Breaking News

YAR AMANA 5-6

 *'YAR AMANA*

Page 5&6

______Washe gari kuwa da wuri Asabe qawar Gwaggo tazo gurin Gwaggo, lokacin kuwa Baffa ya tafi kiwo, cikin zabbin Baffa Gwaggo ta kame biyu dan acewarta wai kud'in furarta da ya qona dan ita ba ta san asaraba, tana ta sababi suka fice sukabar gidan tare da zabbin, niko ina ganin Gwaggo tafice kuma nasan ba yanzu za su dawo ba dan haka nai gudu nazari Allona na wuce gidan Mallam d'aukar Karatu, inda Mallam yai tamin fad'a akan me yasa kwana biyu bana zuwa d'aukan karatu? Haquri na bashi tare da masa qaryar bani da lafiya ne, murmushi Mallam yayi sanan yace "   'YAR AMANA kenan ai duk munsan halinda kike ciki a garinan dan har akasuwa aka cemin anganki kina tallar Fura, lalle Gwaggonki bata san AMANA ba, kuma munanan muna shiri akanta tabbas sai takar'bi hukuncinta na maidaki bazawara da tayi agarinan"

Ni kuwa cewa nayi to "Mallam me kalmar bazawara ke nufi ne?" 

"Hmm 'YAR AMANA wato ita kalmar bazawara tana nufine akan macen da ta ta'bayin aure ta rabu da mijinta ko kuma ya mutu, to wanan ita ba matar aure bace bazawara ce" 

"Amma Mallam aini banta'ba yin aure ba amma Gwaggo take kirana da bazawara to idan nata'bayin aure ina mijin aini bansanshiba?"

"Kwantar da hankalinki 'YAR AMANA ke ba bazawara bace ke yarinya ce budurwa, kawai de rashin imanine irin na uwar riqonki shiyasa take kiranki bazawara"

"To amma Mallam..........

"A'a, 'YAR AMANA karki qara tambaya ta komai iyakacin abunda nasani kenan amma inkina da wata tambaya zaki iya yiwa Baffanki domin shi yadace kiwa kinji 'YAR ALBARKA"

Haka de na biya karatuna mai yawa agurin Mallam, har yaimin qari inda Mallam yake ta yabona akan qoqarina, har akatashemu na dawo gida amma Gwaggo bata da woba, gashi bakomai agidan sai ruwa ga uwar yunwa da take addabata, haka na nemi guri na zauna nayi tagumi domin kuwa Gwaggo ta rufe dakinta da d'an mukulli,  gashi Baffa bai dawo wa gida sai yamma lis, wani tunanine yafad'omin dan haka na tashi na nufi d'akin Baffa na, ko zansami wani abun naci, amma me dakin wayam yake ba komai sai kayaiyakin Baffana, sai Naira hamsin na gani akan tebirin Baffa, yi nayi kamar na d'auka amma sai na fasa saboda ina tsoron kar Baffana ya dawo yana nema, haka na nufi akurkin d'akina mai kama da madafi na nemi guri na ra'be domin kuwa jikina har rawa yakeyi saboda yunwa.



Gwaggo ce da qawarta Asabe agaban Mallamin tsubbu, inda Gwaggo tamasa bayani akan so take arufe bakin Baffa da ma kowa akan 'YAR AMANA domin kuwa so takeyi taringa kawo mata kud'i karkowa yai magana kuma tana so kalmar bazawara tabita har abada domin kuwa ba ita bayin aure, sai de ta tabbata ane momata kud'i, kuma asanya mata tsoron duk wani d'a namiji koda kuwa zaice yana sonta to tace ita bazawara ce kuma ba zata sake aureba.

Malamin kuwa ce mata yayi" angama inde wanan  ai qaramin aikine kede kawai ki zuba kud'i kiyi tafiyarki daga gobe zaki fara ganin aiki" haka Gwaggo tana murna ita da Asabe, ta zubawa Mallamin kud'in zabin Baffa da ta kama tasiyar, sanan suka yiwa malamin tsubun godiya suka bar gurin.




*__________________________*


ABUDULJABBAR ne kwance a d'akinsa akan gadonsa yayi ringine yana kallon sama daga shi sai gajeren wando, FINAH ce ta shigo d'akin cikin gayunta tana wani ya tsina, kallo d'aya ABUDULJABBAR ya waigo yai mata ya kawar da kanshi gefe, ita ko FINAH wani Yarr taji ajiknta kawai sai taji tana buqatar mijinata dan haka ta sauqe labulaye ta kashe wutar d'akin  ta qara gudun ac,  sanan ta cire duk wani kayan jikinta ya rage daga ita sai Fant da bra, hawowa kan gadon tayi tafara wasa da gashin dake kwance akan qirjin ABUDULJABBAR, yana jinta yai banza da ita haka taitamasa wasa amma yaqi ko motsawa tsaki tayi mmmttttsss sanan tace "haba dan Allah mutum sai kace dutse" banza ya kuma yi mata, bakinta takai setin nashi zata had'e amma yatureta can gefe, ya mirgina abunsa yaja pillow yarungume yai ruf da ciki, kukan shagwa'ba FINAH tasa tace " haba dan Allah honey saboda kaga ina sonka shi yasa akullum burinka ka wulaqantani, kwata-kwata baka damu da haqqina ba da ke kanka baka ma tsoron Allah ya kamaka da kaqqina akan ka"

Afusace ABUDULJABBAR ya juyo yace "wani Haqqinki ne akaina Nafisa? Baccin baki damu dani ba bakisan ki kwantarmin da hankaliba, ba ruwanki da ina cikin damuwa ko bana ciki kede kullum kina liqe da Mum, ita Mum d'in haka kika ga tana yiwa Daddy? Ki duba mana kigani Nafisa ai ko kuna tare da MUM inde taga Daddy ya shigo barin komai takeyi ta bishi itama tsohuwa kenan balle ke mai jini ajika, saboda kinrainani bakisan mutunci na ba Nafisa inma ina da buqatarki ba yarda kike yiba sai kinga dama, saide intaki ta ciyoki shine zaki zomin to kisani ni ba dabba bane mutum ne kamar kowa, dan haka ki kiyayeni kisan abunda kikeyi Nafisa"


"Amma Honey ai kasande ni agidan mu bansan wahala ba, kuma da kake cewa Mum tana kula da daddy maybe dama ta saba da wahala ne tun abaya amma ni ba 'Yar wahala bace kuma karka qara cemin Nafisa banson wanan sunan qauyen kakirani da FINAH ko ka sakemin suna"


"Oho sai yanzu ai nagane wato a gidanku ba akula da hakkin miji shi yasa kema baki iyaba ko to wlh bara kiji aure zanqara domin kuwa ina da 'yan mata da yawa da suke sona" wani ihu FINAH tayi tace " wlh baka isaba qaryane ni FINAH nafi qarfin kishiya har abada, dolene ka zauna dani ABUDULJABBAR ni d'aya har qarshen rayuwarka, kuma karka sake kaqara zagin gidanmu na gaya maka"

"Au wato abun ba dad'i ni kuma kike nema ki zagi gidanmu kuma qarin aure ba fashi muddin Ba ki gyara halinkiba". Tashi yayi ya shige bayi yarufo qofa ya sakarwa kansa ruwa.

Ita ko FINAH dolenta ta mayar da kayanta tabar d'akin tana cika tana batsewa.




*Hhmm Wanene ABUDULJABBAR kuma wacece FINAH?*



Alhaji Ashiru shine  asalin mahaifin ABUDULJABBAR Alhaji Ashiru ya kasance d'an kasuwane mai rufin asiri iya gwargado, acikin garin Kaduna amma shi bafulatanine neman kud'i yasa ya fito daga rugarsu ya sauqa acikin garin Kaduna, ya fara kasuwancinsa a kasuwar tredefire dake kaduna inda yake kasuwancin dan kunaye tare da wani mai gidansa inyamuri wato igbo, kuma mai gidanasa yana da Amana har Ya yaye Ashiru yabud'e mar wani shagon wanan shine asalin arziqin Ashiru inda shagonsa yai ta ha'baka harma ya bud'e wasu shagunan nasa na qashin kansa shima ya zuba yaransa, 

Har ya had'u  da wata  yarinya mai suna murjanatu inda suka fara soyayya gadan-gadan domin kuwa murjanatu Akwai son abun duniya, gashi kuma taga Ashiru yana da rufin Asiri ba laifi dan haka ta yarjemar ya isa da iyayenta dama su biyu ne agidansu ita da qanwarta Karima tini Karima tasamu miji kawai Murjanatu iyeyen suke jira su had'a aurensu da ita amma ita ta tsaya ruwan ido, dan haka tana kawo Ashiru ba 'bata lokaci yaje rugarsu ya turo manyansa akai maganar aure, hatta Sadaki dukka iyayen Murjanatu Sunkar'ba, sati biyu akasa ranar bikinsu ai kuwa lokaci nayi akasha bikin Ashiru da Murjanatu,  Karima da Halilu, inda ko wacce aka kaita gidan ta saide Karima tana da kishiya domin mijinta yana da uwar gidansa kuma mutumne mai kudin gaske,  Murjanatu kuwa can tatare da Angonta Ashiru Inda sukai ta'barzar soyayya, bayan shekaru biyu da aurensu ta haifi yaronta ABUDULJABBAR, alokacin arziqin mijinta ya ha'baka inda tafara huld'a da matan manya, dan murja akwai sonyin qarya, inda qanwarta Karima kuwa tana can tana tashan wahalar kishiya dan Karima sam bata da hayaniya shi yasa Alhaji Halilu, yake matuqar sonta, amma uwar gidansa Nuratu, duk ta addabesu kuma bata ta'ba haihuwa ba, gashi itama Kariman yau shekaru biyu da aurensu amma shiru kakeji dan haka yafara tunanin rashin haihuwar daga jikinsa yake, dan haka suka fad'a neman magani, amma likitoci sunsanar mar da zai haihu saide akwai sauran lokaci kuma kwan haihuwarsa bai da yawa.


Haka de rayuwa taci gaba da tafiya har tsawon shekaru  Ashirin, alokacin kuwa tini Alhaji Halilu ya fitar da rai ga haihuwa itama uwar gidan sa haka, itade Karima tana ta addu'a,  saide ta d'au son ABUDULJABBAR ta d'orawa ranta dan tanaji tamkar ita ta haifeshi shi yasa rabin zaman ABUDULJABBAR ma a gidanta yake, inda yanzu ya zama saurayi dan shekaru Ashirin a duniya yaro mai tarbiya da shiga rabkowa domin innarsa Karima sosai ta tarbiyartar dashi ga kuma uwa uba ilimi, inda yake karatunsa akan harkar bin kice har akaturashi qasar America, qaro ilimi Innarsa Karima ita ta tsaya masa akan komai har yabar qasar. 

Bayan tafiyarsa ne Alhaji Halilu ya d'auki Matarsa Karima suka wuce kasar Ijib domin kuwa tace mar tana mafarkin ta haifi jariri amma ana binta za akasheta da ita da jaririn, dan haka Alhaji Halilu yaqara kwad'airuwa da haihuwa dan haka ya d'auki matarsa  Karima suka wuce Ijib dan asake bincika lafiyarsu............



To Karima Allah yaba da Sa'a akan abunda akaje nema

No comments