SARAN BOYE 33
No. 33
..........Koda suka isa can ɗinma wasu jerin motocinne
sukazo tarbarsu tare da bodyguard ɗin papa. Haka suka nufi gida zuciyar Yoohan
sam babu daɗi.
Sun sami tarba da ga ahalin nasu, musamman ma Yoohan da ya jima dama baya ƙasar. Shima yaji daɗin ganinsu sosai, musamman kakarsa data haifi Papa da ƙannen papan su uku mata da yaransu da ya gani sunzo musu, ga kuma kakarsa data haifi Mom itama dai bata komaba har yanzun.
Madam Chioma sai tattalinsa take kamar
ta haɗiyesa dan farin cikin ganinsa, gashi taga ya wani ƙara mata ƙyau da
kwarjini da cikar haiba kamar wanda akaima wankan iji.
Haka dai ya daure yana biye musu
sama-sama dan kamar ko yaushe fuskar dai babu walwala. Ƙasan ransa ma basusan
cike yake da tashin hankalin ganin yanda suka cika gidanba tamkar masu biki,
musamman da ya san baƙar ƴar tsamar dake tsakanin kakanninsa guda biyu. A yanzu
ma haka ya tabbata wannan zuwan na kakar tasu yanada nasaba da zaman mama
Deborah Abujan.
Da ƙyar ya iya zaman mintuna goma a
falon ya gudu sama a cewarsa zai watsa ruwa ya dawo. Yana shiga ya ja tsaki
tare da dafe kansa. Zama yay cikin kujerar dake ɗakin ya zaro wayarsa a aljihu,
sai faman yamutse fuska yake dan har yanzu ransa a ɓace yake akan dawowar dole
da papa ya sakashi yi. Wayar ya shiga sarrafawa cike da ƙwarewa. Kansa tsaye
yay kiran number baba malam dan yana buƙatar yin magana da shi. Cikin sa'a kuwa
bugu uku ya ɗaga.
Sai da suka gaisa
Yoohan yace, “Uncle mun iso gida, amma nifa gobe zan dawo kano”.
“Alhamdulillahi, barkanku da
hanya. Amma mizaisa ka dawo Yahya?”.
Fuska ya ɓata kamar yana gaban
baba malam ɗin, cikin nutsuwarsa da taurin kai irin na samari masu ji da
lokacinsu yace, “Uncle ina buƙatar neman sani akan addinin musulinci. Ta wannan
hanyarne kawai zan iya yaƙar duk wani ƙalubalen da nake hange da ga ƴan uwana.
Ta hanyar neman ilimin ne kuma kawai zan bautama UBANGIJINA. Ba tsoro nake duk
wanda ya sanni yasan na zama musulmi ba. Kawai ina buƙatar kwankwaɗar madarar
ilimine nima cikin kwanciyar hankali”.
Sosai baba malam yay murmushi har Yoohan
na jiyo sautinsa. “Yoohan karka damu kaji, bama sai ka dawoba, inason kabi
komai a hankali kamar yanda ka faɗa. Akwai ƙanina dake anan zaune abujan amma
yana nan basu koma bikin salla ba, dama na shirya masa magana kawai zaka ringa ɗaukar
karatu a wajensa tunda anan kafi zama fiye da nan kano, kaga zaifi maka sauƙi
ko kuwa?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi
alamar tunani, bawai hakan bai masa baneba. A'a tunaninsa shine yanayin
aikinsa, dan ya tabbatar a nan abujar ma ba samun zaman yake ba. Yanzu haka
kwanaki biyar kawai zaiyi ya wuce Lagos. daga can kuma zai shiga Maiduguri.
Yana da tabbacin kuma da wahala ya ƙulla wata guda bai sake barin ƙasarba
ma........
“Yahya ko akwai damuwa ne?”. Baba
malam ya katse masa tunaninsa.
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙewa ya taka
jiki a sanyaye zuwa bakin gadonsa ya sake zama. “Uncle babu komai. Kawai dai
ina duba yanayin aikina ne da baya barina zaman waje ɗaya, sai nake gani kamar
hakan zaiyi wahala a gareni. Inba dai ajiye aikin zanyiba kawai na fuskanci
karatun.....?”.
“A'a Yahya bazai yuwuba, duk da
bansan ya aikin naka yake ba bazan baka shawarar ajiye aikinka ba. Dan mu
musulinci addini ne dake son mutum mai neman na kanka. Ta hakane zaka kare
mutuncinka da tarbiyyarka, ka kuma nema halalinka harka tausayama na ƙasa da
kai da marayun ALLAH. Yahya karka manta kaifa bawan ALLAH ne mai yawan hidima,
sannan bayane goya marayu. Idan ka ajiye aiki yaya masu jira daga garekan zasu
kasance kuma?. Kaf Annabawan ALLAH tun daga farkonsu har zuwa MANZON ALLAH
tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi, tarihi ya nuna mana nauyin dake
kansu na yaɗa kalmar ALLAH baisa sun rayu a rashin neman na kansuba, balle ai
tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada
sana'oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman
halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke.
Murya a sanyaye yace, “Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba
shiyyasa”.
“Karka damu ALLAH yana tare da
mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jinƙai”.
“To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH
ya ƙara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ɗazu
kam hankalina a tashe yake sosai”.
Ƴar dariya baba malam yay masa sukai
sallama ran Yoohan fes. Da ƙarfin zuciyarsa kuwa ya miƙe ya fara zame kayansa
dan son watsa ruwa.
★★★
Tunda suka ajiye wayar
baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa.
hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa
soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata alaƙa ba a tsakaninsu
Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba
dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ƙyautata masa zato
akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Haɗuwarsu ta uku kenan kacal. Amma
ya fahimci wasu ƙyawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su
ba. Ga ƙyauttawa da yarda da yaron ke bashi ɗari bisa ɗari.
Numfashi ya ɗan sauke wani gefen zuciyarsa na
sake ƙarfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma
wata ke gargaɗarsa musamman akan ahalin da Yoohan ɗin ya fito.........
“Malam lafiya kuwa ka
zurfafa a tunani haka?”. Umm data shigo tun ɗazun tanata sallama bai jiba ta faɗa
tana mai katsesa.
Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da
kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba
ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya saƙala cikinnata yana ɗan sake
furzar da huci. “Jannat wani al'amarine yanzun nan UBANGIJI ya saƙaminshi a
cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma
wani sashi na zuciyar tawa yana gargaɗina dason jefani a kokwanto game da
al'amarin”.
“Tom nidai a nawa tunanin sai naga
kamar shaiɗanne Malam. mizai hana ka bama al'amarin wani ɗan lokaci haka, sai
ka duƙufa neman zaɓin ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa”.
“Eh tabbas kinzo da shawarar hankali
Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan
ALLAH”.
“Insha ALLAHU zan tayaka Abban
Nu'aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa”.
“Amin ya rabbil-alamin”. Ya faɗa cike
da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta”.
______________★★★
Kwanakin
Nu'aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai
haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing
mamory shine ya jefasu a cikin matuƙar damuwa.
Yayinda ita kuma da batasan mike
faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ɗauka
da zuwa gaba ɗaya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu
abinda ke sake haɗasu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi
da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.
Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka
mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu
damar yin tunani akan Naser ɗin. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na
tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata faɗa
bace tasan wannan ba ɗabi'ar mutanen gidansu baceba hakan. ‘To minene ya faru?’
ta faɗa a fili cikin sake zurfafa mamakinta.
Kusan mintuna ashirin sai kuma taji
hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma
idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ɗauketa
saboda a maganin nata akwai na barci daman.
Kiran sallar magriba ne ya saka
Umm shigowa ɗakin Nu'aymah ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata
yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yunƙurin fita zata
barta.....
“Umm wai hayaniyar mi naji anayi ɗazun?”.
Ta faɗa cikin katse hanzarin Umm dake ƙoƙarin fita.
Batare da Umm ta juyo ta kalleta
ba tace, “Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci”.
Sosai gaban Nu'aymah ya faɗi, sai dai
kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta riƙe
da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ɗin gida a
yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya
rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta
saka hijjab ɗinta ta kabbara salla kawai.
Koda ta idar bata fitaba tai
zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sanna ta fito
falonsu danta ɗansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare
da ɗora kanta a gefen kafaɗarta.
Ɗan kallonta tayi, kamar zatai magana
sai kuma ta fasa ta ɗaura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya
saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.
“Umm nafa warke”. Nu'aymah ta faɗa tana
murmushi dajin ƙaruwar ƙaunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin
tayi, ta shafa kumatun ɗiyar tata da faɗin, “Ai haka muke fata Nu'aymah, ALLAH
ya ƙara miki lafiya dai damu baki ɗaya”.
“Amin Umm”. Ta amsa mata zuciyarta cike
da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da
damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta
warke.........
Sallamar Adawiya ta katse tunanin
Nu'aymah. Ta ɗan ɗago daga kafaɗar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah
Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a
kansa.
Rungumeta Adawiya tayi cike da
munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu'aymah ta
tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin daɗi take dubansu. Yayinda Abdallah
kam kallonsu kawai yakeyi.
Bayan sun gaisa da Umm, Nu'aymah ta
gaida Abdallah batare data yarda sun haɗa ido ba duk da kuwa shi hakan yake
buƙata tun ɗazun. A tunaninta zasu tafi ne, amma sai taga sunyi zamansu sunata
hira da Umm. Kusan mintuna talatin basu da ko niyyar tafiyar, takaici ya cika
Nu'aymah, dan haka kawai yau itama sai takejin zafin Adawiya akan Abdallah.
Shiyyasa hirarma bata saka baki, tana lafe jikin Umm tamkar wata mage.
Basu bar sashen ba har sai da Baba
malam ya shigo gidan, dama shi suke jira. Zama kuwa yay suka gaisa a ransa yana
mai jin daɗin ganin yanda Adawiya ta kwantar da hankalinta. Yanda tai ƙiba ta
ƙara ƙyau kawai ya isa fahimtar da mai kallonta hankalinta a kwance yake sosai.
Barci ne ya sake kwashe Nu'aymah har suka bar sashen bata saniba. Koda Umm
datai tunanin anan Adawiya zata kwana amma taga saɓanin hakan sai da ta tashe
Nu'aymahr ma ta rakata ɗakinta saboda barcin da tayi.
Washe gari Nu'aymah ta tashi ne
duk a takure. Ba komai ya jawo hakanba sai zuwan su Yah Ab da zaman Naser a
gidan. Maƙalewa tayi a sashensu taƙi fita har rana. Sai da Umm ma ta takura
mata ɗaukar abincin Hajjo ta kai mata sannan ta fita badan taso ba.
Tunda taga takalma birjik a ƙofar
Hajjo taji kamar ta juya. Amma gudun kar Umm tai mata faɗa sai ta daure tayi
sallama. Sai da aka bata izinin shiga sannan ta shiga da wata sallamar a
bakinta. Duk samarin gidanne a she. Sai Rufaida da Hajjo. Nu'aymah ba wani
shiri sukeyi da Rufaidah ba itama, dan ta girmesu, gata kuma da shegen son
girman tsiya, shiyyasa take ganin sai dai su bita. Ita kuma Nu'aymah tsiwa.
A tare kawai tace dasu “Ina yinin ku”.
batabi takan dawa-dawa ya amsa ba ta nufi Hajjo daketa binta da kallon jin daɗin
ganin jikinta ya sake warwarewa.
“Hajjo barka da gida. Ga abinci inji Umm
na”.
“To takwara sannu kinji, yaya jikin
naki?”.
“Naji sauƙi Hajjo”.
“Alhmdllh ai haka akeso dama. Tun ɗazun nake
tsumayen ganinki amma shiru. Tashi ki duba a firiji na ajiye miki fura”.
Sosai daɗi ya kanata. Cike da ɗoki ta
nufi fridge ɗin hajjo ta ɗakko kofin furar tana sakema hajjo godiya. Har zata
fice Naser ya kirata. Badan tasoba ta amsa tare da juyowa tana kallonsa. Ya
sakar mata sassanyan murmushi tare da miƙewa ya nufo inda take tsaye. Bayare da
yay magana ba yay gaba da mata alamar ta biyoshi.
Bataso hakanba, amma sai ta bisa kawai
gudun kar yaga kamar ta masa wulaƙanci. Ɗaya daga rumfar bunun da aka jera guda
uku a harabar gidan ya nufa. Nu'aymah ma dai na biye da shi. Kujera ya ja mata
baya yace ta zauna. Nanma bata musaba tayi yanda yake buƙata. Sai da ta zauna
sannan shima yaja wata ya zauna.
Yana zama Abdallah na isowa wajen kamar
daga sama. Daga ita har Naser kallonsa sukai. Yayi kicin-kicin da fuska tamkar
zai fasa ihu. Batare da yace dasu uffanba yaja kujerar ɗanyan gefen Nu'aymahn
ya zauna suka sakata a tsakkiya.
‘Ikon ALLAH ’. Nu'aymah ta faɗa a
cikin ranta tana kallonsu da mamaki.
“Alhaji lafiya kuwa?”. Naser ya faɗa a
lalace yana kallon Abdallah. Murtani Yah Ab ya maida masa cike da dizgi. “Itace
ta kawo haka”.
“Humm!” Naser ya faɗa yana ɗauke kansa
daga garesa ya maida ga Nu'aymah da mamaki ke cigaba da nuƙurƙusarta a zuciya.
“Kayi haƙuri ka bamu waje magana
nakeson yi da ita Abdallah”.
“Wannan isar ce kuma baka yiba. Duk
abinda zaka faɗa mata inhar kasan ba mara ƙyau bane ka faɗa a gabana mana”.
“Mtsoww! Ai kasan baka isa sakani
yin abinda banyi niyya ba. Nu'aymah tashi muje can...”
Batayi niyyar binsaba a yanzu.
Tayi niyyar kawai tabar musu wajen. Sai dai tana yunƙurawa zata miƙe Abdallah
ya daka mata tsawa. “Koma ki zauna kona mareki!!”. Ya faɗa yana ɗaga hannun
tamkar zai maketa.
Ɓata fuska sosai tayi tamkar zata
fasa kuka. Dan ita kam sun sakata a tsaka mai wuya.
A fusace Naser yace, “Abdallah karka
bari nakai bango da kai, wai shin ina ruwanka dani ne? Naga dai Nu'aymahr nan
ba matarka bace balle kace zakama mutane iko. Idan ada kayi ikon saboda akwai
alƙawarin aure a tsakaninku yanzu saika tuna babu wannan. Ita ɗin allura ce
cikin ruwa mai rabo ka ɗauka........”
“Nine mai rabon kuma insha ALLAHU!!, dan
haka ka kama kanka karka bari a jimu da kai Naseer”.
“Hhhhhh! Abin dariya. Sannu
Abdallah ubana mai bani umarni. ai ka sani kayi sake tun a farkon dama, a yanzu
kuma ta suɓuce maka har avada. A da canma dan ba'a bata dama bane akaso mata
auren dole da kai, amma sai UBANGIJI yay dubeta ya hana hakan.....”
“Naser!!!”
Abdallah ya kirashi cikin ƙaraji da fusata tare da dunƙule
hannu tamkar zai kai masa naushi. Ƴar zabura baya Naser yayi kamar irin yaji
tsoro ɗin nan. Sai kuma ya kwashe da dariya ya kuma ɗaure fuska duk a lokaci ɗaya.
“Oh to ko dukan nawa zakayi ne?!”.
Bai gama rufe baki ba
kuwa Abdallah ya kai masa naushi. Da sauri Naser ya duƙe naushin yabi iska. Ya
sake kai masa wani Baba malam da ke bayansu shi dasu Abbah ya daka musu tsawa.
“Kai!! wane irin shashanci ne haka
kukema mutane a cikin gida da hankalinku?. Ko kunya bakujiba kuka zauna faɗa a
gaban ƙaramar ƙanwarku, wannan ai rashin hankaline da sakarci”.
Duk ƙasa sukai da
kawunansu kowa na huci. Abban su Adawiya yace, “Ku wuce muje ciki. Kema
Nu'aymah shige”.
Sum-sum ta wuce tana danne
dariyar dake cinta a rai tun fara rigimar yayun nata. Tana shiga falonsu kuwa
ta fashe da dariya. Da sauri Umm da Rabi dake a kitchen suna aiki duk suka
leƙo.
“K lafiyarki kuwa kike wannan dariyar ta
rashin hankali?”.
Hannu Nu'aymah tasa da sauri ta danne
bakinta, da ƙyar ta haɗiye dariyar tata sannan ta kalle su. “Wlhy Umm su Yah Ab
ne suka bani dariya”.
Batare da Umm ta tsaya jin ba'asi ba tai
tsaki ta koma kitchen. Rabi kam sai ta nufota tana tambayarta wai miya faru?.
Da sauri Nu'aymah ta haɗe fuska tare da zuba mata harara tabar wajen. Itama
Rabin da harara ta raka Nu'aymahn, a ranta kuwa faɗi take, ‘Zaki gane shayi
ruwa ne yarinya, shegiya mai kama da ƴaƴan aljanu’.
Oho Nu'aymah batasan tanai ba. Dan tuni
ta shige ɗakinta. Sai dai itama a ranta tana matuƙar mamakin munafunci irin na
Rabi. amma sam Umm ta kasa fahimtar akwai wani abu a zuciyar Rabi, dan ita ta
jima da fahimtar hakan, harma a ranta tana zargi Rabin da ɗaukar sirrin Umm
tana fitarwa. Dan akwai ranar data taɓa ganinta bayan ɗakinsu tare da wanda
bata fahimci namiji ne ko mace ba suna magana. Sai dai kafin ta zagaya taga
wanene ta iske sunbar wajen Rabin ma harta shigo ciki. Tun daga lokacin ta saka
mata kahon zuƙa. Taso fahimtar da Umm amma saita hauta da faɗa akan batason
wannan halin banzar, dan Rabi a haife ta haifi Nu'aymah harma wanda ya fita.
Kuma tun Nu'aymah na ƙarama suke tare ita bata taɓa ganin wani abu mara ƙyau
daga gareta ba.
Tsaki tayi kawai da kauda zancen Rabi a ranta
ta koma tuno su Abdallah. Haka kawai takejin al'amarin nasu na sakata nishaɗi.
Ba sai an faɗa ba kowa yasan tana tsananin son Abdallah, ƙaddara ce kawai ta
shiga tsakanin al'amarinsu. Amma a yau sai kawai yanda Naser yay sai shima ya
birgeta. Har takeji zata iya aurensa duk da zuciyarta bawai tana sonsa bane ba.
Amma tunda ta haƙura da Yah Ab zata iya maye gurbinsa da Naser ɗin. Sai dai fa
tasan lallai akwai ƙura a cikin faruwar hakan kuma.
★★★
A ɓangaren su Abdallah kuwa faɗa sosai
su Baba malam sukai musu akan abinda suka aikata. Dan a gabansu mafi yawan
rigimar ta faru shiyyasa basu bi takan jin yanda akai ba. Sai da baba malam ya
tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ya ɗora musu da nasiha kuma, ya kuma sakasu
bama juna haƙuri sannan suka sallamesu.
Suna fitowa kowanne ya wurgama ɗan
uwansa harara da jan tsaki.............✍

No comments