YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 42-43
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA*☘️☘️
Rubutawa Karimatu Abdulhamid
( *MUMMYN MINAL*)
*HAMDALA WRITER'S ASSOCIATION✍️*
🌹 *SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM*🌹
*Masoya na dan Allah kuyi haquri najina da kukayi shiru kwana biyu hakan yafaru ne sakamakon rashin service amma yanzu komai normal nagode sosai da nuna kulawarku agareni ina gaidaku aduk inda kuke Allah yabar zumunci Allah ya sadamu a Aljanna Fiddausi Amin Allah ya da d'amana son manzo{S.A.W} Amin*
*PAGE 42-43*
____Haka Mum d'in FINAH ta gama tijararta taqara gaba domin kuwa sam FINAH taqi saurarta balle tabita, dan haka da masifarta tabar gidan cikin 'bacin rai.
Washe gari kuwa FINAH ce zaune akan kujera a parlour tana kallo tana girgiza qafa, tamkar wata Sarauniya Mum ce tafito daga kitchen d'auke da tren kayan abinci, ajiyewa tayi a table d'in dake kusa da FINAH sanan tace "daughter ga abinci nan na had'amiki"
Yatsina fuska tayi tace "yau wa Mum godiya nakeyi amma ki koma d'aki inagama zanmiki magana domin banason damuwa yau d'inan"
"To Shikenan"Mum tace. Tajuya da nufin shiga cikin room, kawai sai taga ABUDULJABBAR tsaye abakin qofa hanunsa riqe da wata qatuwar jaka, yazama wani big MAN ya tara uban qasimba ga jikinsa ya murje yasake fari da 'yar qiba, murmushi yayi wa MUM, Mum kuwa dafe qirji tayi tace "Innalillahi wa ina ilaihi raj'un, mutum ko aljan?
Itama FINAH da sauri tatashi takalli inda Mum take kallo kawai sai FINAH tayi qara tace "ABUDULJABBAR" luuu tafad'i tasume agurin.
Shiko ABUDULJABBAR cewa yayi nice Mum ba aljan bane d'ankine ABUDULJABBAR nadawo gareki Mummy na"
Tahowa Gareshi Mum tayi tana shafa fiskarsa tana hawaye tana cewa "haba ABUDULJABBAR mai yasa? Mai yasa katafi kabarmu kabar matarka da mahaifiyarka cikin zulumi?"
"Dole ne tasani Mum domin naga kamar bakya buqatata kinfi son NAFISA dani shi yasa natafi nabarku tinda itama NAFISAT d'in bata bin abunda nakeso wanan shine kawai MUM"
"A'a My Son FINAH alherice agareka domin ita mace daya tillo da take qaunarka kadubafa tsawon shekaru uku kenan Tanan tana jiran ka, kayi tinani ABUDULJABBAR da wuya asamu mace irin FINAH.
"Amma fa Mum naga komai da yafaru Har kawo mata abinci da kikayi dama Mum haka kike mata?"
"Eh Son FINAH tatantanci komai dan kuwa komai na mata ban fad'i ba dan FINAH surukar kirki ce"
Juyawa Mum tayi da niyar yiwa FINAH magana kawai sai taga FINAH yashe aqasa ai da gudu Mum tayi kan FINAH, shi ko ABUDULJABBAR wani mugun kallo ya yiwa FINAH ya haye stairs abunsa.
Mum kuwa koda tagirgiza FINAH taga bata tatashi ba, dagudu ta d'auki ruwan gora mai sanyi a acikin firji ta watsa mata ajiki firgit FINAH takawo numfashi tatashi tana duban gurin da taga ABUDULJABBAR
Mum kuwa riqeta tayi tana cewa "lafiya FINAH me yasame kine"?
Cikin firgici FINAH tace " Mum kamar ABUDULJABBAR nagani wlh Mum naganshi yanzu nan"
"Eh FINAH shine mijinki yadawo FINAH dan haka ki kwantar da hankalinki insha Allah zaman da kikayi ba zai zamana abanzama"
Dafe qirji FINAH tayi talumshe ido cikin jin dad'i.
Koda daddy ya dawo sosai yaji dad'in dawowar ABUDULJABBAR fad'a sosai daddy yayiwa ABUDULJABBAR akan dad'ewar da yaje yayi, inda ABUDULJABBAR yai tabawa daddy haquri da qarde daddy yace ya haqura, Shiko ABUDULJABBAR zama yayi agaban daddy dan jira yakeyi daddy ya masa maganar AMANAR SA amma yaji daddy yayi shiru can kuma Daddy yace "tashi kaje ABUDULJABBAR Allah yamaka albarka sai kaje kararashi uwar gidan ka domin kasam sam bakya kyautama taba domin ba ko wacce mace bace zata iya haqurin da tayi"
Jiki asanyeye ABUDULJABBAR ya tashi ya nufi d'akinsa inda ya zube akan makaken gadonsa yai rigigine kansa na kallon sama, tinani yafara azuciyarsa "to me daddy yake nufine da matarsa 'YAR AMANA domin kuwa sam daddy bai masa maganar taba?"
Wata zuciyarce tace "dashi to ko daddy ya mayar da yarinyar garinsu ne"?
Zumbur ABUDULJABBAR yatashi yana cewa " No daddy baisan garinsu ba tayaya zai mayar da ita? yazama dole insan abunyi, amma zan qarawa daddy kwana biyu inga zaimin magana ko bazai minba"
Shi ko daddy ABUDULJABBAR yana fita daddy yace "yaro man kaza kenan kanason Amaryar ka amma kana basarwa niko bazan baka itaba har sai kanemi abarka da kanka domin kuwa nasan yanzu ba iya gane ta zakayi ba".
Mum da FINAH kuwa sai soye-soye da girke-girke sukeyi na murnar dawowar ABUDULJABBAR.
Suna gamawa Suka jere komai a dining abun sha'awa duk wani abinci da sukasan ABUDULJABBAR yana so sunyi mishi kuma da kud'in FINAH, bayi FINAH tashige ta tsalo wanka inda taci ado dawani uban less mai tsadan gaske brown colour, sai walwali takeyi kamar yau aka kawota gidan, parlour tafito tana zabga uban qamshi MUM kuwa na kallon ta tace " masha Allah d'iyata kinyi kyau tamkar wata matar shugaban qasa, bara naje infito miki da angonaki yazo kuci abinci tare" murmushi FINAH tayi tanemi guri ta zauna itako Mum sama tahaye tanufi bakin qofar d'akin ABUDULJABBAR tayi knocking d'in qofar, shiko ABUDULJABBAR jin ana knocking tasowa yayi yabud'e qofar Mum yagani atsaye shafa kansa yayi yace " lafiya Mum?"
"Lafiya ABUDULJABBAR kafito gacan abinci munshirya maka"
"Okay Mum ganinan zuwa"
"Yauwa d'an albarka kayi sauri domin ga can madam d'in taka tana jiranka"
Komawa ciki yayi da tinanin shi kam baisan wani irin so Mum takeyiwa FINAH ba.
Watsa ruwa yasakeyi ya saka qananan kaya na arsenal riga harmless da gajeren wando sosai kayan sukayimar kyau, sai zabqa kamshi yakeyi sauqowa yayi zuwa parlour inda yasamu FINAH da Mum azaune suna hira, kai tsaye dining ya wuce ya zauna cikin yauqi FINAH tatashi tanufeshi kallon sa tayi ido cikin ido tace "Sannu da zuwa Sweety" shi ko d'auke kansa yayi kamar bai jiba, FINAH kuwa service d'in sa takeyi amma tana satar kallon sa, kallon wajen da Mum take zaune FINAH tayi sanan tace " please Mum kid'an bamu guri zangana da Mijina"
Cikin fara'a Mum tace " to Shikenan FINAH Allah yayi muku albarka" sanan Mum tanufi hanyar d'akinta.
FINAH kuwa sake matso da kujerar ta tayi kusa da ABUDULJABBAR sanan ta d'au lokaci ta ibo abinci tanufi bakin ABUDULJABBAR dashi, Shiko tashi yayi tsam yafice a parlour gaba daya, dam FINAH taji gabanta yafad'i wani hawaye ya sauqo mata yashiga bin fuskarta, ga wani uban kishi mai zafi da yatakorata azuciyarta kuwa cewa takeyi " Shikenan Itakam yanzu zaije wasu 'Yan mata daban su kalleshi su kalle mata surar jiki miji"
Dan haka da sauri tatashi tabi bayan sa hangarsa tayi yashige shashin Anti Amarya wani uban kishi ta kuma ji ya ziryarceta.
Shiko ABUDULJABBAR da Sallamarsa ya shiga parlour d'in Anti Amarya, yaran Anti Amarya kuwa suna Ganin sa suka rungumeshi suna cewa "sannu da zuwa Uncle" Anti Amarya ce da take zaune akan kujera tace " ba uncle d'inku bane, yayan kune fa"
Itama Yasmin sai kuka takeyi akan ya d'auketa, ai kuwa d'aukarta yayi ya zauna akan kujera, gaisar da Anti Amarya yayi cikin fara'a Anti ta amsa sanan tace " Sannu da zuwa baqin Italy"
"Yauwa" yace.
Anti Amarya kallon 'YAR AMANA tayi da take kwance cikin kujera tana karatun English novel, cewa tayi "baby tashi kika wowa yayanku abinci da lemon kanan da kika had'a"
Tashi 'YAR AMANA tayi ta ajiye novel d'in dake hanunta mai suna( in between love)
Shiko ABUDULJABBAR d'ago kansa yayi aikuwa idonsa ya sauqa akan 'YAR AMANA da take sanyane cikin riga top pink colour mai shegen kyau da aka rubuta I love you agaban rigar da farin rubutu, sai Jeans sket blue colour ajikinsa wanda ya kamata tabaya dam ta cinyoyinta ma yad'an matseta, kanta kuwa kitson kalaba ne akayisu manya-manya abakinsu kuma akasaka manyan bit, wanda kitson ya zubu har kusan kunminta sai guda d'aya da yake ta rito akan qirjinta, kitchen ta nufa cikin wani matsiyacin taku mai tafiya da hankalin 'Yan Maza dam ABUDULJABBAR yaji gaban sa yafad'i tini yaqureta da kallo yama manta A'ina yake, har tashige, can kuma tafito hanunta d'auke da qaton tre, shiko ABUDULJABBAR sai wasa yakeyi wa Yasmin amma yana satar kallon 'YAR AMANA, ajiye tren tayi agabansa tatashi tanufi bed room, Anti Amarya ce tace "baby baki gaishe shi bafa Yayankune kuma ki koma kitsiyaya masa ruwa a cop d'in" komawa 'YAR AMANA tayi cikin yauqi ta duqa tace " good evening cikin muryarta mai zaqi, Shiko ABUDULJABBAR kasa amsa wa yayi. Tsiyaya masa ruwan goran Swan tayi acikin cop d'in glass da yake gurin sanan ta d'auka tace "gashi broz"
Hanun yakai zai kar'ba kawai sai akajefo abu ajikin kofin ji kake taratsatsa kofin yafad'i ya fashe........
Please dan kusani acikin addu'arku wlh banida lafiya ne
Kuyi mallage da wanan.
Masu son shiga group din NUSAIBA 'YAR AMANA zaku iyayimin magana ta wanan number 09065120158 domin nayi added naku a group din amma fa idan kinsan kin iya sharhi😇
Dan Allah inkinkaranta kitura asauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

No comments