TSANGAYAR MALAM 13-14
_*👳♂️👳♂️👳♂️TSANGAYAR👳♂️👳♂️👳♂️*_
_(Malam)_
*Na*
_Maman Dr_
1️⃣3️⃣-1️⃣4️⃣
Tafiya ɗan malam suke kamar ba zasu je ba ga wahalar yanayin hanya da matsin mota ga zama duk jamma'a sun jigata dan da yawan jama'ar motar sai da suka tausayawa ɗan malam ga shi a ɗaure ga matsi sunyi sunyi malam Ƙasimu cinnaka ya kwance shi ya ƙi da yaga zasu ishe shi ya ce""
""Taɓ ai idan na kwance wannan yaron wallahi kowa sai ya gane shayi ruwa ne a ckin motar nan dan ba ƙaramin ta ƙadirin yaro ba ne ba abun mamaki bane yayi yanda zai kifar da mu gaba ɗaya daga motar mu kife kuma baya ragawa babba da yaro,habawa jamma'ah aka ɗauka da wasu daga ciki suka ce abar shi yayi ta zaman sa a haka dama mutum mugu ne koya mutu sai an ɗaure shi to ashe su da bama bamai suke tafe basu sani ba gwamma da Allah yasa kowa yaji kar wani ya zagaya inda aka yadda zango yin sallah ko cin abinci ya kwance shi su shiga tara,ɗan tausayin da jamma'a suke na ɗan malam,malam ƙasimu cinnaka ya ɓata shi a gunsu kowa ya cigaba da safgar gaban sa.
Sai kusan sha biyu na dare motar ta dira a MARAƊI,inda fasunjoji suka sauka anan inda motoci suke malam ƙasimu cinnaka ya samu wata ƴar ƙurƙura sukayi ciniki da mai ƙurƙurar ya biya suka tafi nan ma suka ɗauki hanyar ƙauyen *ZABAR*,ƙauyen zabar a chan arewa yake da maraɗi tafiyar sa'a uku ce daga maraɗi zata kai ka *ZABAR* ba ƙaramin jigatuwa sukayi ba a dai dai tsangayar ƙurƙurar ta tsaya malam ƙasimu cinnaka ya sauka yasa direban ya taimaka masa suka sauke ɗan malam yaja ƙurƙurar sa ya fece cikin daran,ko da dare ne tsangayar ba ƴar ƙara ma bace ƙattuwa ce sosai cikin sahara sai wasu bukoki da sun kusa ɗari idan basu haura ba a jere da tarin alina kusan fin dubu a a ɓari ɗaya haka malam ƙasimu cinnaka ya tasa ɗan malam a gaba suka fara ƙetar bukokin nan suna tafe suna sarƙe ƙafa da sahara har suka iso bakin wani buka da yafi sauran bukokin girma da faɗi da layu birjik a jikin bukar a saƙale suka tura kansu ciki,abun mamakin wani dattijon mutum ne dan ba za'a kirashi da tsoho ba da ƙwarin sa zaune akan wani buzun gashi shi ba a ƙasa ba,ba kuma a sama ba a zaune akan buzun gashin sai jan wani ƙaton charbi yake da yawansa ya kai dubi biyar da ɗoriya gashi fuskar sa cike take da gimu har ƙasan ƙafarsa daya zauna ya tanƙoshe su,mutumin ya dubi ɗan malam sau ɗaya ya kauda kansa ga malam ƙasimu suka sauya baki chan mutumin yayi gyaran murya ƙarti uku suka fito suka kinkimi ɗan malam suka fita da shi bai san inda aka nufa da shi fa sai daya farka yanzu ya miƙe da sauri yana zare zaren ido.
Ƙoƙarin tashi ya ke jin ƙara a ƙafarsa ya kai idon sa wajan da sauri yana kallo,mari ne a sangalalon ƙafar duka biyun wani hawaye me ɗaci ya ziraro masa kunncin sa idon sa lokaci ɗaya ya chanja ya rikiɗe ya koma jajir ga uban yunwar data addabe shi malam ne ya faɗo masa arai da inna uwaila sai kuka ya ƙwace masa ya kifa kan gwiwarsa yana shassheƙa da gunjin kukan maza wani guntun gaddi ya faɗo bukkar riƙe da wani farantin silba da wani irin abinci da shi ba dambu ba,ba kuma bura busko ba.....
_*Kuyi haƙuri da wannan ban da chaji ƙaunar ku ga TSANGAYAR MALAM,yasa ni dole sai da nayi muku fan's ina yinku🥰*_
_*A nan zan gimtse inda Comments/Share*_
No comments