Breaking News

MUGUN DUHU 19-20


 ⚫```MUGUN DUHU```⚫


_STORY BY MRS ABDULL_✍️

*_____________________________________*

 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*



🅿️_1️⃣9️⃣_2️⃣0️⃣




_Am back kuyi hakuri jina da kuka yi shiru 2days am not well_




*WAYE AHLAN DA SAHLA*



Ahmad da Musa da Asma'u yan uwan juna ne masu hadin kai wanda suka fito tsatso guda ciki daya, Ahmad ne babba Sai Musa sannan Asma'u ,mahaifansu sun rasu a lokaci mabanbanta mahaifinsu ya fara rasuwa sannan mahaifiyar su,tun kafin hakan suka tashi tsaye wajen bawa ƴaƴansu tarbiyya mai tsabta ,sun kuwa samu taimakon Allah domin Allah ya dafa masu, bayan auren Asma'u da shekara 1 Allah yayi wa mahaifinsu rasuwa da wata 2 kuma mahaiyar su itama ta ce ga garinku.

      Ahmad da Musa babu wadda yayi aure cikin su neman kudi suke sosia haiƙan babu zama ,kasuwanci suke na kayan saka wa na mata takalma atamfa leshi material jakankuna sarka da sauransu ,sosia suke neman kudi dukiyar su a hade take babu wani banban ci ,shaguna ne dasu a kasuwa guda biyu a shakare da kayan sakawa na mata.

     ''ahmad shi ya fara zancen aure inda ya samu wata yarinya mai hankali da kamala da natsuwa nan cikin unguwar su kasancewar sanin iyayansa da akayi basuda wata matsala sannan kuma yana sana'a yana kuma da hali na gari aka ɗauki yarinya aka bashi , farida farida KYAKKYAWAR gaske ce son kowa ƙin wanda ya rasa bata da hayaniya sannan bata fiya tashin hankali ba tana da kyau matuka saiday bata yi karatun boko mai zurfi ba,a hakan Ahmad hake mata matukar so da gaske,itama tana sonshi sosai kasancewar sa ba baya ba wajen kyau ga fuskar sa mai dauke da dimlple shi a kyakkyawa ne ajin farko, a haka aka yi auren ahmad da farida inda ya gina cancadeden gidansa mai matukar kyau dayday gwargwado,iyayan farida sunyi kokari sosai wajen zuba mata kayan daki da sauran abubuwan bukata , SOYAYYA rayuwa mai tsafta Ahmad da farida suke komai nasu abin gwanin ban sha'awa, a wannan halin ne Allah y azurta su da ribar aure inda farida ta samu ciki ,nan suka cigaba da rainon cikin har ya kai haihuwa ,sosia take jin karfi jikinta babu wata damuwa dan ita ko wannan kumburin da ake irin na masu ciki bata yi shi ba , rannan naƙuda ya tashi ƙanwar mahaifiyar ta Ahmad ya kira aka kwashe ta sai asibiti,tun wayewar safiya take naƙuda har bayan isha ,tun ana daukar abin na lpya har ya fara basu al'ajabi, karfe 2 da rabi na dare farida ta sunkuto ƙaton danta namiji tana haihuwa kuma jini ya ɓalle kamar an bude tafki , hankalin Likitoci ya tashi matuka ganin sunyi iya kokarin su wajen tsaida jinin dake fita amma hakan yaci tura , har karfe biyar na asuba ana abu daya , yaro day gashi an gyara anyi komai kuka kawai yake callarawa sabida yunwa amma babu abinci,karfe 6 na asuba farida tace ga garinku inda danta ya cigaba da callara ihun neman abinci.

     ''a hakan likitoci suka sanarwa Ahmad da kaninsa da yan uwanta muturwar ta , Ahmad kamar zai zauce wannan yaron kawai yake tuna wa kuka wannan gagara yi yayi sabida azabar da zuciyar shi ke mashi , daƙyar Musa ke lallashin sa shima duk zuciyar shi ta raunana , 

    ''haka likitoci suka bada gawar farida da ɗan ta da ta haifa wanda dole sai madara suka hada suka bashi , 

      Nan akawa Farisa wanka aka yi mata sutura aka sada ta da gidan ta na gaskiya , yaro kuma sai kuka kawai yayi a bashi madara yayi bacci ,da zaran Musa da Ahmad sunga yaro sai kuka domin tausayin shi fal cikin ransu ƙato aka haifeshi amma kafin sati yaro ya zabge ya rame , ranan bakwai din Farida shine ranan suna dan haka Ahmad ya rada wa yaron sunan mahaifin su Ibrahim ,anan take Musa yace yaya AHLAN za'a ringa gaya masa , cikin murmushin karfin hali Ahmad yace duk yadda kace hakan za'a yi Musa , a wajen yayar farida aka ijiye AHLAN ita take kula dashi.

      ''bayan shekaru 2 ne kuma Musa ya samu budurwa shima mai suna FAUZAH, fauzah yarinya ce mai ilimin addini mai hankali da tarbiyya fauzah yar gidan malamai ce gaba da baya domin su gidansu ma ba'a zurfafa ilimin boko ,sosia musa ke son FAUZAH itama haka, a wannan lokacin ne kuma shina Ahmad ya samu wata bazawara mai suna Rasheeda , Rasheeda bazawara ce da mijinta ya mutu sakamakon hadarin mota da yayi ya barta da yara 2 duka mata ,Maryam da zainab , Maryan shekarunta 4 zainab kuma sa'ar AHLAN ce shekarun ta 2 , sosai suka dayday ta kansu inda shi Ahmad yaji Rasheeda ta kwanta masa a zuciya babu wani kokonto.

      ''kasancewar da kudin su suna nema aure ko hada kayan lefe ba abu bane mai wahala ko mai tada hankali wajensu nan da nan aka fara shirya kayan biki ba ji ba gani ƙanwar mahaifiyar su da suke Uba daya ita ke taimaka masu mai suna umma talatu , 

     ''watarana Ahmad ya shirya tsaf yace Musa ya rakashi wajen Rasheeda domin su gaisa,babu musu ya shirya ya sha gaye yana ji da tashe kuruciya ya taje kansa ya gyara komai ya fesa turare sannan suka hau mashin din Ahmad sai gidansu Rasheeda,

     Bayan kamar minti 6 da zuwansu sai gata ta fito sanye da hijabi kanta a kasa tun daga nesa kamshin turaren su mabanbanta ke bugun kofar hancinta ta gane na Ahmad din amma dayan yafi kai mata ziyara ,ta ƙagu taga mamallakin wannan kamshi dan haka daga isowar ta ta daga kai don bawa idonta abinci 

      ''da Musa tayi tozali gaban ta ne yayi mummunan faduwa rass domin sosia yayi mata ,Musa yafi Ahmad kyau nesa ba kusa ba suna kama kam amma daga gayu zuwa iya ado zuwa KYAKKYAWAR fuska da kyan idanu Musa yafi Ahmad ,

     Duniyar tunanin da ta tafi ne yasaka Ahmad tafi domin shi bai gane mai take nufi ba , Musa da ya san dawar garin ne ya kara hade ransa sosai yasha mur da bayi so ma ta kawo asa wani wargi yanzu nan, lpya kuwa Rasheeda? cewar Ahmad uhmm lpya kalau Ahmad barkanku da zuwa ya hanya ?

     ''lpya ƙalau alhamdulillah mun same ki lpya? Amsawa tayi da lpya kalau sannan yace''

      ''musa KENAN kanina da nake baki labari abin soyuwa ta suka duniya daga shi sai kanwata abar so na Asma'u su kadai gareni su kuma zuciyata gaba daya duka AHLAN dafatan kinji dadin ganinsa?

     ''masha Allah kuwa naji daɗi Barka day musa ,cewar Rasheeda

     ''Yawwa Barka matar yaya dafatan kina lpya ? Lpya alhamdulillah ya kasuwa? Da lpya kawia ya amsa sannan yayi shiru.

     ''daga haka bai sake cewa komai ba sai gefe da ya matsa ya basu waje.

      ''suna hira da Ahmad tana satan kallon Musa domin ita fa har Allah Musa yayi mata wallahi dama shine ta hadu dashi ba Ahmad ba , kwata kwata Ahmad bai fahimci komai ba domin shi bai fiya saka ido cikin irin wannan al'amuran ba.

     ''kaf Musa ya gane inda ta dosa dan haka fa yasha mur''

     Bayan sun gama ba kuma suka wuce gidan su FAUZAH ko sallama Musa baiyyi da Rasheeda ba .

     ''anan Ahmad yaga tsantsan tarbiyya,dan tunda suka je har suka dawo fauzah bata daga ido ta kalli wani cikinsu ba, sosai ta burge shi sannan yayi wa kaninsa murna sosia da samun yarinya kamar fauzah.

      ''A bangaren Rasheeda kuwa gaskiyar magana Musa yayi mata ba wai bata son ahmad ba a'a tana sonshi amma Musa yafi burgeta,sai day zata nemi zabin Allah duk abinda ya zartar mata dashi to tana lale marhaban dashi.

     ''cikin watanni uku aka yi auren ahmad da Musa tare da amarensu Rasheeda da fauzah.

    Fauzah tafi Rasheeda komai nesa ba kusa ba ga kuruciya.

    Tunda Rasheeda ta ɗora ido kan fauzah taji babu dadi domin ta fita komai ga Musa yafi Ahmad kyau da iya wanka, taji haushi SOSAI amma kasancewar bata da yadda zatayi ta hakura haka bata nunawa ko a fuska ne kuwa.(Rasheeda irin matan nan ne masu kishi da hassada sosia babu dama ka fita da abu ko yaya sai taji haushin ka akwia irin wadannan mutanen masu wannan zuciyar haka Allah yake halitta su sai shaidan kuma ya shiga jiki da jijiyoyin su ya kara masu abin,Allah yasa mu dace.

    ''anyi biki lpya cikin kwanciyar hankali da natsuwa ,kowacce an kai ta gidanta anguwa mabanbanta aka kaisu , Asma'u tayi murna sosia a cewar ta yanzu ne zata samu wadanda zata ke shawara dasu matan yayunta  ƴaƴanta 2 yanzu haka mace da namiji , namijin yafi AHLAN sosia,macen kuma sa'ar AHLAN.

   ''bayan biki da wata 2 Rasheeda ta dauko yyan ta daga gidansu a wannan lokacin ne kuma shima Ahmad ya dauko AHLAN daga wajen yayar farida.

    ''bayan shekara daya kuma Rasheeda ta  haihu ƴa mace sosia Ahmad yayi murna inda ranan suna aka maida wa yarinya sunan mahaifiyar AHLAN wato farida.

   ''fauzah bata haihu ba har wannan lokacin sai bayan shekara 2 sannan ta samu ciki lokacin AHLAN yana da shekaru 6 a duniya ,sosia Musa yayi murna da duk wani mai son fauzah , Rasheeda ma tayi mata murna bakin cikin ta daya kar ta haifi namiji shine kawai damuwar ta ita kanta ta rasa dalili ,to ashe itama bata san tana da cikin ba ,haka ma Asma'u ƙanwar su Ahmad itama tana da ciki na 3 kenan.

    ''duka haka suka cigaba da rainon cikinsu har yakai watannin haihuwa Asma'u ita ta fara naƙuda ,da matsala yazo sosai dan haka mijinta ya kira su Ahmad waya nan da nan umma talatu suka tafi da wata kawar ta ,tun cikin dare aka kai Asma'u amma har washe gari tana naƙuda , karfe 2 na rana ta haihu , tana haihuwar dan Allah yayi mata cikawa shima minti 5 ya kara Allah ya dauke abinsa..✍️



*Dan Allah ina rokon duk wacce take karanta littafin nan da tayi Saving number ta sannan tayi min magana WhatsApp insha Allah zan gaya mata abinda zai biyo baya dan Allah ina rokon wannan Alfarmar plss sai na jiku....*



_07059305867_




*TALLA TALLA TALLA*


*LITTAFIN JANNAT LITTAFIN DA YAZO DA SABON SALO DA HARGAGI DA RUGUNTSUMI WACCE NI MRS ABDULL NA RUBUTA MAKU SHI WACCE BATA KARANTA BA TAYI MAZA TA GARZAYO DOMIN NEMA TA KARANTA KAN FARASHI NAIRA 200 KACAL DOMIN KUWA JANNAT RETURN YANA NAN ZUWA MAKU DA BAYAN SALLA INSHA ALLAH WANDA ZAU ZO MAKU DA WANI SABON SALON MAI RIKITARWA DA CHAKWAKIYA CIKIN SA WADDA SUKA KARANTA JANNAT SUN SANI KU TANBAYE SU KARON HAJIYA SADIYA DA HUDAY KU TANBAYE SU INA NUWAIRAH,KU TANBAYESU ALWASHIN DA TA BUGA KAFIN A KARKARE LABARIN TABBAS KUNSAN DA CHAKWAKIYA KUN SAURARE NI KU TARE NI CIKIN JANNAT RETURN DOMIN JIN YADDA ZATA KAYA MAI NEMAN JANNAT COMPLETE ZAI YI MAGANA TA WANNAN LAMBAR IDAN BA BIYA ZAKIYI BA PLS KI HAKURA SAI KIN SHIRYA👉*


_07059305867_


*MRS ABDULL ce ✍️*

No comments