Breaking News

SAI A LAHIRA 40

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*



*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 40*



*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






..........Baby ta dubi siyama da ta rike Mata hannu sukayi kallon kuda Atare siyama nayiwa baby kallon gargadi da baby nayiwa siyama kallon wacece ke?


Siyama ta soma kada kanta "karki fara Wallahi anty baby Marin Nan shine karshen kuskure a Rayuwar ki

"Wai anty baby don Allah a me kike kallon kanki? Me yasa Kika zabi cin mutuncin mutumin Nan ne? Don yace Yana sonki? Ni inaga ko makiyi ne ai Bai cancanci wannan tozarcin ba tunda shi makiyin ma takalmin taka nasara ne bare wannan da yace so

"To ki fahimta Mana Baki lura aikin mutum baya sadar dashi da komai ba sai abinda ya aika? Duk Wanda Kika ga ya SHIGA wuta kudin sa yasaka ya shigeta  yayin da Rahamar Allah kawai ke Kai bawa ALJANNAH ba don ya Isa yayi abinda zai shigeta ba Ina fatan kin fahimta?


"To kisaka aranki yadda Kika barshi shima ya barki ba wurinki yanzo ba bare kiyi mishi tozarcin da Kika Saba, ta Yar far da hannu baby ta Isa wurin  Salim tana mishi sallama


Ya amsa Mata Yana murmushi "fita ma zakuyi ko? "Eh da gidan kunshi zamuje Amma ko gobe ne sai naje. Ta Miko mishi IV din daurin auren baby "Ina fatan banci fuskar ka ba idan na gayyace ka daurin auren anty baby? Ya karba Yana murmushi

"Haba ai cin fuska guda Zakiyi min shine ki gayyace Ni daurin auren ki da wani ba Ni ba. Amma na anty baby zanzo in Sha Allah Zan Kuma kawo gudunmawa ki Bata.....

"A a ban yarda ka takura kanka ba idan kayi Mata fatan alkhairi ma ya waratas 

Baby da taji wani bakin ciki na naushin zuciyar ta taja kafa ta wuce ta barsu 

Azahiri dai ba son Salim take ba tunda bashi da harka sai dai karfanfana sai dai wani Abu da ta kasa ganewa shine meye takeji azuciyar ta? 

Sai a yau tayiwa Salim kallon sosai inda ta hango kwarjini da haiba na kyau sai taji ta Kara Jin haushin siyama inda Kuma za a tambaye ta Akan wane dalili take Jin haushin siyama? To ita kanta ba zata ce gashi ba Amma Ni Kam gidan iko na San dalilin ba zai wuce soyayyar Salim ba don mace ko Bata sonka to tana kishin ka so watan ta  don haka baby kishi take Wanda kuma Bai Kai ko ga harara ba don Basu San me take ba.


Sun Dade kafin suyi sallama siyama tabi bayan baby gidan me kunshin inda tun daga Ranar baby ta ke daukewa siyama Kai sai dai siyaman Bata biye Mata  bare gabar tayi tasiri

Agefe Kuma baby na cikin takaicin abinda bashir yayi Mata inda take mamakin wace irin abotace da har yake girmama su fiye da ita 

Saura sati guda biki haj Azumi ta iso kaduna Wai akan idonta za ayi komai don kar Hime ta nuna Mata son iyawa

Siyama ta tarbeta "oyoyo lale marhabin da Azumin Ramadana tafada tana tarbo Azumin. Goggo tayi Mata sannu da zuwa ta amsa tana yamutsa fuska

Baby ta fito tana kallon Azumi

"To kin taho ki samu na tsegumin dorawa ko? To ko tari me karfi kikayi a biki na Zan tarkata ki in watsa can katsina.

Hajiya Azumi tace "to Bismillah marar kunya wannan da ace kusa muke da kinji jiki....

"Mu dai ji jiki don har dambe sai munyi don Ina iya Kada ke Wallahi...

Goggo tace Aiko da kinyi abin kunya 

"Wannan matar da kike gani goggo ganin ta dai dai yake da tauraruwa  me wutsiya wannan idan idanunta suka like an SHIGA UKU...

"To don ubanki zo ki like min idanun.


Azumi ta nufi gidan Khalil inda ta Dora wa matar shi Karan zuka komai tayi sai Azumi tayi magana koma tace Bata iya ba sai akayi sa a badariyya macece me hakurin gaske Amma duk da haka sai da ta kure hakurin ta sai dai da yake Khalil yasan halin uwar shi sai yake ta Bata hakuri akan da angama biki gida zata koma


Aka kawo kayan lefe Kaya na kece Raini harka irin ta girma wadda baby take so sai dai duk yawa da kayatuwar kayan lefen Bai sa baby tayi farin ciki ba don kawai matsala da take ganin bashir zai kawo Mata inda karara ya nuna Mata abokan shi sun fita matsayi da muhimmanci a gareshi

Humaira da su fauziyya nata tsegumin Rashin zuwan ango Wai an fado kasa Babu nauyi inda suka SHIGA satin biki aka fara gabatar da shirye shirye inda Kuma Babu ango Babu dalilin shi ko da yake ai Bai boye Mata ba da ta Kara rokon shi yazo ko kala guda ne sai ma ya tsinke wayar alamar ya gaji da maimaita magana guda

Hawaye ya biyo idonta inda take Jin wani Abu me kama da nadama na zagaye zuciyar ta.....

No comments