Breaking News

MIJIN AMMINA NE SILA 65-66


 ✨MIJIN AMMI NA NE SILA✨

(A heart touching story)


written by Noor Eemaan

wattpad username @NoorEemaan



Juma'at Mubarak to you all my lovely fans, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke.😘



ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍


Page 65-66


_________________📖 "tabbas wanna shine mutumin dana kai wa takardan sammaci ba jimawa gidan sa, toh meya fito yi dashi, ga yanayin sa ya nuna bashi da gaskiya"  matashin ya fada a ransa yana kallon alhaji Shettima da ke cikin halin azaba, sam baya fahimtar kowa da komai.




Babur din sa ya bawa wani mai shago  ajiya kan cewa zuwa dare zai zo ya dauka, kana ya tari mai adaidaita sahu, suka kama Alhaji Shettima aka sa shi ciki dan sahun kana suka nufi asibiti....



 

Direct emergency aka kai shi, suka yi treating ciwon nasa, kana suka kai shi dakin hutu, matashin nan mai suna Mansur kuwa direct gidan alkalin da case din ke hannun shi ya nufa domin sanar da shi halin da ya tsinci alhaji Shettima, kana ya bashi jakar takardun da tsinta a tare da shi....




Jinjina kai alkhali yayi domin a matsayin sa na alkhali ya fahimci wasu abubuwan...take ya bada umarni aka zuba yan sanda ciki da wajen asibitin domin gadin alhaji Shettima, haka alhaji Shettima ya kai kwana ki goma sha biyar cikin asibiti wanda zuwa lokacin ya fara taka kafar tasa.

 police station aka kai shi sai da ya shafe kwanaki 5 Cikin cell wanda ba karamin azaba ya sha ba....




"RANAR SHARI'A"


Kotun cike yake da su, Abrar, Aaban, Hanan, Amal, Adam, Ammi, anty Raheenat, yaya Nadeem, mama, baba, (wanda yanzu ya ji sauki jikinsa) Mummy, Daddy.


Ta wata kofar a shigo da alhaji Shettima gaba daya ya sake fita hayyacinsa babu kyawun gani, tumbin sa yayi kasa alamun babu sauran jin dadi da Hutu, kansa na kasa kunya mai yawan gaske na saukar masa...


Nan mai gabatar wa ya karanto laifi Alhaji Shettima, domin su Aaban basu dauki lauya ba haka alhaji Shettima... Gyara zaman gilashin sa mai shari'a  yayi kana ya ce "alhaji Shettima ana tuhumar ka da yi wa Abrar diyar matar ka fyade, shin kana da ja ko ka aikata?"...



Shiru kotun ya dauka baka jin motsin komai sai sautin kukan Abrar dake tashi sosai, saboda tuno komai da ya faru, Aaban dake gefen ta ya kasa cewa komai saboda yanayi da yake ciki...


Sun dauki mintuna biyar kyakyyawan ba tare da alhaji Shettima ya ce komai ba, haka kawai yaji bakinsa ya kasa motsi, cire gilashin sa mai girma mai shari'a yayi, domin baro baro alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da alhaji Shettima, kallon shi yayi na yan mintuna  kana Cikin hikima ga shiga gaya masa illar zinah hadi da azaba mai tsanani da rabbul samawwati ya tanadar wa duk wanda ya aikata zina kasancewar mai shari'a na da ilimin addini mai zurfin gaske....


Abun mamaki jikin alhaji Shettima yayi wani sanyi kalau, sai yanzu nadama hadi da matsanancin kunyar gamuwan shi da Allah ya saukar masa...


Dago kansa yayi yayin da muryan sa na rawa gwanin tausayi yace " ya mai girma mai shari'a duk abinda kace, nina aikata su, da kaina nayi wa Abrar fyade, yarinyar da zan iya haifa a cikina, hakika na cutar da Abrar da ma Rahilat... Ya karasa yana zubewa kasa yayinda wasu zafaffan hawaye suka zubo masa gwanin tausayi, shi kanshi bazai iya tuna when last da yayi kuka a duniya ba....


"Alhamdulillah! A bisa rashin wahalar da kotu da baka yi ba, kotu ya yanke maka hukunci kisa ta hanyar jifa, har Allah ya karbi ranka, haka Allah ya yanke hukunci wa duk wanda ya aikata zina, alhalin yana da aure, don haka hukunci ka kenan, Allah zai yafe maka wanda laifi daka aikata na zina matukar aka jefa ka ta hanyar jifa, ko da a ranar tashin alkiyama, ubangiji bazai tuhumeka kan wanna laifin na zinah ba Allah ya tsare imanin mu" 



Kallon Abrar yayi yace " Abrar Sajeed Aaban, babu hukunci daya hau kanki kamar yadda yake a shari'a kasancewar ba da son ranki komai ya faru ba.


"Sannan zaka saki Rahilat kamar yadda ta bukuta, domin tana da hujojji masu karfi" mai shari'a ya fada


Kuka mai suna kuka dukkansu keyi banda Aaban da idanunsa suka yi jajur tamkar gauta, kukan Abrar din shi ya fi komai dakula masa lissafa gashi ya kasa hana ta kukan, domin ko magana ma bayason yi.


Haka mai shari'a ya buga guduma kana ya tashi, alhaji Shettima abin tausayi wani kuka mai sautin gaske yake har da majina, nadama mai tsananin yake ji, yanzu ina jin dadin ya kai shi? Ga abin da son zuciya ya janyo masa...



**************************************



Tsaye suka a inda za'a binne shi, gabaki dayan su idanunsu yayi luhu luhu saboda kukan da suka sha, yayinda gefe mutane ne tsaye masu yawan gaske da basa su lissafu ba, wanda sune zasu jifi alhaji Shettiman, gaban Ammi ya durkusa ya ce "Hajiyata!" Sai kuma ya fashe da kuka haka ma Ammi, goge majina yayi kana ya cigaba "ki yafemin ko na samu salama a kabarina ya fada yana nuni da ramin da aka yi domin shi... Hakika son zuciya bacin ta, ga abinda son zuciya na ya jawo min, kiyafemin dan Allah na tuba! na tuba!! na tuba!!! Hajiyata kice kin yafe min".


Kuka mai sauti Ammi ta saki yayinda ta yi kasa itama tace " Alhaji na yafe maka, duniya da lahira"....


"Nagode hajiyata, har duniya ta dane, ina sonki, a yau zan bar duniyar nan mai cike da rudu, amma ko a cikin kabarina ne ina so ki san cewa kina nan a raina" alhaji Shettima ya fada yana buga kirjinshi da karfi...



Majina ya sake ja a karo biyar kana ya cigaba " na yi miki Karya cewa  bana da iyaye, haka na taso ni kadai, toh ba gaskiya bane, ina da iyaye a kano rimin gado a kauyen atawa, na gudu na barsu ne sakamakon wani laifi tana aikata"


Cikin kuka Ammi ta zaro ido, domin bata taba tunanin haka ba, "wani laifi ka aikata?" Ta tambayeshi.


"Akwai wani saurayi mai suna Habu da  muka yi fada, dan mai garin kauyen mu ne, wanda na caka masa wuka a gefen cikinsa sakamakon musu da muka yi kan abinda bai taka kara ya karya ba amma, shaida ya ribace mu har ta kai mu ga fada... na dai barshi cikin matsanancin hali na gudo domin nasan idan aka kama ni hukunci mai tsananin zan karba, amma ban sani ba ko ya mutu ko yana raye, haka zalika ban sani ba ko iyayena na raye har yanzu... Ya fada cikin kuka sosai,,, Sannan ina sana'ar shigo da basara/giya wanda maganar da nake miki su kwaro ma'ana yaran aikina suna hannun hukuma...ya karasa cikin rawar murya sannan ya cigaba da cewa


 " Hajiyata, zaki iya zuwa kauyen mu ke nema min yafiya wurinsu iyayena,  da iyayen Habu da ma kan shi Habu'n idan yana raye ko hakan zai sa na samu kwanciyar hankali a gidana na gaskiya (kabarin)  sunan mahaifina malam Ahamadu, sunnan innah ta kuma juwariyya" ya karasa maganar cikin sigar tambaya


 Duk da dumbin mamaki daya cika ta bai hanata yin magana ba"Zan je, na yi maka alkawari Alhaji" inji Ammi cikin kuka sosai yayinda haushin da tsanar sa na barin zuciya da gangar jikin ta...


"Nagode hajiyata, you re love forever, ina son ki sosai, na sake ki saki biyu, Allah ya hada fuskokinmu da Alkhairi a darul salam" yana fadin haka ya nufi wajen Abrar dake sake tsaye gefen Aaban tana kuka sosai...


"Daddy's girl?" Ya kira Abrar kunya, nadama, mara amfani na saukar masa, I no bana da darajan daya cancanci ki yafe min, amma ina rokon ki dan darajan Allah da annabi s.a w ki yafe min ko na samu kwanciyar hankali a kushewa ta, nasan na cutar dake cuta mafi muni wanda hardly ki manta a rayuwar ki, amma ki taimaka ki yafe min" ya fada yana kokarin yin kasa....


Cikin kuka tace "Daddy!" Sai kuma ta sake rushewa da kuka, cak! Alhaji Shettima yayi, ya kasa durkusawa a kasa ya kuma kasa mikewa saboda zallan mamaki da yake ciki, bai yi tunanin zata sake kiran sa da sunan da bai cancance shi ba, amma har kagon zuciyar sa ya ji dadin sunan kwarai, 


Cikin nadama ya ce "da gaske daddy's girl, kin kira ni Daddy, am your Daddy? Are you sure what you just said came out from the innermost part of your heart" alhaji Shettima ya fada tana hawaye..


Jinjina kai tayi yayinda hawaye suka cigaba da zuba a fuskar ta, jin kanta take kamar zai fashe saboda wani mugun Sara mata da yake yi... Kana tace "na yafe maka duniya da lahira Allah yasa ka kwanta cikin sallama da kwanciyar hankali a kabarin ka...


"Allah ya miki albarka" yace hawaye masu zafin na zubo masa, yayinda yake jin wani nauyi na raguwa a zuciyar sa...


"Ka yafe min kai ma dan Allah, na  shiga gonar da ba tawa ba" ya fada yana kallon Aaban cikin kunya.


Matse hannun Abrar dake cikin nasa yayi kana ya daga masa kai kawai...


"Nagode" alhaji Shettima ya fad'a.


Kana ya kalli alkali yace "ya mai girma mai shari'a ku shaida na mallakawa Abrar dukkanin dukiyata duniya da lahira... na..."


"Nagode, amma bana bukatar duniyar ka, zan dai amsa na gina, asibitoci, gidan marayu, da sauran su duk wani aikin lada domin Allah ya kai ladan gareka" Abrar ta fada cikin kuka


Hawaye ya share kana ya ce "ba komai, nagode miki sosai, hakika hajiyata ta yi miki tarbiya mai kyau, ki dinga yi min addu'a kinji"...


Jinjina kai tayi saboda kukan ta da ya karu.


A hankali ya fara tafiya yana tunkarar ramin sa,  hawaye ke zuba kan fuskar sa, tsoro mai tsanani na lullube shi domin bai san a yadda zai fuskanci ubangijin sa da tarin munanan aiyukan sa ba...


Yana shiga ramin ya fashe da wani sabon kuka, kana ya shiga daga wa su Ammi hannu, hawaye hadi da murmushi da ya fi kuka ciwo na zubo masa 

" zan yi kewar ku sosai" yace yana cigaba da daga musu hannu kana mutanin da aka tanada suka fara jifan alhaji Shettima da dutse....


Sunan Allah hadi da istigifari dauke a bakinsa, rungume Aaban Abrar tayi domin ta kasa kallon alhaji Shettima, yayinda tsoron Allah mai tsananin na ratsa ta da ma dukkanin mutanen da ke tsaye a wajen, shima rungume ta yayi sai yanzu wani kwalla ya zubo masa, domin duk rashin imanin mutum dole ya ji tausayin alhaji Shettima, duk da a baya yana matukar kishi da alhaji Shettima sannan ya tsane shi, amma yanzu ya yafe masa...


Tun yana tsaye kan kafafun sa, har ya zube kasa saboda galabaitan da yayi yi... Daga karshe ya yi Kalmar shahada kana ya daina motsi, alamun ya amsa kiran ubangijin sa...


Wasu mutane ne suka zo suka rufe shi da kasa gaba daya, a hankali gaba dayan su suka isa ga kabarin nasa suna kuka, addu'a duk suka yi masa kana Daddy ya bawa masu gyara kabari kudi kan cewa su gyara ma'ana su yi siminti domin kada ruwan sama ko wani abu ya burma kabarin, har da wasu Karin mutanen100  da kabarinsu ya lalace sosai, ya biyawa domin a gyara, take mutanen suka fara aikinsu...


 (Ya jama'a mu kasance masu taimako musamman wa  marasa hali/kudi, wallahi idan kaje makabartu dole ka zub da kwalla, mutanen da dama kabarin su ya lalace, wanda basu da halin gyarawa, amma wasu na da arzikin biya domin a gyarawa yan uwa muslimai amma basa yi, masu arziki da wadata ku taimakawa mara sa shi, ta haka zamu cigaba da gina kyakyyawar al'ummah, hakika taimako abu ne mai kyawun gaske da baka san ta wace hanya Allah zai biya ka ba, Allah ya bamu ikon taimakawa juna).



Haka suka bar wajen jikin kowannen su a sanyaye tsoron Allah na ratsa su, yayinda hawaye yaki barin fuskar su, kwara ma mazan cikin su. Duniya kenan duk wanda ma ya dauke ta da zafi har ya sabawa Allah toh ba shakka karshen sa da kallo, mummy ke wanna tunanin...



*************************************


Kwana bakwai da mutuwar alhaji Shettima, Ammi ta je har kano tare da rakiyar yaya Nadeem da Anty Raheenat, basu sha wani wahala ba suka gano gidan. Gidane mai zagaye da langa langa, kallo daya zaka yi wa gidan kasan cewa masu gidan na fama da rashin babu... Wani dattijo da wata mata da zata kai 65 years zaune kan wata tsohuwar tabarma, duk da sun tsufa hakan bai hana su Ammi ganin tsananin kamanin su da alhaji Shettima mai rasuwa ba...


Bayan yan gaishe gaishe, babu Bata lokaci su Ammi suka yi masu bayanin komai a takaice, kuka sosai suka yi, domin basu yi tunanin cewa dan su Shettima na raye har yanzu ba, basu wani ja zancen ba suka yafe masa, duk da sun sha tsawgwama a kauyen lokacin da Shettima ya gudu... har gidan mai gari suka raka su Ammi inda ikon Allah Habu na raye bai mutu ba, nan ma suka ta ya Alhaji Shettima neman lafiya, suma basu ja da yawa ba suka yafe musamman da suka ji cewa ya rasu.....


Sakayau Ammi ki jinta ganin cewa ta sauke alkawarin da ta dauka, basu bar kauye ba sai da suka mayar wa malam Ahamdu gidan sa zuwa na siminti, kana aka shafe da fenti sosai gidan ya yi kyau gwanin sha'awa kana suka siya musu kayan abinci mai yawan gaske da zai dade musu, sai suka bawa malam Ahmadu kudi ya kara jari a sana'ar sa... Godiya hadi da albarka mara iyaka suka yi ta zabga wa su Ammi har suka bar kauyen......



**************************************


Sakamakon kukan da Abrar ke sha a yan kwana kin nan ya saukar mata da zazzabi, Aaban yayi yayi da ita ta sha magana ta ki, idan ya bata ma zubarwa take sai ta sha ruwa a zuwan ita lallai ta sha magani, dabara ce ta fado masa murmushi ya saki kana ya juya mata baya ya fara......



Idan kun ga mistakes kuyi hkr ban yi editing ba.




Share fisabilillah✔

Comment✔

Vote✔

Edit❌



Noor Eemaan ce

No comments