SARAN BOYE 30
No. 30
................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin
hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi
yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake
zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu.
Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun
safe fuskarka sai annuri takeyi”.
Da ga Umm har baba malam dariya sukayi,
ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin
farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na
shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda
kike so”.
Sosai farin ciki ya sake
kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har
Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga
Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai
saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu
game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen
cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a
kowane daƙiƙa.
Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta
dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin.
“Nikam naga takaina da wannan hali naki
Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki
zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata
guri?”.
Baki ta tura gaba tana ɓata
fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun
ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zanc........”
Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne
ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata
a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan
maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki
bar tsiwa da rashin kunya? Itaɗin sa'arki ce?”.
“Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba
ALLAH ”.
“Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm
ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta
juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen
ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki
ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko”.
Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi
hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan
zuciyar gadon tazo mata wuya.
Duk yanda Umm tace tayi haka
tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane
Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta
shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana
lafiya sai sunyi faɗa.
Manshanun ta ɗauka zuwa sashen
Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata
damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da
ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata
harara.
Jitai kamar ta juya dan haushi,
amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen
Addah?”.
Banza tai mata tamkar bata jitaba, har
Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu
hannunta ɗauke da Al-qur'ani.
“A'a Aymah ce a wajen namu?”.
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta
da ɗan damuwa tace, “Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina
tambayar Aunty Kubrah tamin banz.....”
Kafin ta ƙarasa
taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana
ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko?”.
“Kai haba Aunty Kubrah daga
tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan
to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun
Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai
masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani.
Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki
rama mata ne?”.
“Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka
mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn
na ɗakinta kinji ko”.
Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana
share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin
yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu
wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata
banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah
na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy,
inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan”.
Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa,
dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata
ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata.
Da mamaki Hajarah ta kalli
Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki
da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?”.
“Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn
ta faɗa a harzuƙe.
“ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa
tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata
da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.
Sai da Nu'aymah tai sallama Addah
ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin
salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar
fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
“Babu komai Addah, Umm ce tace na
kawo miki wannan”.
Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba,
dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun
ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
“Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar
mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake
shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
“Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan
rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan
dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar
asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna
faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima
Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a
cikinsu”.
Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka
fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
“Kubrah!!”. Addah ta ƙwala
mata kira ganin bata a falon.
Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke
da plate ɗin abinci.
“Ubanmi Nu'aymah tai miki kika
daketa?!”.
Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta
kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin
mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
“Ni na faɗa ba ita ta faɗaba,
tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
“Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban
daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
“To amma shine zaki ce mata ƴar iska,
kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban
kowa”.
“Wlhy Hajarah zan sauya miki
kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.
“Kai!! Ya isheni haka,
banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin
kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani
daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wlhy sainayi ƙololuwar ɓatama
mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ƙasa Nu'aymah ce kuma
ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa
makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na faɗa miki”. Ta ƙare maganar
da matuƙar zafin rai tana sake yima Kubrah gargaɗi da hannu.
Sai kuma ta juya ga Nu'aymah dake sauke ajiyar
zuciya a jajjere. “Nu'aymah jeki wanke fuskarki kinji kuma kar naji
wannan maganar a wani waje, kiyi haƙuri”.
Kai Nu'aymah ta jinjinama Addah, babu
musu ta shiga toilet ɗin dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai
musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga
ALLAH hankalinta a tashe yake matuƙa da kalaman Kubrah.
Koda ta koma
sashensu ɗakinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu'aymah yarinyace da bata da
tsoro sam. Amma yanda tai matuƙar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa
barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha
banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi
ALLAH wadai da ita, ƙilama baba Malam da Umm su tsine mata albarka.
Sake rushewa tai da kuka kamar zata shiɗe
wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ƙwala mata kira. Da sauri ta
miƙe ta shiga share hawayen, harta nufi ƙofar fita sai kuma tai saurin dawowa.
Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli
sannan ta fita.
Zaune ta iske baba malam
da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk
kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, “Lafiya kuwa? Naga idonki kamar
wadda tai kuka? Mamana!”.
Kafin tayi magana Umm dake hararta tace,
“Saboda namata faɗa akan rashin kunyar data iya”. (dan ita tazata faɗan datai
matane ya sakata fushi har yanzun).
Baba malam baice komaiba sai maida
kansa da yay ga tv kawai. Fuska a ɗaure Umm ta nuna mata trayn dake a kan
centre table. “Ki ɗauka ki kaima baƙo a falon baba”.
Kai kawai ta jinjina mata ta koma ɗakinta
ta ɗakko hijjab. Batare datai maganaba ta ɗauka tiren ta fice. Sai da ta fice
gaba ɗaya sannan baba malam ya ɗauke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm
da itama take kallon nata.
“Addu'a ya kamata ki cigaba da
mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu'aymah yariyace
ƙarama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata buƙatar yawan takura.
Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ƙuruciyar”.
“Amma Malam ka tunafa ƴa mace ce
ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ƙaddara daba yanzu tana ɗakin miji ba. Wlhy
sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba
nikam”.
Murmushi baba malam yayi yana miƙewa,
“To ayi haƙuri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya
huci zuciyarki”.
Yanda yay maganarne ya saka Umm
yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nishaɗi sosai
kam, musamman data san yafi kowa ƙin jinin tsiwar ɗiyar tasu.
★★★★★★
Murya a
sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya
sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da
ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene.
A gabansa ta dangwarar da trayn, murya
a cinkushe batare data kallesa ba tace, “Ina yini”.
Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani
sabon takaicin ya sake lulluɓe ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa
takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata faɗa harda duka akan tsiwa,
sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene
baƙon nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin
yayunta. Haɗiye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon.
Yoohan da tun shigowarta
idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ɗan ɗago kansa dan
sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani
yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ƙaramar jakkar dake gefensa
da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yay saurin saka mata ƙafa dan
son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare.
Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen
ƙamshin turarensa na nan manne da shi. Shaƙa ɗaya Nu'aymah tayi tai azamar ɗagowa
cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
Idanunsu ne ya shige cikin na
juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai
ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan
hannunsa yay ya rufe mata bakin ruf yau ma, tare da sake manneta a jikinsa
sosai shima a cikin ɗan firgice.
Wani irin mugun bugawa ƙirjinta
ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko
akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka.
“Oh my God! Just relax.
Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.
Cikin rawar jiki hawaye na zirara
ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma
zata kifa yay azamar riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
“Wayyo Abbana ɗan isk.........” ta wage
baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da
manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.
“Wa'iyazubillah!! Iskancin naku
da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?” Kubrah data shigo falon tamkar
an jehota ta faɗa hannu bisa kai tana mai waro idanu waje..
Tashin hankali, tsabar ruɗewa
Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar
hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa.
Saurin sakinta yay yana faɗin
“Ouch!!!” dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ɗoura hannun nasa bisa cikin ya
riƙe yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.
Nu'aymah dake ja da baya tana
hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, “Ɗan iska kawai,
ALLAH ya isa ban yafeba. Wlhy daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai
na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ƙosai, na tsane ka
wl........”
“Hhhhhhh! K! Ƴar iska bar wani
pretending kinji!”. Kubrah ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin falon sosai.
Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai
fita tace, “Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wlhy tallahi kinji na
rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa y.....”
“K dalla saurara mani!
Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna
tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH,
inhar kika sake faɗin tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke
ciki”.
Ƙasa Nu'aymah ta durƙushe tana ƙara
sakin kuka maiban tausayi. Yayin da Yoohan da sam bai fahimci mi Kubrah ke faɗa
ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu.
Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani
shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Muƙut ta haɗiye
maganar tata ƙirjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin suɓutar baki ta
firta ‘Tsarki ya tabbata ga ALLAH’.
Sake ɗaure fuska Yoohan
yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin
wanda Kubrah ke masa na ƙurulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take faɗaba
ne ɗazun, sai dai ya fahimci ba magana mai daɗi takema Nu'aymah ba. Dan haka ya
watsa mata wani mugun kallon da manyan idanunsa yana miƙewa.
Ganin ya nufita ya sata saurin zabura
tai baya, sai dai kuma a mamakinta yama ɗauke kai daga gareta gaba ɗaya, raɓata
yay ya nufi Nu'aymah dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin datasan
a yau babu makawa sai Kubrah ta tona mata asiri.
Handkherchief ya ciro a
aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “Hello!”.
A razane Nu'aymah da batasan da isowar
tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Ta waro idanu waje sosai da saurin
duban inda Kubrah ke tsaye tana kallonsu kamar ta samu television.
Kamo hannunta yay, da sauri ta
dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle
tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin......”
Yatsansa ɗaya ya ɗaura
akan baki. “Shiiii!!!” ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.
Ruf. Tai saurin rufe bakin
kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga
gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yay
mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin
hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar
murya yace, “Silly girl”.
Baya taja jikinta, dai-dai da
sakar mata hannu da yayi ya miƙe shima. Batare da ya kalli ko inda Kubrah take
ba ya ɗauka jikkar da Nu'aymah tai tuntuɓe ya fice abinsa. Ya tabbata idan ya
cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema
kansaba. Dan duk da baiji mi Kubrah ta faɗaba ya fahimci ba abune mai daɗi ba
musamman yanda Aymah take kuka.
Yana ficewa Kubrah ta bi
bayansa da sauri.
“Aunty Kubrah!” Nu'aymah ta faɗa da
hanzari tana miƙewar itama. Amma sam Kubrah batako jiyoba balle ta nuna zata
saurareta ta ficewarta.
اَللَّهُمَّ لاَ
سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta
taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya
zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.
Nu'aymah dake jin wata
hajijiya na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta da sauri. Da
ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba
wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda
wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya..............✍

No comments