MUGUN DUHU 13-14
⚫```MUGUN DUHU```⚫
1️⃣3️⃣_1️⃣4️⃣
''Da kuka ta farka''
Cikin sauri yazo kan gadon ya rike ta a hankali ya miƙar ta zaune ya jingina ta da saman gadon bakinsa sannu kawia yake furtawa.
''wani irin masifaffen kunyar sa take ji ,sosai take kunyar haɗa idanun dashi,dan haka ta sauke kanta kasa ,murmushi yayi kawai ya wuce toilet ruwa mai zafi ya hada cikin katon bucket ya saka mata cup ciki sannan ya dawo bedrom din,cikin low voice yace
''sannu bebe Allah ya Baki lpya Allah ya baki abinda kike so duniya da lahira.
''cikin ziciyarta ta amsa da ameen kawai.
Kokarin daga ta yayi ta yi saurin Dakatar dashi da fadin zan iya a hankali, no ki bari kawai ,kafin tace wani abu ya sunkuce ta yayi toilet din da ita.
Ajiye ta yayi kan toilet seat din yana kokarin diban ruwa ya zuba mata ta dakatar dashi ,''dan Allah ya AHLAN zan iya pls'' , ok Bebe barin jira ki a bedrom kiyi a hankali Allah ya baki lpya yana faɗin hakan ya juya.
Wanka tayi sosai ta gasa jikin ta Domin ba karamin tsami yayi mata ba , tasha wahala aynun a hannun AHLAN.
Sai da ta gama komai ta kimtsa sannan ta fito,gefen gado ta same shi da Lipton a gefenshi a cikin kofi yana ta tiririn zafi, murmushi yayi sannan yace.
''kiyi salla kisha ruwan zafi jikin ki zai sake kinji? '' ita dai kunya yake bata wallahi da to kawai ta amsa''
A shinfide ta samu sallayar dan haka ta hau ta fara dora farali.
Tana idarwa ya mika mata kofin shayin,sosia tasha shi kuma ya mata daɗi sabida sugar da yake ciki tas ta shanye
Komawa gado tayi ta kwanta kawai ta cigaba da bacci cikin kwanciyar hankali,
Karfe 11 na safe ta farka, gagara miƙewa tayi sabida kanta dake mata wani irin sarawa ta rasa dalili ,dole sai komawa tayi ta kwanta tana tasbihi ga ubangiji, sara wa kanta yake sosia sosia haka ta rumtse ido hawaye na kwalalo mata a gefen fuska ,dayday lokacin AHLAN ya shigo yana faɗin ''bebe Baki tashi ba har yanzu? Ganin SAHLA kwance tana hawaye tana addu'a yasa shi tahowa da sassarfa ya iso bakin gadon cikin tashin hankali yake fadin SAHLA SAHLA jikinne? Sannu ,girgiza kai kawai tayi alamar to hawaye ba zuba ta hannun ta rike da kai ,hankalin AHLAN yayi matukar tashi ya rasa inda zai tsoma ransa, toilet ya wuce ruwa ya ɗebo a fanfo mai sanyi sosai da towel yazo yana danna mata a kan ,sannu cikin hankali ya fara sauki jikin ta na yin sanyi har wani baccin ya sake kwashe ta
''ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke zuciyar sa na masa zafi miyasa yayi haka da ya san abinda zai faru kenan da bai yi mata komai ba wallahi Allah ya sa ba wannan jarababben ciwon bane mai wahalar sha'ani ya dawo ba ,shi kadai yayi ta raya abubuwa a ransa shima anan baccin ya kwashe shi tunda ba wani ayki garesu ba shi an bashi hutu wajen ayki na wata guda sai ya gama cin amarci
Karfe biyu suka farka dan haka a gurguje ya wuce toilet yayu alwala yana fitowa itama ta farka,jikin kam da sauki yanzu dan haka ta mike itama tayo alwalar,salla ya jasu ,bayan sun idar suka yi addu'a suka shafa.
A hankali ya kalle ta sannan yace ya jikin? Cikin sanyin murya tace da sauki ya AHLAN sai day cikina yana min ciwo sosai.tayi maganar idanun ta na kawo ruwa
''cikin damuwa yace ciki yanzu kuma? Eh ya AHLAN cikina ,
Ok shirya mu wuce asibiti a duba ki kinji? ''to ya AHLAN amma ina tsoron kar ciwon baya ne ya sake dawowa
A'a ki daina faɗin haka insha Allah Bama shi bane da yardar Allah in Allah ya yarda.allah yasa ya AHLAN ta fada tana buɗe Waldrop a hankali.
Hijab ta ciro ƙato cikin kayan auren ta yake dan haka ta saka shi dama ita bata taɓa yafa mayafi ba ta fita tun tana gida.
Kulle komai suka yi na gidan sannan suka fito harabar gidan.
''gyara mashin dinshi yayi ya fitar dashi waje sannan ya rufe gate din fitowa tayi ta hau bayan mashin din yaja su suka wuce asibiti,suna tafiya kamar zata fado dan hajijiya ke dibanta ,kama rigar sa tayi a haka suka isa hospital din
''Kati suka fara yanka sannan suka bi layi babu layi sosai kasancewar yamma ce,
Babu jimawa suka shiga ,yana riƙe da ita kasancewar jiri da take ji zaunar ta yayi kan kujerar dake gaban teburin likitan shima ya zauna a dayar kujeran.
Kallon ta likita yayi sannan yace mai ke damunki?
Cikin ciwo dake murɗan ta tace jiri nake ji ,yan rubuce rubuce yayi sannan yace sai me? Sai kuma ciwon ciki da kai duka ,ok'' yace sannan yayi rubutu , rabonki da al'ada tun yaushe?
Shiru tayi ta sunkuyar da kai domin tambayar tayi mata nauyi gaskiya abin ya bata kunya bazata iya amsawa ba,dan haka tayi shiru.
AHLAN ne yace kwana ɗaya kenan da daukewar sa, sosai ya ringa kallon cikin idonta kamar mai son karanto wani abun amma sai yace''ok ''
Kuje nan baya akwai toilet tayi fitsari ku bada gwaji a lab yanzu za'a baku result sai ku dawo dashi
''to insha Allah mungode SOSAI cewar AHLAN yana miƙewa.
Itama a hankalin ta mike sannan suka fita
*After few minutes*
Suka dawo da result ,suka bawa likita zama sukayi duka ,inda SAHLA ta rike kanta dake sara mata a hankali,
'Bude result din likita yayi ya gama karantawa sannan ya ɗago kansa a hankali yace
'' congratulations bro matar ka na dauke da ciki na tsawon watanni uku babu kwanaki Allah ya dayyaba ya inganta.ya faɗa yana mikawa AHLAN hannu
Wata razana AHLAN yayi sannan yace kai likita mata ta fa SAHLA ce ko day canji suka yi daga can lab din kawo a maida masu su canza amma wannan SAHLA ce mata ta wacce mukayi aure sati daya kenan ya karisa maganar yana kallon likita fuska kamar zaiyyi kuka.
Kallon shi likita yake da alamar tanbaya, sannan yace kana nufin 1 week ago da aurenku?
''of course '' bai cika week din bama Ina ga saura 2 days sake duba result dinnan likita''
Kallon takardar likitan ya sake yi sannan yace , SAHLA Musa tinka ba shi bane sunan? Shekaru 19 haka ne ? Ya tanbayi AHLAN
Yanzu kam AHLAN ya rasa bakin magana sai SAHLA da ya kalla alamar tanbaya ,ganin ta fishi shiga damuwa da tashin hankali yasa yace calmdown bebe mistake suka yi wajen sakawa amma ya za'a yi kiyi ciki wata uku auren mu sati guda? ''hawayen da suka tarar mata a ido ne suka zubo tace ya AHLAN nice mai ciki wata uku din?
''no wasa ne ki bari tashi muje tashi kinji ?
''mikewa tayi kwata kwata ta daina jin ciwon ya tafi bata sani ba ko tashin hankalin ne ya hana ciwon oho.
Mashin dinshi ya tayar ta hau bayan suka wuce wani karamin PRIVATE hospital ya kaita ,irin dau tanbayar farko na wancan likitan shi akayi mata still aka bata gwaji kamar baza tayi ba sabida tana cikin tashin hankali bata ma son jin sunan gwaji daga gwaji kawai wancan likitan zaice tana da ciki dama da kayi aure sai ciki kuma ma cikin wata uku?
Daƙyar day AHLAN yasa ta tayi suka maida result ay Shima tashin farko yace ciki ne da ita wata 2 da sati 3 ,''babu shiri AHLAN ya mike yana faɗin way duk kunsha giya ne kam ko yau ranan haukan likitoci ne ya zakuyi kuce SAHLA nada ciki kuma ma wata uku ,ba kwana 1 ba wata uku'' ,wani kuka ne ya kwace wa SAHLA wanne irin ciki kuma ta shiga uku ,wani rugugin tashin hankali ne ya ziyarci kanta babu shiri ta zube wajen sumammiya jini na bin kafafunta baki daya.
*Gyara shine mace yar uwa daure ki gyara jikin ki ki kasance mai tsafta a kowanne lokaci kasance mai ado da kwalliya da tsaftar jiki ,idan akace tsafta ya kunshi abubuwa da dama, kiyi wanka ki saka tsaftataccen kaya kinyi tsafta amma ki sani adon da kwalliyar bazata cika ba sai da kamshi ,kamshi ba na daki ba kawai a'a harda na jiki ,dole mace sai tana haɗa wa da kamshi ,zamanto mai kamshi ko da yaushe yadda da mijinki ya danno cikin gida kamshin ki ne zai fara yi masa sannu da zuwa,kaya da suka amsa sunansu kaya masu kamshi arha da inganci a tura miki shi duk inda kike kama daga sari ne ko guda dayday kike so cikin farashi maii sauki zaki turara jikin ki gidanki da kuma tufafinki da daddadan turarukan mu masu kamshi muna da abubuwa kamar haka*👇
_Turaren wuta na daki_
_Turaren jiki_
_Turaren kaya_
_humra_
_Maganin gyaran nono_
*Muna da kala kalan turaren wuta iri daban daban da humra musamman humra dinnan ina sake sanar daku yana da matukar mahimmanci,kayan mu suna da sauki da rahusa babu tsada babu tsawwalawa ku kasance cikin aminci tare da mazajenku mai bukatar saya zata iya tuntuba ta ta wannan lambar dan Allah idan baki shirya ba karki bata min lokaci PLS Dan Allah Kayana suna da sauki kuma ga aminci to dan haka ki shirya kafin kiyi min magana*👇
_07059305867_
*MRS ABDULL ce* ✍️

No comments