SAI A LAHIRA 11
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 11*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan
haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
TUSHEN LABARIN
........Azumi macece masifaffiya Kuma me masifar son kudi shiya masifar Tata ke hauhawa Bata Kuma ragewa kowa in har kaga ta ragawa wani to tabbatar tana ganin shi da wani Abu Wanda zata karu da shi Amma bayan haka Bata ragewa kowa ita kadaima masifarta takeyi bare Kuma a tabo ta. Sai Kuma akayi sa a mijinta mutum ne Mai sanyin hali da Rashin son magana shiyasa idan kaji yadda Azumi ke tusa shi gaba da sababin ta sai kayi zaton danta ne ba mijinta ba
Haka zatayi fadanta ta Kare ba zaice Mata kanzil ba in ma yace din to baya wuce Allah ya Baki hakuri daga haka ba zai Kara tofawa ba in Kuma yaga abin nata ya girmama sai ya fice ya bar Mata gidan sai in dare ya nisa zai sadado ya shige dakin shi don ya San ko abinci ba zata bashi ba haka Kuma tun farar subahi zai fice kafin ta fito hura wutar kayan Sana arta sai dai ya Aiko da Dan abinda ya samu na cefanen gidan Wanda shima wata masifar ce zata girka.
Mijin Azumi dai lamis tsohon ma aikacin gidan ruwa ne Wanda yanzu ya aje aikin kusan zaune ake hannu rabbana sai Dan abinda Ubangiji ya zano Rabon shiyasa Azumi ke Tata mishi Rashin mutunci
Yaransu uku ne Khalil dake can kaduna gidan kanin malam lamis din wato baba shitu Wanda shi yake da rufin asiri daidai gwargwado saboda shi din Dan kasuwa ne shiyasa ya dauki Khalil ya hada da wurin shi mujahid ya turasu karatu jami ar ahamdu bello dake Zaria Kuma Yana agazawa ya'yan shi da Dan abinda Allah ya hore saboda yasan halin da yake ciki har da halayyar matar shi Azumi
Bayan Khalil sai nafisatu dake bin Khalil sai uzairu dake bin nafisatu daga shi Kuma Azumi Bata Kuma haihuwa ba
Sai nafisatu tazamo cikin nemawa Azumi kudi kamar zata Nemo Mata kaff kudin dake cikin garin katsina saboda tsabar talla. Sai akayi sa a nafisatu da Khalil suka gado sanyin halin mahaifin su malam lamis inda Kuma uzairu ya dauko halin Azumi shi yasa take juya su yadda take so musamman nafisatu da ta kasance mace kullum cikin talla take maganar karatu kuwa sai nafisatu ta share sati biyu bataje Boko da islamiya ba duk da malam lamis baya son tallar da nafisatu keyi ba Amma yasan bai Isa ya tofa ba bare ya Hana don haka ya zuba ido
Sai dai akace yau da gobe Taki wasa yau da goben da nafisatu ta Gane muhimmanci karatu sai ta fara nunawa Azumi sai taje makaranta ta dawo ko zata Kara fita talla bayan siyar da Koko da takeyi tun asuba
Azimi ta soma sababi har dai takai da duka Amma nafisatu ta shanye Dole Azumi ta zuba Mata ido har dai nafisatu tayi nasarar Daina fita talla sai dai siyar da Koko kawai Wanda shi Azumi tafi bawa karfi shiyasa sauran Sana o inta ta barsu cikin gida
A yau garin an tashi da hadari tun asubahi yake cida inda Azumi ke gurfane gaban murhu zata sheka Koko
Cikin sa a tana gama sheka kokon iska ya taso Amma sai cewa nafisatu take tayi maza ta fita kafin ruwan ya sauko
Wani bakin ciki ya turnuke malam lamis ganin mahaukaciyar matar shi ke kokarin tura yarta mace cikin duhun asubahi nemar Mata kudi Amma Babu yadda zaiyi yanaji Yana Kuma gani nafisatu ta fice inda uzairu ya daukar Mata bokitin ita Kuma tabishi da robobin Aiko kafin ma su Isa inda take siyar da kokon ruwa ya sauko da karfin shi garin saurin da uzairu keyi don ya dawo ya koma baccin shi nafisatu ta Kama bokitin don ta sauke mishi Aiko Bata rike ba ya sakar Mata sai ko Koko ya kife kasa kif
Ya Kuma juyo abinshi inda ya shaidawa Azumi Wai nafisatu ta zubar Mata da Koko ya zube kasa
Aiko nafisatu ta shigo gidan inda ta iske sababin Azumi inda Kuma malam lamis ke ta godewa Allah da zubewar kokon.
"Dama tunda Kika tashi ayau kike nemar min jafa i tunda Baki so zuwa tallar ba to kin zubar sai kizo mu rungume hannuwa tunda ai kinsan ba komai ubanki ke bani ba " in yayi kokari ne zai dunguro min Dan kilo Ni zanyi na kayan Miya to sai kizo idan ya dubguro min garin Zan raba in Baki naki sai ki nemi na Miya tunda kema zuciyar ki ta mutu ba Zaki zage mu nemi kudi ba to Bismillah Dani kuke magana
Haka ta wuni tana zubar da ruwan tijara inda nafisatu ta fice makaranta ta bar Azumi na sababi shima malam lamis ya fice ya bar gidan fitar shi yayi daidai da zuwan dala me gero wadda Azumin ke dauko bashin hatsin
Aiko Azumi ta rattabo Mata yadda nafisatu ta zubar Mata da Koko....
Dala ta tareta
"To sai akayi Yaya don an zubar Miki da Koko sai akace raba asarar zamuyi ko Yaya?
"To Ni asara ko ta yawun barci banyi kudina Kuma yanzu Zaki bani su in Kuma Babu wallahi gadonki Zan kwale ...
"A a ba haka za ayi ba dalar duniya yanzu wani hatsin Zaki bani in yaso sai mu tashi lissafin....
"Kar ki yaudare Ni don ba yarda zanyi ba idan kuwa na Baki kayana aka Kuma samun akasi to zamu Budi a turbar da ba zamu Kuma gaisawa don Wallahi ga Yan sanda Zan kaiki sai an kulle ki akan kudina....
"Bama za ayi hakan ba ke dai bani kawai zamu tashi lissafin insha Allah
Haka Azumi ta lallabeta ta karbi wani hatsin aka koma Sana a sai dai salon da Azumi ta dauka shine kullum zata bawa uzairu kudi ya siyo Mata nama da yogurt taci abinta ta Kuma ce kudin dala sai ta samu karshe ma sai ta sauya wurin karbar hatsi inda ta share sati biyar Bata Wai wayi dala ba har dai dalar tazo afusace don ayi uwar watsi ita da Azumi don ta Gane yaudarar ta Azumin ke yi......

No comments