Breaking News

YAR AMANA 7-8

*NUSAIBA 'YAR AMANA*💧💧

Page  7&8

Please za kuga sunan littafin ya sanja daga 'YAR AMANA ya koma NUSUIBA 'YAR AMANA.

___Suna isa qasar Ijib kuwa ba 'bata lokaci akafara duba lafiyarsu a qasar, watansu uku a qasar Hajiya Karima ta samu ciki murna gun Alhaji Halilu kamar ya zuba ruwa aqasa yasha,  haka ya qira waya zuwa Nigeria ya fesawa 'yan uwa da abokan arziqi, kowa yana ta murna, amma banda matarsa Nuratu ta naji ta bazama gidan bokaye akan amusu asiri yabisu har qasar da suke ciki ya 'bare, amma Ina ta Allah batasu ba, haka Karima taita renon cikin ta cikin qoshin lafiya,  kuma itama alokacin ne Hajiya Murja taqara samun wani cikin da har tafitar da rai, bayan wasu wattani Karima ta haifi 'yarta mace

asaudiya tamkar balarabiya dan kyau tana kama da uwarta amma tafi uwartata kyau da haske, murna kuwa gurin Alhaji Halilu kamar yayi yaya, Satinta d'aya da haihuwa sukabar Saudiya suka nufi America wajen ABUDULJABBAR sosai ABUDULJABBAR yayi murnar ganinsu inda yarungume jaririyar yanajin soyaiyarta mai qarfi a zuciyarsa, kwanansu biyu a American suka nufi gida Nigeria inda washe garin da wowarsu Hajiya Murjanatu itama ta Haifi  Jaririyarta, nande dangi ya kaceme da murna, inda suka yanshe shawara akan ahad'e sunan Murjanatu da Karima, hakan kuwa akayi inda Alhaji Halilu yai ta'barin kud'i har ana gobe Suna, inda yaiwa Jaririyarsa hud'uba da  FATIMATU, adaren ne, bayan Alhaji Halilu ya gama yiwa 'yarsa hud'uba ya tafi ya kwanta, Karima itama ta kwanta kawai sai taji murya qasa qasa abayan Window d'inta, nanfa takasa kunne taji muryar kishiyarta tana cewa nan shine d'akinta qofar d'akin tana ta gaba inaso kafin gobe a darenan ku kashe jaririyar nan kai harma ita uwar, dan banaso zuwa gaba tasake haihuwa dashi"

"Angama ranki ya dad'e suka ce.


 koda gari ya waye haka aka nemi Karima da jaririyarta akarasa, nema iya nema anyi amma ba labari nanfa hankalin kowa ya tashi baya ma Alhaji Halilu, abu kamar wasa ya zama gaskiya qarshede sunan ba'ayi shiba, har na Murjanatun domin kuwa kowa yana cikin tashin hankali kawai de aka rad'awa Jaririyar Murjanatu suna IKIRAM,  haka sukayi ta nema amma shiru ba labari qarshede Alhaji Halilu har yafad'i rashin lafiya, tinda ga ranar baiqara lafiya ba, ai kuwa Nuratu taci gaba da wadaqa da dukiyar sa son ranta.



Bayan shekaru biyu da faruwar haka Kuwa ABUDULJABBAR ya dawo qasarsa Nigeria da murnarsa dan yazo yaga qanwarsa ta wajen Innarsa Karima domin yana son yarinyar sosai, amma me ya iske wanan mumunan zancen na annemi Inarsa da Jaririyarta anrasa  da sama da qasa, sosai ABUDULJABBAR ya shiga tashin hankali dan har sai da ya kwanta jinya, na kwanaki biyu bayan Ya samu lafiya ne shima da kansa ya shiga neman Innarsa Amma yarasa ta 'bat,  qarshe de dole suka haqura suka ci gaba da Addu'a, ayanzu kam sosai Hajiya Murjanatu take Fantama wa dan arziqin mijinta yaqara ha'baka dan haka take huld'a sosai da matan manya, inda ayanzu babbar qawarta ita ce Hajiya Zubaida matar wani qusan gwamnati ne wanda mijin Hajiya Zubaida Alhaji Halliru yana kud'i har ya qoshi da kud'i,  inda suke da 'yarsu guda d'aya NAFISA wanda suke qiranta da FINAH, gata sosai suke nunawa FINAH sunsakar mata komai abunda take so shi takeyi ko a gida ko awaje ba mai kwa'barta,  inda Hajiya Murjanatu da Hajiya Zubaida suke da wani nufi azuciyarsu na yahad'a yaransu aure daga zaran sungama karatu, wato FINAH da ABUDULJABBAR


Shiko ABUDULJABBAR saboda baqin cikin rasa Innarsa ya kasa zaman Kaduna ya koma Abuja yaci gaba da karatunsa akan harkar (S S) har aka ibi shekaru sanan fa ya shigo kaduna shima kuwa wani aikine ya shigo dashi domin yin binkice akan wasu qusosin gwamnati ciki kuwa harda Alhaji Halliru maina,  mahaifin FINAH, aranar da yagane Mum d'insa tana da Alaqa da gidan Alhaji Halliru Maina aranar yanemi zaibita gidan, ai kuwa taji dad'in hakan dama tana so ta masa zancen FINAH, dan haka tayarjemasa yabita,

Shiko dan ya gudanar da binkicensa da kyau ya nemi zuwa agidan, saide me zuwansa gidan keda wahala FINAH ta d'aura ido akansa tace " duniya ba wanda takeso sai shi, ai kuwa iyayen sunyi murna dan ba 'boye- 'boye FINAH ta furta abunda ke ranta, shi kuwa ABUDULJABBAR ji yayi ya tseneta haka de yabar gidan cikin qunci binkincenma bai iya yiba, abufa kamar wasa magana tazama babba domin kuwa dagaske FINAH ta tadawa iyayenta hankali akan ABUDULJABBAR takeso, nanfa magana tayi qarfi gurin manya, inda shi kuma ABUDULJABBAR yaqi yarda nanfa yaga fushin Mum dinsa muraran dan harcewa tayi inbai auri FINAH ba sai ta tsinemar, dan haka aranar yasha kuka dan shi sam FINAH bata daga layin matan da yakeso shi yafi son mace mai ilimin addini dana boko sai de ita FINAH sam ba ilimin addini a gareta sai na boko kad'ai dan rabin rayuwarta ma aturai ta yita,  gashi Daddynsa shi mutumne ba maison hayaniya ba, dan haka dole ya yarda ya auri FINAH badan yana sontaba.


Wanan shine asalin ABUDULJABBAR da kuma Matarsa FINAH, dama yanda aurensu ya faru.

  

Tinda ABUDULJABBAR ya auri FINAH yake haquri da ita domin Sam bata san haqqin miji ba, ba abunda ta iya sai de ta sheqa ado  ta hakimce akujera,  ba aikin fari balle na baqi komai inyanaso saide qartai su masa hatta girki  kuku namijine yakeyi musu, tini ya dad'e da qera gidansa a sardauna cresence, yana so sukoma ko qila FINAH zata gyara halinta intaga ba Mum amma sam taqi ta koma tace ita tafi jin dad'in zama tare da Mum, dolen ABUDULJABBAR ya haqura suka ci gaba da zama agidan iyayensa ba danson ransaba domin kuwa bai isa ya yiwa FINAH fad'aba yanzu zaiga 'bacin ran Mum d'insa haka yai ta haquri da FINAH har yanzu da suke shara 4 da aure kuma har yanzu FINAH bata samu ciki ba, dan atsarinta ba yanzu zata haihu ba, shiko ABUDULJABBAR yasa mata ido dan shi kam lamarin FINAH sai de addu'a.




_________________________



Yau da wuri Gaggo ta tashi tayi tahad'a furarta domin tana so ta gwada aikin bokanasu tagani yayi ko baiyiba, dan haka tunkafin Baffa ya tafi kiwo Gwaggo ta tasoni bayan nayi Sallar asuba na kwanta, ruwan sanyi ta sheqamin duk da sanyin da ake tsalawa,  haka na tashi jikina nata rawa, Gwaggo kuwa cikin masifa tace "maza kije ki d'aurayo jikinki kizo fitamin da fura ta yanzunan" haka dole naje na shiryo na sake kaya nazo gaban Gwaggo na durqusa na gaisheta lokacin Baffa nacin d'umamen tuwo, shima gai sheshi nayi amma ya kawar da kansa gefe ya 'bata rai abunsa, cikin Sanyin jiki naqara cewa "Baffana barka da asuba" afusace Baffa yace " ke don Allah ki tashi wlh banson ganinki a gabana ji nakeyi kamar na shaqeki ki mutu" cikin jin dad'i Gwaggo tace "  Au kaima Mallam  kafara gano baqaqen halayenta kenan? Shi yasa ai nace talla shi yafi da cewa da'ita domin babu namijin da zai kwashi wanan makirar saide tatazama ahaka tana samo mana kud'i"  bud'e baki Mallam yayi zaiyi magana amma Gwaggo na kallonsa ya kasa dan haka kawai sai yaja bakinsa yayi shiru. Itako 'YAR AMANA cewa tayi Gwaggo ina tuwona". "Ai baki da tuwo a gidan nan yarinya har sai kine momin kud'i tukunna". "Amma Gwaggo yanzu wa zan samu akasuwa bafa kowa?"

"Yo ni ina ruwana dawa zaki samu kawai de kije koma inane ki siyar nide kawai ki kawomin kud'i shine fatana"

Haka 'YAR AMANA ta kinkimi kwaryar furar ta d'aura akan ta, tayi gaba tana kukan baqin ciki, Gwaggo kuwa sai mita takeyi wai idan tamata asara  sai ta biyata.


Itako 'YAR AMANA tafiya kawai takeyi tana kuka domin kuwa taga Gwaggo so take taimata illa arayuwar ta domin ta hanata yin aure, tinda gashi qawayenta yanzu duk anyi auren su,  wasu ma tun suna da shekaru 12 sukayi aure amma ita Gwaggo ta hana kowa ma yazo gunta sbd da mugunta tamaida ta bazawara, kuka sosai 'YAR AMANA keyi domin kuwa Akwai wani Iro d'an gidan mai gari da takeso dan kuwa shine d'an gaye agarin dan abirni yayi karatunsa shi yasa ya wancin 'yan matan garin ke sonsa, amma shi yafison 'YAR AMANA sbd duk tafisu nutsuwa da kuma kyau, ita kuwa Gwaggo baqin ciki takeyi wa 'YAR AMANA dan bata son gidan da 'YAR AMANA zata shiga  tahuta har wataran tace batasantaba wanan dalilin yasa Gwaggo tafara d'auramata tallar nono, domin tarasa mijinma gaba d'aya,   shima Iro duk sonda yakeyiwa 'YAR AMANA  tunda yafara ganinta da tallan nono yadena kulata domin azatonsa wani ya lalatata tafita asahun 'yan mata shi yasa tafara tallar nono, itako 'YAR AMANA koda Iro yadena kulata sosai tashiga tashin hankali, har Baffanta ya gano hakan amma yamata wa'azi akan tabar komai a hanun Allah, dan kuwa lokacin Baffa bai gano Gwaggo na d'aurawa 'YAR AMANA tallar furaba, hakade 'YAR AMANA tanufi kasuwa tana kuka tana tunanin Iro tsohon saurayinta domin itakam tana sonshi sbd iya gayunsa amma gashi Gwaggo ta rabasu, haka ta isa kasuwar ba wasu mutane da yawa har akacika tafara cinikin nonon ga yunwa ta adebeta dole acikin cinikin ta zare kud'i tasayi k'osai taci, sanan taci gaba da tallar ta tun safe nonon baiqareba har yamma qarshede sai da tabi su Iya wata ruga sanan nonon yaqare domin arigar ranarce kasuwarsu,  dan haka  'YAR AMANA bata dawo gida ba sai dare dan kuwa a qafa tadawo domin tana tsoron tabiya kud'in mota acikin kud'in Gwaggo, koda ta iso gida lokacin Baffa har yadawo yayi Sallah yaci abinci yana zaune aqofar gida yana ganin 'YAR AMANA tashige amma ya kasa yimata magana saide abun ya dameshi, acikin gida kuwa tana shiga Gwaggo tarufeta da fada wai kud'inta baigama cika ba bayan tagama irgesu, nanfa 'YAR AMANA tasanar da ita da k'osai kawai tasiya na naira hamsin taci tunsafe aikuwa Gwaggo tarufeta da dukka kamar anaikota, qarshede kwana wahala 'YAR AMANA tayi awanan daren ga Baffa yana son yiwa Gwaggo magana amma yakasa sanan inyaga 'YAR AMANAr ma ransa 'baci yakeyi, tundaga wanan rana kullum 'YAR AMANA idan tafita tallar nono bata dawowa sai dare, sbd inta dawo da sauran nono na gadon asibitima sai yafita jin dad'i, dan haka dolenta sai yaqare take dawowa aitini zance ya yad'u arigar akan wai 'YAR AMANA karuwanci takeyi dan haka kowa yagujeta ya dena kulata ko Iro ma tini ya auri wata qawarta Jimmala, dan haka yanzu 'YAR AMANA tazama na bata dakowa mai qaunarta arugar tinda hatta Baffantama yanzu gudunta yakeyi........



Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere





*ASSATAGAFIRULLAH*🤲

No comments