YAR AMANA 9-10
👩🦰👩🦰👩🦰👩🦰👩🦰👩🦰👩🦰👩🦰
*NUSAIBA 'YAR AMANA*💧💧
Page 9&10
ABUDULJABBAR ne kwance a gadonsa FINAH tana rungume dashi tamkar zata shige cikin jikinsa, wayarsa ce da take kan bed side drawer, tafara ringing cikin bacci yaji ringing d'in wayar ta dameshi, dan haka ya bud'e idonsa ahankali dan sosai yakejin dad'in baccinsa ji yayi anqamqameshi dan haka cikin sauri yaduba jikinsa FINAH yagani ai da sauri ya rabata da jikinsa Domin kuwa jiya da dare haka yaita jiranta tazo tabashi haqqinsa amma taqi zuwa harsai da yayi bacci, jin sake qarar wayar yayi cikin magagin bacci yai picking dan ko suna bai tsaya dubawa ba, kara wayar yayi akunensa tare dayin Sallama domin kuwa yasan kowa ye yaqirashi mai mahinmanci ne agarunsa da wanan layinasa na manyan mutanene na jikinsa, amsa Sallamar akayi da kaukausar murya sanan daga cikin wayar akace " ABUDULJABBAR(SS) inbadamuwa inason ganinka yau a guest house d'ina"
Shikuwa ABUDULJABBAR tini yagane mai qiran dan haka yace " Yes Daddy ganinan zuwa yanzunan" "Okay ina jiran isowarka" akace sanan aka katse qiran.
Shi kuwa ABUDULJABBAR da sauri ya tashi yafad'a bathroom ya sakarwa kansa ruwa, wanka yayi yafito tare dayin alwalar sallar walaha dan lokacin qarfe goma na safiya ya wuce, yana fitowa daga wanka ya shirya cikin wani yadi d'an Abba mai kyawun gaske wanda aka masa d'inkin zamani kayan suyimasa kyau sosai dan da wuya kaga manyan kaya ajikinsa sai de qanana yafi sawa, FINAH kuwa tana kwance ta bud'e ido tana ta kallonsa ji takeyi tamkar tabud'e cikin ta tasa shi dan bataso yafita wata taga wanan kwaliyar tasa wani mugun kishine taji ya taso mata, dan haka cikin sauri tafada bayi ta dauro alwala ta shinfid'a sallaya abayansa itama tafara Sallah, raka'a biyu tayi tassalame shi ko lokacin ya kai ta raka'a 4, bayan yayi Sallama ne ya juyo ya kalleta yace " Nafisa Sallar me kikayi yanzu"? Domin kuwa yasan bata yin nafila, 'bata rai tayi sanan tace " Sallar Asuba mana Honey"
"Nafisa wallahi kiji tsoron Allah ki tunafa Akwai kwanciyar kabari inkayi mai kyau zaka gani inma marar kyaune zaka gani, wata irin rayuwa ce wanan Nafisa sai kace ba musulma ba?"
"Nide honey ka dena yimin mugun fata ai koma menene kai ne sila tun yaushe nake rungume da kai tinda wowarka fa daga massalaci haba honey dan Allah ya kamata fa karinga bani hakkina"
"Amma Nafisa tun asuba kintashi shine kika qiyin Sallah ko kika liqemin ke ga mai miji bayan ba irin jiran da banmiki ba adaren jiya kika qi zuwa kina jira saina biki d'akinki kiji dad'in wulaqantani"
"Eh mana kamar yanda kaima kake wulaqantani ina biyoka ba"
"Okay nidai yanzu fita zanyi ana nemana"
"ABUDULJABBAR yaufa Sunday ba aiki ina kuma zakaje gaskiya kazauna kabani haqqina". "Hhmm to daddynki ne yake nemana"
"To amma daddy ya zaiyimin haka gaskiya ni inason kasance wa da mijina, kaduba fa irin wanan kwaliyar da kayi kallan kafita 'yan mata suyita kalonka gaskiya sai de muje qiran daddyn tare"
"Haba ba inda zaki bini kingama tafiya ta" juyawa yayi ya d'auki takalminsa mai tsafta da kyau yasa ya d'aura agogon diamond a hanunsa, sanan yafice, ita ko FINAH daga ita sai riga da wando na bacci masu dogon hannu ajikinta haka tabishi har parlour yana sauqowa parlour yaga Mum da IKIRAM na zaune a dining suna break fast, zuwa yayi ya durqusa kusa da kujerar Mum ya gaisheta sanan ya tashi yaja kijera ya zauna, FINAH ce tazo tatsaya qerere akan su bako gaisuwa cikin shagwaba da turo baki tace " gaskiya ni Mum kifad'awa Ya ABUDULJABBAR ya jirani inyi wanka mutafi tare".
Shiko ABUDULJABBAR ruwan black tea, ya tsiyaya a aqaramin copy, ya ibi soyeyen arish, yasa peck ya fara ci, Mum ce tace "ABUDULJABBAR meyasa bazaka jirata ba ku fita tare"?
'Bata rai yayi sanan yace " dan Allah Mum kidena biyewa shirmen Nafisa qirafa dad dinta yakemin mai muhimmanci, ita kuma sbd kishinta na jaraba takeso tabini kuma wlh Mum duk kishinta inde naga yarinyar da ta kwantamin sai nanemi aurenta"
Wani ihu FINAH tayi ta daka tsalle ta sheqe ABUDULJABBAR a gaban Mum cikin Masifa tace " wlh qarya kakeyi ABUDULJABBAR ni Nafisa nagirmi kishiya natsere mata nesa ba kusaba ABUDULJABBAR bazan iya shere d'in soyayya ta dawata ba, kainawa ABUDULJABBAR danni kad'ai aka yika" kuka Sosai FINAH tasa, ABUDULJABBAR zaiyi magana Mum tada kamar tsawa tace youre very stupid ABUDULJABBAR mudin ina raye baka isa kaqara aure ba dolene kazauna da nafisa ita kad'ai har abada"
Daddy ne yafito daga shashensa cikin tsawa yace " qarya kikeyi Murjanatu koni nan banfidaran zanqara aureba balle yarona ABUDULJABBAR inyasamu wace yakeso dolene ya aureta domin kuwa nasan komai kawai nasa muku na mujiya ne" dagudu FINAH tahaye sama tana kuka wiwi, wani mugun kallo Mum tayiwa Daddy da ABUDULJABBAR sanan tabi bayan FINAH, shiko Daddy bubuga kafad'ar ABUDULJABBAR yayi sanan yace " karka damu yarona nasan kana haquri ka qara akan wanda kakeyi kaji yarona kuma aduk lokacin da kahad'u da wace ta kwanta maka ko bana raye na baka izinin ka aureta domin kuwa baka da laifi har agurin Allah karka biya ta mahaifiyarka ta cuci rayuwarka sbd rayuwar wata sanan tazo tana da nasani" rungume daddyn nasa ABUDULJABBAR yayi sanan yace" nagode sosai Daddyna"
Da sauri ABUDULJABBAR yafita harabar gidan wanda yana fita Escort d'insa suka taso dan sumar rakiya amma duk yad'aga musu hannu alamun sukoma, motarsa jeep ya nufa mai kyawun gaske ash colour, ya bud'e yayi Bissimillah yashiga sanan yayi addu'ar shiga abin hawa wanda manzon Allah ( S.A.W) ya koyar damu
( *SUBBAHANALLAZI SAKARA LANA HAZA WAMA KUNA LAHU MUQRININ WA INA ILA RABBINA LAMUNQALIBUN*)
Sanan yayiwa motar sa Key yabar gidan kai tsaye unguwar Abuja road yanufa inda guest house d'in Daddyn FINAH yake yana isa qofar gidan ya danna hon mai gadi ya bud'ema sa get d'in aguje ya danna hancin motar sa cikin gidan, yayi parking ya fito a motar alokacin yaga wasu 'yan mata guda biyu cikin shigar banza zasu fita agidan, girgiza kansa ABUDULJABBAR kawai yayi sanan ya shige main parlour d'in gidan, acikin parlour d'in yatar da sirikinasa yana hakimce kan kujera shida muqarabbansa da kuma escort d'insa a tsaye a bayan sa, hannu Alhaji Halliru yayi escort d'inasa ai kuwa duk suka watse suka rage su yasu, shi kuwa ABUDULJABBAR zama yayi aqasa kusa dasu ya gaishesu su uku da surukinsa Alhaji Halliru da kuma abokanasa guda biyu qushoshin gwamnati Alhaji Qasimu, da Alhaji Biliyaminu, bayan ya gaishesune ya tashi ya koma kan kushin ya zauna, Alhaji Halliru ne yayi gyaran murya yace " *SS ABUDULJABBAR Ashiru Maina* munqira kananne domin muyi magana ta siri da kai dan kuwa duk wani binkice da kakeyi akan mu nason rabamu da dukiyar mu tofa munganoka sbd haka muna sonkane shi yasa muka qira ka nan dan ha ka kafad'i abun da kakeso, mu baka domin kadena binkice akan mu sbd da haka ya kagani"?
Gyaran murya ABUDULJABBAR yayi sanan yace " nidai na rantse zanyi aikina da gaskiya dolene mubincika ta yaya dukiyar talakawa ke maqalewa domin kuwa a kullum talakawan Nigeria kuka sukeyi akan ba kud'i suna shan wahalar rayuwa amma ku masu kud'i ba ruwanku kunyi zaune akan dukiyar su, kuna musu dariya sbd haka dole ne muqoqarta wajen qato musu dukiyar su"
Alhaji Qasimu ne yace " au haka kace? Sbd kai baka da kunya fitsararene kasani fa agaban surukanka kake inmunga dama ma zamu iya qwace 'yarmu"
"Tashi ABUDULJABBAR yayi yace "koma me zaku ce kuce domin kuwa ni aikina da gaskiya zanyishi ba da son zuciya ba"
Alhaji Biliyaminu ne ya tashi yace " yaro man kaza karfa kaga muna lala'ba ka d'auka ko muna tsorankane ina tabbatar maka ni bani da mutunci sbd haka karka bari raina ya 'baci domin kuwa rayuwarka zata iya shiga cikin matsala"
Murmushi ABUDULJABBAR yayi sanan yace " aini rayuwata a hanun Allah take ku baku isa kuyimin komai ba kuma ku hanzarta sake kud'ad'en talakawan Nigeria da kuka hau kai kuka zauna ku kasa talakawa nata zagin gwamnati bayan kune 'barayin gwamnatin"
Alhaji Halliru ne ya tashi yasa dariya Hhhhhhhhhhh Sanan yace " anbika ta lallami kaqi to kafita ahanyarmu kadena yimana binkice akanmu idan kaqi kuma zankawar da sanayar dake tsakaninmu da kai nasa amaka rashin mutunci"
"Ai dama ni tini na ajiye wata sanaiya tsakaninmu da ku domin kuwa ni ABUDULJABBAR Maina bana huld'a da azalumai irinku"
"Au haka kace"? Daddyn FINAH yafad'a.
"Eh haka nace ku jirayi sammaci"
Yasa kai yai ficewarsa, Alhaji Halliru kuwa cewa yayi "Shikenan zakuwa kagani...................
Wanan littafin na kud'ine mai son jin ci gaban sa zai biya 300 kacal
Sai a tuntu'beni ta wanan number 08114867197 dan jin yanda za'a biya kud'in.
Sai na jiku masoyan kwarai kuyi haquri dole tasa zanmai da book dinan na kudi saboda wani dalili mai qarfi.
Love you all my pans
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups please
*ALLAH YASA MUDACE*🤲
No comments