Breaking News

SAI A LAHIRA 8


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

                *🅿️age 8*

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




*_Masoyan wannan littafin sadaukarwa gareku Allah ya bar kauna na gode_*





........Ta kalleshi da wani matsiyacin fushi afuskar ta a yau taso ta zubar da hawaye Amma zuciyar ta asoye da wannan bakin cikin kawai sai ta jawo center table ta kwantsama mishi aka  inda gilashin ya tarwatse akan shi har wasu buraguzan gilashin suna nutsewa cikin kanshi sai dai ita da kanta ta tsorata da yadda taga jini ya fantsama a dakin don in har batayi karya ba har kwalwar shi ta hango don haka ya zube adakin sai dai bataji ko dar ba matukar hakan suke nufi to itama hakan take nufi da kashe du daya bayan daya me ma yasa take Bari suna Shanta banza batare da ta illata su ba?


Aguje bashir ya shigo dakin saboda Jin ihun da aka fasa Aiko ya iske mugun aikin da baby ta tafka karisha ma ta shigo tana fadin yau mun SHIGA UKU me DUNIYA Amarya na son karar Mana da masu DUNIYA bashir shida su karisha da sauran abokan shi masu DUNIYA suka fice da bangis zuwa Asibiti sai dai kafin ma su Isa asibitin Rai yayi halin shi saboda jinin da ya hade da kwakwalwar shi don haka suka dawo da gawar shi Kai tsaye suka bude asirtaccen dakin suka saka gawar shi inda bashir ya shigo dakin baby wadda ke ta sharar kuka tamkar wadda akayiwa mutuwa 


Cikin fushi sosai yake inda ita Kuma take cikin radadin zuciya da son ayi mutuwar kasko ya dubeta da Yana zare ido

"Wannan yazamo na karshe da Zaki  Kuma saka wani makami kiyi dalilin kashe min abiki don kawai sun nemi wani Abu da nine na yarje musu gashi Nan kin kashe min bangis ga Steven can Yana jinya duk don sun nuna yabawar su akanki to in Baki sani ba ki sani Ni na yarda na amince musu akan ki So kar ki Kuma yi min haka ke din iko nace Kuma na Basu dama saboda ke kin San yadda nake girmama abotar mu Babu Kuma abinda ba Zan iya yi musu ba Raina ma fansa ne gare su Ni naganki na auro ki da ace daya daga cikin su zai CE Yana sonki ko in sadaukar mishi dake da zanyi hakan don ki Gane yadda Nike girmama su......

Ya cakumi kwalar rigar shi ta hade a hannunta 

"Allah ya tsine maka idan baka kashe Ni ba . Yanzu ne na soma daukar rayukan su muddin zasu sake nuna min halin dabbancin su kafin kaima ka biyo bayan su na tsaneku na tsani ganinku......


Yayi saurin tareta ta hanyar hade bakin su Yana kissing dinta kafin ta kwace tana dura mishi ashar 

"Ai Ni ashirye nake baby ganin bayana sai dai ko idan najuya zanyi tafiya Amma ba kamar yadda kike nufi ba....


"To ka rubuta ka ajiye Ranar da nayi maka sanadin barin duniya zaka tabbatar da shirinka bai shiryu ba....


Ya juya ya bar dakin inda tabiyo bayanshi ta maido kyaure ta rufe bam


Sai dai hankalin ta bai kwanta ba don gidan ma gaba daya tsoro yake Bata 

Azaton ta zata ga sunyi Jana izar bangis da suka kawo gawarshi agidan Amma har tsayin kwana biyar bataga an bude dakin ba bare afito da gawar aje abinne sai ta Kara SHIGA rudani

Iya ta shigo kawo Mata abinci kamar kullum tana ajewa tajuya tana dab da ficewa ta kirata 

"Iya tsaya don Allah

Iya ta juyo kamar ba zata dawo ba sai Kuma ta dawo kamar a tsorace


"Kina bukatar wani Abu ne hajiya? "Haba iya Wai bakin ki baya yi Miki tsami ne da wannan shirun da kike Koko tsorona kike da ba Kya son Zama muyi magana? 

Iya ta soma waige tamkar tana tsoron wani ya shigo har dai ta tabbatar Babu me shigowa kafin ta sauke ajiyar zuciya


"Hajiya ai lamarin ne da ban tsoro Kuma an gargadeni da hakan ne shiyasa Nike kokarin kiyayewa


"Haba iya mu biyu cikin gida Amma daga gaisuwa Babu wata fira saboda Allah?

"Dama tambayar ki zanyi game dame gidan Nan Ina so don Allah kar ki boye min komai duk da na fara gani da idona.........

Kiyi hakuri hajiya an haneni da tona asirin gidan Nan an Kuma CE idan wata magana ta fito ta bakina to abakin Raina  abinda kawai Zan fada Miki shine kiyi ta addua don ina me tabbatar Miki da Baki da mafitar da tafi addua a yanzu domin kuwa kin fado cikin wani hadari Wanda Allah NE kurum zai fidda ke sai Kuma addua  tana gama fadin haka ta Mike da sauri ta bar Mata dakin inda baby tabita da kallo har ta fice inda gaban baby yayi wata matsiyacin faduwa me iya ta sani Wanda har ake Mata barazana da Rayuwar ta haka don ta Fadi? 

Sai taji Bata da mafitar da ta wuce tabi bayan iya ta lallabeta ta sanar da ita abinda tasani ko don ta san irin Shirin da zatayi akan hadarin da take fada don haka sai ta fice daga dakin aguje tabi bayan iyar duk da Bata San taka maiman dakin ta ba Amma haka tayi tayi har tayi nasarar zakulo iyar wadda Bata boye tsoron da tayi ba tabita da kallon ki rufan Asiri 


"Iya ki taimakeni don girman bintu RASULU ki fada min abinda Kika sani akan gidan Nan da masu gidan Nan.....


Iya ta katseta a rude

"Ki rufan Asiri hajiya don Allah kar kisa inyi ta Raina Baki ji na fada Miki an gargadeni da tona asirin kimai ba? Don Allah ki bar wannan maganar indai ba kin gaji da ganina ina Rayuwa ba

Ta soma tura ta alamar Bata ma son agan su

Baby ta riko hannun iyar har zuwa daki Inda ta soma hilar ta sai dai tsohuwar taja ta kafe kan an gargadeta da rufe sirrin gidan da masu gidan 

"Iya Yaya zakiji idan jikarki ko yarki tashiga irin halin da Ni na SHIGA? Shin iya ke ba musulma bace dake fatan ceton manzon Rahama? Shin iya Baki San matsayyin taimako ba ? Maganar da Zaki fada min ba mu biyu kawai ta shafa ba? To na rokeki kiyiwa Allah da darajar magabatan ki ki amsa min abinda na tambaye ki


Tsohuwar ta sauke ajiyar zuciya kafin tace

"To shikenan hajiya Zan amsa Miki abinda kike son tambayar Amma kafin Nan kema zanyi Miki wasu tambayoyi ina son ki amsa min su ta yadda Zan fahimci matsalar ki........

Sukajiyo takun tafiya inda tsohuwar ta rude har fuskarta ta nuna hakan sai kawai ta shige wata kofa ba tare da shawara ba....

No comments