MUGUN DUHU 17-18
⚫```MUGUN DUHU```⚫
_STORY BY MRS ABDULL_✍️
____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
1️⃣7️⃣_1️⃣8️⃣
''Salati umma da Abba suka dauka a tare,da sun sure zasu kama wani ,ita kuwa SAHLA wani kukan ta sake fashe wa dashi kamar ranta zai fita.
''AHLAN kuka SAHLA kuka Abba da umma kuma sunyi jugum jugum sun rasa ta cewa,tsawon mintuna babu wnada ya samu damar cewar komai sai kukan SAHLA da shasshekar AHLAN dake ta tashi.
''Can mahaifin ta yayi ƙarfin halin faɗin '' SAHLA wa yayi maki ciki?
Wata firgita tayi sannan ta fashe da kuka tana faɗin ''na rantse da Allah wallahi wallahi Abba ban sani ba wallahi Abba babu wanda yayi min wallahi ban sani ba''
Miƙewa yayi yana niyyar fara jibgarta AHLAN ya riƙe shi da fadin dan Allah Abba kayi hakuri,abinda kwanciyar hankali bai kawo shi ba bana jin tashin hankali zai iya kawo shi a kai zuciya nesa,niday a yanzu bazan iya shedar SAHLA ba amma tabbas bana ji a jiki na zata aykata abu makamancin wannan da sanin ta sai day kuma wani abun daban.
''hwayen da suka zubo wa umman ta ta share sannan tace ni kaina ina kokonton wannan lamarin AHLAN niday niday fauzah irin tarbiyyar da na bawa ya'ya na irin wahalar da nake sha kansu na tabbatar Allah bazai bani kunya ba bazan taba jin kunya ba kansu ,ya za'a yi SAHLA tayi ciki ina take zuwa yaushe tayi lpyar da har wani zai mata ciki innalillahi wainna ilaihirraji'un.
''allah gamu gareka Allah mun tuba Allah Allah ka sassauta mana wannan al'amari dake faruwa.cewar Abban SAHLA.
Ameen Alhaji ameen ya Allah.
AHLAN kayi hakuri ka jure dan Allah ina mai baka hakuri ka saka wa zuciyar ka salama da ruwan sanyi dan Allah.
''abba koda ace SAHLA ba jinina bace ba kanwa ta bace bana jin irin son da nake mata zai sa na ga bakin ta ko na kasa yarda da ita ,balle yar uwa ta ce Ni na raini SAHLA a gaba na SAHLA ta tashi nasan shigar ta da fitar ta shin ya za'a yi na yarda cewa zata aykata mummunan abu kamar wannan taya ya? 😭
''addu'a ta daya ita ce Allah ya daura mana juriya da hakuri Allah yasa mu cinye wannan jarabawar.
''Allah yayi maka albarka Allah yasa ka gama da duniya lpya lallai ka rike zumunci kuma Allah zai dube ka ,ko bayan raina nasan ina da tabbacin Allah ya kawo mai kula da yayana da mahaifiyar su Allah ya shayar da kai farin ciki 😭cewar Abba yana goge hawayen idon sa,abin yana kure masa tunani shin ina makomar auren SAHLA da AHLAN da wanne ido danginsu zasu kalle su shin ta ina zasu fara wannan bayanin idan AHLAN ya yarda baya nufin kowa da kowa sai ya aminta da su sai yayi wa yarsu KYAKKYAWAR fahimta ,Ya Allah Allah gamu gareka Ya Allah cewar abba.tashi ka tafi dare nayi babu yadda zaka wuce da ita gidanka hakan ba mai yiwuwa bane dole SAHLA gidan nan zata dawo da zama ,zamuyi magana da yaya Ahmad da safe insha Allah Allah ya kara mana hakuri cewar Abba.
Ameen Abba ameen Ya Allah dan Allah ka kwantar da hankalinka kaga kaima ba lapya gareka ba ga ciwon ka baya bukatar tunani haka dan Allah ka daure Abba. Insha Allah Allah ya tashe mu lpya. Cewar Abba
Bayan AHLAN ya fita ne SAHLA ta fashe da wani irin masifaffen kuka salati kawai da tasbihi ga ubangiji take ta rasa wannan tashin hankali dame yayi kama ta rasa dame zata kwatanta shi , umma ne ta kama ta ta daga ta dakin su ita da Khalil ta kaita har yayi bacci da litattafai a gabansa a watse.
''Gado ta zaunar ta sannan tace''
''Ƴata hakuri shine jigon komai cikin rayuwa idan mutum bashida hakuri bashida tawakkali rayuwa takan zo masa bai bai ,bata zuwan masa yadda zai tafi kai tsaye ba tare da matsala ko tashin hankali komai da kika gani a duniya a na iya yinshi daga baya a yi dana sani ko aji da ba a yi ba amma hakuri baya ɓaci hakuri baya lalacewa ba'a jin dama banyi hakurin nan ba ki gwada ki sakawa zuciyar gabas salama a duk duniya komai yayi zafi maganin shi Allah babu abinda ya zo wa zama sai ikon madaukakin sarki.ki hakuri ki cinye wannan jarabawar ki cinye wannan iftila'i ne wannan babban tashin hankali ne zaki fuskanci matsaloli iri daban daban a rayuwa inday wannan cikin da ake ikirarin yana jikinki ya tabbata ya fito dole sai munshiga tashin hankali to amma,duk wani bawa da kike gani akwai kaddarar da Allah ya rubuta masa sai ta same shi mai kyau ko marar kyau ,dole kiyi hakuri ki jajirce banison wannan kukan ki barshi domin baya haifar da komai sai daci da bakin ciki cikin raina.kinji??
''naji umma kuma na ɗauka insha Allah Zaki same Ni mai karbar ƙaddara duk yadda ta zo mani amma abin da ciwo umma da zafi zuciya ta ba Mani zafi idan na tuna babu wanda zai yarda dani , kowa kallon da zai min na daban ne umma ina shiga rudani da tashin hankali idan na tuna wannan tayaya su Ummi zasu dauke Ni wanne irin kallo zasuyi min baba Ahmad wanne irin tunani zaiyyi a kaina musamman Maryam da zainab wanne irin cin mutumci ne bazasu yi min ba dama ga yadda nake a wajensu balle kuma hakan ta kasance shin ya kike gani umma?
'bakomai SAHLA kamar yadda na gaya maki a tun farko komai yana wuce wa a duniyar nan banda ikon Allah hakurin nan day shi zaki yi ta fada muryarta na karkarwa domin zuciyar ta ta karye ta rasa ya zata lallashi yarinya mai kimanin shekaru 19 da wannan iftila'i ya afka ma dole ziciyarta tayi rauni dole taji babu dadi.
''mikewa tayi sannan tace ki huta saida safe kinji?
''to umma sai da safe ina alfahari dake matsayin mahaifiya umma keɗin ta daban ce cikin iyaye Allah ya saka maki da aljanna sakamakon tarbiyyar da kike daura mu a kai bisa dan'uwa na Allah ya biya ki da mafificin alkairi.
'' da ameen kawai umma ta amsa ta fita sabida zuciyar ta ta karye ya za'a yi ya za'ayi ace yarinya mai irin wannan hankali tayi wannan abun ina hakan bazai yiwu ba dole akwia wani abu.
''fitowa tayi tare da fashewa da kuka Abba dake tsaye bakin dakin yana sauraran su ya dauka SAHLA zata fadi wani abin daban sai yaji ba haka ba ,zuciyar sa ta kara tabbatar masa da yarsa bazata taɓa yin abu makamancin haka ba rungume umma kawai yayi ya bata zuwa dakinsa .
''ta kasa daina kuka har yanzu yinshi take haiƙan.
''Alhaji daƙyar na lallashi SAHLA nima bukatar hakan nake amma sabida kwanciya hankalin ta yasa na danne nawa tashin hankalin Alhaji na rasa ta ina zan fara tunanin wannan lamarin Zuciya ta ta gaza dauka.
FAUZAH yanda kika fadi ma yarki hakuri shine maganin komai to hakan yake ,bayan shi sai addu'a,a sannu a jikina nake jin wani abu ne da aka dade ana shuka wa yake shirin fita kowa ya ganshi Allah masani amma tabbas muna cikin mawuyacin jarabawa mai wuyar cinyewa .
Haka dau suka yi ta tattauna lamarin su kama wancan sun kunce su sake haka nan dau da karshe dole alwala suka yi suka fara jera nafilfili akai akai.
SAHLA kuwa zaune take inda mahaifiyar ta ta barta kukan ma yanzu kam ya mata wahala hawayen sun mata kaura domin sun dauki dif sai yau take tabbatar da maganar da ake cewa idan tashin hankali yayi tashin hankali hawayen ma baya zuwa ,ta rasa inda zata tsoma Rayuwar ta taji sanyi ,tunanin ta daya shin yaya danginsu zasu dauki wannan lamarin ta ina zasu dauke shi wanne irin kallo ne zasu yi mata ita da iyayen ta dama yaya da Maryam da zainab kamar zasu tona rami su saka ta ina da sunji wannan mummunar kaddara da ta same ta ay sai abin ya ninka hakan kai tsaye ta faɗa tunanin rayuwar su ta baya ita da AHLAN.✍️
*Kuyi hakuri da wannan ciwon ciki nake pls*
*TALLA TALLA TALLA*
*LITTAFIN JANNAT LITTAFIN DA YAZO DA SABON SALO DA HARGAGI DA RUGUNTSUMI WACCE NI MRS ABDULL NA RUBUTA MAKU SHI WACCE BATA KARANTA BA TAYI MAZA TA GARZAYO DOMIN NEMA TA KARANTA KAN FARASHI NAIRA 200 KACAL DOMIN KUWA JANNAT RETURN YANA NAN ZUWA MAKU DA BAYAN SALLA INSHA ALLAH WANDA ZAU ZO MAKU DA WANI SABON SALON MAI RIKITARWA DA CHAKWAKIYA CIKIN SA WADDA SUKA KARANTA JANNAT SUN SANI KU TANBAYE SU KARON HAJIYA SADIYA DA HUDAY KU TANBAYE SU INA NUWAIRAH,KU TANBAYESU ALWASHIN DA TA BUGA KAFIN A KARKARE LABARIN TABBAS KUNSAN DA CHAKWAKIYA KUN SAURARE NI KU TARE NI CIKIN JANNAT RETURN DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA MAI NEMAN JANNAT COMPLETE ZAI YI MAGANA TA WANNAN LAMBAR IDAN BA BIYA ZAKIYI BA PLS KI HAKURA SAI KIN SHIRYA👉*
_07059305867_
*MRS ABDULL ce ✍️*

No comments