MIJIN AMMINA NE SILA 21-22
✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
Written by noor Eemaan
wattpad@NoorEemaan
Page21-22
Amma dauriya irin tasa ya sa ko afuska bai nuna ba, hannun mummy ya daura afuskarsa ba tare da yace komai ba tsahon lokaci, mummy kuwa sanin halin danta data yi yasa bata furta komai ba sai dan kansa ya sauke hannunsa hadi da ware idanunsa dasuka yi jaa tashi daya, cikin husky voice dinsa yace "mom zamuyi maganan but not now please" ba musu ta jinjina masa kai alamun amincewa
"tnx" yace yana barin wurin cikin sauri...
kan gadonsa ya haye ya fada cikin duniyar tunanin gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ya rasa meyake ji gami da abrar "tausayi ne ko so" domin shi bai taba soyayya ba bare ya sani, abu daya yasani yana jin abu mai girma da baki bazai iya furtawa a kanta ba, tabass yana bukatar mai bashi wanna amsar gwauron numfashi ya saki hadi da lumshe idanunsa ahankali kamar wanda aka wa dole yace "please come back to me decent one"....
bayan sati biyu wanda yayi daidai da dawowar amal daga serving, mummy taji shiru aaban bai ce mata komai ba ranar wata lahadi da misalin karfe sha daya na safe mummy ta nufi dakin shi domin jin ta bakin sa, knocking mummy tayi taji shiru hakan yasa ta tura kofar ta shige yana kwance flat akan gado yayinda ya rufe fuskarsa da rigar abrar nan dai data yayyage komai daya faru aranar daya fara ganinta sai zuwan masa kwakwalwarsa take daki-daki, cikin mamaki mummy ke binshi da kallo ganin rigar mace a fuskarsa yaye rigar tayi wanda yayi daidai ta wata katuwar ajiyar zuciya daya saki ahankali ya ware sexy eyes dinsa dabasu fiye girma ba ya sauke su kan mummy....
kara mayarwa yayi ya rufe, girgiza kai mummy tayi domin halin aaban sai shi, bubbuga kafansa tayi tace "tashi muyi magana" ba musu ya mike ya zauna still idanunsa arufe a maimakon maganar daya kawato sai tace
"son rigar wace wanna!!!"
sai a lokacin ya bude idanunsa ya kurawa rigar ido na yan seconds kana ya ware jan labbansa yace
"rigar ta ce"
"ita wa?" mummy ta tafada cikin mamaki
"mum i don't know her"
yafada muryansa nason fito da rauninsa sai dai dakakkiyar zuciya irin tasa yasa baza'a fahimci hakan ba.
"are you serious ? wait! are you sure you are ok son?"
da dariya na cikin dabi'arsa da babu abunda zai hana shi yi, domin ya fahimci mummy na tunanin ko baya cikin nutsuwa da hankalinsa ne...
"mum am absoutely fine"
"no you are not son! da lafiyar ka kalau da baza ka ce min baka san mamallakiyar wanna rigar ta hannuna ba, ta fada tana daga rigar, toh ya aka yi kasamu rigar"?
kamar bazai yi magana ba sai kuma yace
"rigar wata patient dina ce, na kasa mantawa da ita" ya fada yana sake sauke wani ajiyar zuciyan.
"son ka fada soyaaya" mummy ta fada
cikin tabacci.
abunda yake son sanin kenan dan haka cikin sauri ya riko hannunta yace "mum are you sure? you mean i have fall in love?"
cikin murmushi mummy ta gyada kai hadi da cewa "son kasan ni mahaifiyar ka ce ko? baya ga haka na baka shekaru masu yawa, kasan kuma dole na fika exprience akan rayuwar duniya, so tell me ya aka yi ka sameta? ni babarka ce kayi sharing damuwarka dani, kuma nasan cewa baka da waccce ta fini aduniyar nan right?"
jinjina kai yayi alamun "eh"
"good boy, so tell me who's the lucky girl?"
hannunta ya rigo yafara tunanin yadda zai yi dogon magana domin idan akwai abunda ke bashi wahala toh dogon magana ne "mum i dont no how to explain,.... but na hadu da ita ne aranar da na yi night duty na kuma dawo da safe nayi wanka na koma har kika bani breakfast kin tuna?
jinjina kai mummy tayi alamun
ta tuna nan ya shi bata labarin komai.....
bayan ya gama gaya mata sai ya dora da cewa "tun daga ranar na kasa rabuwa da tunaninta i thought tsananin tausayinta ne mom, ashe na fada sonta ne ban fada bansaniba"...
"noo son baka fada sonta ba, kuma bazaka taba fadawa sonta ba, domin bazan hada jini da wacce ta zubar da mutuncinta atiti ba, kayi gaggawar cireta aranka domin bazan taba bari ta amsa sunan "SURUKATA BA"..... mummy ta fada cikin matsanan fushi, da aaban bai taba ganinta aciki ba
cikin rudewa yace "mom i thought kin ce na fada sonta?
"son! mom ta kirashi cikin fushi kana tace kayi gaggawar cireta aranka, ABRAR kawar hanan ita zaka aura ada nayi tunanin yar gidan mutunci ce, da na baka goyon baya dari bisa dari har in tayaka nemanta amma, not anymore da zaran daddy'nku ya dawo daga kuwait zai je gidansu nema maka auranta ( kasancewar alhaji abdur-rauf yaje kuwait ne kan harkan bussiness dinsa) tana gaman fadin haka ta bar dakin.....
da kallo yabi mummy kana ya sake kankame rigar abrar, babu abunda ke masa gizo sai kyakyawar fuskar sa mai cike da kamala, ga kuma maganganun mummy dasuka sake ninka masa damuwarsa...
"CYPRUS"
Har yanzu dai abrar na nan babu abunda ya canza, saidai hanan na matukar kokari wurin ganin cewa tana debe mata kewa, kamar yau zaune suke adakinsu yayinda hanan ke bata labarin ban dariya domin yau basu je lectures ba, saboda jiya ciwonta abrar ya motsa haka ta dinga dariya hadi da kuka a hall din dasuke lecture, lecturer yace a fitar da ita ta shiyasa hanan tace yau daya su hutu, ana cikin haka wayar hanan ya fara kara "sis amal" tagani baro baro arubuce kan screen din wayarta murmushi ta saki kana ta latsa kore hadi da cewa
"anty amal na"
daga can bangaren amal tace "little hanan yakike ya studys? "
"all fine anty, ina tayaki murnan kammala service dinki"
"see her mouth daman ki samu labari baki kirana ba sai yanzu ko?" amal ta fada cikin wasa
dariya hanan tayi kana tace "eh mummy ta gaya min"
"ai shikenan sai anjima daman nace bari naji muryan little sis dina"
cikin jindadi hanan tace "tnx my big sis much love bye" ta katse kiran...
suna gama wayan sai ga kiran aaban ya shigo, hanan murna kamar tayi me ganin yayyanta suna ta kiranta yau har wani on top take jin kanta lolz...
"hell... au assalama alaykum ya aaban" ta fada tana sosa kai
"yes little how are you?"
"ina lafiya, ya aaban nayi kewar ka faa" ta fada cikin shagwaba.
"really? zaki ganni soon"
"da gaske ya aaban?"
"ina miki karya ne? daddy ya kira ni kuwait akan wani signing da lallai sai ni zan yi yanzu haka ina can zan biyo gobe in ganki kafin nabi flight din yamma"
"gaskiya naji dadi" zata kara magana ya katse wayar....
abrar dake zaune tana murza diamond ring din hannunta, tayi shiru tana sauraren muryan aaban mai sa nutsuwa kasancewar a loud hanan ta sa wayar, ganin hanan ta ajiye wayar sai kawai ta kwabe fuska tamkar mai shirin yin kuka...
"what?" hanan ta fada tana dariya
rungume teddy dinta tayi da kyau ta langwabe kai, sai ta girgiza kai alamun ba komai.
murmushi kawai hanan tayi tace "shagwababbiya kawai"
"naji din" abrar ta fada tana cuno baki...
washegari sai ga aaban a cyprus wani wurin shakatawa mai suna "golden stars" yace hanan taje zai zo wajen ya ganta domin yace bazai dade ba kada yayi missing flight, cikin sauri sauri hanan ta shirya bayan ta lallaba abrar ta rakata sannan suka fice domin tasan ya aaban bayason jira....
abrar na sanye da simple gown white color sai vail dinta daya kasance black babu makeup afuskarta ko digo amma tayi mugun kyau, yayinda hanan ke sanye cikin shigar Pakistan hadi da mayafinsa they were both looking muaah💋 wurin shakatawan ya hadu matuka daya daga cikin kujerun wurin suka zauna tana jiran zuwan aaban...
cikin shigar kananun kaya ya fito daga taxi yayinda ya dora black leda jacket asaman kananun kayan sai ya rufe fuskarsa da sunglass daya yi mugun yi masa kyau kafarsa kuwa sanye take da canvass black mai ratsin fari, cewa taxi driver yayi ya jira shi bazai dade ba domin ya mayar da shi airport...
"hanan bari naje rest room( bandaki) kinga cikina sai murdawa yake, dariyan mugunta tayi hadi da cewa toh ayi festo lafiya"
murmushi hadi da hararan wasa abrar ta sakar mata kana tafara tafiya wanda yayi daidai da shigowar aaban wajen, hankalinsa na kan danna waya soyake ya kira hanan ko tana ta wani bangare domin wurin nada part part ne, dai dai lokacin hanan ta taho.....
KUYI MANAGE YAU BANA CIKIN GOOD MOOD...
SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌
NoorEemaan loves you all💖
https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

No comments