Breaking News

DUK NISAN JIFA 62

 


🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA

*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




                            62




Happy sallah yan uwa




Ya ce" Ai ba dole sai ta aikin gwomnati zai nemo ya ciyar da mu ba, shago nawa gareshi a kasuwa? Idanma bai iya ba ai sai ya koya, in dai aikin gwamnati zai ci gaba da yi sai na yi nazari a kan abinda yake tare da shi, domin kuwa  ni ban ga ci gaba ba a rayuwar da zata kai mutun ga halaka, sam bana son butulci da son kai, ni ba jahili bane ba zan lamunci hakan ba, ai ya tara ya je ya juya ko ya bari ya ringa gurgura idan ya kare sai mu dawo mu zauna du ruwansa aman abinnan da na ga shine yake basu damar jiji da kai, yake basu damar aikata abubuwa kansu tsaye ba tare da shaka, kunya , ko jin tsoron Allah ba na soke shi domin ni tunda na gane cewa ana mutuwa ana kwonciyar kabari, akoy ranar hisabi, na zubar da duniya!"



A hankali Hisham ya kuma yinkurawa zai tashi dan ya basu wuri, domin kwata kwata bai ga dalilin da zai zauna a irin wannan issu na famillu dinsu ba, wannan abu ne da ya dace daga su sai su, abu ne da iya su ya shafa , tabas yana auren yarsu aman ba hakan yake nufin ya zauna a yi irin wannan maganar a gabansa ba


A hankali tsoho ya kai  dubansa kan fuskarsa ya ce" Ka koma ka zauna, sarai na san abinda nake yi yaron nan, ka koma ka zauna ina yin haka a gabanka ne dan ka gane cewa ba duka dangin mayar da aka aura maka bane masu son zuciya duda wa'inda suka fi kusanci da ita ne suka zamanto haka, ka koma ka zauna domin so nake na fahintar da kai cewa ni kakan Aisha da ina cikin hayacina haka ta kasance sai na jinjina na san ku kuka hada kanku, kafin na kaiwa Allah zabi idan har alkhairin junna ne ku ya tabatar min, ka zauna yaron nan domin so nake kamar yadda ka fada aka barshi a wajensa ina so ka bi ta hanyar a sauke shi, ka sani ba tona sirrin iyalina nake dan na wulakanta su ba, aa , hasalima sun gama wulakanta kansu daga bakin lokacin da suka dauki abin duniya dawamame!"


Hisham ya koma ya zauna yana sada kansa, dan Allah yana gani sosai yake jin nauyin tsohon


Kiraye kirayen sallar magariba ne ta saka mahaifin Aisha kara risinawa yana neman afuwar mahaifinsa sanann ya yi bayi ya hado robar da yake masa alwallah da ita ya zo da buta dan ya masa, sai dai sam ya ki hakan ya umarce su da su je masalaci shi da Hisham din sannan ya saka Aisha ta dauki butar ta tara masa robar tana tsiyaya masa ruwan a hankali yana daura alwallar


Sai da ya gama ta taimaka masa sosai ya fuskanci gabas sannan itama ta daura ta dauki abin sallar dake ajiye ta shiga gabatar da sallarta


Tana gamawa tana shafa fatiha ta mike ta koma kusa da kakanta ta zauna wanda yake jan carbi idannuwansa a lumshe


A sanyaye ya ce" Kina son sa? "


Aisha ta dago da sauri ta kale shi, sai ta ga ita yake kallo hakan ya sa ta sada kanta cike da kunyar tambayar da ya yi mata


Murmushi ya dan saki a sanyaye ya ce" Tabas so halita ne jikata, sai dai ban so ba naki ya fi na mijinki karfi  ba dan komai ba sai dan irin yadda rayuwa ta zama yanzun,"


Ya nisa a hankali ya dora da fadin" Shin kina tare da maganar mahaifiyarki dan an maki abokiyar zama kan sai ya saketa ko a kori mahaifiyarsa daga wajen aiki?"


Da sauri ta girgiza kanta ta dago ta kama hannun kakanta muryarta na rawa ta ce" Papy, tun da na gansu tare na gansu, aman kamar yadda ka fada a waya MATAR MUTUN bata auren mijin da ba nata ba, Papy yayama zan kawowa raina raba Bilkisu da Likita?, na tabata mutuncina da yake gani zai daina, Papy .........." ta shiga shashekar kuka ta daga hannunsa ta kai wajen kirjinta ta ce" Nan dina sai ya ringa zafi yana ciwo yana damuna idan na tuna cewa mijin da aka aura min ba asalin sona yake yi ba, aa biyaya da kawaici ya saka yake zaune da ni, bai taba fada min magana ta kiyaya ko ya aikata aikin kiyayar da zai kara tabatar min da hakan ba, asalima ban taba gannin namiji mai dama irin tasa aman kuma yake da sasaukan hali irin nasa ba, Papy itama na girmeta sosai, ba zan ce ga ranar da ta fito dan na aure mata  mutumen da ta buda ido da soyayarsa ta min wulakanci ba, a irin wannan zamani daya daya ne ba zasu tafka wulakanci a kan haka ba, Papy na so kwarai a hada mana gida da ita ba dan komai ba sai dan na karra nuna masu ina son su, zan zauna da su da zuciya daya, papy ni bana cikin maganar saki, wani irin saki? Shin mama ta manta dan matar da nake aure na rike da igiyar aurwn yarta ne da kuma kujerar wajen aikin mijinta? Ni ban san ta yaya take da saurin mantuwa ba, sai ta yi tunanin ai ita ko dan ni an sasauta mata aman ita bata sasautawa mutun dan ni din ba? Papy idan tunaninta ta saka an saki yar wani ita tata yar ta fi karfin sakin ne? Ko a tunaninta kyauna, dirina kamar yadda take fadin ba namijin da ba zai soni ba su zasu saka a yi zaman aure da ni? Idan ta kula ai itama ba haka ba take, yau da gobe ta saka fatar jikinta ta ja baya, komai nata ya ja baya bale zaman yau da gobe? Papy........." sai ta fashe da kuka ta dora kanta a hannunsa tana yi sosai


A hankali ya ringa yin murmushi, murmushi ne yake na godiyar Allah da halin jikarsa bai zamo abin Allah wadarai ba, tabas ya godewa Allah da tunaninta bai zama cinkusashe ba


Dan haka ya dafa saman kanta duda hijab dinta ya tare a sanyaye ya ce" Ki je ki zauna da mijinki da kanwarki, raba maku gida ba wani abu bane idan yana da hali rabawar ita ta fi dacewa hakan zai saka du wace yake gidanta to fa ita ce sarauniya, matsalar raba gida daya ne kwal zumuncin y'aya ....shima idan har tsayaye ne hakan ba zai haifar da matsala ba, Aisha na ji dadi sosai sannan zan baki shawara, ki yi masa biyaya, ki kasance mai hakuri da kawar da kai a kan lamuransa, ki bi shi domin ya isa da ke, ki duka masa dan ya isa da ke, ki so yan uwansa domin Allah ki ki na ki domin Allah, ki tatali arzikinsa ki tatali lokacinsa, ki yi hakuri na tabata zaki kai ga ci, an sha yin auren da ba soyaya sai ki ga kuma hakuri ya sayi soyayar, an sha yin auren da soyaya ce jigon komai aman sai ki ga rashin biyaya da hakuri ya kashe soyayar nan an dawo ana gannin bakin junna, Nana ki rike tsafta, ta muhalinki da jikin ki, ki rike masa tsaftarsa, ki kula da abincinsa sannan ki kula da komai nasa, a haka zaki ci ribar zama da shi sosai kin ji?"


Aisha ta ringa sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin nutsuwa na shigarta, nasihar da ya dace uwa ta zauna ta yi mata ne kakanta ya yi mata kuma ta shigeta sannan ta dauka ta kuma yarda zata ci gaba da aiwatarwa dan samun nutsuwa a tare da mijin aurenta!


A office din HISHAM


Kallon mahaifiyar Aisha kawai yake kafin ya maida dubansa kan mahaifin Aisha


Magana ta ci gaba da fada kamar haka" Kar ka yi, kar ka yi kiran kowa, ka barshi zai huce, idan ba abin tsoho ba aikin nan da shi fa muka dogara mu dukanmu, ba sanadiyar aikin bane har ya samu aka masa aikin nan sannan har jikar tasa ta samu mijin wani? "


Mahaifin Aisha ya yi gyaran murya yana kallonta ya ce" Ashe baki da hankali? Tsalakowa zaki yi kan ubana ko me? Ke kin san bana hada maganar Papa da ta kowa a duniya!, da kike cewa a kyale shi mahaukaci ne shi? Ta yayama zaki ringa fadar magana marar tsari wai da aiki na dogara? Da Allah dai aiki menene banda matakin takawa mai hanya biyu wuta ko aljannah?, uban nawa kike cewa haka? Kin ga dai ina girmama naki iyayen har suka bar duniya, ki kiyayi maganar bakinki, tabas ina da son kudi da son mulki aman kuma ban yi bacewar da har zai yi umarni na take ba!"

No comments