Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 44-45


 *NUSAIBA*

     *'YAR AMANA*☘️☘️



Rubatawa Karimatu Abdulhamid

( *MUMMYN MINAL*)



*HAMDALA WRITER'S ASSOCIATION*✍️



🌹 *SUBBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBBAHANALLAHIL AZIM*🌹


   

         *PAGE 44-45*


*.......* FINAH ce wacce ta jefi Cup d'in da takalminta mai tuddu har Cup d'in ya fashe cikin matuqar 'bacin rai taqaraso gurin tana huci damqar 'YAR AMANA tayi wacce take duqe agaban ABUDULJABBAR tata data tsaye suka fiskanci juna ware yatsunta biyar tayi tashararawa 'YAR AMANA zazafan mari sanan cikin huci tace " wacece ke dahar zaki bawa mijina ruwa? Qarya kikeyi yarinya mijina nawane nikad'ai"

"You are very stupid FINAH!!!!!!!!!!!!!!

ABUDULJABBAR yafad'a atsawace yayin da yake miqewa daga kan kujerar sanan yaci gaba da cewa "ashe haryanzu bakiyi hankali ba kinan amatsayin mahaukaciya mai tamiki da kika mata irin wanan marin haka?"

Cikin 'bacin rai Anti Amarya tace " karaba da ita kawai Abdul kasan shi kare kullum acikin haushi yake"

"Cikin masifa FINAH takalli ko wanne acikin su,  sanan tace "ni FINAH bawanda ya isa ya shiga gonata inqaleshi yayi qarya sanan bara kiji Ramatu dan ma bakida qimar da zance miki Anti domin ke bani da maqiya kamar ki to ina so ki sani ABUDULJABBAR nawa ne shikad'ai zan iya kashewa akan sonsa dan haka baki isa ki tusamasa son wanan lalataciyar yarinyar da kika gama 'bata mata tarbiya da suka gama watsewarsu da qananinki to ni Mijina yafi qarfinku yafi qarfin karuwanci ku"

Tas!tas!! ABUDULJABBAR ya sauqewa FINAH tagwayen maruka Sanan cikin 'bacin rai yace " waike FINAH meyasa baki da tarbiya ne amaryar daddy kike fad'awa haka ashe haka rashin mutunci ki yakai to bara kiji FINAH kike ko mecece inde da wa'yanan munanan halayenaki kikeso ABUDULJABBAR yazama naki tabbas kinyi qarya kuma kinmakaro"


Itako 'YAR AMANA da gudu tafice a parlour d'in tanufi gaden d'in dake gidan shiko JALALULDEEN da yake zaune tare da Baba mai gadi yaga wucewar 'YAR AMANA  dan haka hankalin sa yatashi cikin sauri yabi bayan ta.

Shiko ABUDULJABBAR ajiye Yasmin dake hanunsa yayi yafice a parlour d'in cikin 'bacin rai

Itama FINAH ficewa tayi tana hararar Anti Amarya.

Itakuwa 'YAR AMANA gindin wata bishiyar mangwaro taje ta zauna tana rera kukanta tana jin zafin marin da FINAH tayi mata da kuma qazafin da tayi mata.

JALALULDEEN kuwa yana shiga Lambun ya tsaya kanta cikin tashin hankali yace " my love menene me yafaru kike kuka dan Allah kifad'amin karkisa zuciyata ta tarwatse?"

Ita kuwa 'YAR AMANA koda taji muryar JALALULDEEN akan ta sai ta miqe tsaye ta fuskanceshi. Shima JALALULDEEN tsaya wa yayi yana kallon ta nan suka qure junansu da ido tamkar zasu cinye kansu.


Shiko ABUDULJABBAR yana fita ashashin Anti Amarya kai tsaye lambun gidan yanufa domin yanaso yasamu rest of mine,  yana shigowa kuwa yayi arba da JALALULDEEN da 'YAR AMANA sunqure juna da ido, tsayawa yayi daga baya yana kallon su.


Shiko JALALULDEEN cikin rud'u yace " my love wa yamareki hanun waye nake gani akwance akan kyakyawar fuskarki?"

Itako 'YAR AMANA mai makon tasanarmar kawai saita sa kuka 

"Please my lovely waya mareki!!!!!!!!!!!?

JALALULDEEN yayi maganar atsawace.

Itako  'YAR AMANA kukanta kawai takeyi shiko JALALULDEEN matsawa yayi kusa da ita yana shafa fuskarta kan daidai gurin shatin da FINAH tayi mata yana cewa tabbas inasan wanda yamareki saina ramamiki mutum ukune kawai a gidan nan zasu mareki su zauna lafiya amma bacin su kowa ye ni JALALULDEEN sai na ramamiki.

Shi kuwa ABUDULJABBAR ji yayi zuciyarsa tana harbawa da sauri da sauri tini yafara tinanin maganar FINAH azuciyarsa "ashe dama da gaskene yarinyar 'Yar iskace?"

Bai qarasa tinanin saba  yaga JALALULDEEN yarungume 'YAR AMANA yana shafa bayan ta alamun rarashi kamar yanda India wa keyi.


Atake ABUDULJABBAR yaji qirjinsa yana wani duka zuciyarsa kuwa sai gudu takeyi da sauri-sauri jijiyoyin kansa duk suntashi jajir launin idanunsa ma duk sunsanja sunzama ja tini yaji ya tsani JALALULDEEN da yarinyar da baisan wacece ita ba.


Atake yaji qafafuwansa suna nema su gagara d'aukarsa dan haka da sauri ya juya yabar lambun yanufi shashinsu kai tsaye d'akinsa ya shige ya kulle ya haye gado atake yaji wani zaza'bi mai zafi yarufeshi lulu'buwa yayi da blanket yarufe idonsa amma ina tini yabud'e domin kuwa kawai yarinyar yake gani kwance ajikin JALALULDEEN.  Tambayar kansa yayi azuciyarsa yana cewa " to namenene zandamu ina ruwana dasu tinda ba IKIRAM nagani awanan yanayin ba?"

Sosai ABUDULJABBAR yayi qoqari dan yakawar da abunda ya gani amma yakasa kawai sai yatashi ya fara patrol acikin d'akin yana tambayar kansa " to wanan wai wace yarinya ce haka tinda yaji FINAH tace ai namijin shine qanin Anti Amarya to ita yarinyar wacece?

Mecece ita agidan? Shin wa zai tambaya ne yasanar dashi komai?

Wata zuciyar tace" masa FINAH"

"A'a badai FINAH ba bazata sanar dani komai ba domin kishinta bazai bari ba"

"MUM" wata zuciyar tace dashi.

"Yes! Nasan Mum inatambayeta zata sanar dani komai"


Itako 'YAR AMANA acikin lambu sosai takwantar da kanta aqirjin JALALULDEEN yana rarashinta da kalamai masu dad'i ji tayi hanunsa yafara yawo ajikinta domin kuwa JALALULDEEN hanunsa yasa cikin rigar 'YAR AMANA akan cikin ta kawai sai taji yazura hanunsa cikin cibiyarta ai kuwa take 'YAR AMANA taji wani irin qarfi tureshi tayi ya matsa gefe sai huci yakeyi take launin idanuwansa suka sanja qara matsowa yayi kusa da ita cikin wata irin murya yace " haba my love bakyaso nane ko kinfara son wani bani ba?"

Girgizamar kai 'YAR AMANA tayi 

"To tinda haka ne meyasa baza kibani jikinki ba nayi abunda nakeso ki sanifa nine mijinki nine wanda zan aureki ba wani ba kuma kinsani tinda munason junanmu dan haka ki aramin iya jikinki kawai nad'anyi romances please my love"

Cikin kuka 'YAR AMANA tace " A'a JALALULDEEN bazan iyaba inasonka amma wlh bazan iyaba runguma tama da nabari kayi nayi kuskure, domin kuwa malamanmu sun haramta hakan sanan baffana ma tun ina qarama ya haramtamin yin hakan nan 'YAR AMANA ta tsananta kukanta kawai sai tafice a lambun aguje. Shiko JALALULDEEN zubewa yayi agurin ya zauna yana jin tsananin takaici.

Ita kuwa 'YAR AMANA d'akinta tashige takifu agado tana kuka azuciyarta kuwa tana cewa "ashe JALALULDEEN bani yakeso ba jikina yakeso?

Sai wata zuciyar kuma tace "mata A'a  JALALULDEEN yana sonki kawai de soyayarkice tamasa yawa"

"A'a jikina kawai yafi so bawai niba"

Nan tafara tinanin baffanta da irin fad'an da yake mata akan takare mutuncinta tin tana qaramarta, nan tatina komai na rayuwarta ta qauye harda fad'en da samarin qauyensu suka so yimata Sai Allah yajeho mata agaji nan tatina ABUDULJABBAR nan tatina ashefa shine sanadin zuwanta gidanan nan tatuna korar dasu hard'o suka mata nan tatuna auren ta da ABUDULJABBAR ya kar'ba ahanun su hard'o.

Take 'YAR AMANA tasa wani irin ihu mai qarfi wanda harsai da Anti Amarya tashigo aguje ita da IKIRAM dan adai dai lokacin IKIRAM tadawo daga aiken da MUM tamata.

Cikin rud'u suka riqeta suna tambayarta lafiya?

Fisgewa tayi ahanunsu sanan tace "  qaryane bazan yardaba tabbas bazan yarda da wanan aurenba ai wanan auren ba aure bane kawai anyi shine bisa wani dalili amma ni NUSAIBA wanan auren babu shi agurina.

Cikin rud'u IKIRAM da Anti Amarya suka ce " wani Aure ne wanan NUSAIBA, auren waye akanki?"

"Kutambayi wanda ya kawoni gidan nan tabbas yasan komai kuma ni kam ba auren sa akaina"

IKIRAM ce tace to " Nusaiba wanene yakawoki gidan nan ina daddy ne ni zantambayeshi komai kinji NUSAIBA ki kwantar da hankalinki ba auren kowa akan ki naga kinfara zaucewa akan soyayar JALALULDEEN"

"Haka ne IKIRAM! Anti dan Allah karkubari  arabani da JALALULDEEN domin ina rasashi hauka zanyi"

"Cikin rud'u Anti Amarya tace " nifa banganeba NUSAIBA mekike nufine meyasa daga ke har ABUDULJABBAR kuke zancen za arabaku wa yace za'a rabaku? Bamai rabaku Nusaiba dan Allah kiwarwarenin tsakanin zare da abawa auren wanene akanki domin bansan da wani aureba akanki NUSAIBA....... .


HMMM ACI GABA DA GASHI.

To Fans ku warwarewa Anti Amarya zare da abawa auren wanene akan NUSAIBA 'YAR AMANA


Dan Allah inkinkaranta ki tura asauran groups please




*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*

No comments