Breaking News

FURUCI 73-74

 


🗡 *FURUCI*🗡

         💔💔

       

*(Murd'add'iyar Soyayya)* 💓❣💘


Story and written 

            By 

NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸


               🅿️73 to 74



                   Dedicated 

                          To

                    My lovely  

                     *Ummi*

                         and  

                       Lovely          

                     Daughter 

                     *ZARAH*


           My Novels

*NAYI RAYUWA DAKE* 

*SANADIN ACCIDENT*

*SAKAYAR CUTA* 

*RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*HAYATUL MAHAYAT*

*MUGUN SARTSE*

         Loading....🖊

🗡💔FURUCI!!!!💔🗡


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





🅿 73 to 74





Cikin tashin hankali suka dubi juna ciro wayar shi Alhaji Tukur yayi yakira yaran dayaba umarnin kamo su Ibban bayan and'aga yashiga tambayar shi cikin sauri cikin mamaki yace " haba Alhaji mukuma tayaya zamusan inda yara suke bacin munriga damun danqasu a hannun ku gaskiya kude duba kumamu Kam wallahi kud'in mu mukasani dan babu abinda yashafemu " tsawa Alhaji Tukur yasakar mishi yace " sannu mararkunya to Kam yazamadole kuzo kutayamu nemansu idan aka gansu semubiyaku kud'in ku " cikin fusata barbar yace  " to Alhaji Tukur idan Kuma ba'agansu bafa ? " Wannan Kuma kutashafa idan banga yaraba tofa babu yadda za'ayi nabiya kud'i " kashe wayar shi yayi murmushi barbar yayi yadubi abokan aykin nashi yace 


" Lalle kam Alhaji Tukur baisanmu bane muje kuga yadda zanyi masa " 


Daga haka suka fita tafiya sukayi mai nisan gaske zuwa wata unguwa wadda babu yawan mutane sosai cikinta sannan suka tsaya kiran wayar Alhaji Tukur Barbar yayi bayan yad'aga yace 


" Yanee Alhaji munsamesu guduwa sukayi kazo bayan wannan katon gidan gonar muna wajan amma kataho mana da kud'adanmu idan bahakaba to bazamu baka yaranba idan Kuma kadad'e zamuyi tafiyar mu sabida munada wani aykin bayan wannan " kafin Alhaji Tukur yace wani abu barbar yakashe wayar duban Hjy Himla yayi yace angansu bari naje na amsosu " tashi Hjy Himla tayi yadakatar da ita yace " kibari naje kinsan halin yan'iskan yarannan yanzu zandawo " cikin sauri yafita komawa tayi tazauna


Yana fita yashiga mota yajata aguje Kai tsaye wajan su barbar yanufa yanazuwa yakashe mota yafito fitowa barbar yayi daga la'ban dayake yanufoshi duban shi Alhaji Tukur yayi yace " Ina yaran ? " barbar yayi dariya yace " aydama nace maka sekabamu kud'in mu " ciro wayar shi Alhaji Tukur yayi yace bani account number ka " bashi barbar yayi dandanan 500,0000  suka shiga cikin account d'in barbar jinjina Kai barbar yayi yace " sun qaraso zomuje nabaka yaran " binshi Alhaji Tukur yayi suna Shan kwana wani yajagayo tabaya yashaqama Alhaji Tukur wata powder a hanci kafin wani lokaci Alhaji Tukur yafara gani dishi dishi cikin rud'ewa yace " Kai maikuke Shirin aykatawa ne " 


Wata irin muguwar dariya barbar yayi yace " Kai dalla ware kusamin shi a mota kabiyamu wasu kud'i Yan kad'an shine keke neman renamana hankali to kuwa zakasha mamaki kusashi da sauri Kai shiga motar tashi itama munyi ceqwara ta " sashi sukayi cikin bot d'in mota suka bar gurin 


Anyi lallashin duniya Amma Iftahal takasa denayin kuka shiko Maher tunda yafita baidawoba a gidan Akeey Zaffar kuwa ankawo gawar baby har anyi mata sutura duk dasu Sarki Zaid akayi jana'idar hadda barrister Maher daga nanne yabar gurin cikin tashin hankali Momy tanufi room d'in da'aka kwantar da Ayna Amma Sam akahanata shiga sabida ACP Kabir yace koda babanta ne yazo Kar asake abarashi yashiga dole takoma cikin qunar zuciya Mahaifiyar Ayna da Abban ta kuwa sunshiga cikin mugun tashin hankali 


Duban agogon dake banne jikin bangon parlour ta Hjy Himla taduba tsaki taja sannan tasake Kiran wayar Alhaji Tukur akaro nababu adadi miqewa tayi cikin tashin hankali afili tace 


" To Ina wannan mutumin yashiga ? badai nizai renama hankali ba ? ayko dana nunamishi nafishi iya shirya tuggu " Kiran wayar barbar tayi bayan yad'aga tace " Kai Ina Alhaji Tukur ? " cikin nuna rashin fahimta yace " kamarya fa Hjy ? nagade shi Alhaji Tukur bayaro bane qarami dazaki Kama nemanshi dan karya 'bata tuni mu munbashi yaran yatafiyar shi muma munkama gabanmu dan haka karki sake kirana idan Kuma Kika sake to wallahi sena wular dake " 


Daga haka yakashe wayar shi cikin razana damaganar barbar Hjy Himla tashiga jagaye parlour dede lokacin Abdul yashigo cikin tashin hankali rungumai Hjy Himla yayi yace 


" Momy nashiga 3 Lubna nacuceni tasakani cikin masifa Momy dan Allah ki ceceni nasan idan inadake banida wata damuwa Kuma na tabbatar Zaki tsayamin akan komi " sosai zuciyar Hjy Himla ta tsananta bugu cikin rawar baki tace " 


" Kabar kukan sanar dani meke faruwa ? Mai Lubna tayi ? " cikin kuka yace " Momy Lubna ce tacemin nasaka kaf dukiyata cikin wata kwangila zansamu makudan kud'i jin zanyi kud'i sosai yasa nayarda nasiyar dakomi nawa batare dakin saniba hadda kadarorinki Momy amma dukda haka tacemin kud'in basu kaiba tasani naciyo bashin banking har 30 million amma Momy tun jiya nanemi Lubna narasa nakira wayarta batashiga se d'azu takirani da number dabata qasar nan ba tace min " Kai Sha Sha Sha kasani babu wata kwangila nayi hakanne dan kawai nakwashe kud'in ka duka kayi tunanin dama Wai sonka nikeyi Ina dukiyar kawai nikeso Kuma nasamu dan haka ni namabar qasar Egypt kaje kaida jakar uwar taka kusan yadda zakuyi kubiya bashin banking nan idan Kuma bahakaba kaje gidan yari idan kaga dama kasakeni idan Kuma kaga dama kabar igiyar auran nawa akanka nide bazakasake ganinaba har abada Sha Sha Sha kawai " cikin tashin hankali nanufi gidan su amma abin mamaki megadi yacemin Wai dama hayace suka Kama Kuma suntashi tun kwanaki 5 dasuka wuce " nashiga 3 Momy gidan danike ciki da wannan qaramin company kawai suka ragemin Koda nasiyar bazasu Kai kud'in banking dana amsaba dan Allah Momy kitaimaka banason zuwa gidan yari kece kike cemin bazanyi kukan rashin komiba Kuma Zaki tsayamin akan komi Momy........ " 


Wata irin gigitacciyar tsawa tadaka mishi wadda tasashi saurin jabaya tundayake batata'ba yimai kwatankwacin irin wannan tsawar ba zama tayi aqasa tamiqe qafafu tsayin lokaci takasa cewa komi zuwacan 


Tafasa wani irin ihu wanda yasa Abdul fita aguje kuka tasaki jin irin kukan da Hjy Himla takeyi yasa Abdul dawowa duban shi tayi cikin tashin hankali dafad'a tace 


" Tabbas Kai Sha Sha Sha ne Lubna gaskiya tafad'a munacikin daula Amma lokaci d'aya kamaidamu mugayen matalauta nashiga 9 Abdul idan Kai 3 kashiga ni 9 nashiga Abdul dole sekaje gidan yari nan ayanzu Kam bazan iya yimaka jagora akan komiba Abdul kasakamu cikin tashin hankali " 


Kuka Abdul yasaki yace " haba Momy to wallahi sede muje tare ay kinada hanyar samun fiyeda 30 million ga mahaifin ki Nan gakuma  Yayanki nan Sarki Zaid  gakuma Saraki d'an yayanki kaf d'in su kowa Don ne amma kibarni naje gidan yari Ina wallahi sede mutafi tare " wani irin baqinciki Hjy Himla taji yataso yatokare zuciyar ruri wayarta tad'auka da qyar ta'iya daga wayar cikin tashin hankali akace mata 


" Hjy akwai babbar matsala fa Ayna tana raye kuma gashi gobene shiga kotu fa idan bakiyi wani abuba tofa tabbas munshiga 3 Hjy na tabbatar idan har akashiga kotu da Ayna gobe Kuma shima  Barrister Maher yashiga tofa tabbas mukam munshiga cikin wahala nashiga 3 hjy Himla kinjefani cikin masifa " cikin wata irin murya Hjy Himla tace " garake shiga 3 kikayi nikuwa da cikin shiga 9 nike ayanzu kuwa nashiga 1000 bama 100 tabbas yazama dole nabar qasar nan ayau basegobeba kema kiyi takanki " daga haka takashe wayar tashiga cikin bedroom aguje shima Abdul binta yayi agujan 


Ahankali Alhaji Tukur  yake bud'e idanunshi saukesu yayi kan Maher cikin razana yazaro ido murmushi Maher yayi yace " kayi mamaki ko ? kad'an daga cikin basirar Barrister Maher Ibban Islam kuzo yaganki " duban yaran yayi cikin matuqar mamaki yace tayaya haka tafaru ? " Murmushi Maher yayi yace 


" Kafara bani wannan amsar tukun da 500,0000 da 10 millions wanne yafi ? Cikin rawar baki yace 10 millions " murmushi Maher yasakeyi sannan yace " to sune nabiya akamin ayki 2 nafarko aka dawomin dayarana na biyu aka qwamusomin Kai wa'inda kasa suka sacemin yara suka kaimaka sune nasaka suka koma sukasake d'akkomin yarana har cikin bedroom d'in dakuka kaisu  sauran bayanan yadda akayi zakajisu a kotu gobe in Sha Allah yarana muje ko dama nace ma mom d'in ku in Sha Allah zandawo Mata daku nan kusa " 


Dariya Ibban yayi yaje kusada Alhaji Tukur yace " kagani dama munce maka Allah zaibamu mafita tunda mundogara dashi kaima idan dashi kadogara zamu gani " Jan kunnan shi Islam tayi tace " Ina Ina Ibban wannan baiyi Kama da wanda yadogara ga Allah ba daya dogara dashi dabaze tutar dakowaba balle qananan yara kamar mu muje gida d'an uwana Ina kewar Irfan da Iman muje muji abincin mom d'in mu Mai dad'i ta sumbacemu kamar yadda tasaba kullum sau 3 yau gashi iya 1 mukasamu " riqe hannun ta Ibban yayi yace " zamusamu na 2 yanzu idan munje " murmushi Maher yayi yace " kagani Alhaji Tukur har abada cikin farinciki zamu kasance kagudu kafin zuwa gobe idan zaka iya "




Comments please

No comments