DUDUWA 31
~31~
Kulu na fitowa ƙofar gida ta saka hannun ta ta goge hawayenta ta ɗauki hanyar gidan su kai tsaye da zuwa ƙofar shiga gidan ta chake chak ta tsaya me ta tuno ta juya hannun dama ta sake juyawa hannun haggu,a guje ta faɗa cikin gidan haɗe da yin sallama a bakin ta.
Amsawa gwaggo taye ta juyo da sauri tana hangen me sallamar ganin kulu a wannan lokacin yasa gwaggo matsowa ta kuma ƙurawa fuskar kulu ido ta ce""
""Hauwa kulu.
na'am gwaggo,kulu ta amsa haɗe da yin rumfar gwaggo zata shige ɗaki gwaggo tayi saurin riƙo hannun kulu ta ce""
"Ina zaki shiga daga zuwanki dawo nan naji me ya kawo ki a daran nan ko da mai garin kuke tafe ne.
Aa ni kaɗai ce gwaggo na gaji da abinda mai gari yake mun kullum cikin zage da tsangwama akan ɗan da duduwa ta mutu ta bar masa wallahi komai nayi masa ban iya ba sai yanda ransa yake so ga ɗan banzan ci da shagwaɓa ga rashin ji da ɓarna ni kam dai na gaji wallahi ban haifa ba bazan ci kashi ba a ha.
tun da kulu ta fara zuba gwaggo tayi kasaƙe da baki tana duban kulu har ta gama gwaggo bata ce ƙalaba sai ma juyawar da tayi ta nufi ɗakin ta tana""
ji rani ina zuwa.
kulu ta amsa cikin sauri da"
to gwaggo,haɗe da neman wajan zama ta zauna tana cire gyalen ta.
gwaggo ce ta fito sanye da takalmi da gyale akanta ta dubi kulu da kyau ta ce"
yanzu dai ke bazaki iya zaman aure ba sai zama a gidanku ko kulu.
ba haka bane gwaggo bazan iya cigaba da zama a gidan mai gari ba gaskiya na haƙura da auren sa har ga Allah.
to ai shikenan tazo gidan sauƙi tun da bazaki iya zaman gidan mai gari ba ni ma nan bazan iya zama da ke a gidan nan ba sai ki zauna ke ka ɗai kici abinda zaki ci nan naga wanchan karan da kika dawo gida me ya faru akan ki sai da kamanin kowa ya sauya har maƙofta to ba dani ba gyaɗa a lahira kinga ta fiya ta haka kawai bazaki hanani baci a daran yau ba wallahi ku ƙarata ke da mutanan naku.
gwaggo tayi hanyar waje,da gudu kulu ta figi mayafinta ta sha gaban gwaggo.
zan koma gwaggo yasin sha'afa nayi.
sha'afa kulu yau naga abinda yafi ƙarfina da lafiyar tamu kike sha'afa.
kiyi haƙuri wallahi zan koma da safe dan Allah karki tafi ki barni.
Allah ba zan kwana dake a cikin gidan nan ba sai dai ayi ɗaya cikin biyu ko ki zauna a gidan ke kaɗai ko kuma ni na kama hanya ta na tafi.
shiru kulu tayi gaba ɗaya hankalinta ya koma kan dukan da ta sha ina zata zauna ita kaɗai a gidan yo ko da gwaggon ma tafiya ta zanyi aradu a fili ta ce.
to me kike so nayi yanzu gwaggo.
ki koma ɗakin mijin ki dan shine rufin asirin mu mu duka kar kija mana masifar da zata fi ƙarfin mu kulu ki sa zaman garin nan ya gagaremu.
ai naga ita duduwa ta rasu gwaggo yanzu babu abinda zai faru.
gaba gwaggo tayi kulu ta damƙi mayafin gwaggo da sauri,gwaggo ta juyo a fusace ta na.
idan baki sauni ba wallahi hauwa kulu zan ɓata miki naga har yanzu da sauran ki almatsutsan da har gadon su ake iyaye da kakanni zaki gayan maganar banza da wofi sake ni nace.
gwaggo na jan mayafin kulu najan mayafin tana.
Allah zan koma yanzu yanzun nan.
zaki koma gidan mai garin?
eh zan koma gwaggo amma dan Allah ki rakani tsoro nake ji wallah.
shegiyar gora da ki zauna ke kaɗan mana kiji a jikin ki da an kuma kwatanta abinda ya faru a baya, wai ma ba da ƙafarki kika tako kika zo ba hauwa kulu.
dan Allah na ce gwaggo ki taimaka ki rakani.
hmmm wuce muje tsakaninki da gidan mai gari ai sai mutuwa kulu ke da mai gari yasin mutu ka raba dan babu me ɗaukar ki ki zauna a gidansa kaf dangi da maƙota ba wanda bai san halin margayyya duduwa ba kuma wallahi ki fita harkar ɗan ta dan babu ruwa na duk abinda kika jawa kanki kinji na faɗa miki.
suna tafe gwaggo na kwarkwarawa kulu da tunasar da ita wace ce duduwa idan ita ta manta gaba ɗaya jikin kulu ya mutu har gwaggo taja dinga a kwanar layin gidan mai gari tace kulu ta wuce sai da safe,ba yanda kulu ta iya ta wuce kanta tsaye ta nufi ƙofar gidan, turawa tayi taji ta a rufe ta juyo da kanta da sauri zata faɗawa gwaggo gwaggo ta ce ba sai kin gani ba tsoro ya kuma kama kulu ta shiga dukkan ƙofar gidan da ƙarfi tana"
ni ce kulu a buɗe dan Allah dare yayi.
mai gari naji dan ko rintsawa bai iya yi ba tunani gaba ɗaya ya hanashi sakat,da jin bugun kulu ya miƙe da sauri zai je ya baɗe wata zuciyar ta hanashi ya koma ya zauna kasa jurewa yayi da bugun ya miƙe yayi ƙofar gidan jin takun mutum yasa kulu cewa.
Dan Allah kayi haƙuri ranka shi daɗe dare nayi ka buɗe mun ƙofa na shigo.
da wani ya aike ki kaka fita ki koma inda kika fito tunda ke da kanki kika fita.
kayi haƙuri sharrin sheɗan ne bazan kuma ba Allah kaji na rantse.
hmmm da ban san halinki bane kulu kinga bacci nake kin taso ni sai da safe.
innalillahi,malam kayiwa Allah ka buɗe ni karka barni ni ɗaya a nan wajan malam.
to fa malam na koma kulu ni kin bani ƴar bazawarar dariya wallahi mai gari da malinta oh dare ɗaya Allah kanyi bature.
hiyiiiiiiiyiiiiii malam kayi mun rai.
Allah yai mana gaba ɗaya kulu dan Allah ki koma inda kika fito.
kuka sosai kulu keyi da roƙon mai gari Allah Annabi ya buɗe mata ƙofa mai gari ya dinga dariya yana mutanan na nan waje su taya ki kwana.
wai wani sallati kulu ta rafka har da tsale ta dinga kuka tana waige waige sai da tayi me isarta mai gari ya buɗe mata ƙofa ta runtuma cikin gidan da gudu tayi ɗakin ta tana wani sabon kuka mai gari ya nufi ɗakin na dudu yayi kwanciyarsa bacci me daɗi ya ibe shi.
Tun daga wannan rana kulu ta sassuta daga abinda take zata dafa ta baiwa mai gari abinci har ma da na dudu amma bata ko kallon inda yake bare yi masa wasa ko wanka da sauran buƙatu mai gari da kansa yake yiwa na dudu.
…………………
Tun da dije ta gane da biyu ƴar chakare ta ke fita dije ta fara girka iya dai dai cikinta da na yaranta sai liman idan dije ta zubawa liman rabonsa sai ƴar chakare ta lallaɓa ta cinye nasa ba yanda ya iya ta kuma ƙi dafa masa wani da yaji yunwa tai yunwa sai yasaka dije a gaba yayi ta masifa daje kuwa ta dake ko a bata tanka masa yayi ya gaji ya fuce yau da gobe taƙi gaban wasa liman ya fara ɓuya da dije ta zuba masa rabonsa zai ɗauka ya ɓoya ya cinye tas ya dawo da kwanan a ɓoye idan ƴar chakare ta ritsa shi yace shima bai ci ba yunwar yake ji ainun
*In sha Allah na kusa kammala wanga book,me zafi ya biyo baya💃💃*
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments