Breaking News

DUK NISAN JIFA 60

 


🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




                            60





Bilkisu na amsar wayar ta kara cen kasa ta yi salama


Najeeba ta saki murmushi ta ce" Lalema, sannunki Mairama, sannu fa "


Kunya ta saka Bilkisu kuma labe fuskarta kamar sunna gabanta tana ayana' Ni kam na shiga ukuna da mutanen nan'


A sanyaye ta ce" Barka da safia Gimbiya "


Najeeba ta kuma yin murmushi ta ce" Za'a kawo ki yau na kashe saloon dan gyaranki na samu amincewar mai martaba zan wuni a cen tare da ku "


Dan murmushi  ta saki a sanyaye ta ce" Allah ya kara girma aunty, na gode na gode "


Najeeba ta ce" Ba godiya, mu kin san irin karamcin da mijinki ya mana, ya mana karamci sosai "


Murmushi ta yi tana kara sine kanta cike da jin kunya


Tati na zaune a falo tana duba lokaci, a kadan ya dauki minti arba'in shigarsa dakin sai yanzu ya fito


Kamshin turaren da ya fara isowa ne ya sakata dagowa tana kallonsa


Allah yana gani sai ta ji kamar ta taka tsale dan farin ciki da mamakin yaron nata, wai wai wai Allah, Allah ya yi mata baiwa har haka tana cen tana shan rana kan dan abinda bai taka kara ya karya ba, wani lalausan farin yadi ne ya saka irin mai dabara dabaran nan mai shegen kyau, ba wani mahaukacin dinki akaiwa yadin ba, dinki ne simple riga daidai gwuiwa irin na zamani da wando daidai da shi , sai manchest masu shegen kyau na karfe bakake kirin sai bakar riga da ya saka a ciki sngil, sai bakin takalmi kafa ciki da bakar hula, aman ba karamin kyau ya yi ba haka kuma ba kananun kudi bane a jikinsa tun daga kayan har hular, takalmin da kuma agogon, Manchest din kansu zasu yi jarina (😌), ya hadu ya hade irin yadda hannayen rigar suka masa tim tim abin ba'a cewa komai


Ajiyar zuciya tati ta sauke cike da wani tsadaden farin cikin gannin irin yadda yanzun yake sakewa da ita hankali kwonce ya yi hira da ita ba wata damuwa , ko yanzun yana dosata ya ringa sakar mata murmushi wanda sai ta tsargu, kai yaron nan hala ji yake ita kakarsa ce?


Zama ya yi yana kallon abincin a hankali ya ce" Tati mamana zuba min take yi, ki zuba min nawa da na Billy am"


Tati ta hadiyi yawu ta juyo wajen abincin ta bude, a nutse ta zuba masa ta ajiye masa ta tura masa jus din da ruwa tana kallonsa ta ce" Ita ba shi ba zata ci, ka ci ka gama ka tafi"


Cokali ya saka ya fara dan tsakura yana yi yana kallon Tati ya ce" Wane zata ci? Bata ci wani abin kirki ba fa Tati "


Murmushi ta yi ta ce" Zata ck yanzun, mamanku ce ta ce na zo na dauketa mu je gidan Gimbiya za'ai mata kitso"


Galala ya yi da cokali a hannunsa ya ajiye yana kallonta ya ce" Sai da na ji raina zai kiya, wani irin a je a mata kitso bayan na kanta tati? Ina aka taba fita da amarya washe garin aurenta a zo nan a mata mana ko nawa ne zan biya"


Tati ta hadiye yawu tana tatara kalaman da zata yi anfa i da su dan ya yarda cikin sauki ta gyara zamanta ta ce" Ka gane, ka ga ba'ai mata gyara irin na amare ba, tana da bukatar a je a yi mata gyare gyare a mata kunshi a mata kitso, ka ga Gimbiya ba zata iya fitowa dan wannan ba koda kuwa tana so, mu kuma mu ke so dan haka zuwan ba zai haifar mana da matsala ba idan har muka samu gyaran nan ko kai ba zaka ganeta ba"


Ido ya tsurawa tati, shi kansa bai san lokacin da ya ce" Wai tati bayan yadda take din nan za'a kara gyarata? "


Sosai tati ta ji kunya, aman ganewar da ta yi shi din sai a hankali sai kawai ta gyada kanta tana kakauda kanta dan walahi yadda ka san sirikinta haka take jinsa


Wani murmushi ya yi yana komawa ya dauki cokalinsa ya ce" To bari na gama na kaiku "


Ai kam tati sai da ta ji daria na son kubce mata, lalle Hisham sai a barshi, hankali kwonce ya ji za'a gyara masa watau a yi?


Ita dai mikewa ta yi ta shige ciki wajen Bilkisu


Cike da wayewa ta sakata tashi ta cenza kayanta , katon hijab ta fitar mata sannan ta buda jakarta ta ciro nikaf da safa ta daura mata ta rikota ta ce" Babyna ki saki jikinki wannan kakame jikin bana so, kuma na san kina jin yinwa aman ki yi hakuri idan mun je sai ki ci dan ta ce kar ki ci komai wai"


Ita dai Bilkisu bata ce komai ba a hankali take biye sa Tati har suka fito fallo


Hisham ya tsura mata ido an lulubeta ruf sai idannuwanta kawai ake gani, sai ya ji ya gamsu da shigar tata har ya sakar masu murmushi


Abincin aka fitarwa masu gadi sannan suka shiga bayan motar ya nemo Kader ya zo ya shiga gaba ya tayar suka kama hanya


Shiru shiru kader bai ce komai ba ya saka Hisham jin ya damu, kallonsa ya yi da kulawa ya ce" Kai kuma lafia? Ko baka da lafia ne? "


Kader ya ya kale shi shekeke yana shan kwana ya kai hannunsa wajen bakinsa ya dan ciza ya ce" Han kak, Hisham futar rai ne nake ba bani da lafia ba, nace fitar rai ne nake !"


Tati ta ce" To fa, yau kuma me aka yi "


Hisham ya daga kafadunsa irin shi ya gano din nan


Kader ya dan waiwayo ya ce" Tati, wai muna zaune tare da mutumen nan ashe so yake na mutu? Kin ga jiya fa ashe ni fadan da na yi mata dan su gyara halinsu ita da kawayenta dan abokina na neman mutuwa a kan wannan ta kusankin nan ficiyaya da ita,  nan har ce masa na yi ya shiga rai bace ya mata muzurai ashe ni a shashasha yake daukana, yanzun du ba wannan ba da asuba fa ina kiranta bata dagawa karshe sai kawai nake jinta tana waya, na rikice athsmata na neman tashi na fada masa mu je ya ce aa in je, shine na je ina zuwa na tarar da mamanta a tsakar gida tana wanke kaushi Tati idona idon mamanta na rasa ina zan yi, wai Farida na fitowa da wata gajartarta uwa inuwar magi ce min ta yi ba na ce kar ta saki ta kirayeni ba? Yo dan Allah tati sha nawa zan fadi abinda bai dace a kulani ba? Shikenan ashe ita ta ji haushi kin ji jikina har yanzu zafi Farida cewa ta yi na fita a idannuwanta ta rufe ni Kadiri ni ni?"


Tati ta ce" Asha subahannalahi kai basu kyauta ba su duka, to aman dama kana da ciwon huka ne? "


Kader ya dan waiwayo zai bada amsa Hisham ya ce" Ka ga  a motar nan da Billy ce da inarta ka dauko, idan ka saba wasa da raina ka kula da rayukan nan  biyu  a kansu sai in yi wasan kura da kai, da farida, da danginta baki daya "


Kader ya yi wani shekeke yana kallonsa ya ce" Bari in ajiye su mu gama maganar, Tati zan zo mu zauna walahi a je gidansu tun kafin ta haukatani ina dalili ita ba wada ba ba mai tsayi ba garjeje da ni tana saka ni kwala, Allah dazu hawaye na ji zai zubo min na cije na daure na tsere kar ta ga kukana ta raina maza"


Tati daria na cinta balema da take jin Bilkisu na kilkila daria har tana dan rawar nan da daria ke sakawa ta cije dan tsakaninsa da Allah yake fada a dube shi


Harara ya wula ta madubi ya ce" Dama ina zaka zama matar maketaci kai ka rasa keta a jinninka? Ai abin dauka ake , Allah ya yaye maki kuma in kika fadawa wancen abin na yi kuka dan ta ce bata sona Allah sai na kaimu gegi mun wuni an rasa inda muke"


Hisham kam shiru ya masa yana kallon hanya har suka wuce wajen masu tsaron kofar saloon din gimbiya


Sai da suka dangana da kofar shagon sannan suka tsaya Tati ta fitar da ita ta sakata ciki ta dawo dan daukar jakarta ta ga Hisham tsaye jikin motar


A hankali ya kamo hannunta da jakar tata a hannunsa yana kallonta a sanyaye ya ce" *INA, NA GODE SOSAI, DAN ALLAH KAR KI YI NESA DA MU, KI ZAUNA DA MU*" 


Kamar a mafarki take gannin wannan lokacin, hakan ya sa ta kasa cewa komai sai wasu irin hawaye da suka shiga bin kumatunta ba kakautawa


Muryarta na rawa ta ce" Ka yafe min? "


Hisham ya kuma sakar mata murmushi a hankali ya ce" Na jima da yafe maki "


Wata ajiyar zuciya ta sauke tana kara rike hannayensa ta ce" Na gode, sosai Hisham na gode "


Hishamma ya ringa mata murmushi yana jin wata madaukakiyar kaunarta a cikin zuciyarsa a hankali ya ce" Ki yi tunani a kan mahaifina Ina, kasancewarki a inuwar aure shine cikar kamalarki, zan samu kwonciyar hankali ne idan na ga iyayena na karkashin inuwar aure "


Wannan karron gaba daya ya gama dadaureta da igiyoyin jikinta, a hankali ta kara rike hannunsa a sanyaye ta kuma fadin" Jazakallah "


Hannayenta dake cikin nasa hade da jakarta ya hada a hankali ya sada lebensa da goshinta cikin nutsuwa ya mana mata kisss sannan ya dan matsa yana mata murmushi kafin ya daga mata hannu a hankali ya ce" Sai na dawo daukan ku "


Rasa me zata iya fadi dan tsananin murna ta yi, sai kawai ta bi shi da kallo har suka ja motarsu suka yi gaba


Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta zauna saman kujerar dake wajen na zaman baki ta tsurawa waje daya ido, ashe aurensu da ta jinkirta ta nuna ba za'a yi ba shine sanadiyar kusantuwarta da yaronta?, lale Bilkisu alkhairi ce a rayuwarsu


Ajiyar zuciya ta kuma saukewa ta mike ta yi ciki wajen Billyn

No comments