MIN QALB 33
#Mamuh#*_MQ 33_*
Ahankali ta sulale zaune hawayen datake qoqarin maidawa suka gangaro,haka kawai zuciyarta kejin zafin Abinda yayi Mata din a yanxu
Aqalla koma menene tunda ba mutuwa akace Amatun tayi ba ya
kamata yayi Mata mgn kokuma ya karba Abinda take miqa Masa din,
Share hawayen tayi tareda ajiye cup ahankali ta miqe ta fice
tana qoqarin cire damuwar abin kwata kwata cikin ranta sbd idanma ta barshi
cikin ranta itace zata fi kowa wahala.
Bedroom dinta ta nufa tareda sanyo gyale ta dauko wayarta ta
fito tana latsa Kiran anty salamatu.
Cikin sanyin jiki da kulawa tace"
Anty salamatu menene yasamu Amatun?
Kuna Nan kokuwa anwuce asibitin?
Numfashin damuwa anty salamatu ta sauke cikin tsananin
damuwa tace"
Wlh haka kawai muka dinga Jin nishinta da salati Koda mukazo
harta some ga jini ba qaqqautawa sai zuba yakeyi gamu dai muna isowa asibiti
yanzu tareda MD da Dr salman.
Katse wayar tayi ahankali tareda sauke numfashi tana sake
bawa kanta qwarin gwiwa da hkr ta nufi sashen umme tana amsa Kiran mominta data
Kira tana Mata barkar dawowar mijinta lfy.
Tana shiga umme na fitowa da jaka a hannunta Nuratu na biye
da ita hankalinsu a matuqar tashe musamman umme dako lulluba gyalenta daidai
takasa tadai ratayosa a wuya ta gyara cikin mota idan tashiga.
Fadawa motar tayi itama tace zata bisu zuwa asibitin suka
wuce sbd zumudi ma Nuratu ce ta tuqa motar sbd bazasu jira shigowar driver ba
daga main gate tunda akwai tafiya daga gate din farkon zuwa ciki.
A mota umme ta kalli zarah datai sanyi tana cewa''
Zarah menene yafaru ne? ko bayan magriba dinnan nayi waya da
ita najita lafiya kalau har Ina godewa Allah danaji muryarta tafara sakewa da
walwala,
Shin da akwai matsala ne tuntuni daban saniba kokuwa yanxune
kawai abin yasameta?
Numfashin damuwa anty zarah ta sauke ta kalli ummen cikin
sanyi tace"
Lafiya kalau nabarta bayan magriba dinnan tadaice tanata
fama da ciwon Kai me tsanani sai jiri hakama gskia ta sauya sosai Dan saima ni
nakega kaman batada jini sbd yanda tayi fayau fayau,
Kallonta umme tajuyo tayi gaba daya zuciyarta na bugawa
daidai isowarsu asibitin suka fito suka nufi hanyar dakin dasukasan Dole
tanacan sbd asibitin mijintane aka kawota,
Cikin tsananin damuwa da firgici umme ta kalli anty zarah
bayan sun iso qofar dakin sun tarardasu salman a tsaye suna jira cikin rashin
sukuni
Tace"
Zarah meyasa baki fadamin dukka wannan ba sai yanxu?
Shin Bayan jiri da ciwon Kan metace Miki tanaji?
Dan jujjuyawa tayi ta kallesu ganin kowa ya juyo ya zuba
Mata ido Yana jiran amsarta Jin tamvayar da ummen tayi Mata MD ma dawowarsa
kenan daga amsa wayar Modibbo ya qaraso Yana kallon yanda sukai cirko cirko.
Cikin kulawa tace"
No Kan ne kawai da jiri take min complain to saina Bata
Ibuprofen maganin ciwon Kai........
What??????
Dr Fatima data fito dakin tafada cikin tsananin firgici tana
qarasowa tace"
Ibuprofen?
Wayace kibata Magana batareda taga likitaba ya rubuta Mata?
Shin kinsan maganin dakika batane yasata cikin wannan
hadarin gashi tana qoqarin rasa cikin dake jikinta......
Mene????umme tafada da tsananin qarfi tana zaro idanuwanta
Ta juyo gun zarah cikin kidima tace"
Meyesa Zaki Bata magani bakisan aikinsa ba?
Meyasama baki fadawa kowaba zaki dauki magani kawai kibata
zarah?
Innalillahi Dr Fatima meza'ayi yanzu Dan Allah kada kubari
cikin Nan ya zube Dan girman Allah ku taimakamin ku tsaida cikin Nan.
Nuratu da anty salamatu ma kusan duk acikin shock sukace Dr
Fatima Dan Allah ataimaka.
Salman ma cikin tsananin damuwar yace"
Maganin da hafsatu takawo Mata dazun shine Kika aiko Mata?
Dafe goshi yayi cikin damuwa yace"
Dakin Fara tambayana na duba kafin kibata tunda Ina Nan I
cud have checked.
Mutuwar tsaye zarah tayi tana rarraba idanuwanta a
tsakaninsu cikin tsananin firgici da tashin hankali kowa na jeho Mata tambayar
meyasa meyasa.,
Shin suna tunanin kaman da gangan tabata maganin ne? kokuwa
suna tunanin zata iya cutatar da Amatun be?
Cikin muryarsa data sanyata juyowa ahankali ta kallesa taji
ya fuskanci Dr Fatima cikin murya me nutsuwa yace"
Na menene ibuprofen din?
Na ciwon Kaine Amma irin strong din Nan kwata kwata masu
ciki basa shansa infact kamar abortion pills ne ga masu ciki marasa qarfin jini
ko kadan,
Gskia this is serious sbd gashi ta zubarda jini sosai har
jini ma Muna buqata gskia but yanxu dai we are trying our best mugan mun tsaida
jinin.
Kai tsaye yace"
Wat are the chances na cikin?
I can't say sir but just pray and have faith we will try all
the best we can Dan muma Muna son cikin
Sai Maganar jinin daza'a saka zamu Kira blood bank dinmu
mu....
No bana buqatan na blood bank din afara Shirin diban ledan
jinin kawai.
Kallon cikin idanuwansa zarah keyi tanason ya kalleta ta
karanci yanayinsa da yanda ya karbi zancen itace tabawa Amatun maganin Amma
yaqi kallontan saima qoqarin juyawa dayakeyi yaga Andi da kansa tareda Modibbo
a bayansu suna kallonsa cikin nustuwa,
Cikin alfahari dashi Modibbo ya jinjina Masa Kai yace"
Abinda kace shine daidai bama buqatan jinin wani gurin dabam
munada wainda zasu bada jini da dama...
Andi na kallon fuskarsa dake sunkuye Yana karantar yanayinsa
na kulawa da damuwa da yayi akan iyalin Dan uwansa Khalil alokacinda baya rayen
ya jinjinawa qoqarinsa cikin yabawa yace"
Bama buqatan jinin kowa acikin dangi ma tunda uban Dan
gashinan a tsaye bazai rasa jinin bayarwaba.
Office din Dr ashir suka nufa acan yasake musu bayani tareda
Basu tabbacin Inshallah komai zai daidaita kafin suka tafi.
Iyami da kawu ma tuni suka iso asibitin
Hankalin kowa nasake hargitsa musamman yanxu da kowa yaji
zancen da akwai ciki kowa yaji batareda dogon nazari ba saiyace meyasa zaa Bata
magani ba tambaya
Hakan yasa anty zarah komawa gefe ta zauna cikin yanayi na
tsananin damuwa da danasanin Bata maganin duk tasan cikin rashin sani tayi Amma
yanda firgici kesa kowa tambayar Yana sata muzantuwa duk da Suma ta musu uxuri
sbd tasan firgici ne da tsoron Abinda zai biyo baya.
Iyami ce tadawo gefenta ta zauna tana qoqarin danne
damuwarta ta kalleta tace"
Karki damu zarah ko zubewa cikin yayi qaddararsa ce,
Koni da agabana take kowane irin magani Zan iya Bata na
ciwon Kai tunda bamu sani ba.
Daga Mata Kai kawai zarah din tayi batareda ta iya ko magana
ba
Duk Wanda zaiga gangancin Abinda tayi bazata damuba mutum
biyu kawai takeson su fahimci niyyarta da rashin saninta,
Daga MAHMOUD sai Amatun
Amma sai zuciyarta na ganar mata zaiyi wuya MAHMOUD yayi
Mata kuskuren fahimta sbd yafi kowa sanin Abinda zata iya aikatawa musamman
akan Amatu da kowa ya shaida da zuciya daya take qaunarta.
Cikin ikon Allah ansamu anshawo Kan matsalar jinin ya tsayu
cikinma ya tsayu saidai Kam Babu dogon aiki ko motsin dazai iya taba lafiyar
cikin Dan haka hutu ne kawai akeso tayita yi jinin ma ansaka Mata roba daya
Kuma alhmdlh jikin bai wani Yi baiyiba tafarko har so biyu anty salamatu da
iyami na Bata tea sbd sune suka kwana anan.
Hankalin kowa ya kwanta musamman umme da tunda safe Takoma
asibitin kusan tareda zarah suka iso Dan motarsu atare tashigo harabar asibitin
Kuma kowanne da kayan breakfast ya iso.
Gaisawa sukayi suka Isa dakin tare alokacin anfito da ita
wanka kenan iyami nasaka Mata doguwar riga mara nauyi.
Gaisawa sukayi umme na zama kusada Amatun tana qarasa gyara
Mata Sanya rigar sai kaffa kaffa takeyi Wanda yasa Amatun kallonta tasaki
guntun murmushi tareda riqe hannunta tace"
Umme bafa fashewa zanyiba kiketa Yi kaman kwai.
Babu Wanda be bayyanarda murnarsaba a fili da Abinda tafada
sbd tun bayan rasuwar Khalil yau ne farko datai Abinda yake asalin dabiarta
wato yanko Magana ba taunawa.
Dariyar farin ciki umme tayi bayan tagama gyara Mata zaman
rigar ta zaunar da ita an jingina Mata pillow tace"
Ni ummen Kuma ake fadawa haka Amatu.
Murmushi tayi tace"
Umme ji nayi kamar kina min susa ne Yana sani waiwayi.
Kallon anty zarah tayi zatayi Magana saiga MD ZABEERA
yashigo atake imperial majesty yacika gurin da sanyin qamshi Wanda yasakata
lumshe ido sbd qamshin daya samu karbuwa daga yanayinta na ciki
Anty zarah ma lumshe ido tayi cikin yanayi na damuwa sbd
jiya baikoma gidan ba sai dare sosai yanzu da safe Kuma tana tashi tahowarta
asibiti tayi kawai sbd tayi tunanin Yana Nan din Ashe sai yanzu yake isowa
gashi haryanxu basuyi Magana ba tana buqatan Magana dashi taji nasa tunanin
akanta.
Ahankali ya qaraso ciki Yana gaidasu umme da iyami kafin ya
maida kallonsa kadan akan gadon Amatun wadda ta bude idanuwanta adaidai lokacin
sukai Ido cikin Ido
Da sauri kowannensu ya dauke idanuwansa shi Yana basarwa
itakuma tana Dan tsuke fuska.
Kasa hkr zarah tayi sbd tanason Jin bakinsu su biyun akan
alamarin ta juyo ta fuskancesa cikin tausasa harshe tace"
Ina kwana?
Kallonta yayi a natse ya amsa Yana qoqarin juyawa ya fice
tace"
Ba laifina bane Abinda yafaru jiyan inatason inyi bayani
Amma kamar kowa yakasa fahimtata.
Tsit dakin sukayi sbd Jin zancen nata musamman Amatu
datakejin zancen yanzu.
Umme ce tayi saurin kallon Amatu kafin ta maida kallonta Kan
zarah din tace"
Ba kasa fahimtarki akaiba zarah Amma ta Yaya Zaki yanke bata
Magani without any consulting?
Da idonki Kinga Abinda yafaru da ita akan hakan,
Bai kamata ki kasa fadawa kowa Abinda yake damuntaba tun
farko you should have told me ko Kuma MAHMOUD.
Cikowa idanuwanta sukai da hawaye bayan sunyi jajir ta dago
ta kalli MAHMOUD din daya juya baya din bai fita ba yanajin saukar maganganun
ummen har cikin ransa sbd idan har zarah tayi Dan kulawa ga Amatun bai kamata
suga laifinta ba saidai ba halinsa bane tsayawa hayaniya.
Kallonsa zarah tayi ahankali tace"
Kana tunanin hakan kaima?
Rintse idanuwansa yayi tareda juyowa ahankali ya kalli
Amatun da itama idanuwanta sukai jajir kafin ya kalli zarah din cikin radadin
Abinda zai fada yace"
U could have asked kafin kibata maganin tunda Salman na Nan
kokuma kifadawa ummen tun farko
This is irresponsible of you zarah...
Cikin bayyanarda tsananin damuwarta Amatu tace"
Me kukeyi wa anty zarah haka?
Kallonsa tayi Ido cikin Ido tace"
Kuna tunanin anty zarah zata iya cutatar Dani ne ko me? Ni
banganeba,
Nice nace anty zarah tabani magani idan tanada bayan haka
idan anty zarah tasan Ina tareda wani Abu atare Dani wlh bazata taba bani
Abinda zai cutatar daniba bama haka wlh na tabbata a duniya idan akwai meson
Abinda yake taredani bayan ni da mahaifinsa da Yana Raye to anty zarah ce idan
da ace tasani,
Meyasa zaku dasa ayar tambaya akanta Bayan dukkanin shedarta
yakamata ku bayar,
Umme kadaki zargi anty zarah akaina ko Abinda yake taredani
Dan Allah ko anan gabane hakan Yana karya zuciyar me hakuri wlh,
Zaku iya dasa Mata wani tunani na dabam Bayan ba haka takeba
kunfi kowa sani musamman Kai zatafi Jin zafi idan kayi Mata wannan
tunani""taqarasa fada tana dauke idanuwanta daga cikin nasa daya zuba
mata Yana kallonta da idanuwa a bude sbd akaro na farko ta tayasa fadar Abinda
yake cikin zuciyarsa sbd shine yafi kowa sanin zarah bazatayi ko kusan hakanba
Akan wani bare akan wannan silly yarinyar.
Numfashi ya sauke ahankali tareda kallon cikin idanuwan
Amatun kafin ya juyo ya kalli zarah da idanuwanta sukai jajir cikin kulawa da
taushin harshe yace"
Lets go.
Kallonsa tayi zuciyarta na narkewa,fushinta na wankewa sbd
yanda yayi ya nuna kulawarsa gareta tareda nuna damuwarsa akanta
Cikin sanyi tace meyasa nakesonka sosai hakane MAHMOUD
DAHEER ZABEERA?
Ahankali ta sauke idanuwanta daga kansa tana cewa''
Nakawo Mata breakfast inason zanbata da kaina.
Wani irin kallon are you kidding me?yayi Mata Yana mamakin halinta na rashin
Jin zafi.
Murmushi tasake cikin sanyi tareda daga Masa Kai
Ahankali yace ok tareda juyowa ya fice zuwa office din Dr
Fatima.
Qoqarin zuba Mata abinci umme tayi Amatun tayi saurin hanawa
tana kallon anty zarah cikin murmushi tace"
Umme antyna ce zata bani abinci da kanta Dan Allah.
Kallon zarah din umme tayi cikin Jin nauyi kadan duk da ita
Bata dauki maganarsu cin fuska ga zarah din ba sbd tun farko yakama kafin
kabawa wani magani kabari likita ya rubuta Masa Mana.
Iyami ce taqara dorawa da bawa zarah haquri tareda matsa
Mata ta matso Dan bawa Amatun Abinda takawo Mata.
Cikin farin ciki da cire damuwar Abinda ya wuce din ta
zubawa Amatun kunun gyada da plantain ta miqa Mata tana cewa''
Kici sosai sbd kisamu qarfin haihuwa idan lokaci yayi Dan
karki manta da alqawarin da kukaimin keda Dr khalil na cewa zaku bani Abinda zaku Haifa tun a
wancan cikin na iska.
Dariya kowa yayi a dakin Banda Amatu da kewar Dr da
tunaninsa ya dawo mata.
Yamma sosai aka sallameta Salman ya kalli su kawu da iyami
Bayan dukkaninsu sun fito harabar asibitin za'a tafi gida yace"
Kawu muje saina saukeku a gida su Kuma su tafi a motar umme
ga Kuma motar zarah MD ma Yana cikin asibitin Naga shigowarsa kafin ayi
sallamar inaga Yana tareda likitocin.
Kallon salman din kawu yayi kafin ya maida kallon gun umme
da Amatu yace"
Ai Amatu tafiya zanyi da ita tayi takabarta tareda renon
cikinta a gida sbd hankalin iyami rabuwa zaiyi da ni kaina....
Zaro idanuwa waje umme tayi hakama zarah dashi kansa Salman
din.
Cikin rawar murya umme tace"
Kawu kayi hakuri Amma bangane ainihin Abinda kake nufi ba.
Ina nufin tunda dai dama gida zata dawo ko Bayan takaba
gwara Takoma can din tayi zaman idan yaso bayan haihuwar sai asan nayi......
Bayansa dukkaninsu sukabi da kallo Babu me iya Magana sbd
girgizar zancensa
Ganin suna kallon bayansa yasashi juyawa sai sukai Ido biyu
da MAHMOUD dake tunkarosu cikin tafiyarsa me nutsuwa.
##Mamuh#

No comments