ZAN FASA KWAI 23
*ZAN FASA KWAI*
*Page 23*
.......Cikin ikon Ubangiji ta iso garin Abuja sai dai zaman mota ya jigatata don haka da kyar da gano gidan Kabir inda take ta shessheka numfashi na neman daukewa tamkar me ciwon asma Fulani ta tarbota don wani ikon Allah jinin su ya hadu Ta rungumota tana fadin "Ya Kaka Baki da lafiya ne? Da kyar dungo take magana "Bani da lafiya Aisha ina mutanen gidan ne? Izzatu ta fito ta aunowa fulani harara don Bata so take shiga sabgar tsohuwar "Tashi ki bace min da gani kilbabbiya, ta fada tana hararen humairar Ta tashi ta nufi dakin ta tana tausayin kakarta Izzatu ta dubeta tana dafe da gefen cikinta alamar ciwo yake Mata "Baki da lafiya ne dungo?
"Wallahi kuwa izzatu jiki yaki Dadi Allah yasa Kabir Yana gari ? Yana Nan sai dai inma kudi Kika zo nema bashi dasu don kwanan Nan lamarin sai godiyar Allah
"To Allah ya rufa asiri dama cikon kudine so yayi min don Zan siyar da Yan awakina in nemi magani ........
"Ai da kin bugo waya ba ki wahalar da kanki ba yanzu irin haka ke Dadi kinzo kin Bata kudinki Kuma ba lallai ki samu kudin ba
Sai izzatu ta SHIGA sababi tana fada Wai ba a haka sanar da mutum ake in za a zo wurin shi ba Wai azo ayi mishi tashi na kamaka ba in turawa ne in baka sanar dasu zuwanka ba ko ruwa ba zasu baka ba
Haka Kabir ya dawo ya samu tsohuwar shi cikin halin ciwo Kuma ko ruwa ba a Bata ba bare abinci. Kafin ma ta sanar dashi matsalar ta izzatu ta rigata inda ta Dora da Wai Babu kudi yanzu
Shima sai yabi bayan matar tashi akan dai Babu kudin don ya Gane izzatu batayi na am da bayar da kudin ba
Dungo tayi murmushi "Babu komai Kabir ko aro ne anemo min ciwona Yana bukatar gaggawa.......
"Gaggawa Kuma ? Yo dungo ko mutuwa ta shiga gidan da Babu ai dolenta ta fita
Kabir ya dubi izzatu Yana mikewa inda ya nufi daki ta bishi
"Gaskiya baba Bata da lafiya izzatu Bata taba tambayar kudi wurina ba So Zan Bata duk abinda take bukata........
"To kudin da zaka bani na bikin Barth day din fulani fa ? Shiyasa kaji tun farko na ce baka da kudi ka Bata kudin mota kawai ta koma gida zuwa wata me kamawa idan sun samu sai abata don hidimar zatayi maka yawa
Haka kuwa akayi ya dawo ya sanar da ita ya buga waya ko rancen ya samu Amma abin ya gagara da haka ya aje Mata dubu biyar yayi Mata fatan samun lafiya
Ta Dade zaune tana Kore sauro inda kuma har yanzu ba a Bata ruwa ba bare abinci
Fulani ta fito ta dauko Mata robar madarar laban da abinci Wanda ta zubo Mata naman kaji zuku zuku ta dire gabanta
"Ya Kaka Baki Jin yunwa kikayi shiru Baki Sha ko ruwa ba?
Ta karbi madarar ta soma Sha kafin ta soma cin Naman inda wani ikon Allah sai taji kamar ana rage Mata ciwon Ni Kam gidan iko nace ko ciwo Yana son abinci me kyau
Adakin humaira ta kwana cikin gidan sauro inda dungo ke ta saka Mata albarka washe gari ta hado kayan ta fulani ta kawo ta Tasha inda izzatu ke taksicin wannan kawa zuci na fulani ga jemammiyar tsohuwar
Ai kuwa da ta dawo daga Kai dungo Tasha sai da taja kunnen ta kamar ta cire shi tana fadin Wai Babu ruwanta da tsohuwar
"Haba momy kakata ce Kuma ace Babu ruwana da ita? ......
Ta gwabje Mata Baki
"Baki hada komai da ita ba hanya ko ta rafi nono ko na gora meye hadan kifi da kaska?
Fulani ta shige daki tana gunin Jan kunnen ta da akayi inda Kuma sister mero ta shigo gidan da sallamar ta me kwari.
Arude izzatu ke kallon ta
"Me ya kawoki gidan Nan mero? Me kikazo yi ?
"Haba irin wannan tambayoyi tamkar na SHIGA kabari ko Dan ruwa ba za a bani ba ? Bakonka Annabin ka fa......
"Baki cikin layin bakon ka Annabin ka donke kallon tauraruwa me wutsiya nake Miki don haka Fadi abinda ya kawo ki kiyi ki bar min gidana..........
"Kai hajjaju makkatul mukarramina wannan dogon sharhin tamkar Baki San daga ina nafito ba?
To dama matsalar kudi ce ta kamanni shine na tuna dake don haka milyon biyu kurum nake so ba yawa.......
"Agidan ubanwa za a samo milyon biyun? Wace irin jaka ce ke ne? Kina bina bashi ne Zaki wanko tsantsaman jikinki kice na Baki kudi?
"Karki Kuma zagin ubana izzatu arziki ya hadamu ba tsiya ba ke komai sai an biyo Miki ta bayan gida ake daidaita wa dake? Meye don nace ki bani milyon biyu Ina ce farin cikin da na Samar Miki ya zarta milyon dari? To bani in wuce don bana son ta kaimu ga cacar Baki in kuwa ba haka ba wallahi yanzu ne Zan fasa kwai .........
"Allah ya tsine Miki idan Baki fasa dangin kaji da tsuntsaye ba. Bari in gaya Miki mero na fiki tashanci da iya lalata ban San haka kike ba wallahi da ban yarda na hada hanya dake ba Amma ki sani duk Ranar da Kika kaini karshe na rantse Miki da Allah sai dai ki tsinci kanki kushewa Zan Baki milyon biyu Amma ki kaddara daga kanta ko a mafarki kar ki yarda kice kin sanni don sani na zai zo Miki da matsala..........
"To naji hajiya izzatu dauko min in wuce don sauri nake.
Izztu ta rubuto mata cek ta Bata ta karba tana godiya inda izzatu ke Mata kashedi da idonta
Sister mero ta Mike tana fadin Wai sai gani na biyu.......
"To a gani na biyun ki tabbatar kin taho da likkafanin ki don Zaki zo inda Zaki gama yawo. Mero ta kyalkyale da dariya ta fice daga gidan inda izzatu tayi shiru tana tunanin mero da irin salon da take nufin kawo Mata
Itama sai tayi murmushi"mero kenan muje zuwa Ni dake za agane waye gaba.........
No comments