan nata sai idanuwanta suka
sauka akan wadda ke bayansa ta hadiye sauran murmushinta fuskarta na sauyawa
zuwa bacin Rai da fushin ganinta ta tsuke fuska sosai tana dauke Kai daga bakin
qofar.
Tsayawa Amatu tayi daga Inda take tana sauke Kai ganin irin
kallon qyama da tsanar da ummen ke Yi Mata,
Qarasowa yayi gefen ummen ya zauna Yana kallon fuskarta data
canza yaji ransa yaqara jagulewa ya sauke wani irin numfashi Mara Dadi Yana
dafa hannun ummen cikin kulawa da sanyin jiki tareda sautin daya sakasu
kallonsa duk su duka biyun yace"
Umme Meyesa Zaki dauki halayyar daba naki ba¿
Shin Amatu tanada wani banbanci ne da sauran mutane da Kika
zabi qyamarta ita kadai?
Umme Amatu matar dazan aurace sbd Ina sonta da dukkanin
zuciyata
Shin umme kodan son datakewa dan naki bazaki qaunacetaba
kodan hakan?
Girgiza Kai tayi tana danne 6acin ranta ta kallesa
tace"
Khalil kadaina cewa tana sonka wannan bayan kudi duk duniya
Babu yaren datake ganewa,
Wannan Babu wani buri a rayuwarsu Bayan samun kudi ta ko
wane halin Yaya,
Kudine kawai agabanta ta yanda zata iya yin komai akan kudi
ciki ina fada maka harda mutuncinta zata iya siyarwa akan kudi,
Wlh khalil kaima sbd kudinka take sonka da bakada kudi
bazata taba sonkaba
Irin wannan matar kakeson nabari ka aura Khalil???
Dagowa yayi ya kalli Inda Amatun ke tsaye cikin wani irin
yanayi na damuwa ya sauke ajiyar zuciya tareda cewa''
Zo AMATULLAH,
Zo Nan kusada umme.
Kallon ummen tayi taga ko kallon inda take Bata qaunar Yi
sbd qiyayya ta tako ahankali tazo gefensa ta zauna ahankali Kan carpet din dake
gurin tana sauke kai maganganun ummen na sake jujjuyawa cikin kanta.
Numfashi ya Kuma saukewa cikin wani irin yanayi na damuwarsa
dake bayyane wadda tasa dukansu su biyun kallonsa yasake riqo hannun ummen
cikin sanyin murya yace"
Ummen banfara son AMATULLAH ba Sai danasan asalin wacece
ita,
Nafara sonta ne bayan nasan batada kowa aduniya,
Banfara sonta ba saidanasan a bola ta tashi acan tayi wayo
ta koyi gwagwarmayar rayuwa,
Banfara tsananin sonta ba saidanasan irin wahalalliyar
rayuwar datayi amatsayin almajiri Mara yanci Wanda ta rayu cikinsu amatsayin
namiji bayan tana matsayin mace,
Amatu bakowa mace face yarinyarda wasu bayin Allah suka
taimaka suka daukesu Bayan sungama wahalalliyar rayuwa acikin bola da mataccin
gidaje da shagunan daba'a gamaba,
Babu Wanda yataba kallonsu da idon Rahama,
Babu Wanda yataba duba yanayin shekaru da jinsinta amatsayin
mace ya taimakesu,
Sun kwana da yunwa suntashi da ita,
Sunyi sata dan suci suyi rayuwa,
Maza da yawa sunyi yunqurin lalata rayuwarsu da sunan
taimakawa shin umme Wanda yake ciki irin wannan qaddarar Dan yayi sata dan yaci
ya Hana kansa Zina illa ne dahar za'a gujesa??????
Umme wallahi tallahi ina tsananin son AMATULLAH da dukkanin
zuciyata bansan ta Yaya zanyi Miki bayani ki qaunaci Amatu ba,
Na shirya auren AMATULLAH na zamo gatanta itada zuriarta
Wanda Babu wani Abu dazai sauya niyata akan hakan,
Shin umme kintaba zaunawa kinyi tunanin irin tarin Lada da
farin cikin dazaki samu aduk lokacinda Kika kawo murmushi da farin ciki a
rayuwar marayu?
Umme tarin ladace me yawa wadda zata iya gyara Miki ko wanke
kurakurenki Kuma yabaki nutsuwar zuciya da ruhi....
Zuwa lokacin Amatu kuka takeyi sosai sbd Bata taba sanin
khalil yasan asalinta ba daduk halinda suka Shiga arayuwa Kuma ahakan yake
sonta tabbas yagama bawa rayuwarta girgizar data sauya zuciyarta akansa gabaki
daya.
Umme ma hawaye takeyi sosai tsananin so da qaunar danta na
ratsata...
Ahankali ya zamo qasa ya durqusa gabanta tareda riqo
hannuwanta idanuwansa dasukai laushi na kallonta a karye yace"
Umme ayau gani na durqusa a gabanki Ina roqonki daki ajiye
dukkanin wani burin rayuwa ko komawa Allah kodan samun nustuwar zuciya,
Umme Ina roqonki da ki qaunaci Amatu ki da zuciya daya sbd
bazan iya ganinku acikin halinda kuke cikiba,
Umme......
Bata Bari ya qarasa ba tayi saurin dagosa tana rungumesa
hawayenta na qara tsiyayowa tace"
Nayi maka alqawari Khalil wlh Babu wani al'amarin duniya
dazan sake Bari na 6ata akansa,
Idan dai Amatu ce Kuma wlh na amince maka bazan qara qintaba
idan har na tabbatarda har zuciyarta itama take sonka....
Rungumeta yayi da sauri Yana cewa''
Thank you ya umme.
Share Mata hawayenta yafarayi tareda juyowa ya kalli Amatu
dake kuka sosai ahankali tanajin Sam Bata cancanci soyayyar khalil ba,
Zuciyarta batayi Mata adalci ba son wani 'da namiji a
zuciyarta Wanda ba khalil ba...
Ahankali yakamo hannunta ya dawo da ita gefen umme dake
kallonta cikin wani irin sabon yanayi ya zaunar da ita ahankali yace"
Amatu ga amanar ummi na ki kular min da ita amatsayinki na
matar 'danta.
Dago jajayen idanuwanta tayi ta kallesa kafin ta kalli ummen
ta daga Kai ahankali takasa cewa komai sai binsa takeyi da Ido zuciyarta na
karban zazzafan baqon yanayi akansa
Wanda ta tabbatarda sone me zafi.
Murmushi umme tasaki ahankali tareda kallon Amatun tana nuna
Mata gefenta tace"
Kimin alqawarin zaki so shi fiyeda yanda yake sonki??
Murmushinsa me nutsuwa ya saki Yana kawar da zancen da
cewa"
Umme wannan son Kaine zakice ta Soni fiyeda yanda nake sonta
sbd bazata iya Sona yanda nake sontaba nawa me girma ne.
Murmushi sukayi Banda Amatu dake Jin wani babban al'amari me
girma atareda ita hakanan taji gabaki daya nutsuwarta na barinta.
Haj maryam da Nuratu dasuka jima Bakin qofar palon suna jin
dukkanin Abinda yafaru baqin ciki me girma yarufe zukatansu da idanuwansu
musamman nuratu data gama zaucewa a fusace ta juya tana qoqarin sakin ihun
baqin ciki da zuciyarta dake neman tarwatsewa da gudu Haj maryam tabi bayanta
tana cewa''
Yau tunda Kika juyamin baya Aisha akan danki kowa ya shirya
tashin hankalin dazai biyo daren Nan Dan wlh yau sai takardun asalin Amatu sun
kwana a hannun Modibbo da Andi.
##mamuh#

No comments