Breaking News

NI DA KE 33


 ♣️♥️♣️

     *_NI DA KE...!!!_*

                    ♣️♥️♣️




♥️```Dole muyi rayuwa.........```♥️





_By 😘😘fêêbyrh😘✍️_





Page 3️⃣3️⃣

    "Lafiya....?

 suka tambaye shi baki dayan su, dogon nunfashi yaja ya sauke tarefa furxarda xaxxafan iska daga bakin shi 

     "Dan Allah dad kuce Khalil ya yafe mun har kuma ku yafe mun dan Allah...."

  yayi maganar matsanacin kuka na kufce mishi baki suka Saki gaba dayan su suna mamakin irin wannan al'amarin Anya kuwa yana cikin hanyacin shi? haka suketa maganganu a xukatan su 

      "kwantar da hankalin ka Lamir kayi mana bayani dallah dallah yanda xamu fahimta...."

  dad ya fad'a yana gyara kwanciyar jinjirin dake hannun shi 

  "Dad na xalunci Khalil na cuce shi na bata mishi rayuwa"

yayi maganar yana kuka sosai rik'e baki mom tayi tana Kara mamakin maganar shi 

"Dan Allah ku yafe mun wallahi duniya ta juya mun baya na cuce shi....be gama magana ba dad ya katse shi da cewa

   " wanne cuta ne ka mishi dahar duniya xata juya maka baya kashe shi kayi ne...?

Ajiyar xuciya ya sauke tareda shak'o nunfashi me xafi yace

    "A'a amma na tabbata idan ya mutu a cikin wannan mummunan halin nasan ba shakkah wuta yayi sai dai shi Allah ba axxalun wani bane..."

   "hakane..."

cewar momyn Firdausi.

"A lokacin da muke karatu khalil ba ruwan shi da duk shashancin da muke da abunda ya dame shi da sha'anin wani ba ruwan shi da Yan mata balle shaye shaye da muke shi karatun shi kawai ya saka a gaba duk yanda xanyi in bata masa rayuwa nayi amma banci sa'a ba na bashi mugayen shawara amma koh sau daya be dauka ba naso in yaudare shi in mallaki duk dukiyar da ya mallaka amma hakan yaci tura hakan yasa na yanke shawarar Neman boka Wanda xe tarwatsa masa rayuwa, naje wajen bokaye sama da goma amma duk abu daya ake fada cewar baxa'a samu nasara ba saboda riko da addinin da yayi hakan na hakura da karshe na samu wani bokan nan ne nayi arxiki aka samu akayi masa aikin nan ya fara banxar rayuwa irin wacce nake bukatar yayi nan muka cigaba da hole rayuwar mu ganin Khalil ya fini kwamkwajewa wajen harkar shiyasa na fita sha'anin sa har xuwa lokacin da xamu gama karatu bayan rabuwar mu nayita aika mishi mutane wa'inda xasu mayarda shi baya su kwashe duk dukiyar daya mallaka ganin hakan baxeyu ba yasa na hada shi da salmaty don ta yaudare shi ta kwashe komai nashi......be k'arasa maganar da yake ba suka yi kalima hakan yasa shi yin shiru 

  "Innalillahi wa'innah ilahi raju'un... Haka suketa maimaitawa 

"tabbas yaya Khalil haka ne halin shi duk cikin mugayen... Halayen xamani luwad'i  ne kawai bayayi sai sata amma duk saurin abubuwan ba abunda beyi na boye muku halin shi ne saboda kai ranku ya bace a kanshi shine kadai....dan da Allah yabaku kuma shi kuke gani kuji sanyi a ranku....toh mexe saka na gaya muku yanxun ma don naji dalilin daya saka yake wa'innan mugayen halaye shi na sanarda daku hak'ik'anin gaskiyar tun ba yanxu ba yaso ya tarwatsa rayuwata Allah be bashi sa'a ba sai lokacin da yasamu sa'a ne yayi  mun wannan  ta'asar.....?

Firdausi ta fada tana  kuka me xafin gaske 

  " Ina ma ace Allah xe dauki rayuwata da naji dadi banason na cigaba da rayuwa da yaron nan....dan Allah daddy ku taimaka mun ku kai yaron nan gidan marayu dan wallahi baxan iya rayuwa dashi ba....."

   tana fadar hakan ta fad'i k'asa sumammiya, da sauri sukayi kanta ruwa mom ta dauko daga fridge ta watsa mata  a hankali ta bud'e sexy eyes d'in ta ta sauke su akan dad Wanda ke faman sharar kwallah na tausayinta

"Yi hakuri mamana wannan shine kaddarar  mu baki daya....shiru yayi sanadiyar kuka daya kufce mishi hakan yasa yabar wajen da sauri janta xuwa room d'inta su mom sukayi inda babynta ke kwance yana kukan yunwa kallo daya xaka mishi kasan kyakkyawa ne ajin farko don a fannin kyau ma yaso yafi baban shi kwanciya tayi tana goge xaxxafan hawaye dake rolling a beauty face d'inta dauko yaron mom d'inta tayi tana mik'a mata kauda kanta tayi gefe hawaye na cigaba da gangarowa a gefen fuskarta 

   " kiyi hakuri ki karbe shi wannan yaron besan komai ba hasali ma idan kika cutar dashi sai  Allah ya fitar masa hakk'in shi a kanki dan haka gara ki hakuri ki barwa Allah komai na daya dai Khalil dan uwanki ne dole ne kiyi hakuri da duk abunda ya miki infact bama laifin sa bane laifin lamir ne dan haka kiyi hakuri ki rungume danki hannu bibbiyu..."

  girgixa kai tayi tana cewa 

   "mom kiyi hakuri dan Allah wallahi baxan iya shayarda shege ba..."

   Tafada tana kuka, murmushin da yafi kuka ciwo momyn Firdausi tayi tana cewa

"Amma kuma xaki iya haifar shege....?maxa ki karbi yaron nan inba so kike na tsine miki ba.."

tana gama maganar ta fita daga dakin. ajiye mata yaron a kafa momyn khal tayi nan ta shiga bashi nonon tana kuka fita momyn khal tayi don tana gabbbbbb da fara kuka itama.

A parlour suka same Lamir yana jiran fitowar su xama tayi tana facing d'in shi parlourn ya dauki shiru na tsawon mintuna goma kafin momyn Firdausi ta gyara murya tana cewa "yanxu yaxa muyi mu karye wannan sihirin..?"

ajiyar xuciya ya sauke yace "maganin wannan abun yana gidan nan....don a dakin shi na binne abun...."

xaro ido sukayi gaba dayan su nan suka tashi suka dukufa part d'in khal yaci wuya yana Neman inda ya binne abun a tiles dakyar suka gano wajen nan aka fasa wajen aka fitarda wani kwalba Wanda ke dauke da abubuwan ban al'ajabi a ciki karban kwalbar yayi ya fasa nan saiga mugayen abubuwan da akayi amfani da.





Khal dake tsakiyar yan mata shida Biyu a gefen shi Biyu a gaban shi Biyu a bayan shi sai shafarshi suke suna tsotse shi kwalaben giyoyi ne a gaban shi inda in ya dauki kwalba ya daura a bakin shi saita k'are yake sauketa xiiiiiiiiiirrrrrrrrrrrrrrrrrrrr yaji a jikin shi kamar an xare mishi allura da sauri ya tashi yana ture Yan matan barin  wajen yayi ba tareda ya shirya ba yabar kasan don koh kayan shi be tsaya dauka ba.

Karfe 6:00am daidai na safe jirgin su ya sauka a Nigeria inda bodyguards d'in shi suka xo daukar shi direct gidan su ya nufa Hakuri ya shiga bawa iyayen shi inda kowa ya yafe mishi don daman ba laifin shi bane 

Ranar suna yaro yaci sunan Mallam wato Wanda ya rik'e Firdausi mijin momynta Amma suna kiranshi da Affan Khalil kuwa ya killace kanshi ibada kawai yake ya dauki son duniya ya daurawa danshi wato Affan b'angaren  su dad ma haka ba abunda sukeso ya taba shi.



Bayan shekara biyu.......







Comment and share





😘😘FÊÊBYRH😘✍️

No comments