Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 31-32

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


               🅿️31 & 32 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




 ```Jinjina da d'inbin godiya gareku fans tabbas naji 'korafinku akan na'kara yawan typing  to kunason typing  amma  bakwason yin comment  iyakar ku thanks  eh ha'kika inason godiyar dakuma addu'ar ku amma  yin Comment yana sahun gaba wajan zummar yin typing sabida  tananne zansan mai kuka d'auki sa'kon nawa to idan kunason na'kara yawan typing  nadinga ganin ruwan Comment  da muhawara akan Novel d'in```👌🏻


*_Sannan dan Allah  masu bina ta pc akan natura musu daga farko dan Allah  kudinga tambaya a group  sabida abin yanayimin yawa please 👏🏻 Ana tare all sisters_* 🤝🏻😘


🅿 31 & 32




Mi'kewa tayi rai 'bace tace 


" gaskiya  Muzaffar  kabani kunya wannan  yar 'karamar yarinyar kakeyima irin wannan  hmmm " 


Fita tayi afusace tana fita Muzaffar  yasauke wata irin ajiyar Zuciya  rai 'bace yace " se yaushe zaki saukamin daga jiki ? " fuskar shi tanuna 'bacin rai amma muryarshi takasa fita da karfi kamar yadda Rayhana  tazata jiki a sanyaye tami'ke saurin fita daga part d'in tayi sabida  tsoran abinda zai biyo baya kai tsaye part d'insu tanufa su Sudees suna gurin Momy a can wajan kaka 


Kwanciya Muzaffar  yayi kan cushion d'in jikin shi duk babu 'karfi wani irin takaici yakeji cikin zuciyar shi yace 

" wato ni wannan  yarinyar  zata nunawa futsara kodayake tasan waye namiji tundaga shedanan Sudees  da Shureem  tun tana yar ficiciyarta toni bazan d'auki wannan  fitsararba zanyi maganinta "


Itako Rayhana  tana shiga tayi saurin d'aukar wannan box d'in cire zoban ciki tayi ta'adanashi sannan tad'auki wata abaya tasaka tafita tanayi tana waige cikin tsoro da fargaba tashiga cikin part d'in saurin sauke ajiyar Zuciya  tayi ganin babu kowa cikin parlour  rumtse  idanunta  tayi tanufi cikin bedroom  d'in dake kallon hanyar waje wani irin bugawa zuciyarta keyi tana shiga tabud'e idanunta jin 'karar saukar ruwa cikin toilet  yasata dafe 'kirji saurin aje box d'in tayi kan bed tajuya tafita cikin sauri 


Part d'insu takoma tana shiga tanufi freezer  robar  ruwa tad'akko ko tsayawa neman cup batayiba tabud'e takafa kai seda tasha yakai rabi sannan  ta'aje tashiga cikin bedroom  kullewa tayi sannan  tazauna kan bed tana sauke ajiyar Zuciya  duk tagama furgicewa tsayin lokaci sannan  tami'ke tanufi toilet


Ummi nafitowa daga toilet idanunta suka sauka kan wannan  box d'in cikin tashin hankali ta'karasa wajan bud'e box d'in tayi zaro ido tayi ganin kud'in amma  babu zoban saurin rufewa tayi tami'ke fita parlour  tayi hadimai tashiga 'kwalama kira cikin tsoro suka shigo zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa tsawa tadaka musu tace 


" waye yashigo cikin part d'in nan kuma har cikin bedroom d'ina ? " cikin tsoro suke sanar da ita babu kowa mari tawatsama takusa da ita tasake cewa " kamarya bakuga kowaba shashanci kenan lalle idan kuwa hakane bakuda amfani kuma wallahi kuyi gaggawar nemomin wanda yashigo yanzu ko nayi muku hukunci mafi girma "


Juyawa tayi takoma cikin bedroom ko Shiryawa  takasayi sabida tashin hankali afusace tami'ke tasa kaya cikin tashin hankali take fad'in 


" tabbas akwai wanda yasan komi akan 'batan Twins d'in Muzaffar  gashi ni za'a farasawa cikin matsala bayan bani 'kad'ai na aykata hakan ba ana ganin wannan  box d'in agurina za'a zata har kisan Nabila  inadasa hannu aciki dana shiga uku dole nasan abinyi kuma dole nanemi wadda  yakawo wannan box  d'in " 


Cikin sanyin jiki Muzaffar  yafito daga part d'in Momy cikin mamaki  yake hangen harabar ajiye motoci yadda manyan motoci keshigowa cikin sauri aka bud'e Motar dake tsakiya fuska naga Muzaffar  yasaki had'ida yin Murmushi  yanufi gurin dogarawa suka shiga kirari Muzaffar  yana isa yarungume shi yana fad'in 


" oyoyo yaya Ibrahim  se yanzu kake dawowa agaskiya nayi fushi " Murmushi  Yaya Ibrahim yayi had'ida kama kunnanshi yace " ayi ha'kuri aboki " bata rai Muzaffar  yayi yace " haba yaya Ibrahim  nacefa kadena cemin aboki koda baka auri Aunty  Sumayya ba aykai babban yayane " sakeyin Murmushi  yaya Ibrahim  yace " ammafa lokacin dakake yaro konace yaya sekace a'a aboki dan haka wannan  kalmar bazata mutu ba "


" kayi maza kasanar da 'kanwata Nabila  nadawo kaga wannan  bag d'in duk tsarabar tace hadda wani saban turare kasan aduk lokacin  dana dawo take canja saban turare gakuma tsarabar Twins  gaskiya naso nazo wajan hidimar sunan su ayki yatsareni Allah yasa 'kanwata batayi fushi daniba ? " ganin yadda fuskar Muzaffar  tacanza yasa yaya Ibrahim  yin shiru amma cikin zuciyar shi  cewa yayi Allah  yasade lafiya  cewa yayi sunufi part d'in  maimartaba  dan shi yakeson fara gani kafin kowa 


Suna isa maimartaba  yafad'ad'a Murmushi shi rungume yaya Ibrahim  yayi yace " masha Allah  yau  ga d'ana yadawo zama yaya Ibrahim  yayi sukad'an ta'ba hira sannan suka mi'ke zuwa part d'in  Momy  


A ta'kaice Yaya Ibrahim  d'ane ga yayan maimartaba  uwa d'aya uba d'aya mahaifin shi yabar gida tun kafin rasuwar mahaifin su se bayan wasu shekaru matarshi takawo yaya Ibrahim cikin masarautar nan tun yana d'an 5 yr acewarta mahaifin shi yarasu sosai yaya Ibrahim yasamu gata tun dagaranar mahaifiyar Yaya Ibrahim  batasake dawowaba ayanzu kam sunyi zaton bata raye Momy tari'keshi tamkar d'anta sa'an yaya Ahmad ne yaya Ibrahim  baisan ba Momy bace ta haifeshi se lokacin da za'a aura mishin Aunty Sumayya  sosai yayi mamaki sabida yatashi babu banbanci 


Yasha'ku sosai da Muzaffar  tun yana jariri wannan  sha'kuwar tasa Yakecema Muzaffar  aboki yana matu'kar  son duk wani abinda Muzaffar  yakeso shiyasa yake son Nabila  a cewarshi Muzaffar  yayi dacen mata shidin jami'i ne na CBI bayanan Nabila  ta haihu amma ansanar dashi haihuwar amma har yanzu baisan an kashe Nabila  da 'batan yarantaba wannan  kenan


Sosai momy tayi murnar dawowar yaya Ibrahim  cikin zumud'i wata hadima tashiga part d'in Aunty Sumayya  zaune take itada Islam gaisheta tayi sannan  tace 


" Allah  yabaki nasara dadyn su Amfal yadawo " cikin sauri Aunty  Sumayya tami'ke tasake maimata kalmar " yadawo ? lalle wato babu ko sanarwa balle ashirya mishi tarba " cikin sauri tanufi cikin  bedroom  kai tsaye toilet  tashiga 


Bayan sun gama gaisawa yaya Ibrahim  yasake cewa " haba aboki tashi kakiramin 'kanwata mana akawomin Twins  nasan su basuyi fushi daniba mi'kewa Muzaffar  yayi cikin wani irin yanayi yafita bayan fitar Muzaffar  Momy tasanar da Yaya Ibrahim  batun rasuwar  Nabila  da 'batan Twins sannan tasanar dashi labarin d'ayar matar shi dasu Shureem  sosai yaya Ibrahim  yakad'u dajin wannan  mugun labarin amma yaji sassauci dajin maganar d'ayar matar wato Rayhana  


Muzaffar  yana shiga yanufi cikin bedroom  ganin batanan yasa yafito yanufi cikin bedroom d'in Nabila  zaune yasameta tayi shiru alamar tashiga cikin zurfin tunani tamke fuska yayi yace " ke  ina yara ? kitashi muje ga yayana yadawo kugaisa " cikin sanyin jiki Rayhana  tami'ke  murya asanyaye tace " suna gurin kaka " had'a rai yayi yace banace kidena barin gurin dasukeba to wallahi  idan kika rasa yaranki babu ruwana  kijirani a parlor bari nad'akkosu " 


Fita yayi tabi bayanshi da kallo tace " kai babu wani sassauci atare da kai koda yaushe cikin masifa Allah  kabaiyana makasan Nabila  nabar cikin masarautar nan nahuta "  shigowa yayi rungume dasu saurin amsar d'aya tayi tagefan idanun shi ya kalleta cikin zuciyar shi yace " wani wankan tasake yar 'karamar yarinya da ita se jan hankali tsiya kisani Muzaffar  yafi 'karfin kula 'karamar yarinya " 


Fita sukayi suka nufi part d'in Momy  suna shiga yaya Ibrahim  yami'ke ya amshi yaran cikin girmamawa tagaida yaya Ibrahim  'ko'karin sakin fuskarshi yayi suka gaisa dan duk tausayin Muzaffar  yakamashi ta'a ziyya yaya Ibrahim  yayi mai cikin dakewar Zuciya  yaya Ibrahim  yami'kama Rayhana  bag yace 


" gashi Raihan wannan  tsarabar kice d'ayar bag d'in yami'ka mata yace wannan  kuma ta Twins " godiya sosai Rayhana tayime mi'kewa yayi yamusu sallama  yafita shima Muzaffar  fita yayi zuciyar shi cunkushe da damuwa sawa Momy tayi aka kaima Rayhana  kayan part d'insu fuskantar Rayhana  tayi sosai tace 


" Raihan nalura Muzaffar  yafison Nabila yakamata kimantar dashi Nabila nasan bazai manta da itaba amma ina nufin kisa idanunshi yadena hangenta bata raye kece agabanshi yanzu ke yakamata yakalla farincikin da Nabila tabashi kema kin bashi amma kinasake da damarki akanshi Raihan ke macace kinada abubuwan dazakija hankalin mijinki kicire kunya kibama mijinki kulawa karki bari ciwo yakamashi kinsan damuwa babu abinda bata sawa ki d'auka tamkar mahaifiyarki ce take yimiki wannan nasihar ba mahaifiyar mijin kiba kinga yau tabon rashi Nabila  yafamu cikin zuciyar shi kiyi 'ko'karin samarmai da farinciki kisa yadena ganin yarintarki yazama yana kallonki fiyeda Nabila  hakan zaisa yasamu kwanciyar hankali kema haka tashi kije Allah yayi miki albarka "


Mi'kewa Rayhana  tayi idanunta suncika taf da hawaye cikin zuciyar ta tace " kiyi ha'kuri Momy aurena da Muzaffar  yarjejeniyace bawai nagaske bane bazan iya bashi kulawa irinta mata da miji ba shima bazai saurareniba amma zanyi iya 'ko'karina wajan sashi farinciki amma bazan iyaba wanda bayasona kainaba " 


Tana isa parlour  tabud'e  tsarabar yaya Ibrahim  kayane masu kyau daturaruka masu kamshi da tsada da mayamaye kala kala haka bag d'in su Shureem  suma kayane masu tsada kwasarsu tayi tanufi cikin bedroom  misalin 09:00 pm Muzanbil  yashiga cikin bedroom d'in  Samha hannun shi ri'keda Cup da magani fuska tamke yami'ka mata babu musu ta amsa yitayi kamar tasha tami'ka mishi Cup d'in amsa yayi yafita bin bayanshi tayi da kallo cikin zuciyar ta tace yau zanga zahiri kwanciya tayi kamar tayi bacci babu jimawa yashigo kiran sunanta yashigayi yaji shiru cire jallabiyar shi yayi dagashi se singlet da shotnika hawa yayi saman bed d'in yashiga 'ko'karin rabata da kayan jikinta duk tanajin shi harya sabule mata riga yashiga romantic  d'inta 


Sosai Samha takejin sa'kon cikin jikinta amma tadaure seda yagama fita hayyacin shi duk babu kaya jikin su yaja musu blanket  yafara 'ko'karin shigarta matse kafafunta tayi had'ida bud'e idanun ta tace 


" Sannu Yarima gaskiya  salon takunka yaburgeni sosaifa amma inamai tayaka takaici yau bazaka samu wannan  biyan bu'katar ba " dukda razanar da Muzanbil yayi amma seyadake yace " ke  kinayin haukane keba matata bace? Karkiyi kuskuran yin haka zanyi mugun 'bata miki rai " cigaba yayi da 'ko'karin shigarta  amma tahana ganin tana 'ko'karin zamai matsala yace " haba my wife  Allah  fa zaiyi fushi dake mijin kinefa ? " 


Murmushin takaici Samha tayi sannan tace " zanbaka kaina amma kasanar dani gaskiyar wannan cikin? " sosai Muzanbil yaji fad'uwar gaba amma bashida za'bi dan kam yariga yazo hannu cikin wata irin murya yace " nawane banshirya haihuwa yanzu bane shiyasa nace banawa bane ni shedane akan budurcin ki Samha  nakumasan babu wani namiji daya ta'ba yimiki haka seni " 


Cikin wata irin murya Samha tace " shikenan yarda amma kayimin ha'kuri nashiga toilet yanzu zanfito inajin fitsarine " d'agata yayi yana fad'in karki dad'e "  Murmushi  tayi tashiga toilet  sedata kulle 'kofar tace 


" tabbas Yarima  kacutar dani kasa narasa ganin wannan  daran dako wace 'ya mace take burin gani kabugar dani alokacin kasa naganshi tamkar cikin baccina amma dukda haka sedanayi jinya kasa kaina cikin rud'ani wanda se yau wannan kunlin ya warware daga Zuciyata kasani bazaka 'kara samun kainaba kuma wallahi  wannan  babyn seyazo duniya  in sha Allah "


Cikin kidima da matsananciyar bu'kata Muzanbil yafara ro'konta amma taki rai 'bace yamaida kayanshi yafita yana fad'in yau nine nike ro'kon mace hmmm kiri'ke kayanki Samha bazan sakebi takankiba " 


Abangaran Rayhana  kuwa shirin bacci tayi cikin riga da wando masu taushi turarukan da yaya Ibrahim  yakawomata tafesa sakin sumar kanta tayi tanufi cikin bedroom d'in Muzaffar  kwance tasameshi yarufe jikin shi duka yana rawar sanyi alamun zazza'bi cikin sauri tahau saman bed d'in tunawa tayi damaganar Momy gyaramasu Shureem  kwanciya tayi dagacan wajan bango ta kwanta kusada Muzaffar seseta zuciyar ta tayi cikin wata irin murya tace 


" damuwa bata kamacekaba sojana karka bari ba'kin ciki da damuwa susamu muhalli cikin zuciyar  tsayayyan namiji soja na ka rumtse idanun ka kasa cikin zuciyarka matarka zata baka maganin wannan sanyi " ahankali tabud'e blanket d'in tashiga ciki kamshin turaran jikinta yasake dakar hancinshi lumshe idanunshi  yayi hannunta tazura ta rungumo shi wata irin ajiyar Zuciya  yasauke had'ida jan numfashi mai 'karfi wani irin bugun bugu zuciyar Muzaffar  tashigayi 


Tofa lalle Rayhana  anya kuwa 🥰😜 👌🏻


Daga Al'kalamin....🖊


NPEEDY A AJI 🌸🦚🌸


Comment and share please

No comments