DUK NISAN JIFA 52
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*DUK NISAN JIFA*
_(K'asa zai dawo)_
🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾
*SAJIDA*
*SADAUKARWA*
*GA*
*MASOYA NA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
52
Tana gamawa ta wanke fuskarta da kyau tana jin yanzun zafin jikinta ya sauka hakama dandatsarta da yake yi
Fitowa ta yi cikin sanda tana dudubawa, gannin baya nan ta dauki lafayarta ta nada a jikinta ta zauna ta tankwashe kafafuwanta sosai ta gyara zamanta a hankalo ta fashe da kuka
Hisham na fita daga dakin jikinsa a mace ya karasa kusan Aisha dake zaune saman kujera
Zama ya yi kusa da ita sosai har jikinsa na gugan nata ya zuba mata ido yana kallonta
Murmushi ta sakar masa duka a kokarinta na son sai ta dane kishinta da abinda ke damun zuciyarta
A hankali ya lumshe idannuwansa ya saka hannayensa ya kamo nata yana kallonta, a sanyaye ya ce" Aish "
Aisha ta dago idannuwanta ta sauke a kan kyakyawar fuskarsa
Murmushi ta kuma sakar masa ta ce" Yau baka samu halartar sallar juma'a ba, kuma baka ci abinci ba har yanzu "
Hisham ya ja numfashi muryarsa a sanyaye ya ce" A lokacin da na fito da alwallah ina duba agogo na ga lokaci har ya zarta, Aish cikina kuwa bana jin yinwa "
Murmushin ta kuma yi masa ta gyada kanta ta ce" Ina kanwata ? "
Idannuwansa ya lumshe yana kara rike hannunta a hankali ya janyota jikinsa sosai ya rungumeta muryarsa cen ciki ya ce" Tana cen tana rigima "
Aisha ta yi yar daria domin a yadda ya fadan yana nunawa kamar wanda yake tsoronta ta dan dago tana kallonsa ta ce" To wani abin ka yi mata ne? "
Kansa ya girgiza a hankali ya ce" Wai cewa take an mata auren dole da hammanta ina hammanta ina ita? "
Murmushi ne ya subucema Aisha a hankali ta dago dubanta ta dora saman fuskarsa, hannunta ta saka a hankali tana shafa fuskar tasa ta ce" Ranta ne a bace "
"WANI abin akai mata da ranta zai baci? " ya fada yana rike hannunta a hankali ya kai wajen lebensa ya sumbuta, yana matukar jin yarinyar nan a ransa daga bakin lokacin da take taya shi kaunar Billy, walahi yana girmama irin yadda take dane damuwarta a gabansa, sarai ya san tana cikin damuwar shi yasa shima yake iya yinsa dan gannin bai tauyeta ba
Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Laifi aka yi mata mana, laifi mai girma ma kuwa, ranta a bace yake sosai, kuma ban ga laifinta ba domin mijinta miskili ne ya kasa furta mata kalmar so dan ta girma a gabansa, bai san da nesa da shi ta girma da sai ya ji tsoron ganninta a gabansa, Billynsa mace ce"
Murmushi ya yi, a kasan zuciyarsa yana furta 'Fadin ina sonta ne damuwarta? Bafa shine damuwarta ba, kai anyama ita ta wani damu da ace ana son nata? Gashi dai tana faman tsorata shi domin a da ya gama sakankancewa cewa tana jin an daura masu aure zata kama tsalen murna da farin ciki har sai ya tsawatar mata, aman yanzun sai wani zilewa take tana neman kwonce masa arzuzumi a kasuwa '
Tabararen kukan da Bilkisu ta saki ne ya saka su da sauri kallon kofar, sai kuma suka kalli junna
Da sauri ya nemi mikewa yana jin zuciyarsa na dokawa, ya kamo hannun Aisha a sanyaye ya ce" Dan Allah mu je ki yi mata magana "
Aisha ta shiga raraba ido tana son ce masa kai itafa Allah tsoron fitinar matarsa take aman kuma ina tuni ya jata ya yi gaba da ita hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya tana biye da shi
Dakin ya bude ya shiga tare da Aisha, turus suka yi sunna kallonta, irin zaman da ta yi da irin yadda take rusa kukan abin sai wanda ya gani
Karasawa Aisha ta yi tana fadin" Subahannalah Bilkisu yaya haka? "
Billy ta dago kanta tana kukan ta ce" Aunty Aisha gida nake so, a kaini gida aunty Aisha, walahi ba zan iya rintsawa a wajen nan ba, haba bana baku tausayi ne? Ku duba fa ku gani bani da lafia wa zai kula da ni? Bana iya yin shiru idan ina kukan rashin lafia , Aunty Aisha "
Aisha ta kara sasauta muryarta sosai ta ce" To aman Bilkisu ba gani ba kuma ga mijinki hammanki? "
Bilkisu ta kaleta, a hankali kuma ta saci kallonsa, ya wani hadu da garu ya jingina yana lumshe ido, ita walahi kwata kwata kwana biyun nan sai yake mata kama da wasu yan duniya, da sauri ta cire dubanta gannin kamarfa ita yake kallo ta dan turo bakinta ta rage muryarta sosai ta ce" Ba zaki daina hadani da mijinki a matsayin nawa ba ko?, ki fada masa ya maida ni gidanmu kusa da iyayena ban tashi tarewa da kaina ba gaskiya!"
Sai Aisha ta samu kanta da tunanin to meye a ciki? Dan ka tare d akanka me a ciki? Wannan zamani na warce warcen mazan mutane ba tarewa da kai ba da gata tare da mijinka ko kira ya yi ya ce zo ita bata ga wani damuwa a ciki ba, abinda ba adini ne ya ce a rufeki a kawoki ba? Idanma mijinki ya dauko ki ai a ganninta abin gadara ne, ita fa koda duka kaf jikinta kune ne Bilkisu ba zata samu nasarar saka mata tunanin bata son Hisham ba, ta riga da ta yi sake tun farko ta karanci sonsa da kishinsa a tatare da ita, shi yasa take baya baya tana kafa kafa da dukan wani motsinta a kusa da su, tabas mahaifiyarta ta fada mata cewar koma meye ta riga da ta sha gaban Bilkisu tunda har ta fara amsa kiran matarsa, kuma ta lura yana da adalcin da ba zai wulakantata ba dan tana matarsa ta hadi, aman ita sauraronta kawai take, ba abinda so baya saka namiji ko mace aikatawa, shi yasa take a supporting dinsa, walahi kokarinsa da kamanta adalcin da yake son yi a gareta na matukar kara daukaka girmansa a idannuwanta, ita ta san ba maganar so bace ta hada su, mutuntuka ce mai girma da daraja wace ta fi wani son anfani ainun
Zamansa a gefen Aisha ya sakata kallonsa tana kayse tunaninta
Muryarsa a sanyaye yana kallon Aisha ya ce" Ki ce mata ba adini bane sai an rakota, ki fada mata ta daina daga min hankali bana so dan Allah"
Aisha ta yi murmushi tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da sauri sauri wani irin abu ne ke son dunkulewa ya tsaye mata a kahon zuciya mai kama da nauyi da daci mai kama da mangari da fata, a hankali ya ci gaba da maimaita adu'o'in da takan lazumta dan samun saukin zogi irin na kishi ta dubeta ta ce" Kin ji abinda ogan ya fada? "
Bilkisu ta lumshe idannuwanta ta kuma gyara zama sai kawai suka ji kamar daga sama ta kuma rushewa da kuka harda dora hannayenta saman kanta tana fadin" Na shiga uku na lalace"
Abinda yake danewa ne yake son fin karfinsa, da sauri ya kamo hannunta yana kallinta ya ce" bandirawo, duka wannan din na kina ne?, Billy am duka wannan kukan na tsanata ne?, duka wannan din na rashin kaunata ne ? "
A tare suka dube shi ita da Aisha da sauri, gabanta ne ya buga ita din kanta dan a yannayin da yake tambayar kamar wani dan maraya sannan fuskarsa na nuna matsanancin tashin hankali
Bata kai ga bashi amsa ba ya mike da sauri ya juya ya yi waje, hakan ya saka su dukansu binsa da kallo mai kama da tsorata da yannayinsa
Da sauri Bilkisu ta mike tsaye ta yi taku biyu dan bin bayansa sai kuma ta ja ta tsaya cike da jin kunyar Aisha wace bata taba jinta ba sai yau, da kuma tausayinta
A hankali ta dawo ta zauna a gefenta ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya
Aisha ta kamo hannunta tana kallonta ta ce" A karro na barkatai zan kuma rokarki abinda na san kin san ba laifina bane Bilkisu, ki yafe min kin ji? Ina dora abin nan a kan kaina ne sai na ji da nice yaya zan dube ki?, walahi ba zan boye maki ba da wuya na iya dubanki , sai dai ina so ki ringa duba abu guda Bilkisu, kadarata da kasantuwata daya daga cikin matansa ya kawoni gidanku har haka ta kasance da mu baki daya, sannan na san cewa ko babu ke idan da rabon wasu su shigo zasu shigo, Bilkisu a duniya idan kina son hankalinki ya ki kwonciya ki auri mai kyau, ko me kike hankalinki na kansa , nutsiwarki na tare da shi, ke koda Allah ya yi shi ba mai kale kalen matan bane su zasu kale shi, balantana yawancin mazanmu sunna anfani da damar da Allah ya basu ta kyau ko kudi dan su tagayara yan mata masu karamin kwakwaluwa, Bilkisu idan bayanmuma akoy rabon wasu ina mai neman alfarmar da mu kwontar da hankalinmu mu hada kanmu, kin ganni nan alfarma rayuwa ta min, kuma zan iya rantse maki ina farin ciki da buda ido na ganni a wannan matsayin, ba dan kudinsa ba, ba dan kyansa ba, ko matsayinsa ba, aa Bilkisu dan nagartarsa, dan nasabarsa, dan iliminsa, da kyawawan halayensa, kin ga fa du irin yadda akai masa kutse bai dagani ya makani da kas ba, ni na san ya kuma san ba maganar so bace face mutuntawa da biyaya ga iyaye, Alfarmar mamanki nake ci wada ba zan taba mantawa da ita ba, na sha na duka ina kuka nace da ita ku ke son junnanku kar ta tirsasashi aikata wannan aiki duda tunda na ganshi na kamu da sonsa, aman sai ta min fada irin na uwar arziki wace zata yiwa y'ayanta, ta min kashedi da fadin cewa na fadawa Allah, iean har ni din nan matarsa ce Allah ya tabatar mana da alkhairi, Bilkisu ban san gidan boka ko malan ba hasalima ni din nan ban yarda da cewa wani na iya min abinda Allah bai min ba, Bilkisu ban tara kawaye ba domin kakana ne kawata ya shagwabani, ya sangartani, kuma ya bani tarbiya, Bilkisu Allah ne gatana ina tafe ne tsakanin wa'inda suka isa da ni masu madaukakin hali marar dadi a haka nake son su, nake yi masu biyaya nake iya yina idan na ga abin na kaucewa hanya ne, Bilkisu ni din nan na zama cikas a tsakaninku domin kishiya na nufin wace zata zauna a kamanta maku adalci wanda ko tagwaye ba zasu samu makamancinsa ba ci, sha, sutura, kulawa harta da kalamai......., zaku raba abubuwa mafi daraja a rayuwa, zai zamo koda cuta daya ke dauke da ita duka muna iya kamuwa da ita, muna iya raba abu mafi tsatseni na rayuwa, Bilkisu dole akoy ciwo akoy zafin a diro maka wajenka har a hannaka sakewa, Bilkisu ban ce da ke babu rayuwa na kishi yau da gobe ai sai Allah, aman abinda na sani tunda na ganki na ji ina kaunarki, duda tun a lokacin Allah ya saka maki kin son zama kusa da ni, Bilkisu ni ba zan cutar da kw ba, babar cutar da na makima ta isa itace ta aurar maki hammanki, aman bayan wannan ina so kalmar nan ta KISHIYA mu mayar da ita AMINIYA ni da ke, walahi zan zauna da ke da zuciya daya, ban ce ki fada min sirikanki ba, nima ba zan sanar da ke manyan sirikan da ni kadai suka shafa ba, aman zan zauna da ke ba munarfurci ko boye boyen abinda ya shafe mu, kin ga ki rufa min asiri sansanyar innuwar mijinmu ta zame min mafaka ba tare da kin rikita mana shi ba ya zame mana zaki a cikin gida, ki yarda ki yafe min Billy"
Bilkisu ta lumshe idannuwanta wannan karron hawayen gaske suka ziraro mata a gurbin idannuwanta, a hankali ta dora dayan hannunta saman na Aisha tana kallonta muryarta a sanyaye ta ce" Kin cika sanyi Aisha, sansanyan halayenki sun saka na ji ina kaunarki ni kaina mace bale namiji, Aisha sai da na fada maki ki yaki abinki tun a cen gida domin mijinki kika aura ki daina maganar kin aure mijin wani, Aisha ki daina laso lason nan dan kuwa kina iya cutar da kanki, kin ga yan matan yanzu kadan suke da kirki, yawamcinsu basu da kirki idan kina haka ta yaya kike so mu kama ya mu daka idan ta kale shi?, kin ga ki daina min maganar ko wasu bayan mu dan Allah yana ganni bana son kishiya, tabas na yarda da kika ce ke din nufi ne na Allah kuma na ji a raina na aminta da ke, Aisha nima ki yafe min abubuwan da suka ringa faruwa, sannan ina so ki sani Hammanmu koda a da baya son ki wannan halaya naki na iya siyan maki son a wajensa, ke bama shi ba kowama, Aisha walahi na ji ina manganrinki a raina, Allah ya banu irin zuciyarki........., aman dan Allah ina neman alfarma guda Aisha "
Aisha dake murmushi cike da farin cikin Bilkisun yau ta saurareta har take fada mata cewar Hisham zai sota ita? Ta yi saurin fadin" Ina jin ki "
Bilkisu ta yi dan murmushi ta ce" Ki je ki rarashe shi, idan ya sauko ku maida ni gida dan Allah "
Aisha na son ta tambayeta to a kan me zata koma gidan, amaj sai ta kyale ta dan gyada kai cike da tunanin ta inda zata fara rarashinsa a haka din nan da ya fita
Cike da fargaba ta fito ta yi dakinsa, wanda ta tabata cen ya shiga domin daki biyu nata biyu nasa a falon wanda kowa a dakunnansa akoy suturarsa
Tana shiga ta hango shi saman bed ya kwonta rub da ciki
Da sauri ta karasa kafin a hankali ta wara kafafuwanta ta haye ta bayansa ta dora bayanta a saman nasa ta lumshe idannuwanta
A hankali ya rike hannunta na hagu dake kusa da sajensa yana dan shafawa
A nitse ya juyo da ita gefensa yana kallonta, hakan ya saka itama take kallonsa
Sannu a hankali ta ji hannunsa cikin rigarta a hankali ta lumshe idannuwanta tana jin ya haye cen sama da hannun nasa ya dora saman kan mamanta ta kara lumshe idannuwanta har tana cije dan lebenta na kasa sakamakin aikin da ta ji likita ya fara gabatarwa a kan dan bululun kan mamanta mai duhu
A hankali take neman sidewa jin ya dage rigar nata cikin nutsuwa ya dora lalaisan harshensa mai dumi saman kan ta shiga dan zagayewa
Gaba daya ta kankame kansa da hannayenta biyu dan ta fara tunanin da gaya Likita ke son nuna mata cewar ya karanci abin nan harma ya san ta yadda zai iya sakata kwala ihu a irin wannan lokacin da take neman kanta
"HISHAM ka rufa min asiri Billy na kusa.... " ta fada muryarta na garwayewa da junna hakan ya saka shi dago dubansa a hankali yana kallonta, da sauri ta cire nata idannuwan a cikin nasa sakamakon irin yadda suka yi ja tana sauke ajiyar zuciya, tsoronta Allah tsoronta annabi kar ya ce zai zo mata a yanzu, walahi lamarinsa na firgita tunaninta sosai, abin ba mai mahaukacin girma bane aman girmansa ya isa ya hanna mata kyakyawar tafia a duk lokacin da ya ziyarceta domin sarafa mace mai sunnan sarafa mace Hisham kam ya gama karanta ya yiwa abin farin karatun da idan ya kai keyarki kas kin shiga uku, ke da kanki zaki nema ido rufe ki yi magiyar a sosa maki
A hankali yake sauke ajiyar zuciya ya kama hannunta ya kai kan abin da ya cika masa vaban jalabiya a hankali ya dan matsa yana kara rintse ido domin tunda ya kai kansa ga leben Billy abin ya haniniya ya farka ya shiga sukuwa yana harbin iska
A hankali ta kara dora lebenta kusa da kunnensa ta tausasa kalamanta ta ce" Tana son ka, tana son ka fiye da tunaninka"
Idannuwansa da suka yi nauyi da bacin rai ya bude yana kallonta muryarsa shake ya ce" Bata so na, ta gama kashe min rayuwata na gane burinta ta ga na fadi domin ba yau ba take kwontar ni a gadon asibiti"
Aisha ta kuma lumshe idannuwanta jin ya kara cafkar mamanta , a yanzu ta fara tsorata da kalar romance din, kamar wanda yake son huce haushinta ne ko menene?
Da wani irin tsoro ta kankame shi sakamakon jin tashi daya ya kwaye zaninta ya janye pant dinta kasa da wani irin karfi ya gyara kafafunta ya......mmnm
Um 😂 oh ni jikar Dan buzuwa me kuke son ji🤔, labule sak malamai

No comments