Breaking News

FURUCI 5-6

🅿 5 to 6

Kasa komawa baya *Iftahal* tayi kuma bata'karasaba ganin bashida niyyar tashi yasata 'karasawa akan dole cikin sand'a take tafiya gawani irin bugu da zuciyar ta keyi shiko *Maher* jawoma kwalin sigarin shi yayi yazari 1 yakunna yafarasha ahankali Iftahal tad'auki abincin tajuya cikin sauri takoma bedroom dasauri da sauri takecin abincin sabida masifar yunwar datakeji rurin wayarta yasata razana saurin

d'aukar wayar tayi ganin Kiran mahaifinta yasata razana sosai har takatse batad'agaba sabida tsoro da fargaba seda  yakira yakai sau 3 sannan tad'aga


Tun kafin tayi sallama mahaifin nata yafarayin magana afusace 


" Lalle Iftahal kinbani kunya wato ashe zaki'iya yin aure babu sanin iyayenki gaskiya kinbani mamaki kin zubarmin dakimata kinsan da al'kawarin auran Zayyat akanki ko amma shine kikayi min irin wannan cin mutuncin to kisani daga lokacin danasan kinyi auran ra'ayi nacireki Cikin jerin yarana daga yau babu Ni babu ke Iftahal ma'kudan kud'in dakika amsa nasadakin ki sun isheki hidimar karatun ki sauran hidimar ki kuwa tanaga Attajirin mijin ki  Iftahal daga yau kisa aranki cewa ked'in marayniyace sabida kinriga kin kashe iyayen ki tun lokacin da'aka d'aura auran ki shikuma Zayyat zan musanyamai da Aunty ki Shukura duk da tagirmai shi nasan zatayimai biyayya sabida Shukura bata ta'ba kaucema maganata idan Kika sake kikayi kuskuran kiran wayata ko kika tako 'kafarki zuwa Nigeria Iftahal Ni mahaifin ki Alhaji Ishaq banyafe mikiba "


Kafin Iftahal tayi magana tuni Alhaji Ishaq yakashe wayar shi jefar dawayar  Iftahal tayi tasaki kuka sosai mai tsuma zuciya  tsayin lokaci tana kuka cikin fusata tasakko daga bed d'in wayar tad'auka tanufo hanyar fita banko 'kofar tayi babu tsoro balle shakka tanufi inda Maher yake cikin kuka sosai tashiga cewa 


" Maher tabbas kayi babbar cuta agareni yanzu gashi kasa mahaifina yayi mugun fushi dani nasan Mahaifiya tama haka tayaya kake tunanin zanyi rayuwa cikin kwanciyar hankali bayan iyayena suna fushi dani  dan Allah kaceci rayuwa ta Maher kasakeni kabarni natafi nikam na ha'kurama da karatun gara nakoma gaban iyayena Dan Allah tabbas nayarda nayi kuskuran yin wannan FURUCI!!! kayi ha'kuri Maher kar kazama silar rabani da iyayena "


Sosai kukan yaci'karfinta ta dur'kushe agabanshi tanasakin matsanancin kuka amsar wayar hannun ta yayi yakashe sigarin hannun shi yami'ke sannan yace " kije ki kwanta " tafiya yafarayi cikin sauri Iftahal tami'ke tasha gabanshi  tanasakin matsanancin kuka sosai Maher yahad'a fuska sabida yadda ranshi yayi matu'kar 'baci afusace yasureta cak yanufi bedroom d'in ta yanashiga yanufi saman bed yad'aurata saurin jawoshi Iftahal tayi yafad'a saman 'kirjinta cikin kuka tacigaba dacewa " babu inda zaka sekasakeni " sosai tari'ke  wuyan rigar shi tayadda babu yadda za'ayi yatashi  


Cikin natsastsiyar muryar shi yace 


" Sakeni banabu'katar ko hannun mace yata'bani balle jikinta kuma banason kuka janye jikin ki daga gareni time d'in baccina yayi " sosai Iftahal taji zafin maganar Maher hakan yasa tace " wato kai bakada damuwa ? kasani cikin masifa kananeman barina cikin ta to sede mu kwana anan kuma ahaka har seka furtamin kalmar saki "


Sosai ranshi ya'baci tureta yayi cikin zafin rai yaja tsuki d'aukar wayarta yayi yafita Kai tsaye yahaura sama bedroom yashiga yazauna bakin bed dafe kanshi yayi yana nazari zuwa can kuma yami'ke ya d'akko wayar shi number mahaifin Iftahal yad'auka cikin wayar ta yakira bugu 2 Alhaji Ishaq yad'aga duk da yaga ba number Nigeria bace Koda yad'aga shiru yaji shiko Maher yana tunanin yadda zaiyi magana mai tsayine abinda bai sababa muryar Alhaji Ishaq yaji yana fad'in 


" Wai waye ne yakirani kuma yayi shiru abinshi ? " ajiyar zuciya Maher yasauke cikin natsastsiyar muryar shi yace " barka dawarhaka Abba dan Allah inaso katsaya kasaurareni badan niba dan Allah nace " ina jinka " cewar Alhaji Ishaq iska mahar yafesar daga ba'kin shi sannan yace 


" Abba nine wanda ya auri 'yar ka amma bisa FURUCIN!!! ta nayi hakan ne dan nanuna mata cewa kalmar aure ba abin wasa bace Kuma dan tagane cewa FURUCI!! babban abune yanada kyau kafin kafurtashi kayi nazarin shi zuwa gaba mai zai haifar sabida idan yafito bayakomawa Abba wannan dalilin ne yasaka na auri Yar ka nabiya sadakin datake ganin babu wanda zai iya biya amma ni bason 'yar ka nikeyiba asalima ni babu hurumin mace cikin rayuwa ta inaso kayafemata banaso nazama silar raba d'ah da mahaifi yin hakan babban zunubi ne Abba idan har kayafe mata nikuma zan saketa ka aura mata wanda kake so iya haka ya isa yasata tadinga kiyaye FURUCIN!! ta Abba kadaure kayi yafiya agareta  dan tadawo 'kar'kashin ikon ka nifa banason Yar ka bakuma zan sotaba sabida duk duniya babu macan dazan sakata cikin zuciyata sabida babu ra'ayin hakan cikin raina kayi ha'kuri Abba nima kayafemin nasan kaji 'bacin rai sabida ni " 


Wani irin numfashi Maher yasauke sabida yawan maganar dayayi yanajin kamar numfashin shi zai d'auke karo nafarko dayayi magana mai tsayi haka tsaki Alhaji Ishaq yasaki cikin fusata yace 


" Kagama tobari kaji nariga nacire Iftahal daga cikin 'ya'ya na nakuma manta da ita dan haka kar nasake jin ko muryar ku daga ita har Kai sannan kasake sanar da ita cewa duk ranar datasake ta tako 'kafarta cikin Nigeria ban yafe mataba narufe babin Iftahal cikin rayuwa ta hakama mahaifiyar ta " 


Sosai Maher yaji babu dad'i cikin damuwa yace " shi kenan Abba amma zanyima al'kawari guda 2 dukda banason 'yar ka amma zan zame mata Uwa da uba bazan bari tarasa komiba amma ni bazan iya zama da ita matsayin mata ba sabida babu ra'ayin hakan atare dani  ranar dazata kammala karatun ta to a wannan ranar ne zan saketa kuma nabata damar fidda wanda takeso na aura matashi ko wanene abu na 2 Kai ne zaka tako USA ko Egypt sabida ita cike da tsananin Soyayyar ta dakuma kewar ta  karubuta wannan ka aje lokacin yananan zuwa " 


Sosai Abba yafusata yace " ni ? haba yaro har abada " daga haka yakashe wayar shi shima Maher jefar dawayar tashi yayi yajuya ya kwanta yanafad'in yanzu shikenan nayi sanad'in raba uba da 'yar shi gaskiya banso hakan ba amma nayi al'kawarin had'asu anan gaba cikin tsananin Soyayyar datafi ta dah " blanket yaje yarufe kanshi duka pllow yasaka a tsakiyar cinyoyin shi  yamatse Bananar shi yanasakin Nishi mai 'karfi had'ida muguwar bugun zuciya kamar yadda yasaba kasancewa akullum 


A 'bangaran Iftahal kuwa matsanancin kuka tashigayi sosai tanayin nadamar furta wannan FURUCIN!!!!! a wannan daran duk iya satar bacci amma yakasa sace Iftahal 


NIGERIA


Sosai Hajiya Sadiya tashiga cikin damuwa akan yadda mijin nata yad'auki zafi akan Iftahal akan dole tagoyi bayan shi sabida mugun tsaurin shi shi mutun ne tsayayye Kuma mai tsauri bayason Sha Shanci afusace yadubeta yace " Hajiya Sadiya banason wata ala'ka tasake shiga tsakanin ki da Iftahal Koda takiran wayane idan kikayi hakan to bada yawuna ba  " yana fad'in hakan yafita daga bedroom d'in parlour yakoma yazauna cikin 'bacin rai babban d'anshi dake zaune a parlour yana kallo yadube shi yace 


" Kai Ibrahim jekakiramin Zayyat kutaho tare " cikin rawar jiki Ibrahim yafita zuwa part d'in su bayan fitar Ibrahim Alhaji Ishaq yashiga 'kwalama Shukura Kira cikin sauri tafito tazo gaban shi ta zukunna shima Usman fitowa yayi wato 'kanin Iftahal wanda yake matsayin auta daga shi Ummi batasake haihuwa ba gefan Abba yazauna Kiran Hajiya Sadiya Abba yakumayi tafito cikin sanyin jiki tazauna dede lokacin Ibrahim da Zayyat sukashigo zama sukayi batare da sunce komiba gyaran murya Abba yayi sannan yace 


" Gaba d'ayan ku inaso daga yau kowannen ku yamanta da Iftahal idan kuma nakama wani dayin  ma'amala da ita to wallahi zan d'auki mugun mataki akanshi tunda tanuna ita ta'isa dakanta to taje sannan inaso kowa yasani namaida al'kawarin auran Iftahal dake kan Zayyat yakoma kanki ke Shukura tunda dama kin'ki fitar da miji wannan umarninane babu canji za'a had'a auran naku dana Ibrahim nanda 2 months dan haka kowa seyayi nashi shirye shiryen Shukura " tashi tsaye Usman yayi yace 


" Abba Aunty Shukura Kuma itafa Auntyn muce har shi yaya Zayyat d'in yaya Ibrahim ne kawai yayan ta to tayaya 'kani zai auri Yaya gaskiya Abba ..... " Tsawa Abba yadakamishi dafad'in 


" To sannu ubana wanda yafini sanin komi idan nasakejin bakinka sena cimaka sabida haka kowa yasani nagama magana Kuma babu canji " daga haka Abba yami'ke yabar parlour  jinjina kai Ummi tayi  sannan tanisa tace " iname umartar ku dakuyi ha'kuri da wannan hukuncin na mahaifin ku dan Kam kunsan babu canji ke Shukura kisani namiji bayama mace kad'an Kai Kuma Zayyat babu maganar Aunty Shukura daga yau kafara kallon ta matsayin matar ka " daga haka tami'ke tanufi bedroom tashi Usman yayi yabita Shima Yaya Ibrahim mi'kewa yayi yafita  d'ago kanta Shukura tayi idanunta suncika tab da hawaye cikin rawar murya tace 


" Zayyat nasan Abba yana matu'kar son abinda duk kakeso dan Allah kace mishi bazaka  iya aure naba dan Allah bazan iya kallon ka matsayin mijina ba nadade da kallon ka a matsayin 'kanina ba lalle ne kasamu biyayya taba Zayyat  bazan iya sauke wasu hak'kokin ba kaceceni kaceci kanka  " mi'kewa Zayyat yayi yasaki ajiyar zuciya sannan yace 


" Aunty Shukura kinsani Abba yad'auke ni tamkar d'an dayahaifa yanama fifita Ni akan 'ya'yan cikin shima tun bayan rasuwar  iyayena yari'ke ni tamkar d'an shi babu wani banbanci ko dady nane  se haka kamar yadda  bazaki iya  yin musu da wannan hukuncin ba tonima haka kiyi ha'kuri Aunty Shukura amma idan kinada mafita to kibita nima ina tunanin yadda zanyi zaman aure da Aunty na to amma Yaya zanyi komi Abba yazartar akaina dede amma naso ace yabari nakammala karatuna tunda shekarar 'karshe nike to amma duk abinda Abba yazartar dede ne nabarki lafiya  " 


Daga haka Zayyat yafita yana jinjina wannan lamarin itako Shukura  mi'kewa tayi tanufi bedroom d'in Ummi tanasakin matsanancin kuka tana shiga tafad'a kan jikin Ummi tasake  fashewa da kuka  cikin kuka sosai tace " Ummi yanzu shikenan inaji ina gani zan auri wanda yake matsayin 'kani agareni Ummi dan Allah kiyi wani abu akan wannan lamarin dan Allah Ummi dawane ido zan kalli Zayyat a matsayin mijina gaskiya Iftahal FURUCIN!!! Ki nima yasaka ni cikin tashin hankali Ummi dan Allah "


Rungumai ta Ummi tayi cikin lallashi tace " Shukura ha'kuri zakiyi kiyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkairi sabida gaskiya babu abinda zan iyayi nikam Iftahal manike matu'kar tausayi tayaya zataji dad'in rayuwa cikin fushin mahaifin ta ya Allah kakawo mana mafita cikin wannan lamarin


USA


Cikin sanyin jiki Iftahal tasakko daga saman bed tanufi toilet alwala tayo tafito tatada sallah sosai takeyin kuka cikin sallar had'ida ro'kon Allah akan wannan halin datake ciki har kiran sallar asuba Iftahal tanakan abin sallar bayan tagama yin sallar asuba tami'ke tanajin wani irin matsanancin ciwon Kai toilet tashiga tawatsa ruwa tafito cikin natsuwa take shiryawa har zuwa lokacin tanasauke ajiyar zuciyar kukan datasha bayan tagama shiryawa tsaf tadubi agogon cikin bedroom d'in 7:05 ajiyar zuciya tasauke sannan tace babu amfanin shiga Skul d'in ma dan Kam karatun agareni Sam babu wata fa'ida gara kawai nabarshi zaifi kawai " 


Wasu siraran hawaye suka gangaro saman kyakkyawar fuskarta dede lokacin wata dattijuwar mata tashigo cikin 'karamin parlour bakinta d'auke da Sallama saurin share hawayen nata Iftahal tayi tafito parlour cikin girmamawa dattijuwar matar tagaidata murmushin 'karfin hali Iftahal tayi tace " haba Mama dagirmanki ay nice yakamata nagaidaki bakeba mama dan Allah kibari " murmushi Mama tayi tace nagode sosai dakika bani girmana sunana  Iya Rabi ina d'aya daga cikin masuyima duka ma aykatan gidannan abinci Ni Yar Nigeria ce kamar ki kasancewa ta Yar Nigeria yasa Shanwul za'boni dan yimiki hidima wajan abinci se masu gyaran bedroom d'in ki sud'in Yan nan 'kasar ne se mai tayaki hira itakuma daga 'kasar 'yalla'bai take wato misra konace Egypt ko yanzu breakfast d'in ki angama yana kan dinning nashiryashi dawuri sabida Shanwul yacemin zakishiga Skul 08:00 " 


Murmushin ya'ke Iftahal tayi tace " to Mama nagode amma bazan samu shiga Skul d'in ba kicema Shanwul yatafi hidimar shi kawai breakfast Kuma idan nafito naci sukuma masu gyaran bedroom su gyara parlour kawai zan gyara nan nagode " daga haka Iftahal tajuya takoma cikin bedroom fita itama mama tayi tana fita taci karo da Maher yafito daga room d'in motsa jikin shi gaidashi tayi bai amsaba dama batayi tunanin amsawar tashiba cikin shakka tace 


" Allah ya'karamaka lafiya Saraki kai d'aya ne tak magajin sarautar Egyy ina neman afuwa nakasa saka sarauniyar mu fitowa yin breakfast ayanzu duk da tanada shiga Skul 08:00 agafarceni Saraki Mai nasara senaga kamar gimbiyar tamu batacikin yanayi Mai dad'i sabida tace bazata samu shiga Skul d'in ba agafarcemu ranka shidad'e " hannu Maher yad'aga mata sannan yace 


" Kuje kawai " daga haka yajuya yanufi bedroom d'in Iftahal


Comments and share please

No comments