Breaking News

YAR AMANA 3-4

 👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰👩‍🦰

       *'YAR AMANA

Page  3&4

Wata Mota ce qatuwar gaske fara tas mai shegen kyawun tsiya akan titi cikin garin kaduna, tana falla uban gudu, tamkar zata tashi sama, inda kai tsaye wanan motar tanufi titin dake kan layin (Ahmadu bello way) karya kwana motar tayi ta shiga cikin layin (Ahmadu Bello way) inda ta nufi wani qaton get mai kyau da tsaruwa, aka danna uban hon  d'iiiiitttttt,  a guje security d'in dake gadin qofar ya hangame qaton get d'in, Ya Sallam, domin wanan kyakyawan gini da tamkar ba hannu yayi saba, ya baiyana wanda kai tsaye za'a iya qiran gidan da Aljannar duniya, a guje maruqin wanan qatuwar motar ya fad'a cikin gidan mai kama da wata babbar ma'aikata sbd yawan security's din dake cikin gidan da kuma

tsaruwar gidan, kai tsaye parking space, na gidan Motar ta nufa, inda tayi parking, matuqin motar ne ya fito a guje,  ya bud'e kofar bayan motar wajen mai zaman banza kenan, sanan ya koma ya tsaya a gefe, sai da mintoci kamar uku suka shud'e  Sanan aka sako qafa waje alamun za afito, takalmine shoe sau ciki fari tas aqafar wanan bawan Allah d'in haka ma Wondon jikinsa Farine tas ko d'ison dot na datti babu safar dake cikin takalmine kawai ruwan roka, bayan ya saqalo qafar sane ya qarasa fitowa amotar nikam Mummyn Minal ina ganinsa nace (Tabbbara kallahu Ahsanul kaliqin)


Donin kuwa guy d'in kyakyawan gaskene Fari tas kana kalonsa kaga hausa fulani dukka jikinsa fararen kayana na yunufon d'in 'yan binkicen qasa wanda ma ba sufiye sa yunufon d'in saide in za suyi babban aikine, sude kawai suna binkicen sune a asirce akan duk wasu masu hannu da shuni na qasar nan wato (SS) hatta jakar sa dake hanunsa fara ce tas, Security's biyu ne suka nufo shi suna Saramar d'ayar ya kar'bi jakar aikin sa ya nufi cikin gidan da ita, bin bayan Security d'in nashi yayi cikin takunsa na mazan taka wanda ko da daga jika ta kunsane lalle kasan mazan qwaraine, shi kuma d'ayan security d'in ya take mar baya, kai tsaye Babban qofar Parlour d'in gidan suka nufa inda security d'in dake gabansu ya matsa qararawar qira, ba a d'au dogon lokaci ba, qofar tabud'u Security d'in ya shige  parlour d'in ya ajiye jakar kan Centre table, ya fice, qarasa shigowa cikin babban parlour d'in dake cike da kayan alatu yayi,  wata babbar mace ce Fara tas  a parlour d'in tana hakimce kan kujera 2star, sai wata kyakyawar matashiya da ta kwantar da kanta akan cinyar matar ita kuma matar tana ware mata kitson kalaba dake kanta, gefe d'aya kuma yarinya ce 'yar budurwa da baza ta wuce 13 years ba hanunta riqe da remote tana kallo, Sallama ya musu cikin kaukausar murya wanda da kajin Sallamar tasa za kasan ransa a'bace yake,  da murna 'yar yarinyar ta amsamar Sallamarsa ta tashi ta nufeshi zata rungumeshi cikin murna, shiko da katar da ita yayi yace " haba IKIRAM baki san kin fara girma bane"?   


ja baya tayi tace " haba Ya *ABUDULJABBAR*  wani girma nayi dukkafa yanzu na shiga shekaru 13 yau Yaya na yaushema zaka had'amin birthday party na na cikata 13 years?".  "A'a IKIRAM baza kiyi birthday ba domin kuwa malamai suna ta wa'azi akan birthday d'inan da akeyi ba kyau ta'adar yahudawa ne, kuma kinga manzon Allah( S.A.W) cewa yayi mu bijirewa yahudu da nasara bawai muyi koyi dasu ba, dan haka kimai da hankalinki akaratunki kawai komai kike so zamanki kinji qanwata"  "to Yaya na ta amsa, shi kuma ya nufi gurin kujerar da farar matar nan ke zaune, ita da wanan matashiyar inda sun zuba musu ido suna kallonsa shi da IKIRAM, duqawa yayi akusa da qafarta yace "Mum Sannu da gida nasameku lafiya"?  Murmushi tayi tasanan ta shafa kansa tace "lafiya lau yarona ya aikin naka"? "Aiki da godiya Mum amma wlh mum mutane ba sajin tsoron Allah kwata-kwata yau raina a'bace yake sbd wani d'an iskan attajiri aqasarnan da muka dad'e muna binkice akan sa domin kuwa dukiyar sa tayi yawan adadin da baza ata'ba qiyas tataba, shima kansa baisan iya adadintaba kuma abun ta kaicin anan Mum shine wanan dukiya duk hakkin talakawan qasane suka hamdame shi da magoya bayan sa A Abuja, yanzu haka yana hanunmu bayan artabu da mukasha gurin cafkeshi dan kuwa ya gano munsa ido akan sa shine ya had'a mana gadar zare amma Allah ya tsalakar damu da yaukam saide aka womiki gawata" 


"Subbahanallahi yanzu de ince kana cikin qoshin lafiya ko yarona"? "Eh lafiya ta lau Mum tinda munyi nasarar kamashi kawai de abokanan arqalarsa ya rage mu danqo suma kuma zamu damqosu nan ba dadad'ewa ba" "Shikenan *ABUDULJABBAR*  Allah ya kiye yemin kai aduk inda kake" "Amin Mum" ya amsa.


Kallon matashiyar dake kwance akan cinyar Mum d'in tasa yayi yace " ke *NAFISA*  ki tashi ki kawomin ruwa, Sanan ya tashi yai hayewarsa sama ya nufi dakin baccinsu, ita ko wacce aka kira da  Nafisa tashi tayi tana zun'bura baki tace "gaskiya Mum kifad'awa wanan guy d'in shi mudin yana gida bai da aiki sai sa mutum aiki ni kuma ai ko ke kinsani ni ba 'yar wahala bace ba". Mum kuwa cewa tayi nasani FINAH,   ABUDULJABBAR ne ba yajin magana amma karki damu zan sake yimasa magana ya dena saki aiki ko kuma asamomasa 'yar aiki kowa ma ya huta"


"A'a Mum ni bana son masu aiki mata dan qwacewa mutum miji sukeyi sai kiga suna kalle maka miji kamar mayyu kawai de ki masa magana yadena ta kuramin duk  abunda ya keso yasa Security's d'insa suma sa dan ni bansaba wahala ba"

"Shikenan FINAH ki kwantar da hankalinki zanja masa kunne" to Shikenan Mum" FINAH tace, sanan tanufi kitchen tana qunquni.




_________________________



Shiko ABUDULJABBAR ko da yanufi d'akin baccinsa kai tsaye kayansa ya cire ya jefasu cikin dosbin ya rage daga shi sai bocxer, Bath room ya nufa ya sakarwa kansa shower ruwa yai ta kwarara sosai akansa zuciyarsa nayi masa zafi shin shikam da wanne zaiji ne da magautansa dake son d'aukar rayuwarsa kokuwa da qadarariyar matarsa da aka liqamasa dole kuma kwata-kwata batasan komai na kwantarwa miji hankaliba wai ita nan 'yar hutu,  gashi kuma Mum ba tason Laifinta ko kad'an shi ganima yakeyi Mum tafi son NAFISA da shi,  da wanan tinanin ya fito daga bayin ya zube akan qaton gadonsa yayi rigingine yana kallon Sama, tabbas yana son kalaman da za su kwantarmar da hankali dan yasamu ya shiga nutsuwa amma  gashi har yanzu NAFISA bata shigo d'akinba, wata zuciyar tace "to ma ko tashigo me zata maka inbanda ta qara maka damuwa" tsaki yayi yaja pillow yarungume atake bacci ya d'aukeshi batare da yasha ruwan ba.



Ni ko nace wacce irin mata ce wanan ABUDULJABBAR ka had'u da ita?



Bari muleqa rugar su 'YAR AMANA kafin ABUDULJABBAR ya tashi abaccin.





A'bangaren 'YAR AMANA kuwa tinda Gwaggo ta jefata cikin d'aki tin yamma har washe gari bata bud'eta ba haka 'YAR AMANA tayi kuka hartagaji ta kasa ga uwar yunwa da take qwaqwilarta har tayi baccin wuya ta farka amma Gwaggo taqi bud'eta har rana tafito, koda Mallam zai wuce kiwo da safe da ya tambayi Gwaggo ina 'YAR AMANA sai cewa tayi  tana can tana bacci, dan haka hankalinsa ya kwanta ya fita kiwonsa,  'YAR AMANA kuwa nacan cikin d'akinta ta had'a kai da gwiwa tana tinanin rayuwa ga uwar yunwa da qi shin ruwa dake adabarta,   ita ko Gwaggo tana tsakar gida tana aikace -aikacenta tama manta da wata halitta a gidan,  Sallama akayi a tsakar gidan, da sauri Gwaggo ta d'ago kai tace " Lalelale da zuwar aminiyar kwarai" rungume juna sukayi   suna dariya  tabirma Gwaggo ta d'auko ta shinfid'a musu afilin gidan suka zauna, suka fara hirar yaushe gamo inda Qawar Gwaggo mai suna Asabe take sanar da Gwaggo yanzu aiki takeyi abirni gidan wani Alhaji mai kud'i, Gwaggo tayi shewa tace " shiyasa naganki kina ta kyalli ina ma mana nima wanan tsohon ya mutu ai binki zanyi wlh mutafi nima kisamar min abunyi"

"Shewa Asabe tayi tace " haba Aminiya ina 'yartaki da take kawo miki kud'in tallar fura?"

"Hmm kede bari Asabe nan Gwaggo ta kwashe komai da yafaru jiya ta sanarwa Asabe, Asabe tace " hmm lalle ma mutuminan inyasan wata ai baisan wata ba, yanzu wa zai zauna namiji yana juyashi ai kawai maganinsa zakiyi malama ya koma matar ke kuma kizama mijin ita kuma 'YAR AMANA tasa taze memiki mai kawo miki kud'i, inma karuwa zata zama tazama ,  ba bazawara ba" dariya Gwaggo tayi  tace " to yanzu aminiya ta yaya hakan zaifaru? Kede kisha kuruminki akwai wani Malamina acan gefen rugarnan hatta 'yan birnima suna zuwa gunsa  saboda kyawun aikin sa, dan haka ki shirya zankaiki can gunsa sai yanda kika gidanan, saboda haka kima fito da wanan bazawarar kifita sabgarta haka nan zata dauwama tana  kawo miki kud'i,   kede ki shirya gobe muje

Haka  de suka gama hirar munafurcinsu Asabe tatafi sanan Gwaggo tabud'e 'YAR AMANA tafito tabata guntun d'imamen tuwo taci,  sanan   'YAR AMANA tatashi tayi Salolinta Gwaggo kuwa sai kalonta takeyi tana jin haushinta tamkar ta shaqeta ta mutu kowa ma ya huta, 'YAR AMANA kuwa tana idar da Sallar ta tazari silifas d'inta da yasha faci da tsimma zata fita, wata uwar tsawa Gwaggo ta da kamata tace "ke Marar asali ina zakije haka"? Cikin tsoro 'YAR AMANA tace "zanje d'aukan karatune gidan Mallam nayi kwana biyu banjeba shiyasa" 

"Sannu isheshiya akuyar d'aure ta samu sake, ai ke da karatu arayuwar ki kunyi bankwana yarinya,  sai de ki qare akawomin kud'i dan naji dad'in rayuwata" cikin kuka 'YAR AMANA tace "dan Allah Gwaggo kibarni inyi karatuna wlh ina son karatu kuma ma Baffa yace har da makarantar boko zai sani dan Allah Gwaggo kimin rai kubarni nayi karatu"

"Hhhhhhhhhhh Gwaggo tayi wata dariyar qeta sanan tace "ai 'ya'yan asali suke karatu ba irinkuba tsintatun mage amuku inuwa kuyiwa mutum Rana, dan haka keda karatu saide kiga wasu nayi" itakam 'YAR AMANA gefe ta koma ta raku'be tana tunani wai meyasa Gwaggo take mata haka ne shin ita kam miye laifinta ne dan kawai Baffa tsintota yayi shi yasa Gwaggo taimata wanan tsanar wai ya zata yine dan tasamu tayi karatu kamar yanda Baffanta yakeso? Amma de bari tabari Baffan yadawo taji me zece akan karatunta haka 'YAR AMANA tai ta saqe-saqe azuciyarta har barci 'barawo ya saceta agurin.......



Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere




*ASSATAGAFIRULLAH*🤲

No comments