Breaking News

A GIDA DAYA 9-10


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


      🌹A GIDA D'AYA🌹

🅿️ 9&10


    washe gari...da misalin karfe 8:30 am Khadija ta nufi part d'in Yaya mahmod "hannunta d'auke da flux d'in coffee.

       "ahankali tayi sallama cikin siririyar muryarta".bayan tayi knocking yabata izinin shigowa ciki"kanta ak'asa ta azaje flux d'in agabansa tace".Yaya Ina kwana?"d'ago kansa yyi yakalleta Yana zaune kan kujera"kasancewar yau week end bbu office"lfy qlau."yafad'a Yana ta kallonta"kafin yace "k'arfe nawa zuku fita islamiyya?"still kanta ak'asa tace".sai9:am

     "ok"zubamin coffee d'in"batace komai ba ta zuba mishi"yabi Zara zaran yatsun hannunta, sunsha Jan lalle da kallo"kafin yace". karki sake ki kula ko wane namiji. akwai wani dana aminta dashi Zan had'aku bayada matsala"sosae yabata mamaki akan kalamanshi."to wai Ina ruwanshi data kula samari ko karta kulasu??itafa bata wani son aure...bakyajina?"uhumm!kayi hakuri dan Allah !wlh nima banason samari"ko Yaya auwal d'in sbd yahad'ani da Allah shiyasa natsaya na saurareshi....


"tab'e baki yyi kafin yace"eh ai duk sadda kikaso yin samarin to shine nazab'a miki".


     batace komai ba" tana k'ok'arin tashi aka murd'o k'ofar"atare itadashi suka kalli k'ofar.

*khairat ce*

ansha wanka ,ga eye glass tadad'e fuskarta dashi".wani kicin kicin da fuska tayi" tana jifan Khadija da wani irin kallo"tarik'e k'ugu ta na kallonsu"janye idanunta Khadija tayi ta maida kan Yaya mahmod" dayayiwa khairat kallo d'aya yad'auke kansa.


Ahankali Khadija tace".Yaya Zan tafi cikin gida" ko akwai aikin dazan maka?key yaciro dg cikin wasu keys dake kusa dashi"yamik'o Mata Yana cewa" inkundawo dg islamiyya agyaran d'akin duka"sannan zanzo da abokaina su 3"da k'arfe 4:pm kimana girki....wai Yaya mahmod akan wannan banzan agolar zaka shareni? kanuna tamkar bakasan daniba.cewar khairat tana huci"had'e da kallon khadija tace banza sarkin kwad'ayi itada uwa.....batasan lokacin daya matso gabantaba" saidai taji saukan gigitaccen mari...


cikin b'acin rai yace".na ruwanki da ita? meta miki?" kisani kece agola anan gidan ba itaba"duk ranar dakika koma yunk'urin shiga harkarta Zan baki mamaki wlh .get out! yafad'a cikin tsawa"ita kanta khadijar ta tsorata sosai"

      dafe kuncinta khairat tayi tana hawaye tace".akan wannan abar ka mareni ?harda korata dg d'akinka?wlh bazan yardaba! saina had'aku da hjy daga kai har ita y'ar iskar dake zuwa d'akinka ba'asan me kukeyi ba sai...shiru khairat tayi tana ja da baya da sauri. sbd ganin Yana k'ok'arin tunkarota..da gudu ta fice dg parlourn"


Khadija cikin tashin hankali tace".nashiga ukku Yaya zataje tasanarwa hjy"tafad'a hawaye na zuba afuskarta"damuwarta Kar amusu wata fassara daban .dakuma Kar abin yashafi mamanta"

     *Khadijaaaaaaa*!yakira sunanta "cikin nutsatstsiyar muryansa.yace "kinutsu kiyi shiru" banason kuka kin sani ko?"Yaya dan Allah kaceceni bansan hukuncin da hjy zata yankemunba" da kuma fassara maganar wannan dabansan ko wacece itaba.. (tana nufin khairat)

   shikansa yadai daurene sbd ganin yadda khadijar ta damu."amma bayasan fushin hjy ko kad'an...kallonta yyi yace"kinga karki damu Zan d'auki mataki" muje kitafi islamiyya! yafad'a Yana Kama hannunta....wayyo Allah!wani irin yarrrrrr!yaji ajikinsa had'e da jin wani abu yatsargamishi tundaga tafin k'afa zuwa kansa...ita kanta khadijar taji wani shock"da sauri ta janye hannunta"tanufi k'ofa tana saka takalmin ta.yabiyota Yana cewa". Koda ta tsokaneki bance ki kulataba ,kibarta kinjiko?"dato ta amsa ta fito"sukayi clash da ummi da hjy ta aiko ta Kira Yaya mahmod...


   rik'e ta ummi tayi had'e da cewa"Khadija lfy meyafaru?"


Wannan banzan khairat d'in tazo tana kuka tace" Yaya yadaketa sbd ke ,qkan taganku Kuna rungume da juna.ummi ta fad'a tana kallon khadija.zaro ido Khadija tayi tana salati.

     Ummi tace" ai kowa yasan k'arya takeyi wlh.sbd ansan hakan ba halin Yaya bane"shine hjy tace nazo nakirashi"Khadija na kuka tace ".nashiga ukku ni Khadija! sharrin data Mana kenan?" tafad'a tana sanarwa ummi yadda akayi har Yaya mahmod yakaiga Marin khairat d'in.ummi tace "wlh yamata da sauk'i nasan sbd hjy kebe daketaba"khadija tace". wacece ita dan Allah?"ummi ta tab'e baki had'e da cewa ".y'ar k'anwar hjy ce"Yaya takeso, kuma baya sonta wlh"hjy ce ta tursasashi akan yasota"yanzun dai inta kammala degree d'inta nan da 1 year zasuyi aure"Allah yakyauta kawai Khadija ta fad'a"ummi tace" kijeciki dan Allah karki kulata.in hjy ta kiraki kije kisanar Mata abinda kika sani".kiyi hakuri Khadija dan Allah watarana sai labari insha Allah komai zai wuce ...


 murmushin k'arfin hali Khadija tayi tace".nagode tana wucewa ita kuma ummi tashiga parlourn Yaya mahmod...


Gabanta nata fad'uwa,tadai daure tanata addua aranta."ta shiga parlourn da sallama.hjy da Abba na zaune kan kujera" yyinda khairat ke zaune kan carpet ,kanta ak'asa tana ta kuka...Abba ne ya amsa sallamar had'e da cewa"Khadija zonan!wani fargaba da tsoro taji"amma dole ta daure ta iso agaban abba.ta duk'a tana cewa."gani Abba!


     Abba yace"meke faruwane tsakanin ki da yayanku dakuma khairat??"saida ta furta *la'ilaha illah anta subbahanaka inni kuntu Minal zalim.*

    kafin tace".abinda nasani "Yaya yasakani nakaimishi coffee"bayan nakai harna mik'e zanfito. saita shigo" "nagadai tanata hararata"saina cewa Yaya ko akwai aikin dazan mishi?sai yafara mun mgn"shine tadinga zagina damun gorin ni agolace anan gidan....rufemin baki munafuka! k'arya tayine?cewar hjy  tana hararar khadija".khairat tace". wlh k'arya takeyi ba haka akayiba..abba yahad'e fuska batare daya kalli hjy ba yace".karna komajin bakinki anan.yafad'a Yana kallon Khadija yace".duk abinda yayanku yasakaki kimishi kinji ko?shima yayankine sbd ya Isa dakene.sannan khairat bak'uwace ! bakusan junaba"itace insha Allah yayanku zai aura...sallamar Yaya mahmod da ummi yasaka Abba yin shiru Yana amsa sallamar su.ummi ta wuce ciki"

    Abba yace" Khadija wuce kishiga ciki"tashi tsaye tayi ta wuce"

      Yaya mahmod yazauna kan carpet Yana kallon hjy"ta bankomishi harara"sake gaisheda Abba yyi dukda sungaisa a masallaci da asuba"Abba ya amsa had'e da tambayarshi me khairat tayi mishi yamareta?saigashi bayanin Khadija dana Yaya mahmod yazo d'aya.hakan yatabbatar wa da Abba k'arya khairat keyi.ita kanta hjy taji sanyi aranta da abin bahaka bane.tayaya zatayi sakacin har haka yafaru tsakanin Khadija da mahmod"bacin tasan yaronta mutumin kirkine...to kinji keme zaginta da k'aryatata"Abba yafad'a Yana kallon hjy"shiru kawai tayi sbd batada abin cewa.yaya mahmod yace Abba wani abu tace namata ne?Abba kuwa yashiga mishi bayani ,kamar yadda ummi tayiwa Khadija ad'azun.


   "cikin b'acin rai Yaya mahmod ya juyo yawatsowa khairat mugun kallo yace".I hate u!


Hjy tace "ya Isa kayi hakuri"dg yau kome kake buk'ata kasaka khairat kosu ummi basai kasaka ita khadijarba...Abba yace bazai yuyuba! mahmod tashi kaje"Khadija nada hankali da tarbiya,sbd haka itama k'anwarkace" kasata duk abinda kakeso tamaka"sannan hakima wlh kishiga hankalinki dani zansab'amiki"akanme zaki rik'a nunawa yarinya k'iyayya har haka?sbd kina kishin uwarta ko?"to bari kiji !asma'u nasonki tsakani da Allah"kekuma kin kasa kigane hakan.... tab'e baki hjy tayi tace" nidai banason wata doguwar mgn"Abba bece komaiba. yafice ransa ab'ace.shima Yaya mahmod uffan beceba yafita"hjy taja tsaki had'e da kallon khairat tace"dg yanzun karki koma fad'in abinda baki ganiba"kinga ran alh yab'aci dashi kanshi mahmod d'in"kije kibashi hakuri anjima kina jina?"tamkar ta shak'e hjy haka khairat keji"sbd ganin bbu wanda yagoyi bayanta.cikin  saita kanta tace ".eh hjy zanje nayi yadda kikeso"washe baki hjy tayi tace".yauwa koke fa d'iyata"cikin tura baki khairat tace".to amma hjy ki hanata zuwa sashen sa to.hjy tace".ai banda masaniya ma tanazuwan wlh!"amma angama insha Allah dg yanxun...


Khadija kuwa batasa narwa anty abinda yafaru ba"saitayi shiru kawai tafara k'ok'arin saka kayan islamiyyar ta.dukda abun na nuk'urk'usanta arai.


gaba d'aya duk yaran gidan suka shirya"harda xee suka nufi islamiyya.


*************

Yaya mahmod kuwa  cikin b'acin rai ya wuce parlourn sa"yanajin tsanar khairat na nunkuwa aransa"arayuwarsa yatsani k'arya"shiyasa beyinta,kuma baya shiri dameyinta"hakan yasa yaketa fuskantar k'alu bale a aikinsa na

*jarida*

komai zai faru saidai yafaru amma saiya fad'i gsky.maganin bacci yasha ya kwants"sbd yanason da karfe 1 yatashi yyi shirin zuwa d'aurin auren wani abokinsu"shine yacewa Khadija ta musu girki"dan akwai mutum2"abokansa da sukazo gurin d'aurin auren. zaizo dasunan suci abinci sukoma garinsu"


   Khadija kuwa sai 12:suka dawo dg islamiyya"kitchen ta wuce tasami anty ta sanar mata aikin da Yaya mahmod yasakata."anty tace" to shikenan ai dayake jiya akayo cefane akwai komai...Khadija da mai aikin anty suka tsaya suka shirya lafiyayyen girki"tuni sashen anty yacika da k'amshin girki...fried rice sukayi with pepper chicken"sai dambun nama da snacks.😋


   saidai gaban Khadija nata fad'uwa sbd tsoron taje takai abinci"gashi yace tagyara mishi d'akinsa".

 shikuwa Yaya mahmod Yana fitowa dg sallar azahar"yakoma yad'auki wankan farar d'anyar giznah.ya aza hula saman tattausan gashin kansa."tamkar shine angon sbd kyawun dayayi.lol..kyawun sa da kamalarsa had'e da kwarjininsa sunsake bayyana ajikinsa...sai fitinan nan k'amshi ketashi ajikinsa.duk macen data ganshi saitaji inama inama"😜


har yanufi parking space"saiya tuna da Khadija ko gyaran d'akin yaga bata mishiba"bayaso yadawo da mutane yasameta acan...part nasu yakoma dukda bayaso hjy taganshi"yadai daure ya shiga"bbu kowa aparlourn sai Yaya kabeer da Yaya  Hakeem"suna kallo"gaishesa sukayi ya wuce part d'insu Khadija..bbu kowa aparlourn ,hakan yasa yawuce kitchen inda yakejin motsin mutane"

    Khadija natsaye ta bawa k'ofar kitchen d'in baya"tana had'a coslow!sanye take doguwar riga ta kanti"tafito Mata da coka cola shape nata"kanta sanye da hula, tayi acuci da gashin kanta"

   kalonta yaketa yi tunda k'afar ta harzuwa kanta"itakuwa ajikinta taji ana kallonta"da sauri ta juyo tashak'i k'amshin turaren sa"hakan yasa tahane shine.janye idanunsa yyi Yana gyaran Murya"gaba d'aya duk saitaji kunya"juyawa tayi da sauri bata bari sun had'a ido ba.

"angama shirya komai ne?"muryarta na kirma tace". eh" amma ga coslow nan dana manta banyiba"okay inkingama saikije ki kaimana acan"banaso nadawo nasameki ad'akin kigama da wuri....um um..dama Yaya kayi hakuri, hjy tace" nadaina zuwa ai.hmmmm!Abba yace komai yawuce karki damu kije kinjiko?hjy ta bazatasan kinjeba.dato ta amsa "shikuma yajuya Yana barin kitchen d'in.ajiyar zuciya yasaki sbd bbu kowa aparlourn."yafice zuwa parking space yashiga mota yafita.


Khadija kuwa komai ta had'a acikin trays 3 "harda drinks d cups"fitowa tayi ta wuce waiting parlour"cikin sa'a taga maryam"nahad'awa Yaya Hakeem abinci agabansa"ta zauna kan kujera tana jiran maryam ta gama.saiga hafsat ta shigo" da alama Yaya Yusuf tazo taga ko Yana nan.



"xama tayi kusada Khadija suka Fara fira"har Maryam tagama ,tazo ta zauna kusadasu.alfarmar sukama mata kayan takai sashen Yaya mahmod"ta nema agurinsu"suka ce to suna tashi...


Duk abinda yadace itadasu suka kai" suka kuma kama mata ta gyara bed room d'in da parlourn...kafin suka fito ta rufe d'akin"k'ok'arin tafiya sukeyi"hafsat ta hango Yaya Yusuf zai nufo nan"da alama dg wani gurin yake zai zo yabud'e d'akinsa.


Hafsat tace" lah kujirani dan Allah ga Yaya Yusuf can"Maryam tace." ah ah kedai kitsaya yazo d'in"haka kawai kayi mistake kad'an amaka masifa."ni wlh da Abba zai yarda da hostel nakoma !sai duk yayunmu sunyi aure nadawo"gaba d'aya suka saka dariya...Yaya Yusuf dake k'ara sowa "yabi hafsat da kallo Yana gulmarsu aransa. akan me sukema dariya?Yaya sannu da dawowa !duk suka fad'a atare"fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa.yana nufar k'ofar d'akinsa...wucewa Khadija da Maryam sukayi"hafsat tayi saurin cewa" Yaya wani waje kaje ko?"naga banganka ba."

     Yace "eh "d'aurin auren abokin Yaya mahmod naje."gama sak'onki"yafad'a Yana saka hannu a aljihun gaban rigar sa"yazaro waya toch screem.zaro ido tayi had'e da cewa"wow Masha Allah!yaya nidai ko baby nokia zaka siyamun"dg baya kabani babba.yanzun mama zata tambayeni bansan mezanceba?"in Nokia ce kaga saina kashe inmungama waya"inzan kiraka sai inkuna ko?"k'afeta yyi da ido yanata kallonta"aransa yana mamakin wayonta"sannan yagama fahimta mama jummai batasanshi da hafsat kenan..Yaya kayi shiru? "tafad'a tana kallon sa"sunkuyadda kanta k'asa tayi sbd ganin irin kallon dayake mata.


Ahankali yace"kinfison Nokia d'in?"


Tace" eh"

Yana bud'e k'ofar d'akin yace".to shikenan zansiyamiki da dare"dama nasiya miki sim card"yeeeeeeeeee! tafad'a tana tsallen murna "sai dariya takeyi"dukda tasan wayar ba babba bace"amma tanason tayi ko nokia sbd waya na burgeta inta ganta ahannun Yaya zee"ayanzunma tsoron mama yasa zata hak'ura da babbar"kobayan tayi SSCE saitayi babban...


Shima murmushin yayi yace."gobe fane tafiyar da safe"kai Yaya kabari sai marece mana dan Allah! tak'are maganar da shagwab'a.

      Hafsat kiyi hakuri natafi da safen kinga banaso nayi dare ahanya"kin yarda? yafad'a cikin wata muryar dabatasanshi da itaba"batare data kallesa ba tace". Allah yakaimu to.yace "ameen to kisaki fuskarki mana!nifa wlh Yaya banaso katafi kabarni .kasan dama duk acikinku kafisu sauk'i"d'an murmushi yayi yace" to kibi kowa ahankali karkiyi laifin daza'a miki hukunci"Kuma kimaida hankali a skul. "kinga Kuna last term naku, befi  2 month kuyi exams ba..hafsat dake saurarensa tace." to Yaya insha Allah zanyi duk yadda kace"bara nakoma Kar anemeni.yana murmushi yace" to shikenan k'anwar yayanta"tunda kingama firan dani"lah Yaya bahaka bane wlh"ai zanzo anjima gurinsu Maryam da dare nasan zanganka ko?eh Zaki ganni "yafad'a Yana shiga cikin d'akin.yyinda itakuma ta wucewarta...


##########


Gaba d'aya yaran gidan sun fito zasu tafi islamiyya"adedenan kuma Yaya mahmod yayi horn" me gadi yabud'e mishi get".

    Nurane agdn gaba"sai friends nasu su biyu a back sit..nura yyi murmushi had'e da cewa lah kaga gasu baby (Khadija)can "islamiyya ma zasu tafi kenan?"banza Yaya mahmod yamishi Yana sake had'e fuska"

     shikuwa nura tsokanace sarai yakeyi,sbd yagano cewa Khadija ba Abba bane mahaifinta"y'ar amaryarsace"sannan yanaso yatabbatar da cewa ko Yaya mahmod nasonta ne"shiyasa bayason yakulata"danshi nurama yanada wacce zai aura.


   Fitowa sukayi dg cikin motar"alokacin kuma harsu Khadija sunficema dg gidan."

      part d'in mazan gidan suka wuce"Yaya mahmod yamusu iso parlourn sa.bayan yabud'e k'ofar duk suka shigo.komai yana ajere inda Khadija ta shirya"bud'e komai Yaya mahmod yyi"Yana cewa"kumatso kuyi seving kanku,bbu d'an iskan k'aton dazan zubama komai...Nura yyi dariyar shakiyanci yace harda kaima k'atonne tunda bakada mata"garani tawa matar tana anan gidan"tsaki Yaya mahmod yaja had'e da cewa to namamajo!sarkin sin mata" kayi mana shiru dan Allah.Nura yace"to yayanmu,yyinda Yaya mohmod yamishi banza kawai..bayan yazuma kansa komai yaja gefe yafara kaiwa cikinsa...musbahu d'aya acikin bak'in yakalli mahmod yace ohni abokina halinka na nan?banza Yaya mahmod yamishi ,duk suka saka dariya suna fad'in matarka taga takanta wlh"nura na dariya yace ai anbadashi tuni...


Gaba d'aya kwasar girkin sukeyi sunata santi"nura yace nasanma baby ce tayi girkin nan"musbahu da ahmed sukace gsky ta iya "wannan irin delicious haka"uffan Yaya mahmod bece musuba harsuka kammala cin abincin"sukad'an huta tukum suka mishi sallama"nura nacewa su had'e a office ranar Monday...


Gurin karfe 6:15 Khadija ta nufi d'akin Yaya mahmod sbd ta kwaso kayan abincin dayaci shida abokansa...saidai tana k'ok'arin shiga parlourn sa"zee data  fito dg d'akin Yaya Kamal taganta"saidai ita khadijar bataganta ba..wani irin girgiza Kai zee tayi"ta wuce sashensu bakinta fal da mgn.


Khadija kuwa tana shiga parlourn "baya ciki hakan yasa ta share kawai ta tattare kayan zata fito ,shikuma yashigo cikin parlourn"had'a ido sukayi,tayi saurin sunku yadda da kanta ak'asa"tana wasa da yatsun hannunta"zama yyi akujerar dake kallon ta yace".gobe Zaki rakani anguwa bayan kundawo dg islamiyya"dato ta amsa.yace khairat ta sake tsokanarkine?kanta ak'asa tace".ah ah" yace okay.itakuma ta wuce,yabita da kallo Yana lumshe ido...


Zee na zuwa tasami mama jummai a parlour"Zama ta tashi sbd lokacin sallar magrib yyi"ta zauna jiki asanyaye tace" .mama wlh abinda nake gudu zai faru"da idona naga y'ar iskar yarinyar nan Khadija ta shiga d'akin Yaya mahmod"zaro ido mama jummai tayi had'e da cewa"da gske?


Zee tace "wlh"


Mama tace"d'azunfa  nasami labarin cewa yamari khairat akanta"karfa ace son yarinyar nan yakeyi"hmmmm to wlh saidai Kar ak'ara cewar zee cikin k'unar rai.


Mama jummai tace gobe zuwa Gurin mlm nahayin gada yakamani wlh"amma kafin naje goben saina san yadda nacusawa hjy hakima zancen nan.zee tace"dadai yafi wlh...


    *washe gari*

Tunda aka gama sallar asuba "hafsat ta wuce kitchen"tayiwa Yaya Yusuf cake da dambun naman kaza.sai Gurin karfe 8:3O ta Gama"mama jummai dakebinta da kallon tambaya tace "ke uwar kilbibi duk waye yasaki wannan aikin haka" kin kwashemun nama a freeza?"uhmmmm! Yaya Kamal ne"tab'e baki mama jummai tayi had'e da cigaba da abinda takeyi"hafsat tayi rapping komai ta d'auka ta fito dashi"tana k'ok'arin fita suka had'u da Yaya Yusuf zaishigo yamusu sallama"

     turus tayi ta tsaya tace"Yaya harka shirya ne?Yana kallon ta da kayan hannunta yace "eh "Ina zakije haka?tana murmushi tace".gurinka manah....tsab acikin kunnan mama jummai"muraya k'asa yace kije parking space kijirani nayi wasu mama sallama.dato ta amsa ta wuce ,shikuma ya Ida shigowa parlourn.yaga mama tsaye tana jera kayan break fast kan table"har k'asa yaduk'a yagaida ita"yasanarmata zaitafi"d'an Jim tayi kafin tace". Allah yataimaka ya tsare hanya"ya amsa Yana fitowa.tsaki mama jummai taja had'e da cewa wlh jikinki zqi gayamiki inkindawo"dama shinekikayiwa kayan dad'i haka?

 kikamun k'aryar Kamal yasakaki".


Khadija kuwa yau Yaya mahmod baice takaimishi komaiba"duk saitaji tanason zuwa ko gaidashi tayine"hijab nata ta saka iya gwiwa ta nufi d'akin sa"

       tana k'ok'arin shiga ta hango khairat nata kallonta"gabanta taji yafad'i"tanajin kodai tafasa shiga kawai...

    Yana zaune kan carpet da laptop agabansa Yana latsawa"jikinsa sanye da farar jallabiya.tayi sallama akofar parlourn"kasancewar a bud'e k'ofar take.amsawa yyi batare daya d'ago kansa ba.nesa dashi ta tsaya tace".Yaya Ina kwana?lfy qlau"yanzun da zanma saka akiraki munke girkin jiya yayi dad'i nagode..tayi mamakinsa sosai"murmushi kawai tayi kanta ak'asa tace".bara nakoma dama gaidakai nazo nayi ne"kafin yace wani abu sukaji muryan hjy tana cewa gsky khairat innaje Naga yarinyar nan bata ad'akin nan Zan sab'amiki" sbd  jiyama haka kika Mana k'arya"shiyasa nace bara nazo da kaina....✍️😳🥱🙄


Comments kawai guys🥰🤗

No comments