Breaking News

YAR AMANA 1-2

      *YAR AMANA*

*YA ALLAH KABANI IKON RUBUTA ABUNDA ZA'AK'ARU DA SHI A CIKIN WANAN LABARI NAWA MAI TAKEN .......*✍️  

Page 1&2

"Ke bazaki fito ki tafi tallar furarba sai kin makara kindawo min da saura kinsannide ba mutunci bane dani akan kud'i mudin ki ka dawomin da sauran fura sai na gadon asibiti yafiki jin dad'i" Daga cikin wani d'akin jar qasa dako fulista babu ballanta fenti wata kyakyawar yarinya tafito doguwa fara tas jelar gashinta kuwa har gadon bayan ta wanda sai reto takeyi, du-dudu yarinyar baza ta wuce shekaru 13 ba, jikinta sanye yake da kayan fulani na faritas na asalin wato na saqi wanda yaji ado da koren zare da kuma ja, cikin sanyin jiki taje taduqa agaban matar dake ta mata mita akan tafito, wanda matar tana zauna ne akan kujera 'yar tsuguno gaban ta da qwaryar Nono, cikin Sanyin murya yarinyar tace " gani Gwaggo"

Zungure mata kai tayi sanan tace " munufuka kawai maza ki d'au furar nan kije kisaidata yanzunan ki kawomin kud'ina Caras, saura ki bari wanan munafukin ubanaki ya ganki kuma ban yarda kiyimin 'batan ko sisi ba"


Idona taf hawaye na d'auki qwararyar Nonon wacce ke cike da kindirmo ga qaramar qwarya asamanta ta fura, haka na d'aga daqar na aza bisa kaina, qwaryar na rinjayata mai makon Gwaggo ta taimakamin, A'a baruwanta saima ta matsa gefe tana cewa " nide bansan asara ba mudin ki ka zubarmin da dukiya ta sai kinbiyani domin kuwa ni bana d'aukar asara"


Haka de na fita agidan ina tafiya ina tangad'i ina kuka sbd tausayin kaina domin bani da wani galihu, kai tsaye babbar kasuwar rugarmu na nufa duk da yau ba ranar kasuwa bace amma baza arasa masu siya ba.


Haka ta Shiga cikin kasuwar tana ta yawo amma ba wani ciniki sbd yau de ba ranar kasuwa bace ba mutane da yawa, haka taita yawo arana ga yunwa ga qishin ruwa gashi ko zata mutu ba ta isa ta ta'ba kud'in Gwaggo ba domin kuwa tasan sauran.


Da qar de ta samu ta sayar da rabin nonon da furar dan haka tatafi wata rumfa inda filanawa suke zama in sunzo tallar nono akasuwar, cikin ayarin wasu mata dake cikin fumfar tsafaffi da matasan matan aure ta musu sallama ta nemi guri ta zauna akusa da wata  mata mai d'an yawan shekaru, matar kuwa qare mata kallo tayi sanan tace " ke ko wanan yarinya mai yakaiki tallar fura da wanan qarancin shekarunaki? Alhalin kowa yasani kaf rugarnan da ma kewayenta da sauran rugagenmu yarinya budurwa bata tallar nono har sai de matar aure,  ke kuma ga dukkan alamu ma budurwace bakiyi aure ba, shin awanan rugar kike ko awata ruga?"


"Ih awanan rugar nake kuma sunana 'YAR AMANA"   "to kina da miji ne"?

"A'a bani da miji domin Gwaggo tace " bazanta'ba yin mijiba"

Shiru matar tayi tana jinjina lamarin

Can tace " ni sunana Iya kuma ba arugarnan nake ba muna de shigowa ne tallar fura, ko zaki bimu rigarmu qila furarki taqare?"

" la rufamin asiri kar Gwaggo takarni"  'YAR AMANA tace.


Iya de itakam 'YAR AMANA tausayi tabata dan aganinta ta yaya budurwa zatayi tallan fura a yankinasu lalle abun da Akwai duba aciki.  Haka de sukayi ta hira har yamma 'YAR AMANA kuwa koda taga yamma tayi dan haka ta d'au  sauran furarta takama hanyar gidan su ko da ta iso gida sai  iske Baffa mahaifinta aqofar gida yana alwalar mangariba, aikuwa ransa ya 'baci sosai bai mata magana ba har tashiga gida jikinta na rawa bayan ta masa sannu ta wuce abunta.


Tana shiga kuwa yabi bayanta ya hankad'e qwaryar furar dake kanta atake komai ya tarwatse ya zube ai da gudu Gwaggo ta fito daga d'aki ganin aika-aikan da Baffa ya mata ya sata saranda, Baffa kuwa nunota yayi da yatsa yace "ke mutumiyar banzace ashe ? dama duk irin abunda ake fad'amin gaskiya ne, wato kimayar da 'YAR AMANA TA bazawara kina d'aura mata tallan fura ko? Bayan kinsan budurwa batayi saide mai aure ko bazawara to wlh duk ranar da kika sake d'aura mata tallan fura sai kinbar gidan nan marar mutunci kawai, kide ji tsoron Allah wlh.

Sanan ya dubi 'YAR AMANA cikin tsawa yace  "  bani kud'in hanunki" hanunta na rawa ta miqa masa kud'in, aikuwa ya zaro icce da yake ci da wuta acikin murhu ya bankawa kud'ad'en wuta qurmus suka qone agurin, Gwaggo kuwa kamar ta mutu dan baqin ciki haka takeji.

Baffa kuwa fuuuu ya fice agidan ya nufi massalaci, aikuwa yana fita Gwaggo ta jawo 'YAR AMANA tana dukanta tana zagi har saida takasa motsi sanan ta jefata akurkin wani d'aki taja ta rufe domin aganinta da gangan 'YAR AMANA tayi dare..



Hhhmm mujede zuwa ke kuke tinanin zai faru ga 'YAR AMANA ne?

Gwaggo de tace bata 'daukar asara ga kuma asara nan Baffa ya mata shin ya zata kaya ne?


To arugar su 'YAR AMANA munji budurwa marar miji bata tallan fura to 'YAR AMANA tana da aure ne ko ya abun yake?


Kude kubiyo Mummyn MINAL d'inku domin samun amsosinku



Dan Allah Dan Annabi kiyi shere asauran groups _groups





*ASSATAGAFIRULLAH*

No comments