Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 1-2

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

   

           🅿️ 1&2


 *_Alhamdulilah gashi Allah yasake had'amu a wani saban novel Allah yasa nafara a sa'a Allah kakareni da aykata ba dedeba a cikin wannan book d'in Allah kasa yadda nafara lafiya nagama lafiya Ameen_*




```'Kir'kirarran labarine daga zuciyata  taimakon Allah nikenema akan wannan labarin Allah karka barni da kaina dededa 'kiftawar ido bannemi  shawarar kowaba dan Allah kar wanda yayimin shisshigi cikin labarina please banason hayaniya wanda  yaga bai mishiba bance dole yakarantaba balle adinga 'kananun maganganu  akai nagode sosai masoya```





🅿 1 & 2




BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM




*G* udu sukeyi sosai cikin 'kasurgumin daji amma duk da haka hannuwan su narike dana  juna tsayin lokaci suna gudu 'kara dattiyuwar matar tasaki had'ida fad'uwa cikin kuka yarinyar dake ri'ke da hannunta ta durkusa tace 


"mama dan Allah kitashi sun biyomufa ? "


Cikin wata irin murya matar tace 


"Rayhana inamai umartarki da kibar gurinnan kafin su iso nikam daga nan bazan iya cigaba ba kalli 'kafata macijine yasareni kuma nasan izuwa yanzu dafinshi yagama shiga cikin jikina"


Kuka Rayhana tasaki sosai kicikicin d'agata tashigayi jin 'karar harbin bindiga yasa tadaka mata tsawa 


" Rayhana idan baki tafiba amatsayina na mahaifiyar ki banyafe mikiba zakibari kashemu dukane kije aduk inda kike kinatare da Allah dakuma Addu'a ta kitafi nace "


Wani irin kuka Rayhana tasaki sumbatar hannun mahaifiyar tata tayi tace 


" in sha Allah zamu sake haduwa  Mama mama a ina  danginki suke ? zan ..... "


" Nace kibarnan Rayhana tafi cikin kariyar Allah 'yata "


Juyawa Rayhana tayi aguje cikin duhun bishiyoyi tabuya amma tana iya hango mamanta  wasu 'kattine majiya karfi  ko wannen su hannun shi ri'ke da bindiga cak suka d'auki mahaifiyar ta suka juyada ita jin 'karar Harbin bindiga yasa Rayhana juyawa aguje cikin dokar jejin tsayin lokaci tana gudu dede wata 'katuwar bishiya tatsaya tana sauke numfashi 


Hannuwanta 2 tad'aura saman kanta tasake saka wani irin iho jin sautin kukan jariri yasa Rayhana saurin waiwagawa cikin sauri tafara duddubawa tanabin sautin kuka cikin sa'a idanunta sukayimata  arba da kyawawan jarire twins masu matu'kar kyau cikin kyawawan kayan sanyi 


Cikin gigita tashiga waigewaige kozataga wani amma babu alamar kowa wani irin sauti taji 


" keeee Rayhana kidauki wa'innan Twins d'in mugunta da makirci yasa  anrabasu da iyayensu kituna kalmar mahaifiyar ki idan kika ceci wa'innan yaran to zamu saka idanu akan mahaifiyar ki kuma in sha Allah zaku gana wata rana


Mahaifin wa'innan yaran d'an babban gidane  kuma tsayayyan namiji Rayhana kishiga duniya neman mahaifin su amma an kashe mahaifiyar su kuje tareda kariyar Allah sunayensu Faruq da Haydar kiduba abayan Faruq akwai wani ba'kin tabo tananne kad'e zaki iya banbance su sabida tsananin kamarsu nabarki lafiya "


Cikin rawarjiki Rayhana tadu'ka a gabansu cikin kuka tace 


" wannan wace irin jaraftace yara har 2 kaddara tabani darana tsaka ina yar 19 years nashiga Uku " 


'Daukar  yaran tayi tana d'aukarsu sukayi shiru goya d'aya tayi tasa'ba d'aya wani 'karamin box tagani daga gefan inda suke d'auka tayi batare data bud'eba tacigaba datafiya  sosai tagaji gashi har yanzu takasa hango titi babu motsin d'an Adam ko kad'an 


Duhu taga yamamaye garin d'aga kanta sama tayi wani irin hadarine yahad'u gagarumi tuni jikin Rayhana yafara rawa sabida ita Allah yayi mata tsoran hadari waige waige tafarayi wata bukka tahango d'an nesa da'ita cikin sauri  tanufi gurin addu'a tatsaya  tayi sannan tashiga katifar rimice a cikin bukkar se 'kwaryar nono rufe da faifai dawata fitila sagale daga sama bakin bukkar da asabari kwantar da Faruq tayi sannan ta kwance Haidar shima ta  kwantar dashi wata irin wal'kiya akayi cikin sauri tasauke asabarin takunna fitilar komawa tayi tazauna kan katifar rimin tazubama yaran ido 


Wata irin matsananciyar  soyayyar su taji cikin zuciyar ta Afili tace 


" ikon Allah  yauga Rayhana dayara batare datasan ina tadosaba amma wannan yaran dagani iyayen su ba 'yan wannan 'kasar tamuta ta Cameroon bace sunfi kama da 'yan yankin  Southerly Asia Allah kasadani da iyayen wa'innan yaran  nahuta Waiyo mama Allah yakareki daga sharrin mugun mahaifina "


Wasu irin hawayen ba'kinciki sukashiga gangarowa daga cikin idanun ta bud'e wannan box d'in tayi wani ring tagani mai matu'kar kyau dagani zaiyi tsada se wasu d'aurin kud'i amma ba irin na 'kasar Cameroon d'in bane maidasu tayi cikin box d'in tarufe tagumi tayi zuwacan tace 


" dole nayi binciken wa'innan kud'in nawace 'kasane dole zai zama anan mahaifin farooq da haydar yake zanje kowace 'kasace dan neman shi nikam daga yau Farooq da Haydar aguna sun koma Sudees da Sureem "


Wata irin tsawa da'akasaki yasa Rayhana saurin saka kanta cikin cinyoyinta tuni jikinta yad'auki rawa addu'a tashigayi akan Allah yasa wannan ruwan yad'auke cikin sauri 



" Banayin farinciki idan bangankaba Sojana banajin dad'in kalma idanba takaba babu wanda ya'iya furta haruffan sunana naji babu gyara se kai Sojana "


Waige waige yafarayi yana neman inda zaiganta amma babu alamun ganinta sede murya komawa yayi yazauna yadafe kanshi idanun shi nafitarda siraran hawaye sakejin  muryarta yayi 


" mai nike gani nafita daga idanun Sojana ? a'a karka bari rashina yasa kazama mai raunin zuciya tsayayyar zuciya gareka karta raunana dan rashin Nabila hawayenka masu matu'kar tsadane ba'kinciki ciki yayi 'kad'an yasamesu sede farinciki Sojana ka kalli Farooq da Haydar inada tabbacin zasu wankemaka rad'ad'in rashina dan nikam bazan dawoba ba'kiya sundatse igiyar dake tsakanina da kai Sojana sun datse  rayuwar Nabilar ka n....... "


Mi'kewa yayi cikin sauri cikin dakakkiyar murya yace 


" My Nabila 'karya sukeyi bazamu ta'ba rabuwaba sekin dawo gareni konazo na riskeki babu amfanin rayuwata idan babu Nabila sun rabani  dake sun rabani da Twins d'ina taya zan'iya rayuwa My Nabila kizo mukoma gida kina......... "


Amatu'kar furgice yatashi gawata irin zufa data wanke fuskar shi wani irin mugun kallo yawatsama wanda yatasheshi daga baccin tashi yayi zaune yajingina da fuskar bed d'in yana sauke ajiyar zuciya ruwa mai sanyi yami'ka mishi babu musu ya'amsa yasha duka yashanye ruwan shiru na tsayin lokaci sannan yace 


" haba Muzaffar yakamata karage wannan damuwar  kayarda Nabila tamutu bakuma zata dawoba wanda yafika sonta shine yad'auki abunshi taya zakakasayin tawakkali ? katashi maimartaba yanason  ganin mu a babban parlour "


Tsaki Muzaffar yaja sannan yasauka daga bed d'in hanyar toilet yanufa seda yakusa kaiwa yatsaya juyowa yayi yace 


" Mu'azzam kasani Nabila bata mutuba dan har abada tananan araye cikin zuciya ta "


Idasa shiga cikin toilet d'in yayi binshi da kallo Mu'azzam yayi ya girgiza kai tashi yayi yafita yana jinjina girman soyayyar da Muzaffar yakema  Nabila  kai tsaye babban parlour yakoma d'aukacin iyalan masarutar HAYAT suna cikin babban parlour 


MASARAUTAR HAYAT KENAN wadda ke cikin 'kasar BIHAR  


Sarkin masarautar Sarki Abdurrahaman sarkine adali mai tausayin talakawanshi yanada mata 2 


Sarauniya kilishi itace uwar gida tanada yara 7 Ahmad Abubakar Sumayya se yan 3 Muzaffar Mu'azzam muzanbil se auta Zahra  


Se Amarya Hamdiyya  yaranta 3 Aminu samir maimunatu 


Se 'kannnashi su 2 Yusuf da  Idris matar Yusuf tanada yara 4 kabir jamil Arfat Jidda 


Matar Idris tanada yara 5 jafar Samha Nuraddin Zainab jamila


Mahaifin su yarasu tun bayan wasu shekaru se mahaifiyar su Ayna masifaffiyar tsohuwa kenan magana d'aya idan tayi babu canji dole abi takafamusu dokar 'kin auran bare se 'yan gida komin isarka baka isaba  Muzaffar shine yafara karya dokar kakarsu shiyasa basa shiri har yanzu  


Lokacin da Muzaffar yaje wani ayki Egypt yahad'u  da Nabila Allah yad'ura mishi mutuwar son ta bai koma Bihar ba seda Nabila matsayin matar shi lokacin da Muzaffar yazoda Nabila matsayin matar shi babu wanda  baiyi mamakiba  sabida shi bashida ra'ayin mace cikin rayuwar shi Arfat kuwa tasha kuka kamar ranta zaifita sabida tsananin son datakeyima Muzaffar 


Ganin irin son da Muzaffar yakema  Nabila yasa kowa yatsaneta cikin 'yan'uwan shi mahaifiyar shi Sarauniya Kilishi ita kad'e takeson Nabila se maimartaba amma baya nuna hakan sabida mahaifiyar shi duk tafi kowa tsanar Nabila 


ganin Muzaffar yayi gaban kanshi yasa aka shirya auran sauran 'yan uwan nashi an had'a Mu'azzam da Arfat Mu'azzam yana matu'kar son Arfat amma ita ina hankalinta yana kan Muzaffar har izuwa yanzu tsawon 3 years kenan dayin auran su amma har yanzu babu abinda yashiga tsakaninta da Mu'azzam shi ya'ki tunkararta sabida miskilancin shi ita kuma ta'ki sakin jiki dashi 


Shi kuma muzanbil Samha aka bashi wadda tana matu'kar son shi amma shi bata cikin tsarinshi ko kallo bata isheshiba balle  wata ma'amala 


Sauran yayyan nasu  suma haka aka musu amma suna zaune lafiya cikin soyayyar juna  


Muzaffar yakasance Soja mai babban matsayi  miskili kuma mai zafin zuciya bajin shakkar kowa 


Mu'azzam doctor miskili amma mai sanyin hali ga tausayi 


Muzanbil Lawyer mai masifar jan aji ga mugun wula'kanci yafifita  aykinshi akan komi narayuwar shi 


Tunda aka kashe Nabila aka kuma sace yaran data haifa bayan 1 months da haihuwar su  Muzaffar yadena shiga harkar kowa dama ya kasance mararson magana yasake zama maizafi akan kowa 


Zahra autarsu an auradda ita ga Aliyu yaron ma'kwafciyar masarautar su wato masarautar  Yazeed bisa umarnin kaka wanda  har yanzu babu wanda  yasan dalilin yin haka 


Akwai kishi mai zafi tsakain Kilishi da hamdiyya duk abinda jakadiya tagani agurin Kilishi setakaima hamdiyya gulma Hamdiyya tanajin mugun haushin 'yan 3 Sarki watosu Muzaffar sabida yadda sarki yake mugun sonsu duk cikin yaranshi  Yusuf yana matu'kar hassada akan sarautar sarki danshi bai'ki  yamutubama shi yahau saman kujerar dan acewar shi baiga yaron daya isa yahau saman kujerarba bayan mutuwar sarki ba seshi 


Shiko Idris matar shi ita ke zugashi amma dan tashi babu ruwan shi da shi'anin mulki yana d'aukar shawararta sabida yana tsananin sonta 


Akwai mugayen munafukai a fada musamman wazirin sarki da wambai   


Masarutar Yazeed masarutace mai cike dazalinci izgili da rashin sanin darajar d'an adam 3 dayin auran Zahra ba'kar  wahala takesha cikin wannan masarutar babu mai 'kaunarta har shi Aliyu mugun wula'kanci yakemata 'kanwar shi kad'ai take tausayin ta amma ba'a bari ta taimaketa 


Sarki Yazeed mugun sarkine baya 'kaunar cigaban masarutar HAYAT akwai gaba mai tsanani tsakanin masarautun tunta kakanni yanada mata 2 da yara marassa tausayi irin shi mahaifin shi yana raye kuma shine yake sake hura wutar gabar masarautun 2 wannan kenan 


CIGABAN LABARI


Can 'kasan ma'koshin shi yayi sallama cikin parlour neman guri yayi yazauna wani irin kallo Arfat tabishi dashi tanasakejin muguwar soyayyar shi cikin zuciyar ta mahaifin shi ya gaida da mahaifiyar shi se 'kannan uban nashi daga haka yayi shiru 


Rai 'bace Abubakar yace 


" kai Muzaffar bakaga kaka bane kumaga su Ummi koda mubaka gaidamuba  ay suyaci ka gaidasu ko "


Cikin masifa kaka tace 


" ay yafagaidani tunda banida mtunci agunshi kaima munafiki ay kanaganin shima Muzanbil baiko kalleniba shima Mu'azzam cikiciki yagaidani duk bakace komiba se akan wancan mugun Sojan dakasan dama ba gaidanin zaiyiba "


Dari Ahmed yakuntse ahankali yace 


" kaimade Abubakar Allah ya'kara maka ay kasan halin kaka to sumumu kasau wane irin halin gareni ? najika sarai ay gara Abubakar kai dayake dama d'an babu ruwanane ay kayi shiru bakace komiba anamin d'ibar albarka   "


Cikin sairi maimartaba yace 


" kuyi ha'kuri Hajiya ku kuma karnasakejin komi kunji nagayamuku "


Addu'a maimartaba yagabatar sannan yafara jawabi 


" kai Muzaffar dankai muka zauna ana yakamata kad'angana kasani Nabila tariga tabar duniya bakuma zata dawoba abinda yakamata musa agaba shine waye yasace Farooq da Haydar kuma ina zamugano su "


Tashi kowa yayi yaibayani itako ko ta'be baki tayi tace 


" nifa babu shawarata acikin gano yaran yarinyar datasa Muzaffar karka dokata dan haka kai Abdurrahaman karkasake kirana a irin wannan zaman " mi'kewa tayi tanufi hanyar fita daga parlour itama Sumayya cewa tayi 


" Allah yahuci zuciyar mahaifina akan maganar dazanyi  yanzu ina ganin anemama Muzaffar maganin sammu dan tunlokacin dayazo da Nabila nasan tariga tagama asiranceshi amma Momy ta'ki amincewa  dazancena gashinan har yanzu asirin yana tasiri akan shi asake yimai aure kawai nasan zai manta da waccen banzar Nabila k........... "


" ya'isa haka Aunty Sumayya tabbas kinci darajar kina gaba dani dabahakaba wallahi sanasa kinyi nadamar furucinki akan my Nabila  Allah ya'karamaka lafiya mahaifina ka gafarceni amma muddin akamin aure wallahi se anyi danasanin haka aurena nafari babuwanda yamin balle yanzu dana datse maganar aure cikin rayuwa ta ko ada banida ra'ayin mace se Nabila balle yanzu da babu ita aduniyar ku nikam har yanzu Nabila tanacikin duniyata mahaifina idan anyimin izini zantafi  "


'Dagamai kai maimartaba yayi dan shi kanshi yana mamakin irin halinda Muzaffar yake ciki yanzu barin parlour yayi rai 'bace sallamar kowa akayi cikin sauri Muzanbil yake shirin fita cikin sanyin murya Samha tace 


" Yarima kadaure kayi break kafin kafita nagama had'ama komi yana parlourn 'kasa a dining "


Jin yayi shiru babu alamar magana dan dama tayi tsammanin haka zagayowa tayi tagabanshi  cikin tsoro take hannu tafara gyaramai 'kwalar rigarshi   cikin 'bacin rai yasa hannu yawanketa damari had'ida ingizata azafafe yace 


" idan kika sake gigin yimin irin wannan senayimiki  abinda yafi wannan "


'Dayar rigar yad'auka da bag d'in shi yafita afusace kasa mi'kewa Samha tayi sabida tsananin ba'kincikin daya mamaye zuciyar ta 


A'bangaran Mu'azzam kuwa yana shiga yazauna kan cushion a parlour yanajin wani irin ciwon mara shigowar Arfat yasashi lumshe idanun shi sabida bayason idanun shi susauka akan surar jikinta dan karta 'karamishi zafi  


Kallon shi tayi cikin kiss tace 


" Doctor yau babu zuwa hospital d'inne ? "


Gyara kwanciyar shi yayi batare dayace mata komiba d'aga kafad'a  tayi alamar bai shafetaba   cikin zuciyar ta tace 


" inama Muzaffar ne kwance cikin parlour na matsayin miji dana shayar dashi soyayya tamusamman "


Daga Al'kalamin ✍🏻

No comments