SARAN BOYE 27
No. 27
............Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ɗan naushi gadon da faɗin, “Noooo!!!”. Da ƙarfi kamar mai magana da wani.
Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake
abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a
zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ɗin yarinyar da
ko sunanta baima sani ba. Miƙewa yay daga gadon ya shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin,
ko takalman dake ƙafarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ƙarasa gaban shower ya
tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ƙarfi, tamkar itace tai masa
laifi.
Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa
gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya
wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da
hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon
lokaci ya gama jiƙewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan
ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ƙarasa saman toilet
sit ya zauna yana mai riƙe kansa da hannu biyu....
_______________________
Duk yanda Nu'aymah taso
sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru
tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta miƙe daga zaunen da take kusa da
Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
Sai da taɗan saci kallon Addah da tai banza
dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. “Um.....u.... Zanje su Aunty Zulfah na
jirana”. Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata
kifa dan sauri.
Karo suka kusan ci da Malam ƙarami da ke
shigowa. Tai saurin komawa da baya tana faɗin, “Yi haƙuri Yaya, bansan ka taho
ba”.
Murmushi ya mata da cewa, “Karki damu
Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm”. Ɗan kallonsa tayi kamar
zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake faɗaɗa murmushin sa, “Dama ba wani abu
bane, baƙon da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki.
Shine naje kai miki na Iske baƙya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki”.
Tunda ya ambaci baƙo gabanta ya sake
tsananta faɗuwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin
gaskiya. Sai kuma ta ɗan juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu
hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin faɗin, “Ni
banaso Yaya”.
Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon.
Shi malam ƙarami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka
shiga ƙyalƙyala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
Hajarah ce ta fara farga da yanayin
Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana faɗin, Aunty Kubrah ALLAH
dama nasan ba ciwon kai Nu'aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su
Addah shine duk take a ruɗan nan”.
Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma
mikewa tai ta bar falon tana wani ɗan murmushin da su duka basu fahimci
ma'anarsa ba......
Nidai nace, “Humm”.
“K lafiya? Kika shigoma
mutane tamkar wadda aka koro!”. Umm ta faɗa a tsawace tana kallon Nu'aymah data
shigo falon a guje.
Duƙar da kai tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye
kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace “Umm babu komai fa,
zanje toilet ne”. Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ɗakinta da sauri.
Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai
banda Umm da tabi Nu'aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta faɗa ba.
Tana shiga toilet ɗin
ta maida ƙofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ƙofar ta fashe da kuka
maiban tausayi. A ranta tana faɗin yaya zatai da wannan abin kunya da takaici
da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da
baya bautama ALLAH. Baisan idan ya saɓama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan
haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai taɓa ambaton
ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine
yau akan nata. ‘ALLAH ya isa bazan taɓa yafe makaba’. Ta faɗa a fili tana sake
rushewa da kuka. ‘Na shiga uku ni Zainab, ni.........’
“Nu'aymah!”. Muryar Umm ta hanata
ƙarasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
“Nu'aymah wai baƙya jinane?”.
Umm ta sake faɗa tana matsowa jikin bayin.
Da sauri Nu'aymah tai gyaran murya.
Kafin ta miƙe da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ɗaya taima
mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani
ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar
tata sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito.
Haɗa ido sukai da Umm da ke a tsaye
tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ƙasa da faɗin, “Umm yi
haƙuri, ALLAH toilet ne”.
“Toilet ko kuka?”.
Da sauri ta ɗago ta kalli Umm ɗin. Muryarta na rawa tace,
“Umm toilet ne ALLAH”.
“Toilet ɗin ki kai ma kuka kenan?”.
Baki taɗan tura gaba, “To Umm gudawa fa ce”.
“Mtsoww! K dai bansan randa zaki
bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani
ba”.
“Kiyi haƙuri Umm”.
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai
ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da
tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka
ƙureta, sam bata ƙaunar halin banza.
Duk da tana buƙatar kaɗaici
haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani
ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin
fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka
musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance
haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin
tufƙa da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ɗaya).
Tana zama aunty Rafi'a tace, “Hummm!
Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen daɗi haka?”.
Gaban Nu'aymah yay mugun faɗuwa. Ta ɗago
da dauri tana kallon aunty Rafi'a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take
tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta buɗe baki zatai
magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
Wata muguwar ajiyar zuciya
Nu'aymah ta sauke a ɓoye. Tare da saurin miƙewa zumbur ta nufi su Nanah ta
rungume.
Zuwan su Nanah
gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin yaƙi barin
ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen shaƙar
ƙamshin a jikin Nu'aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa
da wannan ƙamshin ba. Amma sai bataima Nu'aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah
sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.
____________________
Ya jima zaune matuƙa akan toilet
sit kafin ya miƙe ya fara zame jiƙaƙƙun kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito
sanye da Bathrobe fara mai ɗan tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa kaɗan. Towel ƙarami
ya riƙo a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
Kallo ɗaya yayma Solomon daya
kasa haƙuri ya dawo ɗakin duk da korar da yay masa ya ɗauke kansa. Kan Solo a
ƙasa yace, “Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani
hali”.
Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya
dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ɗakin. Zama yay
cikin ɗaya ya ɗora ƙafafunsa saman table ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin
hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da
kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba
malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da
shi........
“Ina buƙatar coffee”. Ya katsema
Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da
“Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin
coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
Ba'afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa
sai ga cikin ma'aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo
inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura
ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya
kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
“Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin
nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo
yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko
inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya
fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.
Yoohan da baisan Solomon
bai fitaba ya fara shan coffee ɗin a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo
akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam
ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba
da zama har tsahon lokaci.
Zuwa can kuma tamkar wanda aka
mintsina sai ya miƙe, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya buɗe
ƙofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangyaɗi
a falo, kansa ya ɗan girgiza ya nufi ƙofa batare da yayi magana ba.
Can ya fita harabar hotel ɗin
da ko ina ke ƙwanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi
yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su kaɗai ke shigowa alamar
masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su kaɗai ne suma, dan wasu
matafiyane ba sheɗancin ne ya shigo dasu ba.
Watsar da komai yay dan
shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka
tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ɗaya ya
zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun
ɗazun.
A cikin tunanin nasa ne
hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk
da ya saka ƙarar can ƙasa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara
nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ɗin dama bana
ku bayi bane, na manya ne masu ji da ƴan canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa
baka amsa.
Lecture ce da ga bakin
Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga
kunnen Yoohan raɗam. Buɗe idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren
wa'azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ɗaya zakai masa kasan kaga
ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren
wa'azin sa.
Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa
sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa'azin nan mutumin ya miƙe,
batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya
koma ciki dan ya kwanta ya huta.
Ko kaɗan Yoohan baiso hakan ba,
dan anzo wata gaɓa da duk mai sauraren wa'azin zai so jin ƙarshensa. Bin
mutumin yayi da kallo harya ɓacema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya roƙe ya
basa ya ƙarasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmiƙe
masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da
maganganun Nu'aymah sai lecture ɗin nan daya saurara ta sake faɗaɗa rauninsa
zuwa ƙololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a
cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ɗan
waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura.
Sake maida idanunsa yay ya
lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga
saukewa a jajjere.
A haka Solomon daya sake
shiga ɗakin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da
wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar
zuciya .
“Ashe kana anan sir?!”.
Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ruɗanin da yake ciki na rashin ganin
nasa da farko.
Yoohan da tun isowar
Solomon wajen yana kallonsa ta ƙasan ido ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani
shegen kallo mai cike da gargaɗi.....
“I'm sorry sir. Madam ce”.
Kafesa da ido sosai yayi, duk da
kuwa yasan Momy Solomon ɗin ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya
miƙe yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a
tashe.
Koda suka koma ɗakin bai
gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya miƙa masa
hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi
toilet ɗin dan ya duba. Shi kuma ya ɗora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo
da kauri ɗin nan ta fara fidda sauti. “Hello Mom”.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi madam Chioma ta sauke
da ga can, kafin cikin ƙasa da murya sosai tace, “My boy!”.
“Humyim”.
Ya faɗa a hankali cikin maƙoshi.
Murmushi mai sauti ta sake da ga can
tana mai ƙanƙame filo a ƙirjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace,
“Mike damunka?”.
Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya
furzar da ɗan huci yana sauke idanunsa da ga table ɗin. “Ba komai Mom, bakiyi
barci ba?”.
Sake narke murya
tayi kamar zatai kuka. Tace, “My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna
tsananin buƙatar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ƙannenka gaba ɗaya.
Amma duk da ɗokin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da
ka ɗauka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja
mun ganka ba”.
“Am so sorry Mom”. Ya faɗa
a taƙaice kawai.
Matse filo ta sakeyi sosai a ƙirjinta.
Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito.
Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na faɗin, “Mom
goodnight, zan kwanta”. Ƙitt ya yanke wayar.
“My b......” tai yunƙurin faɗa sai kuma
taji ƙitt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai
masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata
ƙanƙame papa ya shigo ɗakin nata.
“Wai lafiya kika maƙale anan
bayan inata jiranki a can?”.
Wani irin takaici da baƙin ciki ne ya
kumeta a zuciya. Ta ɗan hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ɗaci
a ranta. Amma a zahiri sai tai ɗan murmushi da cewa, “Ka bari kawai. Solomon ne
ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya haɗamu dan wayoyinsa
duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ƙarshe ma ya
yanke wayar”.
Ƴar dariya Papa dake hawowa gadon yayi.
ya jata jikinsa ya rungume yana faɗin, “Kema kinsan halin yaronki ai. Minene
zai ɓata miki rai a ciki. Maybe yana buƙatar hutawa ne shiyyasa ya kashe”.
Kafin ta samu damar basa amsa ya haɗe bakinsu
waje guda. Duk yanda taso ta ƙwace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar
ALLAH ya bashi sa'a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai
buƙaci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ƙarfi yake nuna
mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan
auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun
nan da bazasu gaza goma zuwa sha ɗaya ba.
To komadai minene yau ya moreta da ƙyau. Daga
ƙarshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fyaɗe.
Da ƙyar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama
ya sacetan.
Yoohan kam koda ya yanke
wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin
kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ɗazun.
A haka Solomon da ya kammala tattare
kayan da Yoohan ɗin ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya
lallaɓa kawai ya ɗauki wayarsa ya fice da ga ɗakin. Duk da Yoohan najinsa bai
motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa
baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da faɗawa
cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al'ajabi a garesa.
Gabannin asuba ya
farka a firgice, da ƙyar ya iya motsa wuyansa da ya ƙage, cikin dauriya da
jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ɗan
sake masa sannan ya miƙe tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a
zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa huɗu sai baiyi magana
ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu'a kamar
yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin buɗewa. Hannu ya saka ya buɗe
Window ɗin. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ƙwala kiran sallar
farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ɗine ko kuma a
cikin hotel ɗinma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa.
Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nishaɗa na musamman..............✍

No comments