Breaking News

TSANGAYAR MALAM 15-16

 _*‍👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️TSANGAYAR👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️*_

                  _(Malam)_

                       *Na*

_Maman Dr

             1️⃣5️⃣-1️⃣6️⃣

Miƙawa ɗan malam farantin yayi haɗe da cewa"gashi kaci na san yunwa kake ji kamar aci babu,ko kallon in da gaddin ɗan malam be yi ba,gaddin ya sake cewa"ka karɓa kaci karka illata kanka nan wajan ba likita babu me maka sannu bare ya kaika asibiti gwamma tun wuri ka amsa kaci ko ya ya ne,idan kuma bazaka ci ba kana ƙara ɓata mun lokaci nayi gaba, ɗan malam ya ɗago kansa ya miƙar da ƙafar haɗe da jin gina kansa jikin bukar ya dubi gaddin dake tsaye akan sa ya ce""a zumi nake ka fita a kai na karka tiƙe ni,"tab a zumi a tsangayar

malam,daga haka gaddin bai ƙara tankawa ɗan malam ba ya sa kai ya fita daga bukar fitar sa ke da wuya wani matashin saurayi da bai fi 14years ba ya rarrafo wajan da ɗan malam ke zaune da mari a ƙafarsa,yana zuwa ya nemi kusa da ɗan malam ya zauna haɗe da cewa.


"Daga gani kai baƙo ne a tsangayar nan,ya sunan ka?


Ban sani ba,sannan bana son takura ka matsa chan in da ka baro kar ka dame ni.


yi haƙuri bani na kar zoman ba rataya aka bani taimakon ka nazo yi naga kai na Allah ne,amma tunda baka so ba'a dole sai anjima,matashin ya fara ƙoƙarin tashi har ya jefa ƙafarsa ɗaya zai taka ɗan malam ya ce""



Attahiru nake,amma ɗan malam ake kira na da shi.


ka ce ni da kai sammakal baban ka malami ne ko limami?

     matashin ya dawo baya ya zauna kusa da ɗan malam,kamar ɗan malam ba zai amsa masa ba sai kuma chan ya ce"


Eh shine sai kuma me ye?



Babu ni sunana SANI ƘOLO babana malami ne daga damaturo nake na kai shekara huɗe a nan tsangayar idan ma ban fi ba.


amma kuma kake cikin mari har yanzu?


hmmm tsangayar malam ɗin kenan duk sanda aka cire ni a mari tofa auna gudu nake akamo ni shi yasa kullum a cikin mari nake amma kai me kayiwa baban ku ya kawo ka naga wani ɗan dattijo ne ya sako ƙeyar ka a gaba ya kawo ka.


Ba baba na bane.


Kut to waye zai kawo ka nan wajan gaskiya to maƙiyinka ne babba,ka ko san tsangayar malam?


hmmm maƙiyi ko maƙiya ai suna da yawa.


taɓ ashe taron dangi aka yi maka kai ko dan Allah su waye waɗannan manyan maƙiyan naka.


bai shafe ka ba,kayi tambayar data dace.



kai kafiya faɗa wallahi daga wani gari ka taho NIGER?



hmm LAMBU daka sanar dani ya tsangayar malam ɗin yake wannan mutumin dake kan wani buzu shi ne malam ɗin?


ƙwarai kuwa baya ƙasa baya samma me charbi dubu biyar da ɗoriya ga almajirai dubu a bayan sa ashe ka ganshi jiyan kenan yayi maka magana?.


na gansa babu abinda ya ce mun sai kallo daya bini dashi nima na kalle shi.


Alhamdulillah,ashe kai me baban rabo ne ina kyauta zaton zaka bar wajan nan amma,Sani ƙolo yayi ƙas da muryar sa yanda in ba ɗan malam ba babu mai iyo jiyo shi ya ce,"duk yanda ze yi maka magana karka sake ka amsa indai kana son barin wajan nan idan ka amsa na rantse maka da Allah kai da tsangayar nan sai dai mutuwa ko dukka duniyar nan za'a haɗu a ƙwatoka baza su iya da malam ba.



gaban ɗan malam ya faɗi haɗe da nuna tashin hankalin sa da tsoro ƙarara a fili ya ce cikin sauri"



kamar ya ya?


sani ƙolo ya ɗan leƙo da kansa waje ganin babu kowa wajan ya dubi ɗan malam muryar ƙasa ƙasa ya ce.


haba mutumi na karka tsorata ka badani da gani kai ma baji kake ba aka kawo ka wajan nan,ka bini a hankali duk zan faɗa maka yadda zamu warware ta amma kafin nan idan an kawo abinci ka dinga amsa ko bazaka ci ba za'a kawo rubutu abaka kasha ka amsa shima karkayi musu da su ka amsa ka kai rubutun bakin ka amma karka sake kasha kana ɗora shi bakin ka zasu fita su barka kar kuma ka yi ƙoƙarin guduwa a yanzu dan za'a gwadaka bila adadin aga zaka fece, ni ɗin nan daka gani anan guduwar ya ja mun da tini na jima a mahaifata dana ɗauki hanya zan fece zan nemi ƙofar dukka wajan nan na rasa har bukokin sai dai na gani a bukar malam yasa a mai dani kar ka kwatanta gudu ɗan malam zaka dawwama anan yasi............sani ƙolo ya maƙale da sauri ya kama""YA AYYUHAL'LAZINA AMANU...


   'Dakata haka ƙolo wa ya kawo ka wajan wannan?


futsari nake ji nace ko zai taimaka ya bani buta.........tasssss wani ƙaton gaddi ya wankewa sani ƙolo fuska da mari haɗe da cewa"


Ni zaka haɗawa ƙarya kana faɗa masa tsurku.


ni babu abinda ya haɗani dashi tunda nayi masa magana bai tanka mun ba na ƙyaleshi kamar bebe idan ƙarya nake ku yi masa magana kuji kamar baya ji bare yayi magana.


Wallahi kasan halin malam gaba da baya idan aka samu tangarɗa akan yaron nan sai ka rai na kanka ƙolo sai na sumar da kai naga me farfaɗoka dan..............,"gaskiya nake faɗa ni ba ƙarya nake ba ka gwada ka gani mana.


na rantse idan yaron nan nayi magana ya amsa sai ka gane baka da wayo ba kai ɗan tarin kai ba hmmm.


na yadda indai ya amsa kuyi mun duk abinda kuka ga dama gaskiya ta nake faɗi,sani ƙolo ya ƙare batunsa da duban ɗan malam da shi ɗin ma yake duban kowanne a cikin su kamar bai fahimci me suke yi ba,gaddin ya juyo kan ɗan malam ya ce""

  


"kai ya sunan ka?



dukum ɗan malam yayi yana duban ɗaya gaddin dake tsaye a gefan sa me maganar ya sake cewa""



kai gaddafi ban tsular na tsule ƙeyar ɗan banza tunda ba zai magantu ba,anan ɗin ma ko kallon inda gaddin ɗan malam bai yi ba sai ma haɗa kansa da gwiwarsa da yayi ya kwanta abin sa sukayi maganar duniya ɗan malam ko gezau bare ace yaji suka fita suka barshi koda suka fita sani ƙolo rarrafawa wajan sa yayi ya koma suka fara magana da ido alamar kar wanda ya tanka akwai ɓoyayye.

**********

Garin lambu ya yiwa malam da uwali zafi basa cikin nutsuwa da walwala ko da yaushe hankalin su da tunanin su na ga ɗan malam a inda ya tsinci kansa musamman malam da har wata rama yayi ya rage shiga mutane sai dai idan sallah zai ja ko kiran sallah a masallaci duk sanda zai sha ruwa yakan roƙi Ubangiji ya duba masa Attahiru ya tsare shi ya kareshi ya kuma shirya masa shi akan dai dai ya zama kamili kamar kowane ɗa,ta wagar hakimi kuwa tayi nisa da shawarta naɗawa malam ƙasimu cinnaka rawanin limanci bisa ƙoƙarinsa da dagewa wajan kai ɗan malam inda ya chanchanta.

      Malam ƙasimu cinnaka na dawowa daga nijer aka sutale malam balarabe daga limanci aka naɗa malam ƙasimu a cikin a zumi garin lambu ya ɗauka da maƙoftan garuruwa wasu hakan yayi musu daɗi wasu kuma ya baƙanta musu shiko malam balarabe Addu'a yayi da Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a wajan sa dan akan gaskiya ba zai sauka ya bi ƙarya ba,gona malam balarabe ya koma haiƙan yake numa masara da dawa da wake sai albasa cikin ikon Allah da ya saka iri sai su fidda kai kayan sa suyi kyau kusan ma a yanzu ƴan kasuwa sun fi siyan nasa tun kan ya kai ga cirewa ake kamawa labari ya jema Hakimi lura da asarar da hakimi ke gabzawa a gonakin sa duk da takin zamani yake aiki.

……………Wasu ƙarti ne su biyu suka shigo bukkar suka kinkimi ɗan malam yana kokawar ƙwacewa basu dire shi a ko ina b sai a muhallin malam dake kan buzu ya ce""

_*A nan zan gimtse in da comments/share*_

No comments