Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 48-49

 


*NUSAIBA*

         *'YAR AMANA*☘️☘️


Rubutawa Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)



*🌹 SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM*🌹



⚖️

*HAMDALA WRITIN'S ASSOCIATION💪*

        _*{{RUBUTU DOMIN CIGABAN AL'UMMA📚}}*_

https://www.facebook.com/111403834371046

          *✨✨{{H.W.A}}✨✨*



          *PAGE 48-49*


_____ Da gudu IKIRAM da Anti Amarya sukayi kan NUSAIBA suna girgizata cikin kuka Anti Amarya take cewa "baby dan Allah kitashi karki mutu dan Allah kitashi NUSAIBA bazan iya juran rasaki ba domin rasaki babbar illa ce agareni dan kuwa kinriga da kinzama wata 'bangare na jikina ina jinki ked'in tamkar 'yace ko kuma qanwa agareni"

Amma ina duk maganganu da Anti Amarya takeyi Itakam Nusaiba 'YAR AMANA baji takeyi ba, dan haka cikin kuka Anti Amarya tataso tadubi daddy tace " please daddyn yara dan Allah  kataimaki rayuwar yarinyar nan kartarasa ranta"

Cikin tsawa daddy yace " mekikeso inyi rahama nafa fad'a miki yarinyar nan matar aure ce da mijinta kuma mijinta shi yakawota gidan nan shin so kike narusa auran d'ana da ita sbd qaninki ko kuma me?"

"A'a daddyn yara ba haka nake nufiba amma wancan auran anyishine bisa wani dalili ba lalle bane ba insunason junansu dan Allah kaduba lamurinan da kyau"

Wani dogon tsaki daddy yaja "mmmmmtttttsss " sanan yafice yabar shashin Anti Amarya cikin 'bacin rai.


Itako IKIRAM dagudu tafita ashashin Anti Amarya shashin Mum tayi tashige dakinta wayarta ta d'auka tana kuka taitakiran Wayar ABUDULJABBAR tana ringing amma ba ad'aga ba dole IKIRAM ta haqura takoma shashin Anti Amarya  tasamu NUSAIBA hartafarfad'o domin tana fita Anti Amarya tazuba mata ruwa tafarfad'o tana qiran sunan JALALULDEEN.

Dubanta IKIRAM tayi tace " ki kwantar da hankalinki NUSAIBA JALALULDEEN bazai barki ba zai dawo gareki domin yana sonki kuma ayanzu nafahimci irin son da kikewa JALALULDEEN dolene yaya na yayi haquri yabar ki ki auri za'binki domin kuwa Manzon Allah ( S. A. W) yace Imanin dayanku bazai cikaba harsai yasowa dan uwansa Abunda yasowa kansa, sbd haka ki yi hakuri kidena kuka"

Anti Amarya ce tace " Shikenan IKIRAM NUSAIBA duk kukwantar da hankalinku guri daya kubani nan da kwana biyu zane momana mafita



*******        ********      *******


Koda dare yayi tsala wanka FINAH tayi tasaka wata fitinaniyar rigar bacci sai zabga uban qamshi takeyi, dama dawuri Mum tagama musu girki dan Mum ita kadai tashiga kitchen din ta girkawa danata abunda yafiso wato tuwon shinkafa miyar alaiyaho da busheshen kifi.

FINAH kuwa na zaune abakin gadonta taji ana qwanqwasa mata qofa tasan MUM ce dan haka sai tatashi taje tabud'e qofar, koda Mum tana mace sai da takawar dakai sbd irin shigar da FINAH tayi sanan Mum tace "Maza sako hijjabi muje nasan yanzu de yadawo koma ina yaje"

Komawa FINAH tayi badan ranta yaso ba tadauki qaramin hijjabi tasaka akan ta sanan suka fita a d'akin suka nufi bakin qofar dakin ABUDULJABBAR, Mum ce ta qwanqwasa qofar sanan tadubi FINAH tace "maza je kan dining nashirya masa abinci ki dauko ki yaudareshi yaci sosai kinji"

Zun'bura baki FINAH tayi tace " nifa Mum kinsan bawai nasaba da wahala bane fa" sanan tatafi tana bubuga qafafu.

Mum kuwa sai buga qofa takeyi amma shiru har FINAH ta dauko abincin tadawo dan haka MUM ta tura qofar kawai sai qofar tabud'e shiga sukayi FINAH ta ajiye tren hanunta akan qaramin table din dake tsakiyar dakin.

MUM kuwa cewa tayi " ki zauna abakin gadon ki jirashi maybe yashiga wankane bari ina zuwa zankawo miki wani tirare"

FINAH kuwa zama tayi abakin gadon harda ma kwanciya gashi maganin matan da tasha sai mintsininta yakeyi. 

Zuwa can sai ga Mum tashigo da wani fitinan turare ahanunta acikin kwalba tabawa FINAH tace " gashi ki shafa wanan aqasar mararki dan lokacin da muke dasawa da daddynku idan nashafa wanan turaren dimaucewa yakeyi"

Dariya FINAH tayi sanan tace "  dama Mum kuma manya kuna amfani da irin wanan kayan"?

Murmushi Mum tayi sanan tace " hmm FINAH kenan ai dama wanan kayan namune bana kubane"

Kar'ba FINAH tayi tashafa atake agurin har Mum zata fita sai kuma tadawo tace " ke ina Son haryanzu bai fito bane?"

"Eh Mum baifito ba"

Jikin qofar bayin MUM taje tabubuga amma taji shiru, dan haka sai tamurda qofar tabude wayam tagani bakowa aciki

Tashin hankali nanfa Mum da FINAH suka fara zagaye dakin suna qwalamasa qira amma shiru.

Kuka FINAH tasa tace " kingani ko Mum bayafa gidan nan qilama ya dade baya kwana gidan nan sbd qin da yakeyi min"

Kiyi shiru daughter bara na tambayo mai gadi ina zuwa"

Haka Mum tafita awanan daran tana qwala qiran sunan megadi aguje Baba megadi yataho yana cewa " lafiya hajiya?"

"Eh lafiya kaga shigowar ABUDULJABBAR gudanan ne"?

"A'a Hajiya ai tinsafe da yafita bai dawo ba"

"To Shikenan" sanan Mum tayi qwafa ta koma cikin parlour nan taga FINAH tana ta takaiwa da kawowa atsakiyar parlour din kallonta Mum tayi tace " My FINAH sai de haquri fa domin kuwa mijinki bai dawo gida ba har yanzu"

Sa hannu FINAH tayi aka tace " nashige su ni FINAH yanzu Mum ya zanyi gashi turaranan dana shafa sai mintsinina yakeyi"

Haquri zakiyi kije ki kwanta adakinsa maybe zuwa anjima yadawo"

Wucewa mum tayi taje tayi kwanciyarta domin bacci takeji.


Itako FINAH dakin ta tanufa dan yaukam tatabatar ABUDULJABBAR ba agidan yake kwana ba shi yasa baya nemanta dan haka maganganun qawarta Zuly yafado mata, inda take cewa " kije kika she kanki akan da namiju abanza yanzu haka shi yana can yana holewarsa ke kuma ki nanan kin hana kanki sukuni"

Dan haka FINAH taci kukanta ga magungunan matan da tasha sundameta dan haka tadauki Wayarta tasaka Number tsohon saurayinta dake kanta taqira wayar ringing biyu aka daga.

Cikin dashewar murya FINAH tace " my Prince kana ina nice FINAH"

Wani ihu akayi daga cikin wayar najin dadi sanan yace " my Sweet FINAH kwana dayawa inanan a hotel da 'yan matana ina goge zafin rashinki amma haryanzu zafin nanan"

"Shikenan my Prince yaukam zafin zai fice kajirani a hotel din ganinan zuwa"

Wani ihu yakuma yi sanan yace "ina jiran ki inan acikin hotel dina"




_________________________



ABUDULJABBAR kuwa bai tashi farkawa ba sai da gari hawaye yayi haske sanan yafarko da sunan ALLAH abakinsa d'aga kai yayi yakalli gurin wasu matasa yagani kewaye dashi majiya qarfi da mugayen makamai ahanunsu, cikin firgici ya tashi yace " ina matata NUSAIBA?

NUSAIBA!!!!!!!!!!!!!!!!! yafad'i sunan da qarfi sanan yace " karkici amana ta Nusaiba karkiyi soyayya da wanina inasonki Nusaiba"

Tafi akayi raff! raff!! raff!!!

Sanan akace da kyau d'an soyayya wato ka ajiyemin d'iyata tana wahala kaikuma kaje kana holewarka ko qaramin dan isa"

Abban FINAH ne yake fada yayin da suka shigo gurin shida muqarabansa wato Alhaji Biliyaminu da Alhaji Halliru

Abban FINAH ne ya zauna a gaban sa akan kujera yace   " kai qaramin qwaro wato baza kafita aharkarmu ba ko? to  munji komai domin kuwa muna da rahoton komai akanka tsawon shekaru har qaro ilimi da kayi aharkar binkice kuma yanzu ma kadawo ne da nufin kayi raf damu to munfi qarfinkq qaramin qwaro ne kai"

Alhaji Biliyaminu ne yace " abunda yasa muka kawoka nan ba komai bane illa wa'yanan kud'ad'e masu yawan gaske da za sufito daga hanun qwamnati mukeso muhau kai shine kai kuma ka baza duk wani tsaro akai tin baka qasar to kayi qarya yaro mudin kanason rayuwarka dole ne kacire hanunka akai inkuma kaqi kawar dakai zamuyi domin baka da wani amfani agaremu dan kuwa 'yar mu ma sbd makwad'ai tiyar uwarka take zaune dakai domin munada labarin komai da yake tafiya"


Cikin harzuqa ABUDULJABBAR yace " to sai me kuka sheni mana sai me ni dama kun hutar dani daga wanan rud'in takaicin zalincin da kuke yiwa talakawa ga kuma hadani da mahaifita da 'yarku keyi dan haka ni ratuwata bata da Sauran amfani kuka sheni kawai.


Dariya Alhaji Halliru yayi sanan yace " baza mukashe kaba amma zamuyi binkice akanka zamu rabaka da abunda yafi mahinmanci arayuwarka mudin baka cire hanunka akanmuba wanan shine last warning da zamuyi maka.

Abban FINAH ne ya bad'awa  ABUDULJABBAR powder afuskarsa tini ABUDULJABBAR ya fad'i agurin ya sume,  matasan dake gurine suka cici'beshi suka fita dashi agurin, cikin motar sa inda suka tareshi nan suka mayar dashi.



MUM kuwa koda gari yawaye tijara ta tayarwa Abba akan wai shi yahana ABUDULJABBAR kwana agidan sbd bayason aurensa da FINAH shide dad ko kulata baiyi ba tayi tijararta tagama tahaqura,  daddy kuwa kaf layukan ABUDULJABBAR yanema amma suna kashe, dan haka ya zauna yana jiran yaga ta ina ABUDULJABBAR d'in zai shigo domin kuwa ransa ya'baci sosai.


ABUDULJABBAR kuwa sai da rana tayi sosai zafin rana tabigeshi acikin motar sanan yafarko, yana bin inda yake da kallo komai da yafaru ne yadawo masa a qwaqwalwarsa wani murmushi da yafi kuka ciwo yayi sanan yace " tabbas bazan barku ba! Bazan bari kuci gaba da aikata 'barna aqasar nan ba kuna cutar wa'yanda basuji ba basu ganiba tabbas nayi alqawari ni qaramin qwaron da kuka rena sai nakawo qarshen zalincinku aqasarnan"

Sanan ya tashi motar sa  yayo gida yana shigowa gida yaci arba da daddy aharabar gidan parking din motarsa yayi a parking space sanan yafito yayo gurin daddy, daddy kuwa na kallon sa ya 'bata rai, qarasowa yayi ya duqa agaban daddy yace " Daddy barka da warka"

"You are very stupid Man"

Ashe dama kai mutumin banzane bansani ba? Ina kaje ka kwana kabar matanka to naji duk abunda kakeyi kuma nagani ni baza kamayar dani mutumin banza ba sbd haka ka kwashe dukka matanka agidan nan kukoma gidan ka daka gina"

"Amma daddy............ " banason musu ABUDULJABBAR sati daya nabaka domin nasan kana da kudi kagama duk wani shiri nan da kwana 5  kaji nafad'a maka ranar juma'a mai zuwa za'ayi walimar bikinka da Amaryar ka, itama IKIRAM da ita zanhad'a inyaso taqarasa karatunta agidan ta"

"Amma daddy dan Allah kasaurareni ina da uzuri hankalina ba akwance yake.........

"ABUDULJABBAR ashe dama ni mutumin banza ne agareka ? ina fad'a kana fad'a?"

"A'a daddy kayi haquri"

"Yade rage naka kaje kasamu Amaryar ka tananan ashashin Anti yara"

Fuuuuu daddy yafice a gidan yanufi massalaci.

ABUDULJABBAR kuwa daskarewa yayi agurin mamaki yakama shi wai Amaryar sa ashashin Anti yara to wata Amaryar tashi kenan, bade NUSAIBA ba 'YAR AMANAR Sa. 

Fuuuu yashige parlour din Mum yaci sa'a kuwa bakowa dan haka yawuce dakin IKIRAM, IKIRAM kuwa tana kallon sa ta tsorata da yanayinsa, jikinta narawa tamiqe tsaye tace "lafiya yaya?"

Cikin masifa yace " Ina AMANA ta dana barmiki yau shekaru hud'u kenan?"

"Yaya wata AMANA kuma"?

"You are very stupid IKIRAM"

Yarinyar danace ki kula da ita tamkar kanki ko kuma ni, tana ina?!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

Yayi maganar da qarfi.

"Cikin rawar murya da tsoro IKIRAM tace " ai ai itace ashashin.............


Hmm kude muje zuwa dan da akwai Sauran kallo

Comments dinku na kadanfa aha zakujini off fa inbanga ruwan comments ba dan last page da naturo banga wani ruwan comments ba


To ma wai FINAH me take shirin yine ni Mummyn MINAL shin da aurana ta zataje gun wani kome? Oh ni 'yasu fans kuban answer.


🤔😳


Dan Allah inkinkaranta ki tura asauran groups, kullum saina roqeku amma banga kuna turawa ba😭





*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*🤲

No comments