Breaking News

DUK NISAN JIFA 57


 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




                            57


*Yaya ibada?*






Wani firgitatacen ihu ta saki tana kara saka hannunta dan ta rike shi, aman ina, ba zata iya hanna Hammanta abin  nan da ya sako a gabansa ba, gaba daya ya birkice mata, cikin gigicewa yake fitar da zazafa kuma dadadiyar soyayarta da ta daskare masa ta masa ila, tamkar bai taba fitarwar ba, tamkar wani  na labe masa a jikinsa haka ya kankameta a jikinsa idannuwansa rintse jikinsa na bari, bari ne na wannan ikon Allah da ya shiga a yau

Sam kunnayensa basa jiyo masa yadda take sauke zazafan nishi da numfashin wahala sai da ya kusan minti goma sha biyar da samun nutsuwa


A hankali ya shiga zare kansa yana mai kallon fuskarta cike da matsanancin mamakin irin juriyar da ta yi


Bai ga aika aikar da ya mata ba sai da ya gama janye jikinsa a hankali ya laluba fitikar kusan bed din ya kara kunnawa yana mai kara sauke dubansa a saman fuskarta

Gaba daya ta rintse idannuwan nata ta yadda ba zai iya hada ido da ita ba, hucin zafin da jikinta ke fitarwa ya saka shi saka hannunsa cikin nata a hankali ya dora kansa a gefen kafadarta


Ya rasa da wace kalma zai fara, ya rasa me zai ce, ya rasa da wani idon zai iya fasara abinda ke cikin zuciyarsa


Gaba daya ya dago ya mike zaune yana lalubar gajeran wandonsa

A nitse ya saka yana kara kallon yadda take son jan wani abin ta rufe jikinta aman ba komai a kusa da ita


Dan murmushi ya yi a hankali ya iya mikewa tsaye ya bude wrdrb dinsu ya janyo abin rufa


Cikin nutsuwa ya dawo inda take ya rufa mata ya kara rage tsayinsa yana dan shafa gaban goshinta har yanzun idannuwanta a rufe suke


Murmushi ya kuma yi ya juya ya dauki wayarsa ya fita a dakin


Kira ya dannawa Kader , yana dagawa ya ce" Ka je asibiti sai ka yi kirana idan ka ga docter umaimah ta baka sako ka kawo min "


Kader ko amsawa bai samu ya yi ba yana gyangyadin gajiya ya mike sai tura baki yake ya fice


Bayi ya shiga cikin nutsuwa ya shiga wanka


Sai da ya gama ya fito daure da tawul ya buda wajen yana mai kallon agogon dakin gannin yanzun kusan karfe biyu ne a kadan ya kusan minti ashirin a kan yarinyar da bata taba yin harkar nan ba?


Murmushi  ya yi yana kara hasko jarumtarta, bai taba tunanin wai a ranar da zai zo mata ba zata tara masa mutane ba, kasancewarta mai yiwa allura kuka shine yau ta iya jurewa? Sam bai saka mata jikinsa baki daya ba aman fa ya saka mata wajen mai wuyar shiga kuma ya haka daidai gwargwado duda ba karfi ya nuna mata ba, bayan magiyar da son kwatar kanta da ta yi bata yi masa koke koke da ihun da zata saka masa jin abin ya fice a ransa, 


Murmushi yake yana jin kansa wani iri, a hankali ya zauna yana jiran kiran Kader , wayar tasa ya shiga wajen mesage ya dano number Aisha ya rubuta mata mesage kamar haka "Kin yi baci? "


Yana turawa kiran na shigowa ya daga, sanar mata dukan abinda yake bukata ya yi sannan ta mikawa Kader ya ce" Ka kawo min "


Kader ya ce" Yanzu kuma? Dare fa ya yi "


Hisham ya ce" Minti ashirin na baka ma"


Kashe wayar ya yi gannin mesage din Aisha  watau idannuwanta biyu?


Gyara zamansa ya yi ya danna mata kira


A sanyaye ta dauka da muryarta da ta shake  ta yi masa salama


A nutse ya ce" Me ya hanna ki barci ne? "


Aisha ta gyara kwonciyarta rike da fillow ta ce" Ba komai "


Kansa ya dan shafa a hankali ya ce" Aisha kin ga ban dawo ba ko? "


Aisha ta gyara kwonciyarta a karro na ba adadi ta ce" Eh, aman ba komai ai na san kana tare da kanwata ne"


Murmushi ya yi ya ce" Kin san rigima take ji shine na yo gidanta da ita, in sha Allahu da sasafe zan zo"


A kasan zuciyarta  ta shiga furta 'Gidanta kuma? Dama raba mana gida za'a yi?' 


A bayane kuwa sai ta ce" Allah ya bamu alkhairi likita"


A hankali ya ce" Aisha? "


Amsawa ta yi tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da wani irin karfi cike da tunani kala daban daban 


Hisham ya ce" Ki yi adu'a kafin ki yi baci "


Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce" Ka kula da kanka Likitah"


Idannuwansa kawai ya iya lumshewa zuwa lokacin yana jin kiran Kader na shigowa ya mike ya nufi hanyar fita


A hankali Aisha ta ajiye wayar ta dauki fillo din ta dora saman kanta ta fashe da kuka

Kuka ne take mai zafi wanda ya tokare mata kirjinta, kuka ne take na tsananin kishin mijinta, tunani ya kasa barin kwakwaluwarta kan yana cen ya yi abinda yake yi da ita, baban tashin hankalinta a yanzun koda tana shan wahakar saduwa da shi aman ta fi jin dadin hakan fiye da wahalar, wani irin kishin kamshinsa, laushin jikinsa, yannayin da yake tafiar da ita ne suka hadu suka hadasa mata wani curaren dutse a kirji wanda bata iya samun saukinsa ba sai da ta fashe da wannan matsanancin kukan 


Ko jin daurin aurensa bai tada mata hankali irin haka ba, a nan ne ta gyada kanta tana jinjina lalema idan Bilkisu ta ji su a dazun tana da hakuri, lale tana da hakuri, da ita ce ai sumewa zata yi ko ta afko masu, bata san abin haka yake da ciwo ba sai yanzu, abin ba na ka taba yi ko baka taba yi bane, abin zafi ne da shi koda baka san ana yinsa ba, abu ne da yake da ciwo, lale ta jinjinawa mata, ta jinjinawa kuma Bilkisu domin a irin yadda suke da shakuwa ta tausaya mata jin ihunta da ta yi

Luuuu ta yi da idannuwanta tana mikewa zaune dan bata tunanin idan har zata iya rintsa idannuwanta a yau, kishi ba karya bane, kuma du matar da ta iya sarafa kishinta ta hanyar kisa da kawar da kai lalle jaruma ce, a sanyaye ta sauko ta nufi bayi ta dauro alwallah ta dawo

Saman salayarta ta hau ta shiga gabatar da ibadarta ko zata samu sanyi a zuciyarta, kiran da ya yi mata ta ji dadinsa dimin ko ba komai ta tabata bai mantata ba, maganar raba masu gida kuwa bata ji dadinsa ba dan ita ta so ta kama kafar Billyn ta samu shiga, sai dai ba komai ta tabata idan da rabon zamansu ya dore ba zai wulakanta ta ba



Hisham na bude Dakin Kader ya kawo hannunsa  zai kuma bugawa da sauri ya tsayar da hannun nasa yana fadin" Au ashe kana kusa, wai menene yake faruwa ne yau aikena kake ta yi tsakiyar dare bayan ka san bana son fitar dare , tsakani da Allah hala dukan yar nan ka yi? Kai yanzu Hisham baka da hakuri daga ce maka ka mata jan ido ko meye ne na ga du idannuwanka kamar mashayi bayan daga shayi baka shan komai?"


Hisham ya amsa yana kallonsa ya ce" Kana ta surutu tsakiyar dare baka ko jin kunya "


Kader ya dan saka hannunsa ya tare kofar yana kallon jalabiyar dake jikin Hisham wace yanzun mai ruwan ash color ce


Yar yatsarsa ya nuno ya ce" Ni kam kamar ba da wannan jalabiyar muka zo gidan nan ba, ina wancen  din take ne? "


Hisham ya dakata da mamaki yana kallonsa


Kader ya karra ruko idannuwansa ya dafe tsatsonsa da hannunsa yana kallonsa ya ce" Aman idan ka aikata abinda muka yi da kai ba yanzu ba Hisham ka ji kunya! Yanzun Hisham kai din ne ka zo a haka dinka mikowar ingozoma gaban yar da ka raina?, Hisma kai kam akoy jarababe kuma abin nan ya bani kunya sosai da sosai, ban san haka zaka min ba na zauna na baka shawara dan kar a raina min kai to ko dai da karfi ta maka? Irin yadda kawarta ke min fada na tabata zasu aika, to yanzun kuma hala da gaske wancen din da ya saketa namiji ne ko dai dan ta bata maka rai ne? "


HISHAM ya zarro  ido cike da mamaki da sauri ya juya ya ajiye ledar ya juyo yana fadin" Ni zaka yiwa iskancin da talatainin dare dan ina daga maka kafa? To nauyin kirjina ya sakeni ni da kai shege ka fasa !"


Da sauri Kader ya juya yana ayatul kursiyu dan dare ne baya iya doguwar tafia da dadare sam baya son fitar dare, a bayane yake karantawa wai kar Allah ya hada shi da mutanen, har fadi yake ka zo sun zo aka hade  lokacinsu ne ko me suka yi maka kai ka ja


Hisham yana tsaye yana kallonsa har ya shige dakin da aka tanadar masa idan sunna gidan Bilkisun kafin ya juya ya koma ciki yana gyada kansa da yima kansa Alkawarin da safe zasu raba raini, duka kaf abinda ya dura masa zai amayar masa da abinsa










































           Mahalo

No comments